Showing 39001 words to 42000 words out of 165545 words

Chapter 14 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

363

cayay ta hau gado ta kwanta, shi kuma ya kwana a ƙasa saman tabarma.


________________________


Haka zaman nasu ya cigaba babu tsangwama babu sakin jiki wa juna, har dai jikin Ahmad ya ƙara sauƙi, yanzu kam alhmdllh ya wartsake, sai dai ciwo irin na zuciya da ya ƙi barinsa, wannan kam kowa yasan abune mai wahala ace ya barshi da wuri, musamman idan aka ƙiyarsata da irin son da yakema Samina.
Tunda yaji ƙarfin jikinsa ma ba zaman gidan yakeba, barcine kawai ke kawosa, zuwa goma sunyi karin kumallo ya fice shago, bata sake ganinsa sai uku na rana, yay wanka yaci abinci ya sake ficewa, daga nan kuma sai sha ɗaya na dare ko goma da rabi zai shigo.
Wajen barci kuwa tana saman gado shiko yana ƙasa a tabarma, babu wani abu na muzgumawa da yake mata, sannan babu najin daɗi, itako tsakaninta da shi sai girmamawa kamar yanda ta saba tun can da suna gida.
Duk da ta lura hankalinsa baya gareta hakan bai damunta, ba itaba ai dama kowa dai yasan Samina yake so, to miyasa zata ɗaɗara kanta da ƙasa akan sai ya sota.
Kuma dama bawani saurayine da ita ba data ƙwallafa ma rai balle yanzu sonshi ya damu zuciyarta.
Yana fita zata dawo tsakar gida suyita hirarsu ita da Maman Ama, kokuma ta ɗakko Ama taita mata wasa ita da Ahmad da take kira yayanta..

Yauma tunda ya fita gidan nasu ya zarce, sai da ya shiga suka gaisa da malam da iya sannan ya shiga sashensu, Ayyah kaɗai ya iske a gidan Gwaggo ta fita, ya gaidata cike da girmamawa yana zama a gefenta.
Gwaggo ta kallesa da kulawa, “Ɗan albarka yaya dai? Naganka wani iri�?.
Murmushin yaƙe yayi kaɗan yana duƙar da kansa, kamar bazai ce komaiba daboda nauyin maganar a harshensa sai kuma yaja numfashi, a ɗarare yace, “Ayyah! Sonake nabar garinnan, inaga hakan zai bani ƙyaƙyƙyawan nutsuwa, har yanzu nakanji zuciyata sam babu daɗi a cikinta, komai baya burgeni, komai baya sakani nishaɗi, koma bai sakani farin ciki wlhy Ayyah�?.
A yanda ya ƙarasa maganar sai tausayinsa ya kama Ayyah, ta dafa kafaɗarsa tana faɗin, “Ɗan albarka na sani, nasan kana cikin damuwa har yanzun, musamman ma da rayuwar gidannan take neman juyewa zuwa wani abu daban, banƙi kabar garinnan ba, sai dai ka tuna yanzu bakai kaɗai bane, gashi yarinyarnan gaba ɗaya bata wuce sati biyu ba, anya tafiya ka barta a wannan yanayin bazaisa mutane su fassara abun da butulci ba?�?.
“Hakane Ayyah, nima nayi wannan tunani, amma a ganina tafiyar shine mafita, ita kanta yarinyar maybe a yanda nake kallonta zai canja�?.
Shiru Ayyah tayi tana nazarin maganarsa, bawai bata yarda dashi bane, ta gamsu da duk bayaninsa ɗari bisa ɗari, amma Umm-Rumana take tausayi, bai kamata a haɗa mata zafi uku ba a ganinta.
Ta sauke nannauyan numfashi tana mai kallon Ahmad ɗin kamar baƙonta, “ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi to, mu miƙa lamarin hannun UBANGIJI, idan tafiyar tafi alkairi ALLAH ya tabbatar, idan ba ita bace ALLAH ya canja maka da mafi alkairi�?.
“To amin ya rabbi Ayyah, sai ki tuntuɓi baba da zancen shima muji mizaice�?.
“Babu damuwa, insha ALLAHU zan masa maganar, itama Gwaggo zan sanar mata ta tayamu da addu'a�?.
Kansa kawai ya iya jinjina mata, daga nan suka ɗora da wata hirar, duk dama Gwaggo ce ƙarfin maganar, Ahmad kam sai ihhm da a'a.

