Showing 78001 words to 81000 words out of 165545 words

Chapter 27 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

387

Hannu kawai Samina tasa a ka ta dafeshi, zuciyarta na zallo tamkar zata faso ƙirji ta faɗo ƙasa dan tashin hankalin da take hange a gabanta.......


____________________________________

Haka rayuwa take juyi-juyi, lokacin da Samina ke cikin wancan tashin hankalin gasu Ahmad kuwa farin cikine mamaye dasu shida ƴar Rumanan sa.
Dan bai fita a gidanba sai bayan sallar la'asar, yayi wankansa yaci gayu cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau sosai, Rumana kanta ta kasa ɗauke idanunta a kansa, sai satar kallonsa take, da taga zai juyo sai tai azamar ɗauke kanta daga sashensa.
Ɗan murmushi yay yana girgiza kai, ya tako a hankali inda take zaune a saman tabarmar, hannunsa yasa ya miƙar da ita, hannunsa ɗaya a ƙugunta ya mannata da jikinsa, ɗayan hannun kuma ya ɗago haɓarta yanda zasu kalli juna.
“Hajiyata wannan gulmace, ki kalli mijinki kanki tsaye saboda nakine ke kaɗai�? ya ƙare maganar da hura mata iskar bakinsa a fuska.
Murmushi tayi idonta lumshe, ya ɗora goshinsa akan nata shima yana murmushin, “Babie R murmushi na miki ƙyau, amma sam baƙyasonyi saikin gadama�?.
Idonta ta buɗe dan mamakin zancensa, to shikuma fa daya fita iya ƙin son yin murmushin.
Ɗan mintsininta yayi a hannu, hakan ya sakata sake manne masa a jiki tana ƴar dariya, “Yaya ALLAH da zafi?�?.
Shima dariyar yayi yana sumbatar kumatunta, “K ai jarumace Babie R nasan ɗan zafin nan bazai damekiba, bara na ƙara�?.
Tai saurin riƙe masa hannu tana dariyar, “A'a wlhy na yafe, naji niba jaruma bace�?.
Sakinta yay yana dariya sosai da cewa “Aini nasan inda jarumtar babie na take�?.
Rumana datasan inda ya dosa tai saurin rufe fuskarta da ɗan kwali.
“Kiyi tuwo gaskiya na gaji da waɗannan kayan maiƙon, bara naje idan na samu yaro zan aikosa da cefane, idan ban samuba kuma saina ƙarasa gida sai Abu ya kawo�?.
“To a dawo lafiya, tunda ni dai an hanani komawa�?. Ta ƙare maganar a hankali yanda bazaiji ba.
Sai dai kuma sarai ya jita ɗin, ya dai sharetane ya ida ficewa abinsa fuskarsa ƙunshe da murmushin da su Kausar sukaci karo dashi.
Baiko dubi inda sukeba ya nufi hanyar fita daga gidan, da kallo suka bisa kafin su kalli juna suna taɓe baki.
Maman Ama tace, “Nifa mutanen nan yanzu maɗaukakin mamaki suke bani, munafukan da kamar bazaka saka musu yatsa a baki su cizaba amma yanzu ji salon bariki kala-kala�?.
Tsaki Kausar taja tana cigaba da saka lallin da take a yatsun hannunta, tanaji a ranta itace ya kamata ta samu wannan rayuwar soyayyar da take gani wajensu Rumana, dan mijinta duk yafi mazan gidan arziƙi.
Itama dai maman Ama abinda ke ranta kenan, gani take tafisu komai, kuma ta girmesu, ya kamata ace koman su ta dinga sani.

Rumana dai da batasan sunaiba ɗakin ta kuma kimtsowa ta fito itama dan wanke ƴan kwanikan abincin da sukaci, tana zama su Fa'iza na shigowa gidan da cefanen da Ahmad ɗin yace zai aiki, da alama a hanya ya gamu dasu dai, cikin mutuntawa suka gaida su maman Ama dake binsu da kallon ƙurilla suka amshi wanke-wanken Rumanan suka ƙarasa suna hirar data shafesu ba tare dasun damu da su Kausar dasuka kasa kunne suna saurara ba.
Suna gamawa suka koma ɗaki suna baje babin firarsu musamman akan candyn su dake matsowa, dan jarabawa uku kacal ta rage musu su ƙarasa.
Rumana na girki daga ƙofar ɗaki sukuma suna daga ciki ake hirar
harta kammala tayo wanka sannan ta koma ɗakin suka cigaba da shaftarsu.
Sunayin sallar la'asar suka wuce islamiyya abinsu aka bar su Kausar iyayen gulma sunayi, tunda su basu da aikinyi basu kuma kallon matsalolin gabansu saina wani.
Kusan tare suka shigo gidan da Ahmad, dan ya daidaita lokacin dawowar tasune dama, su Fa'iza daga can gida suka wuce, ita kaɗai ta dawo gida, yanda suka shigo tare gidan saika ɗauka tare suke dama.
Rumana ta buɗe musu ɗaki, shi Ahmad ma bai shigaba ya amshi buta yay alwalar magriba ya sake fita.
Yanzu Umm-Rumana ta lura baisan kaiwa dare a waje yanzu tunda ya dawo, idan kinga ya daɗe to zuwa sallar isha'ine zai shigo.
Wani lokacin suyi kallo a wayarsa wani lokacin kuma ma tana karatune shi yana latse-latsen wayar, inda bata ganeba ta nuna masa yay mata ƙarin bayani.


