Showing 93001 words to 96000 words out of 165545 words

Chapter 32 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

398

Leda ya miƙa mata yana tsokanarta akan Yau daɗi zasuci kenan?.
Rumana tai dariya tana faɗin, “Kai Yah Abu wane kayan daɗi fa?, ɗan kunun ayane kawai zanma Yayanmu tunda ya mana zuwan bazata�?.
“Wlhy kuwa, ai Yah Ahmad ya iya wayo, kofa a gida babu wanda yasan da zuwansa, ganinsa kawai akayi�?.
Rumana tace, “Lah wai harsu baba ma Yah Abu?�?.
“Aikam harsu in faɗa miki. bara naje Yah Mudan jirana yake nakai masa, sai mun dawo shan kunu�?.
“To ALLAH yasa da gaske kakeyi, zanko ajiye dan ALLAH ka dawo�?.
Yana gab da fita yace, “Wlhy wasa nake karki ajiye, yau aiki garemu a shago na masu biki�?.
Roƙonsa ta shigayi akan ko cikin su Kamalu ne ya aiko su karɓa masa, shidai ya fice yana jaddada mata karta ajiye.
Koda ta haɗa markaɗen Ahmad ta aika ya kira mata Aysha yarinyar maƙwaftansu, ta bata tayo mata markaɗen, zama tai ta tace abinta ta haɗa duk abinda ake buƙata ta saka ƙanƙara bayan ta juye a ɗan boket na plastic ta rufe abinta, ta sake kimtsa ɗakinta tai wankanta gab da magriba ta shige ɗaki bayan ta sake kunna turaren wuta na tsinke, ta fito ta samu garwashin uwatar da maman Ama tai girki ta diba taje ta saka turaren wuta na tsugunno tayi kamar yanda yaya maryam ta koya mata sannan ta zuba na ɗaki a sauran rushin, salla ta fara gabatarwa kafin ta gyara jikinta, wasu siket da riga daya kawo mata wancan zuwan ta saka, sunko mata ƙyau sosai, dan dama sawarta ɗaya tun yana nan, bayan tafiyarsa kuma ta ninkesu da sauran ta ɓoye abunta, a tsarinta dama dai tafi son taringa kwalliyar dare dasu idan yana gari.

Bayan sallar isha'i kaɗan kuwa sai gashi ya shigo, lokacin ta kammala zuba masa kunun ayar a kofi tana goge wanda taɗan zuzubar a ƙasa ne.
Sannu da zuwa tai masa, ya amsa yana ajiye ledar hannunsa dake ta ƙamshi idonsa a kanta.
Kayan sun zauna mata ɗas ajiki, musamman yanzu datai ƴar kibarnan.
Ita kanta yanda yake binta da kallo sai da kunya ta kamata, ta kai tsunman waje ta ɗaurayo hannunta ta dawo.
“Wai miye sirrin ƙyawun nan ne ta wajena?�? Ahmad dake kallon Umm-Rumana ya faɗa.
Tace, “Kai Yayanmu, kai ba'a tambayeka sirrin ƙyawun da kaiba sai ni wane ƙyau nayi?�?.
Hannunta ya riƙo ya ɗorata saman cinyarsa, “ALLAH Babie karkiji batun wasa kin wani haɗu sosai, kinyi ƙiba da haske kamar ina kusa dake�?.
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana faɗin, “Wlhy kana bani kunya Yaya�?.
“Kwantar da hankalinki, anjima kaɗan zaki bani kunyata ai yarinya�?.
Tashi tai a jikinsa tana dariya, ta ɗakko filet ta buɗe ledar daya shigo da ita, gasasheshen balangune daya samu tsafta da iya gashi, ga tumatur da albasa da cucumber yasha sunata bada ƙamshi mai daɗi, ta ajiye a saman tabarma kusa da juk ɗin data zuba kunin ayar.
Tashi yay ya cire rigarsa ya zauna da dogon wandon da singlet, itama ya nuna mata gefensa.
Bata musaba ta zauna, ta tsiyaya masa kunun ayar a karamin kofi ta ajiye a gabansa, ɗauka yay yasha yana lumshe idanu.
Ya buɗe a kanta tare da fadin, “Babie na kinaji dani fa�?.
Guntuwar dariya Rumana tayi ita dai, tace, “Goron albishir ɗinne ai kafin ama fadamin na bayar�?.
“Ina my Ruman, bashi nake so matsayin goron albishirba, ki ɗauka wannan na sannu da zuwane kawai, goron albishir ɗina na musamman nakeso da gwauro baya samunsa�?.
Ƙasa tai da kanta tana ƙara mamakinsa a ranta, idan ya zubo magana saika ɗauka bazai iyaba.
Cikin nutsuwa ya zayyane mata abinda ya kawoshi kamar yanda yayma su baba bayani a gida, farin cikin daya lulluɓe Rumana batasan sanda ta faɗa jikin Ahmad ba ta rungumeshi.
Cikin dariyar da yake mata ya samu damar lalubo bakinta ya manna nashi...........🌚🤫😝✍�?



