Showing 66001 words to 69000 words out of 165545 words

Chapter 23 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

366

tunda ya kunna fitila ta farka, amma kunya ta hanata koda motsin da zai gane.
Sake shige masa jiki tai tana faɗin, “Uhm-uhm�?.
“Uhm-uhm ko? to ai nasan maganink......�?
Kafin yakai ƙarshe tai azamar raba jikinta da nashi, ta matsa baya tana juya masa baya.
Sosai abin ya bashi dariya, dan haka yay murmushin da har take jiyo sautinsa.
Bargon ya yaye yana zura ƙafarsa ƙasa da faɗin, “Matsoraciya da ki tsaya mana�?.
Ita dai batako motsaba harya buɗe ɗakin ya fita bayan ya zira doguwar riga.
Har lokacin ana ɗan yayyafi, shiyyasa Ahmad da yayo alwalan sai ya dawo ɗaki.
“Wai bazaki tashiba?�? yay maganar idonsa akan Umm-Ruman da har yanzu take naɗe akan gadon, ita duk wayonta sai ya tafi salla zata tashi, amma jin ya dawo ɗakin ya bata tabbacin anan zaiyi shima.
Tashi tai da ƙyar, dan har yanzu gaɓɓanta ba daina mata ciwo sukaiba, ga ɗan zafi har yanzu tanaji, bata yarda tama kalli sashen da yakeba koda wasa, shiko yana tsaye saibin ta da kallo yake sabida ganin yanda take tafiya da ɗan ɗingishi, duk da ya lura da ɗunbin jarumtar da takeson nunawa dan ganin tafiyar ta tafi dai-dai.
Sai da ta ficene ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa da buɗewa lokaci ɗaya.

Cikin dauriya da ƙarfafa kanta take taku saboda ruwan da akasha, danma tsakar gidan nasu duk sumintine, alwala itama tayi bayan ta shiga bayi ta fito.
Lokacin data dawo ɗakin yana zaune yana jiranta, miƙewa yay idonsa a kanta, itako taƙi yarda yanzun ma ta kalli ko sashen da yake, baice da ita komaiba harta kimtsa tazo inda yake tunda taga alamar jiranta yake ya jasu sallar.
Hakan kuwa akai ya jasu suka sallaci asubahi, bayan sun idar yaja dogayen addu'oi a garesu da al'ummar musulmi baki ɗaya.
Koda suka shafa Rumana na zaune a bayansa batako motsaba, kanta dai a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Zamansa ya gyara ya jingina da jikin hado yana mai fuskantarta, sai dai baice komaiba kallonta kawai yake tamkar ya samu tv.
Ai sai jikin mutuniyar taku ya nemi fara tsuma, cikin salƙewar halshe ta fara gaishesa,
“Uhm u..hm Yaya ina kwana, ya gajiyar tafiya?�?.
Guntun murmushi yayi yana ɗora dukkan hannayensa saman gadon cikin miƙar dasu, har sannan kuma idon nasa a kanta yake.
“Lafiya lau Amaryar Ahmad, ya ƙoƙari?�?.
Shiru tai dan bata fahimci ƙoƙarin mi tayi ba.
Ya sauke hannayensa tare da kai na damar ya ɗago haɓarta, “Kalleni nan�? yay maganar babu wasa.
Dolenta ta ɗago idanunta a hankali ta saka cikin nasa daya kafeta da su.
“Bakin ya mutu ne?�?.
Yay maganar yana matso da fuskarsa daf da tata.
Itakam ta rasa yaya zatai da Yah Ahmad, shi baisan kunyarsa takeji bane halan? Tun daga dawowarsa jiya ya koma mata tamkar bashiba a komai.......
Iskar daya busa mata saman idanu ya sata lumshesu sosai tsigar jikinta na tashi, ya jawota gaba ɗaya jikinsa, ya cire mata hijjabin tare da faɗin, “Yaya jikin?�?.
Baki taɗan kumburo masa kaɗan da faɗin, “Nidai lafiyata lau fa Yaya�?
“Oh ALLAH? Shike nan kinga to bara mu maimaita�?.
A zabure tace, “Yah Ahmad mi?�?.
Yanda tai maganar hawaye na zubowa lokaci ɗaya saman kumatu ne ya sakashi yin dariya, yaja hancinta kaɗan tare da dungure mata kai yace, “Mai raki kawai, iya tasan har ita kika kira saboda ragwantakarki saita miki dariya�?.
Cusa kanta tai a jikinsa tana murmushi, jiya kam a ƴan gidansu ai babu wanda bata lissafo ba, har Tahir dake shan nono bata mantaba, yo taji azaba, ashe abun da gaske babu sauƙi........
Ahmad ya katse mata tunani da faɗin, “Kinga tashi kije ki kwanta, wannan barcin da muka ɗau bashi idan bayinsa akaiba zai haddasa ciwon kai�?.
Da ƙyar Rumana ta bar jikinsa ta miƙe, bata yarda ta kallesa ba taje ta haye gadon ta kwanta, shima da yake binta da kallo tashin yay yacire rigarsa ya hau gadon.
Jinsa a jikinta ya saka sabon tsoro bijiroma Rumana, ta lafe tamkar mai barci tana sauraren mizai biyo baya, sai bataji komaiba, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ahmad daya jita ya murmushi kawai.


