Showing 147001 words to 150000 words out of 165545 words
Kai Ahmad ya dafe, yasan Haysam yarone mai matuƙar wayo da basira, kullum ta ALLAH kuma ƙwalwar kansa faɗaɗa takeyi, ya sake girgiza masa kai, ƙasan ransa na tunanin wace amsa zai bashi ya huta.....
Durƙusawar da Rumana itama tayi kusa da shine ya sakashi kallonta, ta dafa hannun Ahmad dake a kafaɗar Haysam tace, “Babana tausayin Abbunka nefa ya sakani hawaye, kaga abu ya faɗa masa cikin ido, amma kuma sai yake gayamin naji tsoron ALLAH a duk inda nake, karna ringa shiga maganar manya, karna ringa shiga abinda ba'a sakaniba, karkuma na saɓama UBANGIJINA, idan nayi akan kuskure na nema gafararsa, dan dukkan mai saɓama UBANGIJI to ƙarshensa baya ƙyau, hakama mai saɓama iyaye baya gamawa da duniya lafiya, wuta ake sakashi, sannan MANZON ALLAH baya cetonsa a ranar kiyama.......�?
“Ummie!�? Haysam ya kirata cikin katseta.
Ta amsa da “Na'am Haysam�?.
“Ummie ita lahirar to a ina take?�?.
Kallon juna Ahmad da Umm-Ruman sukayi, sai kuma duk suka maida kallonsu ga Haysam ɗin.
Ahmad yace, “Lahira ba'a ganinta, sannan babu wanda zaice maka yaje ya ganota balle ya baka labarinta, sai dai UBANGIJIN al'arshi ya bamu labarinta a littafinsa mai tsarki na AL-QUR'ANI, a wajaje daban-daban, yayi mana bayanin abubuwa masu yawa da zasu faru a cikinta, duk wanda ya mutu a yanzu yana barzahu ne, sai ranar da za'a busa ƙahone kowa zai tashi yaga kansa a lahira, harda ƙwari da dukkan nau'in kowacce halitta da UBANGIJI ya taɓa rayawa a doron duniya�?.
Nanma dai shiru Haysam yayi, dan maganganun sun masa girman da bai fahimci komaiba a cikinsu sai ƙalilan, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru saboda chocolate ɗinsa daya hango, dama ita yazo ɗauka.
Jikinsa ya zame daga garesu yaje ya ɗauki abarsa ya dawo jikin Ahmad ya zauna yana bashi akan ya ɓare masa.
Amsa Ahmad yay ya ɓare masan, yana amsa ya miƙe yafice yana ƙwala kiran sunan Aunty Zainab.
Da ga Ahmad har Umm-Ruman ajiyar zuciya mai ƙarfi suka sauke suna kallon juna, Rumana ta kwanto jikin Ahmad shiko ya rungumeta.
“Abu Haysam!�?
Ta kira Ahmad murya a narke.
Idonsa a kanta ya amsa da “Uhyim Umm-Haysam!�?.
“Daga yau karmu sake ɓoye masa abu mai muhimmanci da ya shafi rayuwa ko addininmu, ƙwaƙwalwarsa a yanzu a wanke take, komi muka sanar masa zai zauna a cikinta, zama irin na har abada, zai kuma riƙesu a ransa su amfanesa harma da yaran da zasuzo a bayansa�?.
Kanta Ahmad ya shafa tare da sumbatar laɓɓanta, sai ya zarce da kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ture kansa tana faɗin, “Yaya wlhy yaronnan zai iya dawowa�?.
Murmushi yayi yana lumshe idanunsa da har sun kaɗa sun canja launi.
★★�?**★★★★�?**★★�?
Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa, yau fari gobe tsimma, su Umm-Ruman anata karatu da rainon ciki, sunyi ƙawaye da suke ƙaruwar juna, kafin wani dogon zango larabci ya zauna raɗam a bakin Umm-Ruman.
Wannan cikinma ya sakata tayi ƙiba fiye da na Haysam, hakan yasa ta zama wata babbar mace ga ƙyawun da ya sakata, Ahmad kansa idan suna zaune bai gajiya da kallonta, kowane motsinta idonsa na kanta, ita harma kunya abin ke bata.
Ba kowa yasan Rumana nada ciki ba, dan Yaya Maryam tai gum da bakinta akan maganar, saboda gudun shaiɗancin su mama Gaje wadda tana gidansu kam cikin wani irin yanayi mai wahalar fahimta.
Suna waya da mutanen gidan kuma kullum babu fashi, sai dai yawan rashin lafiyar da takance tanayi wasu ke zargin ko cikinne.