*_Masu bin littafin ƙwai cikin ƙaya kuwa, saina tattare part 1 zan turo duka insha ALLAH, na gaji da wannan asha ruwan tsuntsayen nima, zaku iya ganina a koda yaushe da izinin UBANGIJI🥰🥰🙏🏻_*




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(30)*


.............A yanda salon yazo tuni Umm-Ruman ta bada haɗin kai wa yayan nata cikin nata ilimin data ƙara samu akan nada, ta mance da wata aba wai ita kunya, sai dai Ahmad yay liɓis a zaunen nan sannan ta iya ƙoƙarin janye bakinta tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa.
Ya lumshe idanu yana jingina da bango da sake kanannaɗeta a jikinsa yana sauke numfarfashi.
Kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya iya buɗe baki da ƙyar yace, “Da gaske dai Ruman ta girma�?.
Shiru Umm-Ruman tayi tana sake lafewa a jikinsa, ita kanta tasan yau ta zaƙe da yawa, ba komai ya jawo hakanba kuma sai missing ɗinsa.
Tace, “Nidai Yaya ban girmaba�?.
Murmushi yayi yana kai hannu ya zame ɗan kwalin kanta, sumarta dake a ɗaure babu kitso ya shaga shafawa a hankali, kafin ya zame ribbon ɗinma gaba ɗaya ya saki gashin nata mai tsawo da cika, yanason gashi sosai, dan yana ɗaya daga cikin abinda yaso tattare da Samina, ashe baima saniba Rumana tafi Saminar,
“Miyasa babu kitso Babie R?�?.
Yunƙurawa Rumana tai ta tashi daga jikinsa, kanta a ƙasa batason su haɗa ido tace, “Zafi nakeji�?.
“Zafin kitson?�? yay maganar murya a shaƙe.
Fuska taɗan ɓata tana langaɓe kai tace, “Eh wlhy Yaya�?.
Yayi wani ɗan moso mai sauti yana kai hannunsa kan gashin, “Miyasa wani lokacin ke raguwace? Yanzu nan kitsone keda zafi?�?.
Babu shiri ta kallesa da ƙyau, dan ita dai tasan zafin kitso babu sauƙine, “Yaya kitsonne babu zafi?�?.
Shima idanun ya fiddo kamar yanda tayi yana cewa, “Duk zafinsa ya kai randa kikai tamin raki�?.
Yanda ta ɓata fuska tai gefe da ita na alamar shagwaɓa tsagorontane ya saka Ahmad ƙyalƙyalewa da dariyar da bai niyyaba, ya jawota ta dawo jikinsa, “Kinga wasa nake gwal ɗina, ba ke baceba gaskiya�?.
“Ni babu wani wayo da zakaimin bayan kanata faɗa�?.
“To na daina faɗar, haba zinariyar zuciyar Ahmad�?.
“Naƙi wayon�? Rumana ta faɗa tana ɗan dukan ƙirjinsa na wasa.
Dariya sosai ya shigayi yana ƙoƙarin riƙe hannayenta amma taƙi bari.

Karaf kuwa wannan wasa nasu a kunnen mijin maman Ama daya shigo gida a lokacin, shiga yay ɗakinsu yana tsaki, maman Ama ta kallesa da mamaki tace, “Lafiya Abban Ahmad?�?.
“Mtsoww mutanenki mana, wai yaushema har ya fara abinda mazan ƙwarai keyi?�?.
Itama tsakin maman Ama tayi tana taɓe baki, “Ko baiyiba ai ayi mana bariki dan muce anyi, karma kilakinsu ya dameka, hakama wancan zuwan sukaita wannan abun sai kace wani namijin gaske�?.

