Showing 153001 words to 156000 words out of 165545 words

Chapter 52 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

392

Koda suka isa gidan Maman Ma'aruff taci karo da Inna mari bayan sunyi sallama ta fito dan taga wanene sai cewa tai “Yauwa yallaɓai ga kakarta nan, ku haɗa da ita�?.
Inna mari na tambayar ba'asi aka cukuykuyeta zuwa cikin motar ƴan sanda, sannan suka kutsa kai suka tattaro Mama gaje dake tsakar gida zaune zataci abinci, iya kuwa ta fita sayo waken ƙosanta na gobe.
Itama dai kwasarta sukai sai cikin mota, duk da roƙon da take musu da tambaya sunƙi saurarenta.

Babu tausayi babu imani mahaifin Mufida yasa aka jibgi su Inna mari duk da tsufanta, sai da sukai musu lilis sannan suka barsu.
Iya na dawowa ƴan anguwa suka sanar mata abinda ya faru, nan take ta rikice tahau kuka, ta saka aka kira mata ƴarta a waya ta sanar mata komai, hankalinta tashe tazo gidan ita da mijinta, haka suka bazama neman station ɗin da aka kai su mama gaje tare da ƙanin mama gajen shima isa, amma basu samuba har dare, dole suka dawo gida.
Washe garima haka sun fita bin stations suna tambaya, amma duk inda sukaje sai ace ba nanbane, har inda aka kai su inna mari sunje amma ance ba nan bane, a kwana na huɗu sukaga abin yafi ƙarfinsu sukaje suka faɗa gidansu Ahmad.
Shi Mudan ma ya manta da anyi abun, dan bai sanarma kowaba, koda suka dawo daga Shema, sai randa su Iya sukazo.
Kai tsaye Baba Yusha'u yace shikam babu ruwansa, dan baida alaƙa dasu yanzu kam.
Baba Hamza ne ya tsawatar masa akan wannan furuci, ta ya zaice baida alaƙa da mama gaje bayan gasu binta, dole Baba Yusha'u yay shiru.
ALLAH sarki Baba Hamza, haka ya tasa ƙeyar Madan gaba akan suje su bincika suma, su Iya kuma suje gida su huta, amma sai sukace karya damu suje taren kawai.
Da farko Mudan yaso yin yawo da hankalinsu, to amma da ya tuna dashi za'asha wahalar, ga kuma dinkuna jibge a shago suna jiransa ga zuwa makaranta sai kai tsaye ya rakasu station ɗin da yake da tabbacin su Mama gaje nacan, amma a zuwan dai bashi da tabbas dan kar baba yaci ƙaniyarsa.
Suna isa kuwa suka iske maman Ma'aruff a wajen.

Su baba sunsha wahala kafin a basu su inna Mari, dan sai da ya saka Mudan ya kira Ahmad a waya suka haɗashi da d.p.o din wajen, baisan mi Ahmad ɗin ya faɗa ma d.p.o ɗinba ya yarda, kuma da yake shi baba tare sukazo a wancan lokacin da aka rufe Samina akan faɗansu da Basy sai d.p.o ɗin ya sake aminta da maganar da sukai da Ahmad, nan take ya bada belin su Mama gaje.
Hankalin su Baba ya tashi ganin yanda aka fiddo su Inna mari, jiyay ƙwalla sun cika masa idanu, harya kasa haƙuri sai dai yayma dpo ɗin ƙorafin irin wannan duka da sukaima mata haka, matanma tsoffi kamar waɗannan, musamman ma Inna Mari.
Dpo yayta bama Baba haƙuri akan wlhy shi bayanan komai ya faru, hasalima baisan halin da su Inna Mari sukeba sai yanzu, yay taima ƴansandan da sukai abin faɗa tamkar zai cinyesu ɗanyu.
Su dai su baba sun kwashi su mama gaje zuwa asibiti kamar yanda Mudan ya bada shawara, dan tausayi suka koma bashi, harma yay dana sanin bai tura ƴan sandan can gidanba.