A haka dai a kwana a tashi cikinta ya cika watannin haihuwarsa, wata safiyar Juma'a ta tashi da naƙuda, Ahmad na ƙoƙarin shirin yin massalaci dole ya ajiye ya kira Gaddafi suka ɗauketa a motarsa harda matar Gaddafin suka nufi asibiti.
Suna isa ma akaga haihuwar ta rigada ta taho gadan-gadan, dan danan aka shiga bata taimakon gaggawa.
Wannan haihuwar Rumana taci wahala, kafin ALLAH yasa ta sunkuto ɗanta namiji mai kama dasu sak.
Murna wajen wannan ahali ba'a magana, kafin su baro asibitin har labari yakai Najeriya, kowa yanata mamakin wannan al'amari tunda dai ba'asan Umm-Ruman nada cikinba hasashene kawai wasu keyi.
Hotunan yaro kam sunata yawo a wayoyin ƴan uwa, anatama juna barka da arziƙi.
Bakin Ahmad kam ai yaƙi rufuwa, ita Rumana ma har mamaki take, sai kace yaune aka fara masa haihuwa.
Kasancewar jikinta Alhmdllh zuwa safiya aka sallamesu suka koma gidansu, Jiddah matar Gaddafi ita ke tsaye akan Rumana da komai, sai wata dattijuwar balarabiyar ƙasar Morocco da suke a ɗayan sashen gidan, itama taketa gyara Rumana tamkar ƴar uwa ta jini, dacan sukan gaisa, idan taga Haysam taita jansa, wani lokacinma jikokinta kanzo su ɗauki Haysam ɗin. to amma wannan haihuwar ta Umm-Ruman sai ta sake ƙarfafa zumincinsu sosai fiye da da can.
Tun randa Ruman ta haihu Ahmad yayma yaronsa huɗuba da suna Yusha'u, sunan ƙanin babansa, kuma mahaifin Umm-Ruman, zasu ringa masa alkunya da *_Abu-Talib_* Uncle ɗin MANZON ALLAH (S.A.W).
“To sai muce ALLAH ya raya Abu-Talib�?.
Ba'ai wani taron sunaba, amma dai sunɗanyi walimar cin abinci ta abokan Ahmad na karatu dana Gaddafi, sai maƙwaftansu.
Hakama ƙawayen su Umm-Ruman na makaranta sunzo suma.
Jama'ar gida nata ALLAH ya raya mai sunan baba Yusha'u.
Haka Rumana taci gaba da rainon yaronta Abu-Talib tare da karatunta, shima yaron dai masha ALLAH, yana kama da Haysam, rayuwa ta cigaba da shuɗawa komai na sake cigaba gasu Rumana, rayuwar gidansu abin sha'awa da burgewa, hakama ƴaƴansu kamar ka sace ka gudu, idan saɓani yazo a saɓa, a kumazo a fahimci juna komai ya wuce.
Kafin wani dogon zango Abu-Talib ma ya kai girma, shima Rumana ta yayesa ba tare da Ahmad ya saniba, dan tasan zai iyayin faɗa.
Ranar da akai yayen gudunma kar yay mata kuka ta banka masa maganin barci tace mura yakeyi, da yake Ahmad a gajiye yake daga makaranta sai bai kawo komai a cikin ransaba ya yarda, washe gari ma haka taima Abu-Talib, sai da ta jera kwana huɗu tana haka, ta dai fahimci yaron ya ɗan manta da nono sannan................✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_8448_*
...........Sai a ranar da Abu-Talib ke cika sati ɗaya da yaye Ahmad ya fahimta, kasancewar Juma'a ce babu makaranta, sun dawo daga massallaci shi da Haysam sai yayo musu tsaraba irin ta yara, to anba Abu-Talib nashi amma kuma na hannun Haysam yakema zari, dan haka yaketa ƙoƙarin kwacewa, shi kuma Haysam ya hanashi.
Su dai su Rumana na kallonsu suna dariya, saboda yanda ake kicimillin rigimar dolene kai dariya, Abu-Talib akwai rigima, ga zafin nama na hanzari da ALLAH yaba yaron, ko zazzaɓin haƙora yake inba yakai matukar kaisa ƙasaba, baya hanashi yin wasa, sai dai su suyita jin tausayinsa. Zainab kuwa tana ɗaki kwance tasha magani saboda zazzaɓi da takeyi.
Can rikici yay rikici Haysam yaji zafin tsole masa ido da Abu-Talib yayi wajen son amsar abun hannunsa, shi ko ya tureshi ya faɗi, aiko ya fashe da kuka dan yaji haushi.
