Showing 141001 words to 144000 words out of 165545 words

Chapter 48 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

401

a make Ma'aruff yake sai ƙwalwar kansa ta bashi wani abu daban, tun a daren ya fara dukanta sai dai abun bai nisaba ta gudu bayi ta ɓuya, shine ALLAH ya taƙaita abun.
Da safe kuma bata fitoba har yabar gidan, ya kumaje ya yini da abun a ransa ko a office ɗinma, shinefa yana dawowa abinci kawai yaci a sashen Mufida yanufo sashen Saminar ɗauke da yarinyarsa da Mufida ta haifa masa.
Sai kuma gashi ya taki babbar sa'ar isketa a falo kwance tana tunanin Ahmad da ayanzu ya zamemata abokin rayuwa.
Ganin yana cikin hankalinsa yasa tai tsamanin babu abinda zai faru, sai dai ina, batasan a yanzunnema zai farunba.
Basu yarda ta ɗaukar musu yarinya, dan haka yanzuma kallo ɗaya tai musu shida ƴar tashi ta ɗauke kanta, sai dai tambayar daya jeho mata makamanciyar ta jiya ya sata tashi zaune a rikice.
Tun ana zancen da fatar baki har takai ya ajiye yarinyar ya maƙure Samina, dan ya tabbatar mata idan bata sanar masa dawa take tarayyaba sai ya halakata.
Tashin hankalin da Samina take cikine ya sata birkice masa itama, yana kai mata duka tana ramawa, kafin kace kwabo sun kaure.
Sosai hayaniyarsu ta kaure gidan, a kuma lokacin ne Afrah ta rarrafa zuwa ga wata kwalbar ruwan lalle da Samina ta ajiye gefen kujera ta ɗauka ta saka a baki, sunata danben bala'i itako tana wasa da ita har ALLAH ya bata nasarar buɗewa ta juye ruwan cikin bakinta ta shanye.

Mufida duk tana sashenta tanajin wannan bala'i, sai kwasar dariya takeyi, daga ƙarshe ta fito da nufin zuwa tasha kallon zahiri baji da kunneba, sai dai ta iske kallon zahiri kuwa wanda batai zatoba ko tsammani.
Dan daidai baby Afrah na shure-shuren mutuwa ne ga dafara na fita a bakinta fara tas ta kumfa, ihun da ya dawo da hankalin Ma'aruff da Samina ta ƙwala tana nufar Afrah, suma duk sai suka kalli wajen.
Ma'aruff shima ya isa da gudu suna jijjiga Afrah tare da Mufida, daga ƙarshe dai ya fisge yarinyar ya fita da gudu da ita waje, Mufida da Samina suka take masa baya a matukar tashin hankali.


*_RUBUTACCIYAR ƘADDARA_*

Tabbas wannan yanayi ya cancanci a kirashi da suna Rubutacciyar ƙaddarar Samina, dan kuwa bayan ankai Afrah Asibiti, likitoci na amsarta mufida na kuka ta kira ƴan sanda akan bazata yardaba Samina ce tai yunƙurin kashe mata ɗiya, mai makon Ma'aruff da yasan gaskiyar lamari ya hanata, tunda dagashi har Samina basusan mi Afrah taci ba ko yay sanadin shigarta wannan hali, sai yay shiru Mufida ta kira ƴan sandan.
Samina na gida cikin matuƙar tashin hankali, dan basu bari ta biyosu ba, bayan tafiyarsune kuma ta fahimci abinda Afrah tasha ɗin.
Ƙaddarar dake biye da ita ta sakata ɗauke kwalbar ruwan lallen tasa a shara tare da goge wajen wai dan kar Mufida ta juya abun kota zargeta🤦🏻‍♀.
Batasan hakan datai shine babban kuskuren data tafkaba a rayuwarta kuwa.
Dan tana kammalawa babu jimawa sai ga Mufida da ƴan sanda, basu wani tsaya jan zanceba suka wuce da Samina tana kuka da rantsuwa akan ita ba ita ta aikataba.
Sai dai sunƙi saurarenta, haka suka wuce da ita station.
Kafin aɗauki dogon lokaci kuma magana ta fara baje dangi, har gidansu Samina takai.
Babu kuma mai faɗin gaskiyar lamari sai cewa ake Samina ta bama ɗiyar kishiyarta fiya-fiya ta mutu saboda ita tana baƙin cikin bata haihuba.

