Showing 105001 words to 108000 words out of 165545 words
wlhy, kai wannan yarinya akwai bariki anan, idan ta samu shashar kishiya tuni take ƙwace mijin�?.
Wata dariya mai nuna tsangwaron hassada Maman Ama tayi, ta riƙe haɓa tana fadin, “Kaini wannan abu ya ɗauran kai, ciki fa? To wai yaushema akayisa?�?.
Dariya sosai ƙawar tata ta sanya, “Kai kujimin ƙawata da wani batu, mata da miji har kike tambayar yaushe tai ciki?�?.
Ai dolene nai wannan tambayar ƙawata, kinsan mufa wlhy dukma ɗauka muke bai taɓa taɓata ba, ashe munafukan sunsan tsiyar da suke a ɗaki idan sukai bulum, to wlhy babu mai ce miki ga daren farkon yarinyarcan a gidannan�?.
“Ƙawa kinsan wasu matanfa akwai dauriya wlhy, koda sunsha wahalar bazasu bada wata ƙofar da wani zai fahimcesu ba, kuma kinga ai tanada iliminta yarinyar ga wayo, kune dai dama kuke raina ajinta, amma irin masu sanyin nan kedai gansu ki barsu�?.
“A to lallai na yarda da maganarki wlhy, ohni kujimin wani sabon zance�?.
Haka dai maman Ama taita wannan sambatu ƙawarta na mata dariya, ALLAH ALLAH take a gama taron sunan nan ta gumtsama Kausar da maman Aysha.
Rumana kam bama tasan sunaiba, dan tun bayan fitar su kwanciya ta koma ta sake yi, ahaka mutane sukaita ɗan shishshigowa yin salla.
Washe garin da taron suna ya watse kam ai kasuwar yi da cikin jikin Umm-Ruman suka ci, dan ba ƙaramin tsaya musu yayba a rai, saboda yazo musu a bazatar da ko a mafarki basu taɓa kawowaba, aiko duk inda tayi idanunsu na kanta, tunma bata fahimtaba harta fara fahimtarsu, itadai addu'ar neman tsarin ALLAH da sharrinsu tai ta jefa musu, dan tarasa wannan kallon har hanji na minene haka? Ina kuma dalilinsa?�?.
Tunda ga lokacin basu da abin magana sai wannan ciki, ita Maman Ama ko nata bata kulaba sai na Rumana, ita Kausar ma ga jego tanayi amma hakan bai hana idonta zama akan wani ba.
_________________________________
Dawowar Ahmad da kusan sati huɗu sannan aka nemesa, ashe tuni ubagidansa ya bada takardunsa wa ƙaninsa.
Cikin fargaba da addu'ar samun nasara suka isa wajen ƙanin ubangidan nasa shi da shi harma da Happy da tai musu rakkiya.
Abunda yaso kaɗa hantar cikin Ahmad ganin shine kaɗai bahaushe a waɗanda aka amshi takardunsu, addu'a yay tayi a zuciyarsa, ya turama Rumana text message akan ta tayashi da addu'a itama.
Koda ta gani murmushi tayi, cikin ranta tana maijin tausayin yayan nata da ƙaunarsa.
Amma su Ahmad interview, kowa a ransa da fatan nasara, ance nanda zuwa kwana uku zasuji sakamako, wanda duk ya haye ya tsira, wanda bai samuba kuma yay haƙuri.
Idan nace muku Ahmad ya bar hankalinsa kwance a kwana ukunnan nai ƙarya, duk ya kira su baba yace su sakashi a addu'oinsu, hakama ƙannensa duk a faɗa musu kowanne yay masa addu'a.
UBANGIJI mai Rahma ne kuma mai jinƙai, a randa kwana ukun ta cika ko kasuwa kasa fita yay da wuri, kusan sha ɗaya saiga baƙo masu gidan sunyi, shidai yaje ya buɗe masa gate ya dawo ya cigaba da shirin fitarsa, yana gab da kammalawa sai ga Happy da gudunta, tunda yaji gudu yasan itace, kaɗan daga aikinta kuma tace zata rungumesa, dan haka ya juyo yana kallon ƙofa a tsume.
Aiko koda ta shigo ɗakin kansa tayi gadan-gadan, yay azamar ɗaga mata hannu yana faɗin, “Kinga tsaya�?.
Dakatawa tai tana kumbura fuska.
Yace kinga kiyi haƙuri, mu addininmu da al'adarmu sun banbanta da naku, haramunne a addininmu mace ta taɓa balle ta rungume namijin da ba muharraminta ba, shima namijin haka, sannan babban abin kunyane a al'adarmu ta hausa fulani.
Cikin kaɗa ido da hannu Happy tace, “Okey na fahimta, amma dai kun cika tsauri da yawa�?.