To su dai su Ahmad ma basusan sunaiba, sunacan suna firarsu cikin nutsuwa da nunama juna zallar aminci ba tare dasun damu da kowaba ko lamarin kowa a gidan, dan in zaka karsu basa faɗa maka yanda kowacce take rayuwarta a gidan ba da mijinta.
Suko anbi an saka musu idanu ko wanne motsinsu abin ayi tsogumine.
Tana kwance kanta bisa cinyarsa yana wasa da gashinta, wayarsace a hannunta take kallon hotuna suna firarsu cikin nutsuwa.
Har kusan goma da rabi sannan Ahmad yace su tashi haka nan su kwanta barci yakeji.
Batai musuba ta tashi tai kaye-kaye tayo alwala da brush kamar yanda shima yayo, sanda ta shigo haryayi shirin barci ya haye gado, itama kimtsawa tayi bayan ta kashe fitilar ɗakin har Ahmad na mata tambayar lafiya.
Ca tai masa babu komai.
Murmushi kawai yayi yaɗan girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.
Sai da ta gama ƙumshe-ƙumshenta sannan ta hawo gadon.
Yau ɗinma dai sun gwangwaje juna da soyayya mai tsayawa a rai, duk da dai Rumana ta yabama aya zaƙinta, dan Yah Ahmad ɗin bana wasan yara bane.
Shi kansa yasan tayi laushi bana wasaba, yau ma wankansu sukai a roba ya fita ya zubda ruwan ita kuma ta goge inda sukaɗan ɗiɗɗisar da ruwan.
Aiko tunda suka kwanta Rumana batai ko juyiba tsabar gurzuwar da tayi, a hakan kuma bayan sunyi sallar asuba ya sake nuna buƙatarsa, babu yanda ta iya dole ta amince kodan gujema fushi.
Aiko harda ƴan ƙwallanta, dan ita kam jarumtarsa tsoroma take bata, inhar haka za'a cigaba dayi lallai akwai jan aiki a gaban mata kenan?.
Da ƙyar Umm-Ruman ta iya tashi bayan sunsha barcinsu kusan goma na safe, haka ta daddage ta miƙe domin haɗa musu abin kari.
Shima tashin yayi, ya zira jallabiya ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin tana ƙofar ɗaki ta kunna risho.
Ciki ya wuce, ita kuma ta cigaba da ayyukanta, bayan ta ɗora ruwan cikin ɗakin ta koma, yana kishingiɗe a tabarma dan haka ta samu ta gyara gadon, ta ɗan share ɗakin ta gewayeshi, har tsakar gidan ta share ta wanke bayi, duk wannan hidimar da takeyi kuma Maman Ama bata gidan, tunda Kausar tai nauyin da bata iya zama suyi gulma to bata iya zaman gidan, to dama ita mijinta ƙarfe bakwai yabar gidan, shiyyasa sam bata kallon irin wannan lokacin matsayin safiya.
Rumana dai ta gama haɗa kalacinta, ruwan wanka ta sirka taje tayo, sai da ta fito sannan ta haɗama Ahmad.
Koda ta faɗa masa ga ruwan wanka bai musaba ya miƙe yaje dan ya yo, saboda shima a damuwar son tsarkake jikinsa yake.
Kafin ya fito Rumana harta shirya, ta mulke jikinta da ƙamshi.
Koda ya shigo itace ta taimaka masa ya shafa mai kamar yanda ya buƙata, duk da tanajin nauyinsa haka ta daure danta lura bayason yace ai masa abu ake masa gardama.
Itako yanda yake sakewa da ita a yanzu ai bata fatan taga ɓacin ransa sam.
Iya gajeren wando da singlet kawai ya saka ya zauna sukai breakfast, bayan sun kammala yace ta fiddo masa kayan da zaisa, dan Sufyan zaizo suje makaranta ne.
Taji daɗin wannan girmamawa tashi, dan haka ta zaɓo masa kayan da tasan idan yasa suna ƙara masa kwarjini da ƙyau, da taimakonta ya saka hardasu hula, tsaf ya fito asalinsa na bahaushen arewa, ta saka masa turare.
Kuncinta ya sumbata yana miƙa mata agogonsa da faɗin, “Thanks�?.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi, ta kama hannunsa ta ɗaura masa agogon.
Ji take kamar tace ya zauna kawai taita kallonsa......
Ya katse mata tunani da faɗin, “Bara muje inaga ya iso ga kiranshi nata shigowa, sai mun dawo�?.
“Tom Adawo lafiya, amma mi za'a dafa?�?.
“Komaima ki dafa, Abu zaizo, ki duba a kayan dana cire zaki samu kuɗi saiki bashi yayo cefane�?.
Yana gama faɗa ya fice, ita kuma ta bisa da addu'ar dawowa lafiya.