A asibiti kuma babu wani bayani dangane da jikin Afrah daga likitoci, sunata dai shigi da fici ɗakin da aka kwantar da yarinyar saboda Adam da ya tsaya tsayin daka akan komi...............✍�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻


............Komai ya hargitse, gaskiya ta gaza fita a bakunan mutane, kowanne furuci ya fito na zargin Samina ne kai tsaye.
Ca ake bata ɗauki ranta a bakin komaiba ita kanta dama, dan ta taɓa shan fiya-fiyan shiyyasa yanzu ma ta bama ƴar mijinta.
Mama gaje ta koma tamkar ƙaramar mahaukaciya, hakama inna mari, ga baba Yusha'u yace babu hannunsa a ciki, Babansu Ahmad da Mudanseer ne keta shigi da fici station ɗin amma ko ganin Samina an hana misu, dan ƴan sanda sunci kuɗi sunyi haniƙan wajen Mufida data sake ɗaure komai da wasu zantuttukan, Ma'aruff kuma ya gaza kare Samina ko sau ɗaya.
Afrah bata mutuba, amma yarinyar na cikin mawuyacin hali, harma takai sai an mata aiki a ciki saboda ɓannar da ruwan lallen yay mata a wani sashe na kayan hanjinta.
Yanzu ana maganar shiga kotune, dan haka akace su baba suje kawai su nema lauya😢.


*_YARO TSAYA MATSAYINKA, KADA ZANCEN ƳAN DUNIYA YA RUƊEKA_*

Wannan kalma itace dai-dai da abinda ya dace a ambatama Samina ko zata zamo mai tuna mata baya.
Dan kuwa a yanzu babu mai goyon bayanta, kowa ALLAH wadai yake furtawa a gareta tareda bada shaidar munanan halayyarta, abun mamaki dukkan iskancin da sukayi da Ma'aruff saiga zantuka nata fitowa.
Har takai wani video ya fita nasu amma ba'a ganin fuskar Ma'aruff ɗin saita Samina, sai dai duk wanda yasan ma'aruff yanajin muryarsa dake fita a videon yasan shine, kuma gashi a gidan gonarsane.
Hankalinsa ya tashi matuƙa, dan waɗannan videos ɗin da sukaitayi da Samina duk a cikin tsohuwar lop-top ɗinsa ya adanasu, data samu matsala ya gaza fiddasu sai yay tunanin ƙilama sun goge, shiyyasa bai damuba, saboda ya rasa muhimman abubuwansa da yawa a cikin lop-top ɗin, to ashe wasu bidiyo ɗin sun maƙale🤦🏻‍♀.
A watan jiya daya shuɗe Mufida ta roƙesa ya bama ƙaninta lap-top ɗin zai gyara yay amfani da ita, saboda babbar lop-top ce kuma batasha wahalaba, kuɗine kawai dake ɗawainiya da Ma'aruff shima ya sakashi ajiyeta.
Baiyi musu ba ya bashi, ashe acan wajen gyara ƙanin Mufida sukaga wasu daga cikin bidiyo ɗin da basu gama fitaba shida abokansa, sai dai ya karɓe ya ɓoye, bai kuma taɓa sanarma kowaba har Mufidan, sai yanzu da wannan abun ya taso saboda son tozarta Samina yaron ya saki videos ɗin shi a tunaninsa Samina ce kawai zata tozarta banda Ma'aruff, tunda a ko ina babu fuskarsa sai muryarsa, wani wajen kuma Saminar cema kaɗai a bayin gidansu tai masa video ta tura masa.
Abu kamar wutar jeji yayta yawo a kafafen yanar gizo da wayoyin mutane, tare da hoton bikin su Saminar da wata budurwar da ma'aruff din ya taɓa yaudara itama ta ƙara, hakama irinsu Basy da wasu tarin ƴammatansa suka samu hanyar sake tozartashi.
To lamarifa sai ya sake canja salo, dan ahalin Ma'aruff ɗansu kawai suke ƙoƙarin karewa da son kare mutuncinsa.

Ranar a gidan su Samina duk wanda kaga baiyi kukaba to lallai sai dai idan bai mallaki hankalin kansa da zai fahimci halin da ake ciki bane, wannan tashin hankalinne ya saka jikin malam rikicewa aka kwashesa zuwa asibiti.


*_SAUDIYYA_*

Ahmad na makaranta kiran baba ya riskesa, bai ɗagaba dan sannan suna lecture, sai da ya bari ya fito sannan ya kirashi.
Tun a yanda yaji muryar baba hankalinsa yay masifar tashi, Baba yana share hawaye ya sanar masa abinda zai iya, dan bai iya buɗema Ahmad komai ba a zancen.
Shiru Ahmad yay kawai yana sauraren baba, bayan sun gama wayar da Baba sai ya kira Mudanseer, ko gaisawa basuyiba ya tambayi Mudanseer abinda ke faruwa.
Komai Mudan bai ɓoyema Ahmad ba, har maganar cikin da akece Samina taje dashi gidan Ma'aruff ɗin, da duk shaiɗancin da suka dingayi a titi lokacin shi yana cikin mawuyacin hali na ƙulafucin sonta.