Murmushi Ahmad yay mata yana girgiza kai, yace, “Ba tsauri mukai da yawa ba, wannan ɗabi'ace mai ƙyau, domin an daraja macen ma ne anan, kinga ba kowanne shashasha ne zaice zai kai kazamin jikinsa ko hannunsa kanta ba�?.
Shiru tai tana kallonsa, da alama dai maganar ta mata tasiri, ya ɗauke kansa shikuwa yana faɗin, “Miya faru kike zuba gudu?�?.
Cikin kauda abinda ya faru ta washe baki tare da dirga tsallen murna, tace, dama zuwa nai na maka albishir, “Uncle ɗina da yazo yanzunan yake tabbatar mana ka samu aiki�?.
Da sauri ya kuma waro mata manyan idanunsa, “Da gaske kike?�?.
“Da gaske mana, Dady yace kazo ma�?.
Binta kawai Ahmad yayi, amma yarasa yanda zai musalta farin cikinsa na wannan albishir na Happy, a tare suka isa falon su Happy ɗin.
Dady, Momynta, sai baƙonsu wanda takardun Ahmad ke a hannunsa, kujera Dady ya nunama Ahmad ɗin, ya zauna yana gaishesu tare dama baƙonsu barka da zuwa.
Da ƴar fara'arsa ya amsa yana faɗin, “Ahmed kai mai sa'a ne, duk da kasancewarka bahaushe ɗan yankin arewa kaci nasarar samun aiki, aikinma a gurbi mai daraja�?. ya ƙare maganar yana miƙama Ahmad ɗin takardun hannunsa.
Ahmad na buɗewa yagani a gabansu Ahmad ya sauka ƙasa yayma Ubangiji sujda, duk da kallo suka bishi na mamaki, Momyn Happy kasa haƙuri tai sai da tai masa tambaya.
Shiko yay mata bayanin yayi hakanne domin nuna godiyarsa ga UBANGIJINSA domin shine yay masa wannan rahmar.
Su dai dariyama sukai masa, baiko damuba suma yay musu godiya sosai da wannan karamci da sukai masa babu ko sisinsa.
★★★★�?
“UBANGIJI mai hikima, kuma gatan bawa, mai bayarwa ga wanda yaso akuma lokacin da yaso, yayana naji farin ciki sosai da wannan cigaba da muka samu, maganarka ta tabbata, da kace na zaune baiga gariba, sannan motsi yafi zama, dan bawa baisan ina alkairinsa yakeba�?.
Lumshe idanu Ahmad dake kwance yana sauraren nutsatstsiyar muryar Babie R ɗinsa ta cikin waya yayi, yay sansanyan murmushi yana sake ƙasa da muryarsa, “Ngd Gwal ɗina�?.
“Yayana miye abin godiya, fatanmu dai ALLAH ya baka ikon tsare gaskiya a duk inda ka samu kanka. ya kuma baka ikon cin halalinka komai ƙanƙantarta, ya tsareka daga haramun komai yawanta dan bata da amfani�?.
“Amin ya rabbi Babie R, yanzu mizan samu goron albishir?�?.
Wata ƴar dariya Rumana tayi daga can, takai dubanta gasu Salima dake barci, sannan tace, “Mi kake buƙata Zumana, kuma yaya?�?.
Kwanciyarsa ya gyara yana sauke ajiyar zuciya, yace, “Komi na samu zanyi murna Gwal ɗina�?.
Numfashi ta sauke a hankali tare da sumbatar wayar cike da salo.
Karon farko da Rumana tai ma Ahmad abinda baiyi zatoba, dan haka ya tashi zaune sosai cikin mamaki yace, “Babie R!�?.
A ɗan tsorace Rumana dake dariya ƙasa-ƙasa tace, “Nayi laifi ko yaya?�?.
Dariya yaɗanyi mai sanyi shima daga can, “Laifi kuma Gwal ɗina? Ai abinda ban taɓa zato bane akaimin, ngd da wannan goro sosai�?.
Murmushi Rumana tayi har yanajin sautinsa, tace, “Ai kafi ƙarfin haka daga gareni Zumana, wannan ma bashi bane Goron, saika dawo zaka samu goro na musamman�?.
A take tsigar jikin Ahmad ta fara tashi, ya marairaice mata murya kamar wani yaro yace, “Da gaske Babie R?�?.
Tace, “Insha ALLAHU Sweet Yayana, farin cikina, mai hana kukana zuba�?.
Gaba ɗaya Rumana ta gama cakar da Ahmad, ji yake tamkar ya rufe ido ya buɗe ya ganshi a gabanta, jininsa sai wani gudu yake da sauri, hakama gashin jikinsa dukya mimmiƙe, sai yake ganin kamar ana ƙara mata wayone kullum.