A asibiti sosai su Inna mari sukaji ciwuka, gashi duk sun galabaita, dole dai aka basu gado, tare da taimakon gaggawa, komai Mudan ne ya biya na asibitin, dan sai da aljihunsa yay kankat harya haɗa da cin bashi.
An kwantar dasu tsahon kwana uku kafin a basu sallama.
Daga Mama gaje har inna mari sunsha kuka bisa wannan tashin hankali, dan tun daga wannan lokacinma dai Inna mari lafiya ta gagareta, sai da ta kaita da kwanciya cutar ajali, haka zataita rusar kuka da sambatu, tare da kiran sunan Samina ta yafe mata, sai dai ina Samina batajinta, hasalima tana ɗaya daga cikin waɗanda Saminar tafi tsana a yanzun a duniya.
Takai kusan watanni uku tana jiyya ALLAH yay mata rasuwa.
Wannan mutuwa ce ta kuma susuta mama gaje, lamarin da ake tunani na taɓuwar hankali ya sake bayyana a gareta, dan itama haka kawai saita kama surutai, kokuma tai zaune jugum ba im ba im-im, saita haɗa kwana biyu bataima wani magana ba, komai sai dai tayita binsa da idanu.
A lokacin Ahmad har waya yasa aka bata yay mata gaisuwa, sai dai ko Umm-Ruman bai sanarma rasuwarba, dan tana fama da laulayin cikin Abu-Talib lokacin.


Ɓangaren su Ma'aruff kuwa sai komai ya koma yay lif, dan mahaifin Mufida ya fahimci bazasu sami abinda sukeso ga Ma'ruff ta wannan hanyarba, dole ya tirsasa Mufida ta koma lallaɓa Ma'aruff.
Sai dai lallaɓawar sam batai amfaniba, dan shan giyar da yake ta kuma ɓaci sosai, Har takai hantarsa ta taɓu ba tare da kowa ya saniba, a tsaitsaye ya fara ciwo tamkar wasa, tun yana ɗaukar lamarib ba komaiba har abun ya kaisa ga kwanciya, dukda mufida tasan baida lafiya taƙi faɗama mamansa ta kuma ƙi taimakonsa zuwa asibiti, saima takurama rayuwarsa da tai da batun ɗakko takardun nan.
Jikin Ma'aruff yayi matuƙaryin tsamari, har takai ranar ya gaza a yin komai yana ɗaki kwance rijib, yanaji wayarsa na ring tunda farar safiya amma ya kasa ɗauka ya duba wanene mai kiran, gashi sam baiji koda motsin Afrah ba a gidan balle na Mufida.
Hawaye masu zafi suka gangaro masa a kumatu, inda zai iya da tuni ya ɗauki wayarnan ya kira Mominsu ya shaida mata halin da yake ciki ko zai damu taimako daga garesu.
Har kusan azhar babu motsin Mufida, hakanne ya tabbatar masa bama ta gidan, koma bata kwana a cikinsaba, dan tun jiya da magriba dama yaji kamar motsin fitarta, daga nan bai sake jinta ba, to duk zatonsa kodan yayi barci da wurine harta dawo bai saniba, sai dai zuwa yanzukam yaji a ransama bata dawo ba tun jiyan.
Jiyo knocking ƙofar da ake da ɗan ƙarfine ya katse masa tunaninsa, dagaji dai ba bugune na lafiya ba, gashi duk yanda yaso tashi ya gaza hakan, kuma yana tunanin Mufida kullesa tayi....
Bai kai ƙarshen tunaninsaba ya jiyo maganar mai gadi sama-sama yana faɗi musu anya kuwa yana nan?.
Sai kuma ya jiyo maganar Mominsu kamar tana kuka, ya rimtse idanunsa zuciyarsa na sake salon bugu, dan kuwa dai tabbas yaji a jikinsa babu lafiya......
Maganar ƙanwarsa data zagayo ta bayan Window ɗin ɗakinsace ta sakashi jin sassauci, ta shiga sallallami ganinsa kwance a gado da alamar yana cikin mawuyacin haline, da gudu tabar wajen tana ƙwala kiran sunan mominsu da tabbatar musu yana ciki kwance.
Nan take suka fara ƙoƙarin ɓalle ƙifar, cikin amincin ALLAH suka sami nasara da taimakon baba mai gadi.