Babban tashin hankalin Ahmad halin da akace malam yana ciki da Baba Yusha'u, haka ya koma gida a wani irin yanayin da Umm-Ruman ta gaza fahimta.
Tai masa tambayar duniya yana bata amsa da babu komai, daga ƙarshe sai kawai ta zuba masa ido tana kallo, dan ita dai tsagwaron damuwa take hangowa tattare dashi, gashi babu wanda ya sanar mata da abinda ke faruwa ita kam daga mutanen gida.
Koda lokacin ɗakko Haysam yayi daga makaranta sai itace ta fita ta ɗakkosa, alhalin inhar yana gida ca yake ta zauna ya ɗakkosa.
Da suka dawo duk maƙale masan da Haysam yake bai kulashi ba, daga ƙarshema da Haysam ya fara fitinar kuka akan bazaici abinciba sai da Ahmad ɗin kamar yanda ya sabar masa, sai Ahmad ya daka masa tsawa kamar zai dakesa.
Yaro bai saba da ganin Abbunsa hakaba, tsoro ya kamashi ya ƙanƙame Rumana yana kuka da ɓoye fuskarsa.
Ɗauke kai Ahmad yayi duk da baiji daɗin yanda yayma yaronba, tunda shi minene laifinsa a ciki?.
Aiko har yamma Haysam bai sake bin koda sashen da Ahmad yakeba, itama Zainab tana shigowa gidan ta fuskanci akwai matsala, dan har Rumanan ma bata cikin walwala sam.

Zuwa sallar magriba ya samu wani kiran daga Nigeria, hankalinsa tashe ya ɗaga, dan tun ɗazun girarsa ke rawa gabansa na faɗuwa tamkar wani abu zai faru dashi, hakama Rumana ta tsinci kanta a cikin wani irin tsoro.
Koda ya ɗaga a tsorace sai yaci karo da tashin hankalin abinda dama yake jima tsoron, wato dai ALLAH yayima Malam kakansu rasuwa😭.
Sakin wayar kawai Ahmad yayi ya zube cikin kujera hawaye masu zafi da ƙarajin tsanar Samina na tasiri a ransa, yasan mutuwa dolece akan kowa, sannan kuma dama ALLAH ya rubuta yau malam bazaiyi kwanan duniyaba, amma tabbas Samina ce sanadi, dan ɓacin ranta shine sanadi.
Ta zubar musu da kimar gida, ta kunyata ƙoƙarin tarbiyyar da iyayensu suka gina a garesu da saka shakku a cikin ta ƙannensu masu tasowa gaduk namijin da zai iya neman aurensu.
A ruɗe Ruman ke tambayarsa miya faru? Sai dai ya gaza bata amsa sai hawaye yake irin waɗanda ya jima baiyiba a rayuwarsa.
Barin wajen tai taje tai kiran gida itama, sai dai daƙyar ta samu Number Salima, itace ta sanar mata komai dake faruwa da yay sanadin barin malam duniya dukda dai dama kwanansa ya ƙare.
Ranar sunsha kuka ita da Zainab, har sai da Ahmad ya dawo lallashinsu.



__________________________________

Bayan rasuwar malam da kwana huɗu za'a shiga kotu, har sannan kuma Samina bata da lauya, hakan yasa baba kiran Ahmad akan maganar, duk da ɗacin wulaƙantarwar da Samina ta jamusu a idon duniya.
Ƙiri da muzu Ahmad ya bama baba haƙuri akan shi babu ruwansa akan wannan maganar, zai biya kuɗi dai a canjama Baba Yusha'u asibiti kawai.
Tun baba na masa faɗa harya koma lallashinsa, da ƙyar ya yarda akan a samo lauyan to, idan kuɗin da zai buƙata baifi ƙarfin aljihunsaba ya biya, idan sunfi ƙarfinsa sai dai mama gaje itama ta kawo wani abu.

Dole aka yarda da wannan magana ta Ahmad, dan koda aka samo lauya sai ya noƙe ya bada abinda baifi rabin kudin da lauyan ya buƙataba, dole mama gaje ta fidda wata kaddarar acikin wadda suka saya suka tara da kudin ma'aruff din ta saida.
A wajen rasuwar nan ta malam babu abinda ake mata ita da Samina sai ALLAH wadarai, ko fitowa batason yi saboda kunya.
Tayi wani firi-firi da ita saboda damuwa da tashin hankalin da take a ciki.