Kasa jurewa yay ya yanke wayar kafin ya tafka abin kunya, yay luf akwance tamkar wanda akaima bugun tsiya.
Daga Rumana kuwa murmushi taitayi, dukda itama tana masifar jin kewarsa, ta shafa cikinta tana maijin ƙaunarsa da ɗokin zuwansa duniya idan ALLAH ya ƙaddara hakan.
________________________________
Ɓangaren Samina kuwa a yanzu babu abinda ya tsayama rayuwarsu a rai ita da su Mama Gaje kamar cikin Umm-Ruman, da yake yanzu Ahmad kan barta taje gidansu lokaci-lokaci mama gaje jitake kamar ta gatsi Rumana da haƙori idan taje, fahimtar hakan da Ammi tayi ne ya sakata kuma dagewa Rumana da addu'a, dan ranar cikin dare fitsari ya fiddo Khadija ƙanwar Rumana sai taji Mama gaje nata kiran sunan Rumana a tsohon daren nan, lallaɓawa tai ta leƙa ta jikin Window mama gaje, dayake a kwai ɗan haske khadija tai ido biyu da Mama Gaje na busa wani abu a hannunta tana kiran sunan Rumana, hankalin khadija yay masifar tashi, kasa haƙuri tai saida ta bugama Amminsu ɗaki a hankali, ALLAH yasa bata da nauyin barci ta tashi ta buɗe mata, harta farama Khadija faɗa akan hakan da tayi, babba da ita tana abun yara mike faruwa.
Khadija tai ƙasa da murya tana sanarma Ammi abinda ta gani, fitowa tai itama jikinta har rawa yake ta leƙa Window mama gajen, a lokacin ma sunan Rumana dana Ahmad ɗin take kira tana sheƙa abun hannunta a ƙasa saikace mai shiƙar hatsi.
Wannan Abu yay masifar tada hankalin Ammi, a wannan daren kam batai barciba daga ita har Khadija...............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻: https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(34)*
...............A lokacin da mama Gaje ke wancan shaiɗanci Umm-Ruman na kan sallaya tana karatun Qur'an, ta idar da nafilfilinta tamkar yanda ta saba a kowane dare idan har ALLAH ya bata iko, randa kuma takejin nauyin jiki koda ta farka taji bazata iyaba sai taita addu'ointa daga kwance har barci ya sake kwasheta, tama daɗe bata tashi ba a kwanakin nan, saboda yanayin jikinta, amma yau tun kusan sha biyu da rabi sai barcin ya ƙauracema idonta, dole ta miƙe tayo alwala a tsorace ta dawo, shine ta fara gabatar da salla kafin ta ɗauki Al-Qur'ani ta shiga karatu a hankali.
Tabbas taji gittawar abu ta gabanta tamkar iska, sai dai koda ta ɗago ido bataga komaiba, bata kawo komai a rantaba ta cigaba da karatunta kawai.
Tunda Safe sai ga Khadija gidan, yanda ta iske Rumana cikin farin ciki suna karyawa ita dasu Fa'iza ne ya sakata jin sanyi a ranta, bata sanar mata komaiba dasu Salima zasu wuce gidama saita bisu.
Koda ta dawo ta faɗama Ammi Rumana na cikin ƙoshin lafiya sai itama taji sanyi har ranta.
Ta cigaba da mata addu'ar neman kariyar UBANGIJI a koda yaushe.
Randa Rumana tazo gidan kuma saita ƙara bata wasu addu'oi tace ta dage dayi a kullum tana kuma shafe cikinta shima.
Rumana ta amsama Ammi da “To�? cikin jin kunya, dan tunda maganar cikin nan ya bayyana Ammi bata taɓa maganarsaba sai yau.
★★★★★★
Su Mama gaje sunta jiran suji sakamakon aikinsu amma tsit, sai ma Umm-Ruman da tazo gidan cikin ƙoshin lafiya, hankalinsu ya tashi, a ranar taje ta sanarma Inna mari.
Sai ta hauta da faɗa akan kodai batayi yanda malam ɗin yaceba, tunda dai gashi aikin da yayma Samina yayi ƙyau, dan yanzu haka tana kan cin duniyartane da allura, duk da dai bawai yabar shaye-shayensa bane, randa kuma tsautsayi ya gifta yakan jibgeta, sannan tun randa yaga Rumana da Ahmad kusan kullum saiya mata maganar Umm-Ruman, har cemata yake da yasan da wannan ƙyaƙyƙyawar a gidansu mizaiyi da ita sauran bilicin.