Yanda suka shigo suka iske Ma'aruff ya kuma birkita dukkanin tunaninsu, suka shiga share hawaye da jera masa tambayoyi, sai dai bai iya basu amsar ko guda ɗayaba shima, sai binsu da kallon tsoro yake ganinsu duk da raunuka a jiki an liƙe da bandeji.
Babu maganar jan dogon zance sukai ƙoƙarin cewa a kaisa asibiti, duk da sunsan basu da ko sisin kwabo tare dasu, amma suna tunanin shi ƙila a samu wani abu a accaunt ɗinsa tunda da alama su Mufida basu taɓa komai na nan gidanba.
Ramar da yayice ta saka suka iya ɗakkosa su uku ba tare da sunji wani uban nauyiba sam, suna shirin sakashi a motane wata motar tai hon, hakan yasa Momi cewa maigadi yaje ya buɗe gate yaga wanene?.
Babu jimawa sai ga baba maigadi ya dawo a kiɗime, momi ta shiga tambayarsa ko lafiya?.
Yace, “Hajiya wlhy wai wasune sukazo suke maganar nan gidansu ne�?.
Cikin matuƙar razani ƙannen Ma'aruff da Mominsu sukace, “Gidansu kuma?!�?.
“Wlhy kuwa hajiya, gasu nanma zasu shigo......�?
Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu har mutanen suka ƙaraso, sai wani cika suke da batsewa.
Su dai su Momi sun zuba musu idanu kawai.
Ɗaya a cikinsu ne ya fara bayani ko gaisuwa babu balle lura da halin da Ma'aruff yake ciki baiyiba, “Hajiya mune waɗanda suka sayi gidannan, kuma hajiyar da suka sayar mana sun tabbatar mana kafin muzo kun tashi, amma kuma sai gashi mun iske saɓanin hakan�?.
Baki buɗe duk suke kallonsu, cikin ƙannen Ma'aruff ɗaya ta samu baki faɗin, “Hajiya kuma? Wace hajiyace ta saida muku gidan bayan ga mai gidan nan shi baisan anyiba?�?.
Kallon juna sukai suma, ɗaya yace, “Bamu gane mi kuke nufiba?, to mudai Hajiya mufida sunanta, kuma ita da Mahaifinta suka kawomu mukaga gidan sati uku da suka shige, tun a ranar muka biyasu rabin kuɗin, jiya kuma muka cikasa biyasu sauran suka bamu takardun gida yau ɗinnan da safe�?.
Baya kawai momi tai ta yanke jiki ta faɗi a sume, nan take hayaniya ta kaure.
Ma'aruff ya amshi takardun daƙyar ya duba, tabbas takardun gidanne, to amma a garin yaya sukaje hannun su Mufida bayan yasan suna gidan momi?.
Bai samu amsaba saboda tashin hankalin da suke ciki, masu gida kuwa sallama sukai musu suka tafi akan sun basu nanda sati guda su kwashe komansu su basu gidansu suna bukata.
Babu wanda yabi ta kansu, dan suna a ruɗanin da baki bazai iya furtawaba sam.


★★★★�?

