Showing 21001 words to 24000 words out of 165545 words

Chapter 8 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

360

Samina ne ta ci mata mutunci yanzun nan.
A gabanta Samina taja Fa'iza suka fita, danta rakata ɗakin Ayyah ta duba Ahmad.
Batai yunkurin binsuba, dukda tanason taje tai masa sannu itama.

Sun shiga ɗakin da sallama, Ayyah na tsaye akan Ahmad ita da Iya kakarsu suna lallaɓashi yasha magani, sai kumbura fuska yake tamkar zaiyi kuka.
Iya ta dungure masa kai tana faɗin, “Ragon kawai, ni nama taɓa ganin namiji na tsoron magani inba kai ba Amadu�?.
Sake tsuke fuska yayi yana langabe kai gefe idonsa akan Ayyah dan taji tausayinsa.......
Ayyah zatai magana cikin son yin dariya su Samina sukai sallama, koda suka shigo bai kallesu ba, sai Iya ce tace, “To ai yanzu kasha tunda ga matarka nan ko�?.
Bai tanka ba, sai ruwan dake hannun iya ya amsa tare da watsa sauran maganin hannunsa cikin baki ya matse ido yana tuttula ruwa a baki ya haɗiye da ƙyar.
Yana gama shanyewa kwanciyarsa yayi a gadon Ayyah na karfe yayma kowa banza.
A hakane su Samina sukai masa sannu da jiki, takuma ƙara fahimtar fushi yakeyi da itane da gaske.
Duk kuma sai taji babu daɗi, jikinta yay sanyi sosai, gwiwarta a sanyaye ta fito ta koma ɓangarensu.


_______________________________

Wasa-wasa dai sai da ciwo yaja Ahmad kusan kwana uku, dan daga ciwon kai abu sai ya koma zazzaɓi, har saida yasha ledar ruwa biyu, kullum sai Samina tazo gaishesa, amma baya kulata sam.
A yaran gidan duk wanda sukazo gaisheshi yana amsa musu koda a gabantane, amma ita sai baya kulata.
Duk da abin na mata ciwo sai ta daure ta faɗama Sufyan halin da ake ciki, Sufyan bai tsaya mata rufa-rufa ba ya sanar mata ganin da sukai mata a ƙofar gidan su Inna mari, harma ya nuna mata video din daya ɗauka dan yaga tana neman musa cewar itace.
Laƙwas jikinta yayi, nanfa ta shiga haɗo ƙarya ta shirya masa akan ita bata da alaƙa da Ma'aruff, saurayin ƙawartane Nafy, tayi kuskure amma ya bama Ahmad hakuri akan shiga motar ma'aruff ɗin da tayi.
Dole dai akan wannan magana sai da Sufyan yasaka su zama su uku ya sasantasu, Samina harda kukanta tana bama Ahmad hakuri.
Daga baya bayan masifar da taci a wajensa yace ya hakura.

Tun daga ranar komai ya sake koma musu kamar da, suka cigaba da tattali da soyayyar junansu, yayinda a ɓoye Samina take tare da Ma'aruff, idan yaso su haɗu gidansu Inna mari take zuwa su haɗu a can.


★★★★★★

Ɓangaren yaya Maryam kam babu wanda yasan miya faru, sai ga mijinta har gida yazo yana bama su Baba hakuri akan abinda yake mata, sannan itama ya bata haƙuri da neman afuwarta.

Babu irin tambayar da Ayyah bataima Ahmad ba akan ya sukayi da mijin Maryam ɗin, amma yaƙi faɗa, yace shi babu komai.
Ƙyalesa Ayyah tayi kawai badan ta yarda ba, amma ta fahimci koma minene shine ya aikatashi, kuma ko Maryam ɗinma bata san asalin miya kawo gyara a cikin lamarin auren nata daya nema hargitsewa ba a shekarunnan..

