Showing 117001 words to 120000 words out of 165545 words

Chapter 40 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

399

Ayyah zancen ya kamata Rumana ta shirya suje asibiti a duba lafiyarta saboda haihuwar gidace.
Ayyah ta gamsu kuwa da maganarsa, ta shiga ɗakinta ta saka Umm-Rumana kimtsawa, Yaya Maryam data fara isowa ta ɗauki jaririn suka fito.
A ƙofar gida suka iske Ahmad yana jiransu, ya sauke idanunsa akan Rumana da itama take satar kallonsa.
Ƙasa tai da nata tana murmushi, dan haka kawai ta tsinci kanta dajin kunyarsa.
Shiko sai yaga ta ƙara masa haske a ido duk da sanye take da hijjab, bai iya cewa komaiba ya nuna musu hanya alamar suje.
Umm-Ruman ta buɗe baki a hankali tace, “Yaya ina kwana?�?.
Kamar bazai tanka ba sai kuma yace, “Sai yanzu aka tuna dani?�?. Yay maganar yana raɓawa ta gefenta zai wuce.
Binsa tai da kallo tana bin bayansa, dama Yaya maryam ita tayi gaba bata tsaya inda suke ba.
Napep suka shiga ita da Yaya maryam, shi kuma ya hau mashin ɗin Sufyan dake jiransa dama sukabi bayansu.
Koda suka isa asibitin su Ahmad ne sukaita shigi da fici har suka samu ganin likita.
Sai da Doctor ta tabbatar Rumana bata da matsala, sai ɗan ƙari data samu wanda dama tun daren jiyan takema iya complain ɗin zafi, musamman ma da zatai mata wanka da safe, dan kasa zama tai cikin ruwan sai da iya tai mata jan ido, ashe ɗan ƙarine tayi kaɗan.
Duk wani taimakon da ya kama Dr Hajarah ta bata shi, harda shawarwarin yanda zata kula da yaronta, ta rubuta magunguna ta bama su Ahmad akan a sayo ma Rumana.
Amsa yay suka tafi, su Rumana kuma da yaya maryam sukaje inda za aima jaririn allurar Iminazeshon tunda yayi dai-dai da ranar da akeyi.
Sun ɗan ɓata lokaci a asibitin, dan har ɗaya suna can, sai da komai ya kammala sannan suka fito, yaya Maryam da Umm-Rumana suka nufo gida.
Shi da Sufyan suka wuce kwata ya sayo nama mai ƙyau yayo cefane suka dawo suma.
Daga Gwaggo har Ayyah sunji daɗin hakan da yayi, ya iske ƴan uwansa duk sunzo, sunata masa murnar samun ƙaruwa.
Yayinda Sakina ta tasashi gaba da fadin, “Inye su ɗan ƙanina an girma, abun mamaki wai Amadi da ɗa�?.
Harara ya zabga mata kawai ya wuce, tako cigaba da kunnashi har sai da yay mata ƙwafa sannan, amma dai baice komaiba😂.
Barcin da baiyi isashsheba a daren jiya shiya addaba masa, dole ya shiga ɗakin su Mudanseer ya kwanta kuwa.
Umm-Ruman taji daɗin zuwansu asibitin sosai, dan magungunan da aka bata sun taimaka ma jikinta ta kumajin ƙarfi, bata sake ganin idon Ahmad ba har bayan sallar magriba.