Shigowar su Fa'iza daga makarantar allo ya sakashi miƙewa ya fice, shago ya shiga domin ya samu ya rage ɗinki, dan babu laifi sun ɗan tara da yawa.
Yana tsaka da yanka wata atanfa fallatsetsiyar mota tazo gaban shagon ta faka, kallo ɗaya yay ma motar ya ɗauke kai saboda hango Ma'aruff da yay a ciki.
Sai dai kuma ya kasa daurewa, dan yasan dai dole Samina yake jira, ilai kuwa sai gata ta fito cikin kwalliyar duguwar rigar Material datai mata masifar ƙyau, rabonsa da ganinta tun washe garin aurensu, ta ƙara fari da alama man bilicin ɗin ta cigaba da shafa a binta, bai iya daina kallonta ba har ta shige motar Ma'aruff yaja suka bar anguwar, yanda ya bulo ƙasa zaka tabbatar da biyu yayi hakan saboda Ahmad.
Ahmad yaja dogon tsaki yana ɗauke kansa, hakan yasa Mudan dake ɗinki ɗagowa ya kallesa, danshi tunda yayma motar kallo ɗaya bai sakeba saboda takaici.
Kamar Mudan zaiyi magana sai kuma yay shiru ya cigaba da ɗinkinsa, shima Ahmad ɗin dai yankansa ya cigaba da yi dukda zuciyarsa babu daɗi sam.


★★★★★★

Ma'aruff kam yana barin wajen dariya suka kwashe da ita shi da Samina, cikin dariyar yake faɗin, “Mutuminki fa ya shaƙa, kinga harar da yake wulloma motarnan, na tabbata ji yake kamar zuciyarsa zata faɗo dan baƙin ciki�?.
“Manta da shi luv ɗina, ni ko kalloma bai isheniba wlhy, yanzu ina zamuje?�?.
Gefen titi ya samu ya gangara yay fakin, hakan ya saka Samina kallonsa da faɗin “yaya haka kuma? Miyasa muka tsaya anan?�?.
Juyowa yay sosai yana kallonta da wani murmushi a kan fuskarsa, ya ɗan matsota idanu a narke, cikin raɗar magana yace, “Babyna bazaki ganeba, ina cikin wani haline�?.
A ɗan ruɗe Samina ke faɗin, “Miya sameka?�? tana maganarne tana dube-duben jikinsa�?.
Hannu ya ɗora a kafaɗarta yana kuma narke murya, “Bafa ciwo najiba, damuwar a nan ne�? ya kamo hannunta ya ɗora saitin zuciyarsa.
Ƙoƙarin janye hannun tayi amma sai ya riƙe sosai yanda bazata ƙwaceba, ya fara murzashi kaɗan-kaɗan cikin nasa hannun mai taushi, “Haba babyna ki gane mana, wai sai yaushene zaki ban dama koɗan rage zafi munayi, kinfa san kece zan aura, aurenma nan da kwana kaɗan, kinaso ace yau ga mijinki a gidan karuwai ko yana huɗɗa da karuwa?�?.
Da sauri ta girgiza masa kai, ya lumshe ido yana hura mata iska kaɗan-kaɗan akan fuska, ganin ta lumshe nata ya sake kai fuskarsa dab da tata har suna shaƙar numfashin juna.
“Baby karki hanani kanki, namiki alƙawarin babu abinda zai shiga tsakaninmu inba ɗan kiss hakaba, shima dan na samu nutsuwa ne kawai kar wata ta lalata miki ni, dan harga ALLAH a matse nake, shiyyasa banson aurenmu ya gaza wata ɗaya, amma gashi kekuma kince muyi haƙuri ki ƙarasa karatunki nanda watanni shida, niko yamun nisa Samin ɗina�?.
A hankali ta buɗe idanunta da suka shige cikin nasa, tsigar jikinta sai tashi take saboda dama itama a bukacen take, duk yanda taso ta hanashi hakan sai ya gagareta, saboda wani tsantsar sonta take hange cikin ƙwayoyin idanunsa, itama idan son samun tane suyi aurensu nanda wata ɗayan kamar yanda ya buƙata, amma sai mama gaje tace tajashi harta gama makaranta dansu ƙara tatsar kuɗaɗen da zasuyi mata hidimar biki na garari da sai ya tsayama ƴan gidansu a rai da Ahmad, wannan shawarar ce ta saka Samina cemasa ya bari ta gama makaranta kawa......
Saukar laɓɓansa kan natane ya sakata ƙanƙame jikinta, dan wannan shine karo na farko a rayuwarta.
Duk hanyar da Ma'aruff ya ƙware akai sai da yabi Samina ta sakar masa jiki yay kissing ɗinta sosai, sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.
Koda suka dai-daita kunya hanata kallonsa tayi, yaje da ita wani wajen motsa baki, duk yanda yaso taƙi fita su shiga tare, dan gani take kowa zai gane abinda sukayi, Ice-cream da gasashshiyar kaza da kayan ciye-ciye ya lodo mata ya dawo, daga nan gida ya maidota, inda ya hanata fita suka cigaba da hirarsu a mota.