★★★★★★�?

Basu farkaba har kusan goma, har lokacin kuma dai garin ana yayyafi irin yaf-yaf ɗinnan, hakan yasa garin ɗaukar shiru kowa yana cikin ɗakinsa, sai irinsu maman Ama ƴan gutsiri tsoma da ake yawan leƙa waje aga wazai fara fitowa, dan ita dukda yayyafinnan tuni mijintama yabar gidan.
Kausar ma dake fama da ciki kusan tara ta fito ɗaura musu abin kari, ananne suka haɗu da maman Ama.
“Waisu waɗannan bazasu tashi bane? Garin ALLAH ya waye amma ƙofa a garƙame?�?.
Dariya Kausar dake sauraren mama Ama tayi tana gyara buhun ledar data ɗora saman kanta saboda kar yayafi ya jiƙata, tace, “Ke ko sai an nuna manafa miji ya dawo jiya ko�?.
Baki maman Ama ta taɓe, “Saikace wata tsiya mijin ke iyayi matan�?.
Kausar ta sake yin dariya tana juye shayi a kofi mai murfi, “Ko baiyiba ai yaɗan lalubi abinda zai iya, wlhy ni idan nice ita tuni zan tona maka asiri na kashe auren, banga amfanin namiji gareni bai iya taɓukamin komaiba, ai ko ganga batason ajiya burinta kullum a kaɗata ta bada sauti balleni da ƙuruciyata da komai�?.
“Ke kika san dokar ai�? ‘Cewar maman Ama tana harar ƙofar ɗakin su Rumana da basusan sunaiba ma�?.

Rumana ce ta fara tashi, ta janye jikinta da yay mata nauyi daƙyar daga na Ahmad ta sakko, barcinsa yake sosai dan haka baiji saukarta ba, ƙofar ta buɗe ta fita bayan ta cika buta da ruwan zafin daya ajiye a filas ta fita da brush a hannu, tsakar gidan babu kowa, dan sun gaji da leƙe-leƙen sun zauna waje ɗaya, hartayi brush ɗinta taje bayi tai tsarki sosai ta fito babu wanda ta gani, taji daɗin yin tsarkin kuwa, dan sai taji kamar an mata gafara.
Ɗakin ta koma, ta maido risho bakin ƙofa daga ciki ta kunna domin nema musu abin kari.