★★★★★★

Bayan sallar isha'i Ahmad ya shigo gidan, da gani dai yaje gida yayo wanka, dan yanzu sanye yake da ƙananun kaya da suka ainahin fidda ƙuruciyarsa da kwarjini saɓanin yanzu da yake sanye da yadi.
Sai da ya shiga sashen baba suka gaisa, acanma ya iske Gwaggo, dan dama tunda Rumana ta dawo gidan Ayyah ta barma Gwaggo mijin, iyakarta tayi abinci kawai.
Bayan ya gaidasu duka suka ɗan tattauna da baba, yay masa maganar yima yaro huɗuba.
Ahmad yace, zaije yanzu yayi, dan da safe ya shigo zaiyi ya iske mutane sunyi yawa.
Gwaggo dai na jinsu bata tankaba har Ahmad ya tashi ya fita zuwa ɗakin Ayyah dake ƙofar ɗaki zaune ita da Mudan dake cin abinci suna hira.
Sannu sukai masa ya gaida Ayyah.
Fuskarta faɗaɗe da murmushi ta amsa da ce masa ya shiga abincinsa na ciki.
Ɗakin ya nufa ya shiga da sallama, su Fa'iza dake zaune suna taya Umm-Ruman hira duk suka miƙe, raɓawa sukai suka fice suna gaidashi.
Sai da duk suka gama fita yana tsaye idonsa kafe akan Rumana dake cin farfesun da Ayyah tai mata na naman da Ahmad ya kawo ɗazun.
A hankali ya taka zuwa gaban gadon inda ɗan jaririnsa ke kwance naɗe a cikin zani, zama yay ya ɗaukesa ya aza bisa cinya.
Rumana dake satar kallonsu tace, “Sannu da shigowa�?.
Kallonta yay kaɗan yana maidawa ga yaron tare da amsa mata, yay masa kiran salla a duka kunnensa yana faɗin, ALLAH ka raya *_HAMZA, Sunan Uncle ɗin MANZON ALLAH, jarumtarsa yasa akan masa laƙani da zaki,(ALLAH yasa kaima ka kasance magajinsa a wajen addini da jarumta) sannan magajin Baba, (ALLAH yasa ka kasance mai kwaikwayon halayya na ƙwarai irin na baba) dan haka alkunyarka itace (Haysam, ma'ana Lion) kenan, ALLAH yasa ya zama zaki mai kare martabar addininsa a duk inda ya tsinci kansa, ya sanya albarka da alkairi a rayuwarka my lion har ƙarshen numfashinka, ALLAH ya hanaka kasancewa a cikin masu aikata fasadi a ban ƙasa, ka zama ɗa na garin abin alfaharinmu, abin alfahirin MANZON ALLAH a ranar da ya ambata al'umarsa su zama_*
Rumana dake saurarensa kanta a ƙasa tace, “Amin ya ALLAH Yaya, ALLAH ya Rayasa akan turbar addini�?.
“Amin Gwal ɗina, amma banji kin maimaita sunanba�?.
Murmshi Rumana tayi tana ɗan ɗago ido ta kallesa, ya ɗaga mata gira da wani salo.
Ɗauke idonta kawai tayi, tace, “To ALLAH ya raya Haysam�?.
“Muna godiya Umm-Haysam �?.
Nanma murmushin tayi, ya ciro dabinon dake aljihunsa ya saka a baki ya tauna sannan ya zare hannun da yaron ya saka a baki ya haɗe bakinsu bayan yay bismilla ya zuba masa.
Ɓata fuska yay yana motsa baki, hakan ya saka Ahmad ƙura masa ido yana murmushi, ya yafito Rumana da hannu alamar tazo ta gani.
Bata musaba kuwa ta taso zuwa garesu, har lokacin fuskar yaron a yamutse take yana dai cigaba dajin sabon ɗanɗano a harshensa, sai kuma ya koma motsa bakin alamundai shanye kayansa yake.
Murmushi sosai Rumana takeyi itama.
Ahmad ya ɗago yana kallonta shima yana murmushi, “Gwal kinga ƙwaɗayin da kikayi ko? Duk kin gogama yarona�?.
“Ni wlhy a'a, shidai yasan inda ya kwaso kayansa�?.
Dariya Ahmad yay yana sumbatar kumatunsa, yace, “My Lion kaji Ummienka ko? Karka damu zamu rama�?.
Ita dai Rumana kallonsu take cike da sha'awa, ya kuma sumbatar goshinsa.
Tasowa yayi yazo gabanta ya durƙusa, tare da ɗora mata shi saman cinya, ba tare da ya janye hannunsa ba ya ɗago ido yana kallonta, duk yanda taso janye nata ya hanata dama, murya ƙasa-ƙasa yace, “Please gwal, yi feeding ɗinsa na gani�?.
Tana ƙoƙarin janye idanunta yay saurin jawo hannunsa daga cinyarta ya riƙe haɓarta.
“Haba babie R sai anja mani aji�?.
A ɗan shagwaɓe tace, “Nidai Yayah ALLAH kunyarka nakeji�?.
Gira ɗaya ya ɗage yana mata wani kallo mai saka zuciya nutsuwa, “Gwal zuman ki ne fa, wace kunya kuma ta rage miki bayan kin haifomin My Haysam duniya Huyim?�?.
Yanda yaketa wani marairaice matane ya sakata bin umarninsa tayi yanda yakeso.
Yanda take ta matse baki da yaron ya kama ne ya sakashi yin murmushi, “Miya farune Gwal ɗina?�?.
Cikin ɗan yarfe hannu tace, “ALLAH akwai zafine Yah Ahmad�?.
“Oh sorry, to kona tayashi�?.
Babu shiri ta buɗe idanunta tare da zarosu waje.
Dariya yay yana matsawa baya, “Kinga wasa nake karki hanani barci da waɗannan idanun hajjaju�?.
Itadai shiru ta masa, shiko ya koma kan tabarma ya jawo tiren dake gefe yana buɗewa dan yasan abincinsa ne.
Yanda ya ƙureta da idone ya sakata janye yaron tana gyara rigarta, dama ta gaji, dan tsakanin daren jiya zuwa yau ta kula yaron nan cin tsiya zaiyi, dama da daddare da kuka Ayyah ta tirketa ta bashi nonon, yauma ɗin sai an tuna mata kokuma yana kuka sannan.
Yaron ta gyarama zanin da yake a ciki ta miƙe zuwa ɗan katifarsa mai net dake babban gadon Ayyah ta sakashi sannan ta dawo ta zauna.
Yanda tai shirune ya saka Ahmad kallonta yana fadin “Malama wai na zama surukinki ne?�?.
Rumana tace, “Eh mana�?.
Tsayawa yay yana kallonta, yace, “To miyasa?�?.
Fiki-fiki tai masa da idanu tana ɗauke kanta bata bashi amsaba.
Yay ƙaramar ƙwafa da faɗin, “Zan kamakine yarinya�?.
Ita dai murmushi kawai tayi.