Washe garin addu'ar Malam ta uku aka shiga kotu.
Su Mudan hankalinsu yakai ƙololuwar tashi lokacin da aka iso da Samina kotun. dan dagani kasan taci ɗan banzan duka na fitar hankali a wajen ƴan sanda.
Ko gani idonta ɗaya bayayi saboda kumburi.
Yanda akaima Samina ɗauri tamau akan wannan al'amura yasa ko a kotun komai yay tsamari, dan kuwa sun ɗauki kwararren lauya da yaci kuɗi na tashin hankali, saboda dangin Ma'aruff ma suna goyen bayan Samina ta shiga wani halin da zai kaita jail saboda mutuncin ɗansu.
Aiko sai gashi hujjojin da duk sukazo daga mutane da ƙwarewar lauyansu ta saka wannan shari'a ɗaukarsu ga nasara.
Ruɗanin da Samina take ciki yasa duk tambayar da akai mata take badata cikin zurma kanta, daga ƙarshe shari'ar sai bata bada wahalaba kai tsaye alƙali ya yanke hukunci wa Samina.
Ɗaurin shekara bakwai a gidan yari, saboda yunƙurin kisan kan ƙaranar yarinyar da batajiba bata ganiba da tayi, sai tarar kudi mai tsoka da za'aima Afrah aiki da kula da rayuwarta har ta samu sauƙi.
Daga haka kotu ta tashi.
Duk da Ahalin Ma'aruff sunso ace ɗaurin rai da rai akaima Samina shekara bakwai ɗinma tai musu daɗi, dan koba komai dai tayi nesa da rayuwar ɗansu.
Kafin a wuce da Samina Ma'aruff ya bata takardar sakinta uku cif, ta damƙeta a hannu tana wani irin kuka mai ciwo da cin ƙahon zuciya, musamman yanda taga Baba hamza na share hawaye da gefen babbar rigarsa, haka aka sakata mota aka wuce.

Sai dai kuma abinda dangin Ma'aruff basu saniba tana ƙasa tana dabo acan kuma tsakaninsu da Mufida.
Dan kuwa dai ana gama wannan case sabuwar masifa ta tashi tsakanin Ma'aruff da Mufidar, wanda ta rikiɗe ta zama faɗan family ɗinsun gaba ɗaya ma.


__________________

Ɓangaren su baba kam sun shiga matsanancin tashin hankaki da wannan hukunci da akaima Saminar, sai dai basu da yanda zasuyi su hana, suna gani tana kuka aka sakata a mota domin kaita prison.
A take wajen mama gaje ta yanke jiki ta faɗi, sai asibiti aka wuce da ita.
A tsakanin nan kam wannan ahali nasu Ahmad basu da abin faɗa sai dai Alhmdllh kawai.
Hakan yasa Ahmad ya zage da addu'ar ALLAH ya sama musu sauƙi, dan har ɗaukar su Umm-Ruman yay sukaje Makkah sukai addu'oi a ɗakin ka'aba.
Dan suma duk da suna can suna a yanayin da yake dai-dai da wanda mutanen gidansu ke ciki a najeriya.

A hankali al'amura suka cigaba da lafawa, dukda dai zukata sun gaza mantawa dasu sam, baba yusha'u yanata samun sauƙi, hakama mama gaje ta samu sauƙi, sai dai ta rame matuƙa, damuwa ta maidata tamkar wata zararriya, haka zaka sameta zaune jigum tayi tagumi saboda tunani.
Ranar da akai addu'ar arba'in ɗin malam akai zaman mitin a gidan, wanda Baba Yusha'u ya roƙa akan ayisa.
Yana hawaye yake neman gafarar ƴan uwansa akan dukkan abinda ya faru ta sanadin iyalinsa, hakama mahaifiyarsu iya ya nema gafararta itama, kowa yace ya yafe masa, tunda ai ba shine ya aikataba, suma da suka aikata ɗin ALLAH ya shiryesu ya ganar dasu gaskiya harma da ƴan baya masu kalar tunaninsu.
Bayan gama tattaunawa da neman gafarar juna baba Yusha'u ya maida kallonsa ga mama gaje da tai jigum tun zamansu mitin ɗin, uffan bata iya furtawaba sai kallonsu kawai take kamar doluwa.
Yace, “Gaje bazan iya cigaba da zama dakeba duk yanda naso jurewa, wlhy ganinki kaɗai sakani takaici yake da tashin hankali, kece sanadin komai, kece kika rusa mana zuri'a, tun daga aurenki har zuwa yanzu ban tsinci wani abun alkairi bayan na haihuwaba tattare dake, to acikin haihuwarma saida kika haddasa komai na baƙinciki wa rayuwata da ahalina, alhakin yaronnan Ahmad kawai ya isa hana rayuwarki samun salama, Samina ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login