Tana cikin juye ruwa filas ɗin Ahmad ya farka shima, lalubawa yay kozai jita sai yaji wayam, ya buɗe idanunsa yana tashi zaune, ganin tana aiki sai yaɗanji sanyi a ransa, bata yarda ta kallesa ba harya sakko a gadon, ya ɗauki brush da buta ya fita baice da ita komaiba.
Lokacin daya dawo harta gama kwashe ruwan ta kashe risho ɗin, daga bakin ƙofa ya miƙo butar ya ajiye ya juya ya fita.
Ganin hakanne ya saka Rumana ƙoƙarin fara gyaran ɗakin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dandanan ta kammala, tana shara Ahmad ya dawo riƙe da leda ƙarama a hannunsa.
Matsa masa tai ya shige, ita kuma ta fita da sharar waje, koda ta dawo saita iske yana fito da kayan tea daga jakkar da yazo da ita, batace komaiba ta kawo kofuna kamshin ƙwai soyayye dukya gauraye ɗakin.
“A ledar nan akwai bired�?. Yay maganar yana cigaba da maida kayan daya fiddo daga jikkar.
Cikin sanyin murya Rumana ta amsa da “to�?.
Bayan ya kammala zama yazo yayi, da taimakonsa ta haɗa musu shayin, ita dai duk taƙi yarda su haɗa ido, duk da shi Ahmad yanata buƙatar hakan.
A takure tai wannan kari, har suka kammala ta tattare komai ta fita da wanke-wanke, shi kuma ya ɗiba ruwan wanka ya sirka da wanda ta zuba cikin filas ɗin ya nufi bayi.
Tana bakin rijiya ya wuce, hakan yasa ta bisa da kallo, dan batasan zaiyi wankanba aida ta haɗa ruwan takai masa.
A lokacinne Kausar ta fito daga ɗakinta, sai da ta harari Rumana data juya mata baya kafin ta ƙaraso tana ƴar dariya, “Oh ni su amarya anyi bulum a ɗaki saboda yau oga ya dawo?�?.
Murmushi kawai Rumana tayi, ba tare data bata amsaba tace, “Ina kwana�?.
Nanma saida Kausar ta harareta ta wutsiyar ido sannan ta amsa, zuwa yanzu garin yayi ɗaf babu yayyafin, sai wani ɗan hasken rana daya hasko mai ɗumi.
Kausar tasan dama Rumana ba biye mata zatai suyi surutuba, amma sai ƙoƙarin janta take da hira, Maman Ama da taji motsinsu sai gata wuff ta fito daga ɗaki tamkar an jefota.
Itama Rumana gaidata tayi da tambayarta lafiyar yara, maman Ama ta amasa suna gulmar Rumana da ido itada Kausar, ahaka Ahmad yazo zai shigesu suka shiga gaishesa.
Amsawa yay kawai, ba tare da ko kallonsu yayiba ya shige ɗaki, sunata surutunsu ita dai Umm-Rumana na wanke-wankenta, tana kammalawa kuma ta miƙe tama bar musu wajen, da tabbacin Ahmad ya gama shiryawa ta shiga ɗakin, sai kuma ta iske saɓanin hakan, yadai gama shafa mai yasa singlet da boxer yana kwance a gadon ƙafafunsa a ƙasa.
Shigowarta ce ta sakashi buɗe idanunsa ya zuba mata, yayinda ita kuma dukta dabarbarce tana neman juyawa ta koma saboda yanda ta gansa.
Katseta yay da faɗin, “Zonan�?.
Tamkar zata fasa ihu haka taji, ta matso shikuma yana tashi zaune sosai, saurin riƙo hannunta yay ganin tana neman durƙusawa, “K wai nazama surukin kine?�?.
Yay maiganar yana ɗorata saman cinyarsa.
Kanta ta girgiza masa.
Yace, “Magana da baki nakeso�?.
Daƙyar tace, “A'a�?.
“Eh mana, ba gashi bakison kallona ba, idan ina ɗakinnan duk sai kibi ki takura kanki�?.
“To kayi haƙuri, bazan sakeba�?.
“Inma banyi haƙurinba ya zanyi Ruman, kinga tashi na gwadaki naje shago naɗan sama miki kayan da zakije wajen bikin gobe, yau dai ki kwanta ki huta�?.
Idanunta suka cika da ƙwalla, danta saka ran zai barta taje tun yau, da ƴar shagwaɓa tace, “Amma Yaya miyasa bazan fara zuwa tun yauba?�?.
Kallonta kawai ya tsayayi, kamar zai shareta sai kuma yace, “Gobenma na gadama bazaki jeba�?.
Bakinta taja ta tsuke, bata sake koda tariba.
Ya miƙar da ita daga cinyar tasa shima ya miƙe, tef ya ɗauka yazo gabanta ya tsaya, karon farko dazai gwadata dan zai musu ɗinki, hakan bai taɓa faruwa ba, dan baya gwadasu sai dai yace su kawo kayansu yay amfani dashi.
Salon da ake gwada ɗinkin ya saka tsigar jikin Rumana keta tashi, badai ta yarda ta motsaba saboda yanda ya haɗe fuska, tasan dai haushin maganar bikice da tayi, itama saida ta furta ne taga wautarta.
Yanayi yana rubutawa, harya kammala ya ɗauki kayansa ya saka, sabuwar shaddace mai ƙyau kalar ruwan sararin samaniya, duk da bamai tsada bace tai bala'in masa ƙyau, ga ɗinkin ya zauna ɗam cikin ƙyaƙyƙyawar surarsa, ainahinsa na Barumen bakatsine ya fito masha ALLAH, ballema yayi aski da gyaran fuska, ƴar ƙasumbar daya ajiye ta sake fiddo taswurar nutsatstsiyar fuskarsa, hannunta daya kamone ya maidota hayyacinta, ya saka mata turare a hannun.
Kallonsa ta ɗanyi sai ya nuna mata jikinsa alamar ta saka masa.
A ɗan kunyace ta fara fosa masan, sai da ta tabbatar ko ina yaji sannan ta dakata, hannunta ya kama ya jata gaban gadon, shi ya zauna ita kuma tana tsaye a tsakanin ƙafafunsa idanunta a ƙasa tana kallon hannayensu.
Yace, “Kina jina�?.
Kanta ta ɗaga masa, sai kuma tai saurin cewa, “Eh�? saboda tuno gargaɗinsa.
Ya murza hannun nata yana cigaba da faɗin, “Ki kwanta ki huta, bance kije cikin matannan ki zauna ba, zan aiko Abubakar ya kawo miki abinda zakici, sannan abinda ya faru tsakanina dake sirrinmu ne, koda wasa naji bakinki na bama wani labari koda su Fa'iza ne bazakiji da daɗiba, ki kama bakinki�?.
Cikin rawar murya Rumana tace, “To yaya, insha ALLAH zan kiyaye�?.
“Good�? ya faɗa yana miƙewa, matsota yay jikinsa ya rungume yana sumbatar kanta da shafa bayanta, a hankali ya furta, “ALLAH yay miki albarka�?.
Rumana dake lafe jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa ta amsa da amin a cikin zuciyarta tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata ido..
Ɗago kanta yay ya kama fuskarta ya saka cikin tafin hannunsa yana kallo, ganin taƙi kallonsa sai ya ɗora goshinsa kan nata, “A kalleni mana madam�?.
Kunya ta sake kama Rumana, taɗan saki murmushi da a maƙoshi kawai taji sautin kayanta, shima ya sumbaci laɓanta ya ɗago ya sumbaci goshinta sannan ya saketa.
Ɓaƙar ledar daya ajiye gefe ta viva ya ɗauka yana faɗin, “saina dawo mizan zo miki dashi?�?.
“Ba komai Yaya�? ta faɗa tana ɗan satar kallonsa.
Kaɗa kansa yay yana nufar ƙofa bayan ya zira takalmansa baƙeƙe a ƙafa, “Shikenan saina dawo�?.
“Ka gaidasu, ALLAH ya tsare�?.
“Amin�? ya faɗa yana ɗaga labulen ya fice.