Rumana ta ɗauki Abu-Talib ɗin tanama Haysam faɗan abinda yayi.
Ganin yaƙi yin shiru bisa lallashin da Ruman ke masa Ahmad yayma Rumana magana akan ta bashi nono mana ƙila yay shiru.
Murmushi kawai tayi tana cigaba da lallashin Abu-Talib.
Ahmad da yay zaton batajisaba ya sake maimaitawa, nanma sai tai murmushin tana faɗin “Karka damu Yaya zai shiru, ya riga ya girma da nono ai�?.
Da mamaki yake kallonta, tare da nuna alamun bai fahimceta ba.
Yace, “Wai kina nufin mikenan? yayesa zakiyi?�?.
Tace, “Ai nama yaye ɗin�?.
Ahmad yay masifar tsura mata idanu, sai dai fuskarsa ta nuna alamun ɓacin rai, hakan yasa Rumana da ta fahimta sai ta ɗauke kanta, dan tasan dama za'ayi hakan ai inhar ya sani, ko na Haysam ma dan baya ƙasarne.
Baice mata komaiba a lokacin, sai dai kuma hirar da akeyi yabar yinta, daga ƙarshema ya ɗauki Haysam ɗin tare da amsar Abu-Talib da ga hannunta suka fice.
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai, ita dai bataga abin fushi ananba ai, shekara ɗaya da wata bakwai miye laifi idan ta yaye Abu-Talib dan ALLAH?.
Bata da mai bata amsa dan haka ta share ta cigaba da harkokin gabanta kawai.
Tun tana tsammanin dawowarsu kusa har magriba babu labarinsu, ta taso Zainab dake kwance saboda magriba.
Haka tai zaune ita kaɗai shiru har tara na dare, dan Zainab ma ta sake komawa ta kwanta.
Tana shirin barci suka shigo, ya kwantar da Abu-Talib dake a kafaɗarsa yana barici, Haysam kam ido ras, sai zuwa yay ya rungume ƙafafun Rumana yana fadin, “Ummie oyoyo�?.
Juyowa tai tana murmushi, tace, “Babana kun dawo?�?.
Tai maganar tana satar kallon Ahmad da ke ƙoƙarin shiga toilet fuska babu walwala..
Haysam kuwa na ƙoƙarin bata amsa, da labarin inda sukaje.
Sam hankalinta baya a kan yaron har Ahmad ya fito, yazo ya ja Haysam ya cire masa kayan jikinsa sannan ya ɗaukesa zuwa bathroom, tana nan zaune suka fito yayi masa wanka, ita dai batace komaiba harya gama shiryashi ya tafi kaisa ɗakin Zainab inda yake kwana yanzun.
Yaɗan jima kafin ya dawo, tasan yanacan yana lallaɓa Haysam yay barcine.
Ita kuma lokacin tanama Abu-Talib wankane yana kuka, ta kammala ta fito tai masa shirin barci shima ta bashi tea, ƙinsha ma yayi, data fahimci a ƙoshe yake saita ƙyalesa kawai ta kwantar dashi.
Alokacin ne Ahmad ya dawo ɗakin, nanma ɗindai bai kalli inda takeba, ita dai ta daure ta tambayesa ko akwai abinda yake buƙata?.
Sai cayay mata a'a.
Shiru kawai tai tana kallonsa, ya shiga bayi yayo wanka ya fito yay shirin barci, har lokacin idonta biyu kuma tana zaune.
Koda ya kammala shirinsa sai ya kwanta tamkar baisan tanayiba.
Zuwa can itama ta gaji da zaman da tunane-tunane ta matsa jikinsa ta kwanta tana gyara musu bargo.
Ahmad najinta amma sai baiyi ko motsiba, tai guntun murmushi kawai tana lumshe idanu, hannunta nakan ƙirjinsa tana yawo dashi.
Tace, ”Haba Zumana, minayi haka da zafi ake irin wannan fushin dani ne wai?�?.
Shiru yay mata tamkar bai jiba, bata gajiba dai ta sake maimaitawa, nanma yay shiru, itako bata fasaba ta cigaba da neman harmutsa masa tunani.
Da Ahmad fa yaji yana neman hawa Network gashi yana fushi sai yay saurin riƙe mata hannu, “Miye haka wai Ruman? Ki barni barci nakeji�?.
“Yaya ya za'ai na bari bayan kana fushi dani? Yanzu yayen da nayi shine laifi dan ALLAH?�?.