An karɓi su Ma'aruff cikin gaggawa saboda asibitin su Adam sukaje, hankalin Adam yayi masifar tashi da ganin halin da Ma'aruff yake ciki, ya kwana biyu basu haɗuba saboda shima aiki yay masa yawa a tsakanin nan.
An samu damar ceto rayuwar mamansu Ma'aruff da hawan jini ya nema saka zuciyarta bugawa, yanayin da take na firgici yasa dole akai mata allurar barci danta samu hutu.
Ma'aruff kam gwaje-gwaje aka shiga masa, bayan bincike mai zurfi aka gano hantarsa tayi masifar kamuwa da ciwo harta harbi ƙodarsa, ba komaine ya jawo hakanba gareshi sai giyar da ya maida ruwa🤦🏻‍♀�? .
Hankalin ƴan uwansa ya kuma tashi kololuwa, basusan yanda zasu fassara wannan tsakaninba a rayuwarsu, a daren jiya ƴan fashi sukai musu dirar mikiya a gida bisa jagirancin mahaifin Mufida da ƙiri da muzu babu kunyar ALLAH yazo musu a zahirinsa, bayan ya gama zayyane musu komai dangane da burinsa a kansu tare da zage momi tas sannan suka ƙwace komai, dukkanin takardun company ɗinsu da dukkanin na kaddarorinsu, ya kuma saka akai musu dukan tsiya, dukan da yay tunanin momi ta mutune suka fice suka barsu.
Sai dai da yake shi rai a hannun ALLAH yake ba wani shegeba, sai ALLAH yasa babu wanda yama samu wani mummunan rauni, sai dai sumar da sukai da kuma ciwuka da targaɗe ga wasunsu.
Da taimakon ma'aikatan gidan aka kaisu asibiti tun a daren, shinefa aketa kiran Ma'aruff bai amsaba, hankalin momi ya tashi ta matsa sai tazo ta ganshi duk da tana cikin halin rashin jin daɗin jiki, amma tana tsoron kar shima su Mufida sun masa wani mummunan abun, shinefa sukazo suka iske wannan musibar kuma ta saida gidan Ma'aruff din dasu Mufida sukayi da halin ciwo da yake a ciki.


*_MAI RABON SHAN DUKA, BAYAJIN ƘWAƁO SAI YA SHA_*

Dolene a kira ahalin Ma'aruff da wannan kalma, dan itace dai-dai da yanayin da suka tsinci kansu a ciki a halin yanzun kam.
Lokacin da duniya ke kai masa babu wanda ya isa faɗa masa giya nada illa ga ɗan adam, yasha faɗama Samina cewar kuɗinsane, jikinsane, sannan ra'ayinsane, sai gashi itama giyar kuwa da dukiyar sun tabbatar masa da su lokacine dasu, sannan shi komai a rayuwa da bawa yakeji dashi wata rana labarine, (watarana ma masu labarin baza'a samuba inji babana😭, haka yakansha faɗa mana cewar duniya labari, watarana masu labarin babusu😭😭🙏🏻, ya rabbi ka gafarta masa da dukkan waɗanda suka rigamu kwanta dama).
Momi dake ganin Samina bata dace da rayuwar ɗantaba saboda ɗiyar talakawace ita, shiyyasa ta aura masa ɗiyar ɗan uwanta wanda batasan shaho bane a gareta, ya daɗe cikin shawagin ganin ya ɗauke dukkan wani jin daɗinta, ga samako nan ya biyo baya wanda ya dace da ita.
Duk tsiyar da Ma'aruff ke aikatawa ta shaye-shaye da lalata ƴaƴan jama'a sarai ta sani, kuma tanaji tana gani amma soyayyarsa ta rufe mata ido ta kasa ƙwaɓarsa saboda karta ɓata masa rai ko makamcin hakan.
Gashi yau babu dukiyar, babu lafiyar, babu komai da suke tunƙahon dashi ko taƙamar, komai ya ƙare, komai ya lalace tamkarma ba'a tarasuba.