★★★★�?

Wannan tafiya dai kam ta zamewa Umm-Ruman alkairi, dan kuwa dawowarsa ta canja tsarin zamansu gaba ɗaya, babu abinda zatacema ALLAH sai dai godiya akan hakan.
Dan yanzu Yah Ahmad hankalinsa baki ɗaya akanta yake, yana ƙoƙarin ƙyautata mata, suci kuma mai daɗi koda dai bamai yawabane.
Gefe kuma ya ƙara mata jarin dubu biyu akan nata nada ta ƙara kayan maƙulashe na yara da take saidawa a gida, wanda a hankali zuwa yanzu yaran anguwar sun gane, sukan shigo su saya.

Satin Ahmad uku yay haramar komawa porthercout, tafiyar tasa tai dai-dai da kammala jarabawar su Umm-Ruman da kwana biyu kacal.
Da farko baba birkicewa yay akan Ahmad bazai sake komawaba, tunda a tafiyarsa ta farko ya saɓa masa alƙawarin zai zo gida da wuri amma baizo ɗinba saida ya kwashe wata ɗai-ɗai har kusan shida, to yanaga idan kuma ya sake tafiya yanzun sai nan da shekara guda kuma.
Ahmad yay magiya yayi roƙo da nuna nadamarsa tare da bayanan da zasu fahimci abinda ya jawo daɗewar tasa a wancan karon amma sunƙi fahimta sam.
Harma ya haƙura da komawar ya kira Nura yace ya tafi kawai sai kuma ana gobe kamar yanda ya shirya Baban yace ya shirya yaje saboda malam yay masa magana akan ya barsa ya koma kawai, dan basusan alkairin dake cikin hakanba, gashi tun a zuwan farko sunga canji daga Ahmad ɗin.
Sai da baba yaja masa dogon gargaɗi akan amma wlhy karya wuce wata biyu.
Ahmad yayi godiya sosai, tun a daren yay musu sallama da abokansa ya nufo gida.
Tunda ya sanarma Rumana maganar tafiyar sai duk tai laƙwas, dan a yanzu tamafi jin zafin rabuwar tasu fiye data farko.
Ganin yanda duk tai la'asar saiya shiga kwantar mata da hankali, tare da kalamai masu sanyi, bayan soyayya mai tsayawa a rai daya nuna mata a wannan daren.