Matsaloli sun sake kunno kai tsakanin Samina da Ahmad, dan ta sake birkice masa ya rasa kanta.
Gashi yanzu abubuwa yake gani a wajenta wanda bashine ya siya mata ba, yasan kuma iyayensu basu da ƙarfin saya matan, dan har waya ta canja, tun tana ɓoye masa har komai ya fito ya ganta da wayar.
Duk iya tuhumar da yay mata kuma taƙi sanar masa gaskiya.
Abinda ke ƙara tada masa hankali kuma da ita sam yanzu batajin shakkarsa balle akai ga tsoro, ƙiri da muzu take masa rashin kunya idan yay mata faɗa akan kuskure.
Dan akan wayar nan daya gani a hannunta sosai rikici ya ɓarke a tsakaninsu har takaisu ga zuwa gaban kakanni, saboda maganar taje wajen iyayensu mata, sukuma suka gumtsawa mazan, daga nan ne kuma su iya sukaji suma, malam Rabi'u kuma ya kira Ahmad ɗin da Samina domin yaji gaskiyar maganar.
Da farko Samina ta musa, amma da taga babanta na neman dukanta a wajen saita faɗi gaskiya.
Ran kowa ya ɓaci ranar a gidan, dan haka take a wajen malam Rabi'u tsoho mai ran ƙarfe ya tsaida watan bikin Ahmad da Samina, a cewarsa ko haya gwara a kama musu su fara zama kafin ALLAH ya hore asan abinyi.
Kowa yaji daɗin yanke hukuncin da Malam yayi, dan kuwa kusa aka saka bikin, wata biyu kacal, lokacin Samina ta gama exam ɗinta, a cewar malam taje gidan mijinta ta ƙarasa karatun, tunda dama shine ya nace akan sai tayi
Wannan abu ya mugun tada hankalin mama gaje da Samina, dan zuwa yanzu dai gaba ɗaya tunaninsu ya karkatane ga Ma'aruff dake kashema Samina kuɗi tamkar baisan ciwonsu ba.
Ahmad kuwa ji yake kamar an masa rahama, dan sakayau ya jisa, shi kansa dama a buƙace yake da auren ainun, saboda muguwar sha'awar da ya fahimci yana da ita akan abokiyar halittarsa............✍�?


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*(8)*

............Sosai hankalin mama gaje da Samina yake a tashe, tunda suka baro sashen su Baba Rabi'u sai suka kasa zaune suka kasa tsaye.
Samina da ke share hawaye tace, “Wlhy mama bana sonshi yanzu, kinajifa wai ɗakin haya ɗaya za'a kama a ajiyeni kafin komai ya warware? Har sai yaushene komai ɗin zai warware a garesu baki ɗaya, tunda muka dawo rayuwar gidannan a talakawansu muka iskesu, shekara kusan goma sha takwas basuyi arziƙiba sai yanzu da za'a cuceni za'ace zaizo, wlhy nama kula danginmu ƙashin tsiyane dasu, shiyyasa duk wanda sukaga ALLAH zai ɗaukaka sai su nema dakushesa, kaf yaran gidannan da sukai aure tunda kan su yaya Maryam har zuwa su yaya Binta waccece ba'a cikin wahalar rayuwaba?, kowacce matsalolin fatara da babu sun gama isar rayuwarta, duk sun lalace sun zama wasu tsofaffi sa'anninku, babu wata mai gidan nunama sa'a a cikinsu. Mama kinga kuwa gidan Ma'aruff inda zai ajiyeni, wlhy ko za'a haɗa kaf dukiyar ahalinmu bazata sayi wannan gidanba, na rantse da ALLAH ko sama da ƙasa zata haɗe bazan zauna da Ahmad ba, inba hakaba kuwa ALLAH guduwa zanyi daga gidannan......�?
“Ki gudu ina? Babu inda zakije yarinyata, dolene ko sunaso ko basaso su baki wanda kikeso, dan koni ban amince ki rayu da Ahmad ba, yaron da ko rigar sakawa ta kirki baida ita, ki kwantar da hankalinki duk nasan maganinsu, ni warkice dai-dai da ƙugun kowanne shege wlhy, iyakaci dai suce ya miki wahala ko? To su faɗi duk abinda yay miki za'a biyashi, dan sune matsiyata�?.
Samina dake shashshekar kuka tace, “Yo mama dukkan wahalarma da yaymin ɗin ta nawace? Wlhy nasan ko Ma'aruff yaji saiya ninka masa ma abinda ya kashemin ɗin�?.
Tsaki mai ƙarfi Mama Gaje ta ja tana yin ƙwafa, ji take a ranta koda aurenta zai sake mutuwa bazata yarda Samina ta auri Ahmad ba, dan tasan ko barin gidannan tayi akan auren Samina da Ma'aruff gaba zataci ba bayaba, tunda da dai zasu jiƙe da naira ne.

Duk surutan da Mama Gaje keyi ita da Samina a kunnen Baba Yusha'u ne dake alwala a tsakar gida, amma sai ya nuna tamkarma bai jiba, ya ajiye butar hannunsa ya fita.
Ammi ma duk a kunnenta komai ya faru, amma saitayi kamar batasan anaiba, da dai ita ba kishiyar uwa bace data basu shawara akan suyi haƙuri kar son zuciya ya kwashesu suyi GUDU DA WAIWAYE.......