Koda ya gama cin abincin sai da Ayyah tai masa magana yazo ya wuce gida sannan ya fito yana ɓata fuska.
Ita dai Umm-Ruman sai dariya take ciki-ciki, ya harareta da mata alamar wai zai kamatane ai sannan ya fice.

★★�?

Washe gari wajen goma na safe sai gasu maman Ama, sunzo barka ita da Kausar, sunzo da ɗan ƙullin Omon su, ita dai Rumana ta amshesu hannu bibbiyu.
Sunata santin yaro da fadin sun rasa da wama zasuce yana kama, ita ɗin ko Ahmad.
Ita dai batace dasu komaiba, kusan yini sukai a gidan, dan sai bayan zuhur sosai suka wuce.

____________________________________


Ɓabgaren Samina kuwa Basy na fita ta kawo musu ƴan sanda tayi, tsabar ta fisu rashin mutunci tasa har Ma'aruff ɗin aka kama sukaje suka garƙame kuwa.
An tafi dasu babu jimawa ƙanwar Ma'aruff tazo gidan, mai gadi ya zayyane mata komai daya faru, hankalinta tashe ta kira Ummansu ta sanar mata, acan suka haɗu police station ɗin da sauran ƴan uwanta.
Da yake ƙasar tamu ta zama mai kuɗine mai faɗa aji, ƴan sanda sunajin sunan Ma'aruff jikinsu har ɓari yake suka fiddosa suna bama su Ummansa haƙuri.
Shine yace a fiddo Samina ma, amma Ummansa tace sai dai itama a nemi iyayenta su fiddata.
Baiko musaba yabi maganar Ummansa suka tafi suka bar Samina a station.
Samina naji tana gani Ma'aruff da ƴan uwansa suka fice suka barta a station ɗin, dukda kasancewarta matarsa ta sunna, su kuma matar ɗan uwansu.
Wani cikin ƴan sandan yaji tausayin Samina, shine yace ta bada Number wani cikin ƴan gidansu a kira.
Rasama tawa zata bada tayi, sai ta basu ta mama gaje, an kira yafi sau biyar bata shigaba, tai shiru tana tunani, ta bada ta Ahmad ne kokuwa ta babanta?.
Wata zuciya tace ki bada ta Baban dai, koba komai mahaifinki ne zai rufa asirinki, amma Ahmad ya samu ƙofar miki dariya ne.
Wannan shawarar tabi tabada ta Baba, bugu biyu kuwa ta shiga.
Kasa magana tai sai ɗan sandan ta bamawa ya sanarma Baba yusha'u halin da Saminar ke ciki, da kuma a inda take............🧐✍�?