Kwanansu Ma'aruff uku a asibiti mummunan al'amari ya sake zuwa garesu, dan kuwa dai ƴamfashin da baban mufida yasa sukazo suka ƙwace komai nasu Momin, shima sun ƙwace komai daya amsa saboda yaƙi biyansu kamar yanda yay musu alƙawari, shinefa suka bishi har hanyar birnin ikkon daya fece wato legas, suka ƙwace komai sannan suka saka tirela tabi takan motar da suke ciki.
Babu wanda ya shura kaf ɗinsu, Baban mufida, mamanta, ƙannenta mata biyu da namijin daya fidda video ɗinan nasu Samina, sai Mufida da Afrah.
Wannan tashin hankalin gawarwaki da Momin ma'aruff ta gani na ahalin ɗan uwanta ya saka jininta ya sake ƙololuwar hawar da ɓarin jikinta ya dakata da aiki.
Saiga Ma'aruff na kuka rurus tamkar wani mace, ƴar ɗiyar ƙwaya ɗaya daya haifa a duniya ya ƙwallafama rai ta tafi ta barshi, ya tuna sanda Samina ke roƙonsa akan karsu zubar mata da ciki amma sukaƙi saurarenta, ya tuna ƴammatan daya saka aka zubarma ciki duk dan gudun karya haifi ɗan shege.
Kuka yake tamkar ransa zai fita, Adam yana lallashinsa, amma ina bama yajin wannan lallashin, sambatu kawai yake da fallasa sirrin abubuwan daya aikata a rayuwarsa ta baya lokacin kudi nakai masa, ga ƙyau, ga lokaci, ga ƙuruciya, ga dama duk shi kaɗai.
Ko a mafarkinsa bai taɓa tunanin riskar irin wannan ranarba, kai kodama kwatankwacinta, gani yake tunda ALLAH ya basu bazasu taɓa zuwa ƙasaba har gaban abadan, komai zai cigaba da zama bazasu rasaba.

★★★★�?

Haka rayuwa taci gaba da tafiya Ma'aruff da momi suka cigaba da jinya, tun suna asibiti ana kula dasu har aka tattarasu aka maida gidan, dan Adam ɗinma dake taimakonsu yaji nauyin yamasa yawa dan haka ya sahilema kansa.
Basu da komai sai gidan dasu Momi suke ciki, anan suka cigaba da zama cikin yanayin rayuwa mai tsanani, ƴan aikin gidan duk sun gudu, matsin rayuwa da abinda Ma'aruff ya shukama ƴaƴan wasu ALLAH ya jarabci ƙannensa suma da tsintar kansu a wani mummunan hali, dan kuwa ƙiri da muzu sun zama karuwan cikin gida, saima sun fitane zasu samo musu na abinci, lokacin da Ma'aruff ya fahimci halin da ƙannensa suke ciki yayi baƙinciki mai tsanani, yayi kuka yayi nadama mai yawa akan lalata rayuwar ƴaƴan jama'a da yayi, yakuma tabbatar da ita wannan rayuwar idan ka cutar da wani yanzu tun a duniya ake fara ganin sakamako bama sai an mutuba.
Haka suka cigaba da rayuwa komai na ƙara lalacewa da taɓarɓarewa har tsahon waɗanan shekaru, duk wanda yasan Ma'aruff a yanzu ya gansa bazai yarda shineba, yayi baƙi ainun, ga cikinsa yawani zama ƙato, haka zakaga wani lokacin yayi wata mahaukaciyar kumbura tamkar za'a taɓashi ya fashe, wani lokacin kuma sai kaga yaɗan sauka, lamarin abin tausayi da matuƙar tashin hankali.
Itama dai Momi tanata fama, da kuma ALLAH ya kawo iyakar abin a wani daren lahadi ta amsa kiran UBANGIJIN al'arshi.
Su Ma'aruff sunsha kuka sosai, har shima jikinsa yaso ruɗewa.
Wannan mutuwarce ta girgiza ƙannensa sukace aure zasuyi, ALLAH kuma ya taimakesu suka samu mazan auren a hannu, duk da basu kai yanda sukai fataba, dan inda a dacan bayanema sukazo sukace suna sonsu tabbas zamasu iya cewa zasu halakasu, dan ko ƴan aikin gidansu basu kaiba.
Amma halin rayuwa yau sai gasu matsayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login