A tsaitsaye Baba Yusha'u ya shiga sashen iyayensa shi da baba Iliyasu, sun ɗanyi magana suka fito a tare riƙe da malam Rabi'u zuwa massalaci, inda acan suka iske baba Hamza ma, yayi mamakin ganin Malam a massalaci yau, dan sam baya iyawa, yakai kusan wata huɗu ma ko waje bai leƙoba, dan ya tsufa sosai.
Salla aka tayar, bayan an idar mutane na niyyar fita Malam Rabi'u ya saka baba liman roƙon alfarmar su dakata.
Babu musu akaita dawowa, ciki kuwa harda Ahmad da abokansa, shima yayi mamakin ganin kakan nasu a masallaci, jira yake kawai su fito ya tambaya.
Mamaki ya sake kamashi jin liman ya ambaci cewar Malam ne yace jama'a suyi masa alfarmar tsayawa.
Abu tamkar daga sama yaji ana ɗaura aurensa da Saminar sa, mutuwar zaune yayi a wajen, duk taɓashin da abokansa sukeyi na alamar tambaya da taya murna bai iya kula kowaba, bayan an kammala ɗaurin auren jama'a suka shiga zuwa bashi hannu suna tayashi murna, hannun kawai yake iya miƙa musu yana amsawa da amin a saman laɓɓa, amma a zahirin gaskiya baya tare da duniyarsu sam.

Falalu ƙanin Samina da suke uba ɗaya, wato ɗan ɗakin su Umm-Rumana ne ya shiga gidansu da zancen ɗaurin auren.
Babu shiri Samina dake ban ɗaki tana wanka tajawo zani ba tare data ɗauraye kumfar jikinta ba ta fito kamar wata taɓaɓɓiya tana faɗin, “Kai Falalu ubanmi naji kake cewa?�?.
Yaron yaɗansha jinin jikinsa, hakanne ya sakashi haɗiye murnar da yakeyi yana komawa bayan Amminsu ya ɓuya, Samina ta daka masa tsawa tana sake tambayarsa abinda ya faɗa.
A dai-dai lokaccinne Mama gaje tayo waje itama daga ɗaki, dan da salla takeyi, saboda sauri har tuntuɓe tayi, kaɗan ya ragema ta faɗi ta dai samu ta riƙe ƙarfen barandarsu.
Falalu dake a laɓe bayan Ammi da tai tsayuwar sojan badakkare yace, “Ai dai malam ne ya ɗaura miki aure da Yah Ahmad yanzu a massalac.......�?
Wani ihu Samina ta kurma tana buga tsalle ta dire ƙasa, sai gata wanwar a sume zani a gefe.
Jikin Umm-Rumana na rawa taja Zanin gadon Ammi dake a kan igiyar shanya ta yafama Samina saboda tsirara take.
A lokacinne kuma iyayensu maza duk suka shigo, harma dasu Ayyah da matan Baba Iliyasu, dan casuke wani abunne ya faru da Saminar.
Ahmad ma da Mudanseer sai gasu sun shigo, nanfa kowa ya rufu akan Samina, yayinda Mama Gaje keta kuka akan bazata yardaba idan ƴarta ta mutu, tunda tace batason auren miyyasa zasuyi?.
Kalaman mama gaje sun fahimtar da kowa daga ina matsalar take, hakan yasa Gwaggo zare jikinta tabar sashen ganin an zubama Samina ruwa ta kawo numfashi.
Samina dake hawaye ta fara sakin sambatu, “Wlhy kozaku haɗa wuta ku sakani bazan zauna da Ahmad ba, nace bana sonshi, na rantse da ALLAH sai ya sakeni, inba hakaba kasheshi zanyi, wlhy saina yankashi da wuƙa idan kuka matsa saina zauna dashi, randa aka kaini a ranar zan kashesa, garama na ƙare rayuwata a prison da na zauna zaman aure dashi�?.
Da sauri Baba Yusha'u ya buge bakin Samina, ya kuma kai hannu zai doketa Baba Hamza ya riƙe hannun yana girgiza masa kai.
Daga ƙarshema sai yaja hannunsa suka fice, baba Iliyasu na biye dasu.
Mudanseer da zuciya tazo masa kusa ya nuna Samina yana zagi, “Banza kawai mara tunani, to dan uwarki saiki tashi ki kashesa ga shinan, butulu kawai mai manta alkairi, kwaɗayayya mara tarbiyya, idan kika kuma zagin Yah Ahmad a wajennan wlhy kafin ki kasheshin ni saina kasheki dan uwark.......�?
Jan Hannun Mudanseer Ayyah tayi tana share hawaye, “Kaga ya isa haka Mudanseer, idan ita bata da hankali kaima baka da shine? Kunga ku wuce muje�? tai maganar tana jan Hannun Ahmad dake tsaye kawai yana kallon kowa kamar ya samu TV.