Kausar da maman Ama da har yanzu suna inda Rumana ta barsu suna gulmarta duk suka zuba masa ido a kaikaice, harya fice kowacce da abinda take saƙama ranta.
Shiko baima san sunaiba, dan basu ishesa kalloba.

Yana fita Rumana ko bakin gadon ta zauna tana sauke numfashi a hankali daɗan murmushi, yanzu kam ta yarda Yaya Ahmad natane bana yaya Samina ba kamar yanda kowa ke faɗa a baya, abinda bata taɓa kawowa ba koda a mafarkinta, ALLAH kenan, mai tsara yanda yaso, ga kuma wanda yaso.
Miƙewa tai ta ɗora ruwan zafi a risho danta samu tai wanka, bata fitoba saida ta juyo a botiki, matan gidan nata ƙoƙarin ɗora sanwar rana, batace da kowa komaiba ta shige bayi.
Sai da ta fitone maman Ama ke tambayarta wai ko zataje gidan bikine?.
Murmushi Rumana tayi dan tasan tambayar da biyu ce, sosuke suji ko Yah Ahmad zai iya barinta taje?.
Sai kawai tace, “Mizai hanani zuwa, zan dai jira su Fa'iza suzo mu wuce�?.
“A'a, toshi angon bacan ya nufaba da bakibishi kun tafi tare ba?�?.
Karon farko Rumana taji zata iya maida murtani, dan haka tace, “Maman Ama mi kikeci na baka na zubane?�?.
Shiru kuwa bakin maman Ama ya rufe ruf, suka kalli juna itada Kausar cike da mamakin Rumana, itako batabi takansu ba tai shigewarta ɗakinta tana jan tsaki a zuciyarta.
Har tai shirinta bata sake jiyo tarin kowa a cikinsu ba, sai ga sallamar Abu, taji daɗin ganinsa, ya ajiye mata ledar dake hannunsa yana tsokanarta da faɗin, “Wannan ai kece amaryarma ba waccan fanɗararriyarba�?.
Dariya Rumana tai masa, “Kai Yaya Abu wace fanɗararriya kuma?�?.
“Amaryar gidanmu mana mai kan goba�? ya faɗa yana miƙa mata ledan hannunsa, “Gashi inji Yah Ahmad�?.
Amsa tai tana godiya, ga ƙamshi dukya cika ɗakin, dagaji kasan kazace.
Abu da ko zama baiba yace, “Bara na fece amaryar Yaya�?.
“Yah Abu ina zaka fece, “dan ALLAH kazo muci�?.
Dawowa yay da baya yana rage murya kamar zaiyi gulma, “Hajiya takice ke kaɗai, tamu nacan a shago ina faɗa miki a ƙyafe, gara naje kafin Yah Mudan ya handame rabi ya banni da ƙwala idanu�?.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login