Kiran sallar farko na asuba ya tashi yay wanka, ya kimtsa tsaf sannan ya wuce masallaci, ana idar da salla bai zaunaba ya shigo gidan, duk yayma mazan gidan da suka dawo daga masallaci tare sallama.
Tunda ya dawo Umm-Ruman taki yarda ta kallesa saboda hawayen da takeyi, shi kansa dauriya kawai yakeyi, ya cire sim card ɗaya daga wayarsa ya bar ɗaya, gabanta yaje ya zauna a kan sallayar suna kallon juna, dukda ita ta duƙar da kanta taƙi kallonsa.
Ya haɗiye abu mai ɗaci daya tokare maƙoshinsa tare da kamo hannunta ya riƙe cikin nasa yana murzawa a hankali.
“Haba Babie R, maimakon na samu ƙwarin gwiwa daga gareki saikiyita kuka kuma? Na zaunefa baiga gariba, akwai abubuwa masu muhimmanci a gabanmu, idan ban tashi na nemaba wazai bamu?, maganar karatunki kwanan nan zakiga jarabawarku ta fito, fatanmu kufita da results masu ƙyau, dukda su baba sunce su Fa'iza aure zasuyi inhar mazansu sun amince zan ɗauki nauyinsu kutafi makaranta, dan yanzu anzo zamaninda sai kanada ilimi ake yi dakai, kimin addu'a kinji, namiki alƙawarin insha ALLAHU wannan karon bazan daɗeba zan zo, dan tunaninkima bazai bar zuciyata ta hutaba da har zan iya jan lokaci mai tsayi ban gankiba, nangaba kaɗan duk inda zan saka ƙafa kema taki na wajen, dan bazan iya nisa dakeba sam kinji�?.
Ba tare data ɗagoba tace, “Kayi haƙuri yaya na daina kukan, ALLAH ya tsare mini kai aduk inda ka tsinci kanka, ya azurtaka da samun halali mai albarka, ya nisantaka daga haramun komin farincikin da zata kawo maka, ALLAH ya kareka daga sharrin duk wani abu mai sharri, ya baka ikon cika alƙawari a sauke nauyinmu dake kanka�?.
Ahmad yay sassanyan murmushi yana sakin hannunta ɗaya ya ɗago fuskarta, hawayen ya share mata yana faɗin, “To kukan ya isa haka ko, nagode da addu'arki gareni�?.
Kanta ta jinjina masa tana haɗiye kukan tare da masa murmushi.
“Yauwa Babie na kokefa, ga waya nan insha ALLAHU kullum zakijini karki damu kanki�?.
Da mamaki ta kallesa ta kalli wayar, “Yaya yazaka ɗauki wayarka mai tsada ka bani, kaikumafa to?�?.
Murmushi yay mata yana shafa fuskarta, “Umm-Ruman duk tsadar wayarnan batakai ko darajar yatsan hannunkiba balle ke kanki tafi ƙarfinki, karki damu ALLAH zai buɗa, insha ALLAHU zan sai koda ƙaramace kafin muga abinda ALLAH zaiyi, kinga zata ɗan ɗauke miki kaɗaici kina ɗanyin kallo idan babu abinda kikeyi kinji, wannan karonma duk abinda kike buƙata Mudanseer zai kawo miki, ga wannan dubu ukun ki riƙe a hannunki saboda wani abun nasan ba iya tambayarsa kikeba dan dukya gayamin komai, ALLAH yay miki albarka kinji�?.
Godiya sosai Rumana ta shiga yimasa, farinciki da kaunarsa na sake mamayeta, haka ya mike ya ɗauki ƴar karamar jikkarsa daya saka abinda zai buƙata, itama mikewar tai ta rakosa har soro tana cigaba da share hawayenta.
Har zai fita ya dawo da baya, hannu biyu ya kamo fuskarta ya haɗe bakinsu, kusan minti ɗaya sannan ya saketa cikin sauke numfashi da sarƙewar halshe yace, “I love you so much Umm-Ruman, zanyi missing ɗinki da komanki�?.
Jikinsa ta faɗa tana fashe masa da sabon kuka, dan kalmar daya furta tazo matane a bazata, bai taɓa furta mata itaba sai yanzun, bayanta ya shafa yana murmushi, kafin ya janyeta daga jikinsa a hankali ya juya ya fice zuciyarsa na suya.
Rumana ta jingina da bango tana cigaba da kukanta, ta ɗauki kusan minti biyar a wajen sannan ta koma cikin gida..............✍�?



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(26)*


............Gaba ɗaya yinin ranar haka ta yini sukuku fuska babu walwala, su maman Ama sunyi gulmar harsun gaji, har dare bata iya sakin jikintaba, dan koda su Salima sukazo bata shiga sabgarsuba, tunma suna tsokanarta har suka koma tausayinta da lallashi.
Washe garima dai zuciyarta duk babu sukuni ta tashi, gashi ta gwada Number ɗayan layinsa daya cire amma bai shigaba, hakan ya tabbatar mata dai yana a ƙasa ɗin tunda dama babu waya ya tafi.
Su Salima na gama tayata aiki suka tafi gida, ita kaɗai suka bari tunda yanzu babu makaranta, sai islamiyya.
Kwanciyarta tayi a ɗaki, alwala kawai ke fiddota, abincima ƙin dafawa tai sai shayi ta haɗa tasha ta sake kwanciya.
Kusan bayan la'asarne tana kwance tajiyo hayaniya a tsakar gidan, bata motsaba balle ta fita, dan daga ɗakin tana iya jiyo komai, kishiyar Kausar ce tazo gidan ashe take ciwa maman Ama mutunci akan munafunci data saka Kausar ta ƙulla musu wajen mijinta akan biyan kuɗin makarantar yaranta.
Hayaniya dai sosai har maƙwafta suka shigo, wasa-wasa dai saiga gida ya cika, dan yanda nakeji ana hayaniyar sosai kamar za'a fasan bangon ɗaki kawai ya isheni amsa.
Har sukaci suka tsire bayan mijin maman Amatullah ɗin ya shigo aka raba daƙyar ban leƙaba, sai fatan shiriya da nake nema musu kawai.
Tun daga wannan ranar maman Ama da Kausar suka shiga gaba, babu mai kula wani a cikinsu, nidai nawa kallone, duk da kowannensu yana neman laɓewa ya shigo jikina danya soki ɗan uwansa, sam bana basu fuska nikam, danaga ma abin zai zama takura saina koma yin har wanke-wanke a babbar robata a cikin ɗaki kawai, dama dai shike fiddoni tsakar gidan harna daɗe asamu damata, wani lokacin kuma su Fa'iza keyi.