Koda suka koma sashensu ma zama kawai yay ya dukar da kansa ƙasa yana kallon sumintin ƙofar ɗakin iyayen nasa, yayinda Mudanseer da Abu keta zage-zage Fa'iza da Zainab na tayasu, Sadiya ko tanada sanyin hali tamkar su Ahmad, sai tayi shiru kawai tana share hawaye.
Gwaggo kuwa ai saikama rantse batasan mi ake yi a gidanba, sai aikinta take kamar komai bai dameta ba, nanko jin zuciyarta kawai take tana tsitstsinkewa kamar zata faɗo ƙasa dan damuwa.

Cikin lokaci ƙanƙani gidan ya harziƙe, dan bakin Samina bai mutuba sai da baba Iliyasu ya lakaɗa mata dukan kawo wuƙa, tai tiɓis ɗin da ko yatsa bata iya ɗagawa.
Mama gaje kuwa ta fasa kuka da kururuwar za'a kashe mata ƴa.
Kafin kace kwabo labari ya fara fitowa a anguwa, dan duk maƙwafta najin abinda ke faruwa.



________________________________

Yanda Samina ke ambaton ƙiyyar Ahmad a bakinta abun na bama kowa mamaki, duk da dai an fahimci harda ruɗin ƙyale-ƙyalen duniya ke kwasarta, amma tabbas akwai zuga dake aiki akanta, bakuma kowa bane ke zugata sai mahaifiyarta Mama gaje, saiko Inna mari kakarta da itama tai ɗare-ɗare a zancen, gefe kuma gasu Nafy sunayi ta waya da zahiri idan sunzo gidan da ƙaryar dubata.
Dan dukan da baba Iliyasu yay mata ciwo sosai ya sakata, ko magana mai ƙarfi ta kasa yi.
Kuma Ahmad ɗin dai da bakinta bai gajiya da munanawane ya samo likita ya dubata, ƴan kuɗin dake aljihunsa na ɗinki da aka biyasa ya cire ya biya kudin magani dama duk abinda aka buƙata.
Tun anama Samina mazurai har iyayenta maza da Amma suka koma lallashinta dukdan ta kwantar da hankalinta ta fahimci halin da ake ciki.
Sai dai sam taƙi fahimta ɗin.

★★★★�?

Tsahon kwana huɗu abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, saima neman ɗakin da zasu zauna haya akeyi.
Ahmad kuwa yaƙi cewa kowa komai, sai bushewa yake a tsaye saboda damuwa, harya fara duhun baƙi, gashi abun na neman taɓa masa aikinsa na ɗinki, dan yanzu ya daina yin komai sai tunani.
Wanka wannan sai Ayyah ta sakashi a gaba yakeyi, hakama abinci sam bayason ci sai an masa faɗa.
Yana ƙaunar Samina sosai, duk wannan haukar cin mutuncinsa da takeyi bama yajin haushinta, a ganinsa canja masa ita akai kawai, dan Saminar sa ba haka takeba da can.
Gashi duk yanda yaso su haɗu taƙi bada ƙofar hakan, duk sanda ya aika a kirata zagi ma take maido masa, idonta ya rufe gaba ɗaya, burinta kawai Ahmad yay zuciya ya saketa.

Yau data kasance duk yaran gidan na ma'auri sunzo gidan akan wannan maganar aure data bama kowa mamaki, masoya sun zama maƙiya, wanene a anguwar baisan soyayyar Samina da Ahmad ba, sai dai baƙon da bai wuce sati ɗaya ba.
Binta yayar Samina ta kalli Saminar dake kwance a saman gadon Mama Gaje tana sharɓar hawaye, ga zazzaɓi daya rufeta saboda ƙuntata kanta da takeyi a kwanakinnan.
“Humm anya Samina kina ganin kuwa kinma kanki adalci a wannan gaɓar? Anya kuwa kece Samina ƙanwata dana sani mai tsantsar ƙaunar Yah Ahmad. Mike ruɗaki hakane kike son tafka babban kuskuren da anan gaba baki da hanyar gyarashi? Miya shiga kankine? Samina kibar biyema mama wlhy, dan daga ita har Inna mari babu mai faɗa miki gaskiya akan batunnan, kwaɗayi ya rufe muku ido ku duka, kun manta UBANGIJI dake bayarwa bai manta da shi yah Ahmad ɗinba, sannan kuma aiba ALLAH ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login