Koda Ahmad ya fito da ga shago zaije masallaci sallar magriba kallo ɗaya yayma motar yay gaba abinsa, zuciyarsa na wani irin ƙuna tamkar zata fito waje.
Har suka dawo sallah Ma'aruff da Samina na'a motar, hakanne ya saka Ahmad shiga cikin gida ya amsar musu tuwo shi da Rumana ya fito domin tafiya gidan.
Har abokansa na tsokanarsa akan yau da wuri haka zai wuce?.
Murmushin yaƙe kawai ya iya musu ya wuce abinsa yana tsaida mai napep.


_________________________


Yau gidan namu ya kasance na mutum Uku, dan kuwa amarya za'a kawo mana, amma dai bazawara ce kamar yanda Maman Ama ta sanar min.
Tun da hantsi ƴan uwanta sukazo sukai mata jere, hakan yasani yini a ɗaki dan ni bancika son sakewa cikin mutane da yawaba, musamman ma waɗanda ban saniba.
Ban sami nutsuwar zaman wajenba sai da suka wuce bayan la'asar, sannan ne na fito nai wanka, na dafa taliya dai-dai cikina dan nasan Yah Ahmad ba dawowa ci zaiba, tunda ya cemin yau yana da aiki sosai a shago, maybe shi da gida sai dare.
Daga nan ƙofata na fito na saka kujera ina duba buks ɗina na makaranta, dan ban fidda ran Yah Ahmad zai barni na zana koda ssce ne ba.
Jefi-jefi nakan amsa maganar Maman Ama da duk rabinta gulmar dangin baƙuwar amaryarmu ne da sukazo sukai jere.
Ni dai ban yarda nace komaiba, iyakata dariya ko nace ALLAH ya ƙyauta, daga ƙarshema da naga zata takurani sai na ɗauki kayan karatun na shige ɗaki kamar zanyi wani aiki a ciki, zama na nai, ban sake fitowa ba sai da aka kira magriba, nazo nai alwala na koma ɗaki, dan baƙi sunɗan fara shigowa, da alama dai dangin angone da zasu tarbi amarya.
Ni dai gaishesu kawai nayi nai shigewata.
Zan kabbara salla biyu a cikinsu suka leƙo wai na taimakesu da buta suyi alwala, miƙa musu nayi na kabbara salla ta, ina cikinyi suka shigo, ganin salla nake suka shinfiɗa tabarma suma suka tayar.
Koda muka idar basu fita ba, sai hira suke jana da ita, duk tambayoyin nasu dai akan son sanin nima amaryace?, ina ɗan amsa musu abinda zan iya saboda naga sun girmemin sosai.

Muna idar da sallar isha'i ne Yah Ahmad ya shigo da sallama, ganin bani kaɗai bace sai ya koma da baya ba tare da yace komaiba.
Hakan da suka ganine ya sakasu miƙewa suna min godiya, a tsaye suka iskeshi, suka gaidashi suna barin wajen zuwa ƙofar ɗakin maman Ama da sauran ƴan uwansu suke can sukai salla.