Ranar da Yah Ahmad ya cika kwana goma da tafiya ina kwance a ɗaki bayan sallar zuhur ina kallon film ɗin da Abu ya turomin a waya kira ya shigo, ɓaro-ɓaro Number Yah Ahmad da yay save da suna *My N2* ta bayyana, wani farin ciki ya kamani, na lumshe idanu ina haɗiyar numfashi da sauri-sauri, kamar maijin tsoron taɓa wayar haka na danna alamar amsawa, kafin nakai wayar kunnena a hankali.
Dagani harshi babu wanda yay magana kusan Seconds goma.....
“Babie R�? ya Ahmad ya faɗa a hankali cikin katse shirunmu.
Idanu na sake lumshewa ina murmushi, nima na amsa a hankali da faɗin, “Uhyim Yayana�?.
“Har yanzu dai Yayan?�? ya sake faɗa cikin sanyaya murya.
Dariyace taso kufcemin yanda yay maganar irin kamar a shagwaɓa ɗinnan, na danneta da ƙyar, amma sai jinai yace, “Dariyama kike mani ko? Babu damuwa zan rama ai nima�?.
“Ba dariya nakeba fa Yaya, ina yini?�?.
“Badai haƙura zanba saina rama, ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?�?.
“Alhmdllh Yaya, sai dai kewarkafa�?.
Daɗi ya kama Ahmad jin furucin Rumana, yay murmushi mai sautin da har take jiyowa, “Nima hakan take Babie R, gaskiya kice na dawo gida�?.
Dariya Umm-Ruman ta sanya masa, dan yanzun kam ciki shagwaɓa yay furucinsa na ƙarshe, tace, “Tab ai yayana idan ta nice ka dawo da gudu ma, to amma kuma banason ka wahala, kai zamanka ina nan ina maka addu'a�?.
“Da gaske Babie na?�?.
“ALLAH kuwa yaya�? tai maganar da alamun jin kunya.
“Tom shikenan ta hannun damar, yanzu miye labari?�?.
“Labarai kam da yawa yayana�?.
“To wanne zan samu daga ciki?�?.
“Saika zaɓa ka darje�?.
Yace, “Inye kaga Ahmad ɗan gatan Ruman, to abani na soyayya�?.
Siririyar dariya Rumana tayi tana rufe fuska kamar tana gabansa, tace, “Kai yaya ALLAH sai nake ganin kamar ba kaiba�?.
Dariya sosai ta bashi shima, dan haka ya shigayin kayansa, “Wato kamar ba niba ko? To ai kece kika maidani hakan Babie R, shiyyasa nake yaba ƙoƙarin ki, dan na kula da zafinki kikazo dan kin tsare ko ina babu wasa�?.
“Nagode Yayana�? Rumana ta faɗa tana share hawayen jin daɗi dake silalo mata saman fuska.
“Nine ya kamata na gode miki babie na, yanzu dai ki huta abinki, muna kasuwane, dama nakirane saboda yanzun nan na ɗora layin akan waya, idan muka tashi zan kira kinji�?.
“To Yaya ALLAH ya bada sa'a, sai anjima�?.
“Okey babu damuwa, amma idan na sake kira karnaji wannan Yayan�?.
Murmushi Umm-Rumana tayi, koda ya yanke saita sumbaci wayar tana rungumeta a ƙirji.
Tun daga wannan kiran sai yazam kullum da daddare Yaya Ahmad saiya kirani, nikuma nakan kirashi da safe na gaishesa.

Ɓangaren su Maman Amatullah kuwa sunyi gabarsu ta kusan sati uku suka koma suka sake ɗinkewa kuwa, a raina nace kudai aiki ya sama.
Tunda kuma suka ƙyalla ido suka ganni da babbar waya a hannu duk sai hankulansu ya tashi, a daren ranar muna jiyo Kausar na tafka rigima da mijinta akan sai ya saya mata babbar waya.
Shiko yace baida kuɗi yanzu, idan zatai hakuri da tata tayi, idan bazataiba to saita sayama kanta shidai baida.
Wannan furuci ya kawo musu rigima sosai, dan har cemasa take mijin Umm-Ruman ɗan balaguro da bai kaisa komaiba gashinan ya sayama matarsa tana ɗaga musu hanci a gida da ita, wlhy bazata cigaba da riƙe waya mai madannaiba itama ƴar shafi ɗinnan takeso mai shan jini.
Wannan al'amari ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login