Ajiyar zuciya taɗan sauke bayan fitarsa, ta zauna a bakin gadon tana cije baki, wlhy jikinta sai ciwo yake mata, “kai Yah Ahmad babu sauƙi�? ta faɗa a fili tana matsa cinyoyinta.
Dole ta sake daurewa ta tashi ta sake kimtsa ɗakin da kyau, sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta samu nutsuwa, barci ne sosai a idonta amma haka ta daure ta zauna jira Abu.
Shima babu jimawa yazo saboda kiransa datai ta waya, kuɗin ta ɗakko ta bashi kamar yanda Ahmad ya faɗa, ta lissafa masa abinda zai sayo.
Da yake aiken na mai hankaline bai jimaba ya dawo, itama ta miƙe batai son jikiba tai abincin.
Dan danan ta kammala ta tsaftace wajen tamkar batai ba, alwalar azhar tayi ta shige ɗaki, har lokacin su Ahmad basu dawoba, aiko tana idan da salla kasa jurewa tai tasa filo ta kwanta a wajen, cikin mintuna ƙalilan barci yay gaba da ita.



__________________________________

Hajiya Samina matan masu hannu da shinu, yanzu kam babu laifi tana ɗan samun yanda takeso wajen angon nata, sai dai fa shan giyarsa da ɗura mata maganin hana ɗaukar ciki yana nan yanayi bai fasaba, idan tai masa gardama taci dukan banza.
Matsala ɗayace yanzu taso tasota a gaba, wato maganar ƙara aure da mahaifiyar ma'aruff take yawan yi masa, duk da shi dai bai amsa zaiyiba hakan na tada hankalin Samina matuƙar tiƙewa.
Dole ta lallaɓasa akan tanason zuwa gidansu cikin satin nan, dama baifi sau biyu ta taɓa zuwaba a cikin kusan wata huɗu da aure, amma gidan iyayensa kam dukda ana hantararta haka yake sakata taje dole, gidansu kam ya hanata, data ambata zaice mizataje tayo? Bayanma ba wani buƙatar ganinta sukeba ƴan gidan nasu, idan kuma kannenta sukazo yayta fushi yana faɗin shifa bayason wannan shigi da ficin.
Hakan na mata ciwo a rai, amma tana dannewa dan a zauna lafiya.
ALLAH ya dorata a kansa kuwa yau ya barta, amma yace sai ranar talata, batai musuba ta amince tunda dai ai nanda kwana biyune kacal.


___________________________________

Sai bayan la'asar su Ahmad suka dawo, tare da Sufyan suka shigo gidan, amma sai Sufyan ya tsaya a ƙofar ɗaki sai da Ahmad ya fara shiga saboda sunyi sallama basuji Rumana ta amsaba.
Kwance Ahmad ya isketa tana barci, da alama ma ko sallar la'asar batayiba.
Wani ɗan tsigunno yayi a gabanta yakai hannu ya shafa fuskarta, jikinta da ɗan zafi kaɗan, bai kawo komai a ransaba game da ɗumin jikin nata, ganinsa kawai dan tana a cikin ɗakine.
A hankali ya fara kiran sunanta yana cigaba da shafa fuskarta, “Umm-Ruman;�?
A hankali ta buɗe idanunta a kansa, ganinsa tsugunne a gabanta ya sakata sake buɗe idanun nata sosai tana kallonsa, murya a sanyaye tace, “Yaya kun dawo?�?.
Kansa ya ɗaga mata, ya miƙa mata hannunsa ta kama ya taimaka mata ta tashi.
“Koma salla bakiyiba halan?�?.
“Eh wlhy Yaya banma san anyiba, banyi zaton barcin nawa zaiyi nauyi hakaba�?.
Hijjab ɗin daya ɗakko yake ƙoƙarin saka mata, “Ai gara da kikayi ƙyaji daɗi, tare muke da Sufyan�?.
Tayashi saka hijjab ɗin tai tana faɗin, “Yana ina to?�?.
“Gashi a ƙofar ɗaki, munyi sallama ne baki amsaba shiyyasa ya jira na shigo naga lafiya?�?.
“ALLAH sarki, kuyi haƙuri banjiba wlhy, ya shigo to�?.
Izinin shigowa Ahmad ya bama Sufyan, ya ɗaga labulen ya shigo sallama ɗauke a bakinsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login