Sannu nai masa ina amsar leda viva dake hannunsa, wadda Ayyah ta sako masa kwanikan tuwo a ciki.
Da yauwa ya amsa yana zama a bakin gadon, “Waɗannan fa?�? yay tambayar yana kallona.
“Uhm baƙine ƴan tarbar amaryar da zata tare a gidannan yau�?.
Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru, saboda wayarsa da tai ring, ɗagawa yay suna magana, wadda na fahimci dai akan ɗinkine.
Kwanikan abincin na fiddo a ledar, koda na buɗe naga tuwo sai bance komaiba na maida na rufe.
Dai-dai ya ajiye wayar, hakan yasashi faɗin, “Da ruwan zafi a gidannan?�?.
“Eh, akwai wanda na dafa ɗazun�?.
Miƙewa yayi tsaye yana ƙoƙarin cire maɓallan rigar jikinsa mai dogon hannu, “Juye min shi naɗan watsa, zafi ya isheni banzo nayi wanka ɗazun ba�?.
Da “To�? kawai na amsa masa, na shiga bin Umarninsa tamkar yanda ya bada.
Bayan na haɗa ruwan bayin naje nakai masa, lokacin dana dawo harya cire kayan ya saka jallabiya, ya ɗauki kwandon soso da sosan sa ya fice. Ni kuma sai na kwashe kayansa da ya cire ya ajiyemin saman gado, a raina inata tseguminsa, wani lokacin sai naita ganin kamar Yah Ahmad bai karatu mai zurfi ba na boko, dan sam bashi da irin son gayunan da ƙwalisar samarin yanzu masu irin shekarunsa, yana dai da tsafta gwargwado, amma itama tunda abunnan ya faru tsakaninsa da Samina sai tayi rauni, jiba fa, rabonsa da wanka tun ƙarfe uku da wasu mintuna na yammar jiya, sai yanzune kusan takwas da rabi na dare zai sakeyi, inba sa'a ba daga haka kuma sai gobe da yamma.
“To ke ina ruwanki?�? wata zuciyata ta faɗa cikin gargaɗina.
“Haka nefa wlhy�? na faɗa a fili kamar mai bama wani amsa.
Kafin ya fito najiyo hayaniya ta ɗan fara cika gidan, da alama dai tawagar amarya sun fara shigowa...........✍�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WhgANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo




*(15)*



...............Shigowa yay yana jan tsaki, da alama dai hayaniyar gidance ta bashi haushi, ni dai bance komai ba na amshi kayan wankan na fito waje danna zazzage ruwan jikin soson, ta wani ɓangare kuma na bashi damane ya kimtsa.
Ina kallon wasu suna nunani, da alama dai ana gulma tane, oho basu dameni ba, sai ma na ɗauke kaina daga garesu.
Guɗar data cika soron gidan ne ya tabbatar mana da cewar dai amarya ta iso, ilai kuwa sai gasu sun shigo da ita.
Ni dai ina daga ƙofar ɗaki ina kallonsu, har aka shige da ita ɗakinsa suna callara guɗa abinsu.
Murmushi na ɗanyi, dan sun tunomin da randa nima aka kawoni gidan ina rusar ihun kuka.
“Sai kin gama kallonsu zakizo ki bani abinci ne?�?.
Muryar Yah Ahmad ta maidoni hankalina, da sauri na girgiza masa kai ina faɗawa ɗakin jikina har ɓari yake.
Zaune na iskeshi saman tabarma, ya cire jallabiyar yana sanye da wando dogo mai taushi da riga, da alama dai na barcine.
Tuwon na zuba masa miyar kuɓewa ɗanya sai ƙamshi take, dukda babu nama a ciki girkin tsoffin mata irinsu Ayyah daban yake, musamman ma akan abinci irin na gargajiya da a yanzu yake gagarar matan hausawa, wata sai tai maka tuwon masara kaji tamkar ya jiƙe saboda tsabar rashin bashi nutsuwa.
“Kaɗan zaki saka�? yay maganar idonsa nakan wayarsa.
Na amsa da to ina ƙoƙarin saka masa dai-dai misali a filet ɗin.
Koda na kammala sai na koma gefe zan zauna, amma sai ya katseni da cewar, “K mi kika ci?�?.
“Da yamma na dafa taliya naci da mai da yaji, yanzu banajin yunwa�?.
Baice min komaiba ya fara cin tuwonsa hankali kwance, kallo ɗaya zakai masa kasan yanajin daɗinsa sosai.

Yana tsaka da cin tuwon niko ina zaune gefensa kaɗan ina sauraren hayaniyar da gidan ya ɗauka mukaga an ɗaga labulen ɗakin kamar da gayya, da sauri na kalli ƙofar sai naga matashiyar mace ce ma, kafin nayi magana ta katseni da faɗin, “Mai ɗakinnan ruwan sha zaki sammin dan ALLAH�?.
Miƙewa nai ina faɗin, “To�? hakanne ya sakata shigowa gaba ɗaya tana kalle-kalle kamar ta ajiye wani abu a ɗakin, sai kuma naga ta fita da sauri tana cewa, “Ya salam, kuyi haƙuri dan ALLAH, wlhy bansan maigidanki na nanba�?.
guntun Murmushi kawai nai mata na miƙa mata ruwa waje.
Ta amsa tana cewa “Na gode�?.
Ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login