Wannan abu na sosa zuciyar Samina, shiyyasa take sake jin tsanar Rumana a kowacce daƙiƙa ta rayuwarta, bataƙi ace yau ga gawar Umm-Ruman ba a duniya.
Mama gaje dai ta taima Inna mari rantsuwa akan duk tayi yanda yace, hakan yasa suka koma wajensa washe gari.
Bai ɓoyeba ya sanar musu gaskiya akan samun aiki yaci Rumana ko Ahmad abune mai wahalar gaske, danshi Ahmad ma akwai tsari tare dashi tun yana yaro cikin iyayensa sukaima duk yaransu, shiyyasama ko aikin farko da sukai akansa dan karya samo komai a neman kuɗinsa aikin yaƙi tasiri. shima sai daga baya ya fahimci hakan. Umm-Ruman kuwa bata wasa da ibadar ALLAH, tana cika kowacce salla ta farilla, sannan bata bari lokacinta ya shige akan ganganci sai dai kuskure.
Yace, “Kunsan ba aikin dake bamu wahala kamar na mutumin da bai wasa da salla, mukan daɗe bamuci galaba a kansaba, sai dai idan UBANGIJI ya ƙaddara hakan arayuwarsa. Yanzu gashi matsala ɗaya bata jini saboda ciki, amma da ace tanai sai mubi wannan hanyar musamu nasara. Idan kuma zakuyi haƙuri harta haihune to, randa ta haihuma zamu iya salwantar da yaron ita kuma aikinmu ya shiga jikinta�?.
Shiru su mama gaje sukai suna nazarin maganarsa, Inna mari ta katse musu tunani da faɗin, “Babu damuwa mun yarda kawai malam, amma babu yanda za'ai kafin sannan aɗan saka rashin jituwa tsakaninta da mijin nata?�?.
Dariya malam yayi yana faɗin, “Badai za'a barta ta hutaba kenan? To zan gwada na gani idan za'a dace, amma ita ƴar uwar tata Samina ta kwantar da hankalinta ta shiga jikinta sosai, ta wannan hanyarne kawai zamu san komai daga gareta har watan cikin nata�?.
“To shikenan Malam wannan ba matsala bane zamu sanar mata�?.
Sun masa sallama suka taso suka taho gida suna ƙara jin haushin Ammi da Rumana da basu tsare musu komai a rayuwa ba.
★_★“★_★”_�?
Da ƙyar su mama gaje suka shawo kan Samina akan shiga jikin Umm-Ruman, dan da da farko taƙi, yanda ta tsani Umm-Ruman ai ko maganarta ta tsana a mata balle har akai ga ta raɓeta, ita yanzu hakama ko za'a kasheta bazata iya gane gidan da aka kaita kafin Rumanan ba.
Ta dai fara karɓar Number Rumana ɗin wajen yayarta Bintu da hakan ya ɗaurema kai, haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya da ƴar uwar tata akan amsar wannan Number ta Rumana.
Da farko ma kamar karta bata, sai taga idanma bata batanba ai zataje ta samune wajen wani.
Abinda kuma su mama gaje basu saniba a yanzu duk motsinsu Ammi na hankalce dasu, sannan ta kuma dagewa tuƙuru wajen jefan ƴarta da addu'oi harma da cikin jikinta data lura shi ya tsone musu idanu.
_________________________________
Haka rayuwa ta cigaba da turawa, kwanaki na shuɗewa suna zama satittika, yau da gobe kayan ALLAH har takai cikin Umm-Ruman ya fara fitowa sosai, danma dai cikin fari dama ba wani girma ya cikaba, sannan gata doguwa kuma masha ALLAH.
Ahmad ma dai ta ɓangarensa komai sai hamdala, dan kuwa ya fara zuwa aiki, gefe kuma ga kayan kasuwarsa sun haɗa hannu da Nura, shima duk ranar weekend yakanje kasuwa.
Ya samu ya sake aiko da kuɗin hayarsu, dukda ma tunaninsa ya fara bashi ɗakko Umm-Rumana su taho nan, dan yanzu bazai dinga samun lokaci mai yawaba na zuwa gida ya jima kamar da.
A hakama da ƙyar ya fisge a wannan karon yazo gidan akan zaiyi sati ɗaya kacal.
Kowa yaga Ahmad yasan rayuwa ta fara canja masa sosai, musamman yanda yay ɓul-ɓul dashi ga alamun kwanciyar hankali na musamman tattare dashi, ya ƙara zama Gentleman na gaske, ga gayu tamkar ba shine yay shushaina ba da talla a titi.
Ita kanta Umm-Ruman bata iya ɗauke kanta daga garesa, dan gaba ɗaya ya rikiɗe ya canja mata, sunsha soyayyarsu mai tsafta tare da tattalin da yake nuna mata saboda tausayinta