*_Jiya wayatace ta zafafani shiyyasa nima na saku a zafi, sai da nagama wahalar typing kusan 2pages sannan komai ya goge, kaina cakewa yay nama rasa mizan sake rubutawa, kawai sai na kunna waƙa naitaji dan takaici😔😏._*





_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 *_38_*


*_BULKUMA🤫_*


...........Baba Yusha'u da baba suka kalli juna, dan a hansfree ya saka wayar tasa, kuma suna tare da baba zau,ne a ƙofar gida.
Takaici ya hana baba Yusha'u magana, ransa a ɓace ya tura wayarsa aljihu yana faɗin, “Wlhy sai dai ta shekara dubu acan�?.
Da kallo kawai baba ya iya binsa, cikin ransa yana tunani to miya kai Saminar police station da aurenta kuma?.
Kansa kawai ya girgiza ya ciro wayarsa daga aljihu ya shiga neman number Ahmad, yanata maimaita sunan station ɗin a ransa dan karya manta.
Ahmad na gida lokacin yana shirin fitowa zasu fita shi da Sufyan kiran baba ya shigo masa, ɗagawa yay cikin girmamawa ya gaishesa.
Baba ya amsa yana faɗin, “Amadu kana inane?�?.
“Baba gani a gida, amma ina shirin fitowa ne�?.
“Yauwa to maza kazo gida ka sameni yanzun nan kaji ko�?.
“To Bana, ALLAH yasa dai lafiya?�?.
“Sai kazo dai�?.

Ahmad dake sanye cikin baƙar shadda daketa maiƙo sabuwa dal ya sauke numfashi kawai, bazamuce mai azabar tsada bace, dai-dai ƙarfin talaka mai abunyi a hannu, shaddar ta masa ƙyau sosai, sai kace wani ɗan masu hannu da shuni, ga ɗinkin da akai mata na zamani ya kuma fidda cikar haibarsa da haska choco fatarsa da jindaɗi ya kuma gogewa har wani ƙyalli-ƙyalli take.
Hula ya ɗauka kalar golden da akai adon gaban rigar da ita ya saka, zuciyarsa sai kuma mamakin kiran baba yake, yana zancen zuci ya ɗauka link ɗin hannun rigar shima golden ya saka sannan ya fesa turare a gurguje yasa wayarsa a aljihu ya fito.
Kausar ce kawai a tsakar gidan tanama ƴarta wanka, tabi Ahmad da kallo harya fice, zuciyarta na mamakin irin wannan ɗaukar wanka da kullum Ahmad keyi sai kace wani ɗan wani da wata, su dai sun saka ido suga shin neman nasa jikinsa kawai yakemawa kokuwa harda Rumana?, dan sudai randa sukaje barka basuga wani sabon abuba daga Rumanan.
Shidai Ahmad da baisan tanaiba yana fita ya hau mashin ɗin Sufyan da yazo dashi, sosai mashin ɗin ya masa ƙyau, duk budurwar data gani dole ta ƙyasa harda masu burin auren mijin novel (🥴😂⛹‍♀).


“ƴammata a kula, wannan garan na anguwarku dake zuwa miki da koɗaɗɗun kaya, babu mota, babu ƴan canji, da kin kama abunki kin riƙe wlhy kece zaki saitashi yafi mijin novels ɗin da kike hange komai, dan mazanmu ba banbanta sukai da mazan novels ba, sunma fisu komai idan baki saniba, bar hangen abinda yake gaibu kama zahiri ki amfana duniyama ta amfana, ƙyalƙyal banza shirmene, ƴammatan wajema sun isheki, dan waɗannan da kike hange masu siffar mazan novels ɗin mafi yawansu a rigane wlhy, babu hali babu tarbiyya, sai ƙalilan daga cikinsu, dan duk inda aka samu na banza to akwai nagari, sannan ko wane namiji da kika gani komin garancinsa yanada izzarsa, dan wannan cikin jinin maza take, saikin saka ido zaki ranfo cikar haiba naki shima, kwarjini, isa, taƙama, harma da tsagwaron sarauta daga jinin gwarzonki, zan faɗa a fili, na faɗa ɓoye, na faɗa da kuwwa, agaban kowa kuma, wlhy mazanmu sunfi mazan novels ɗin da ragwayen zukata ke ɗauka wani abin burin samu, ƴammata harma da wasu matan auren a kula sosai, da rarrafe yaro kan tashi, duk wani mai arziƙi ko shugaba, mafi yawansu da zaki bibiyi tarihinsu sai kinci karo da gwagwarmayar da sukaci a rayuwa kafin sukai ga mtsayin, kema idan kin auri wannan ɗan dakon wataran shine zai biya jirgi ya masa dako, daki auri wanda ya tara gamma ki auri wanda zaku tara tare, ko mata ɗari zai kalla bayanki suke, sannan kimarki a wajensa daban take koda shine shugaban ƙasar Nageria kuwa🤸🏻‍♀🤫, lamarin fa duk bugene😹🤷🏻‍♀️⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀.

A ƙofar gida Ahmad ya iske baba na jiransa, ya kafe mashin ɗin yana nufar wajensa.
Sai da ya durƙusa ya sake gaishesa sannan baba ya faɗa masa abinda ya faru.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login