A matuƙar fusace ya juyo gareta yana faɗin, “Okey bama abune mara ƙyauba kikayi? Yanzu ace Umm-Ruman ina cikin gidannan harki yayemin yaro ban saniba? Duka shekararsa nawa? Ɗaya fa da wata bakwai, saurin mikikeyi da bazaki barshi ya cika shekara biyunba? Okey ke yanzu kin girma ko? Duk abinda kikaji yuwuwarsa cikin rai baƙya buƙatar kowa a cikinsa, hakafa kika yaye Haysam ban saniba, nai miki shiru a lokacin shine yanzuma kika sake saboda kin gama rainani ga sa'anki ko......?�?
Innalillahi kawai Rumana ke ambata, ganin yanda ya birkice da masifa tamkar ba shiba, akan ƙanƙanin abunda ita bata kallesa wani abun kirki ba.
Sai da ta bari ya gama sannan, ita dai batace uffanba, ranar ma kwanciya kowa ƙarshen gado yay barci, tasan ko haƙuri ta bashi sai dai ta sake tunzurashi yay sama, to garama tai shiru da bakinta yafi alkairi, idan ya huce daga baya ta bashi haƙuri.
Da safe kuma yay ficewarsa makaranta bayan yasan tana kicin tana ƙoƙarin haɗa musu karin kumallo.
Koda ta fito taga ya fita hakan ya mata bala'in ciwo a rai, har ƙwalla tayi, ita dai wannan saurin fushin na Ahmad bata sonshi sam wlhy, gashi da mitar fushi, idan yay zuciya takan jima bata shawo kansa sun dai-daitaba, danma dabarun da Iya ta bata tana ƙoƙarin aiki dasu, dan lokacin bikin su Fa'iza da suka ɗan daɗe a gida akwai randa Haysam ya faɗo daga kan gado yana barci, ita dai tasan a tsakkiyar gado ta kwantar dashi, yaronnan wajen mirgina-mirgina ya dawo gefe, daga ƙarshe ya faɗo ita kuma tana waje suna hira da iya, tofa sai faɗowar Haysam tai dai-dai da shigar Ahmad ɗakin, ya nufesa da gudu ya ɗaukesa, yaro yayta kuka, iya ta amshesa tana dudduba jikinsa sai ta fahimci yaji ciwone a hannu, ta kaisa wajen Malam ya duba sai ya tabbatar ciwo yaji, a take malam yay masa gyara saboda ya iya, aka sakamasa magani. To aiko wannan lamari ya zafi Ahmad, danshi a ganinsa laifin Rumana ne data kwantar da Haysam a bakin gadon saboda sakaci, haka ya zauna ya zazzaga mata masifa a ɗaki daga ƙarshe ya koma fushi, Rumana taci kukanta a ɗaki ta share hawaye, kwana biyu basa kula juna Iya na lure dasu, sai dai yanda basu faɗaba itama bata tankaba, sai aranar na ukune suna gab da komawa Porthercout Iya ta zaunar da Rumana tana koya mata dabarun zama da Ahmad ɗin. ta kuma tabbatar mata mafi yawan halayyar Ahmad ya samosune daga kakansu Malam Rabi'u mijinta, shiyyasa idan Ahmad ɗin na abu takan tuna ƙuruciyarsu da Malam sosai. Umm-Ruman taji daɗin wannan shawarwari na Iya, da sune kuma take samun damar fuskantar Ahmad ɗin a duk lokacin da yayisa.
Itama kasa cin komai tayi, sai Haysam da Zainab ne sukaci, shima Abu-Talib ta bashi nashi da yake iya ci sannan sukai shirin fita.
Kwana biyu yana haushi da ita, a na ukun kuma ta ƙara durƙusawa har ƙasa ta bashi haƙuri tana hawaye da amsar laifinta.
Sai da taita masa magiya kafin ya nuna ya haƙura tare da mata gargaɗi sosai akan karta sake.
A take ta rungumeshi, daga nan aka canja tasha zuwa wadda tafi ƙarfina🥱🤫.
“Dama ance faɗan masoya hutu😂⛹♀�?.
***********************
Rayuwa ta cigaba da shuɗawa su Rumana ana shekara ta Uku a makaranta, yayinda Ahmad yaketa ƙoƙari akan nasa karatun shima, dan haka sam baya wasa da damarsa.
A lokacin shima Abu-Talib an sakashi a makarantar su Haysam, hakama Subayya ɗiyar Gaddafi, yanzu hakama Jiddahn ciki gareta tsoho itama.
Bayan shuɗawar wasu watanni Jiddah ta haihu namiji, su Rumana akasha hidima.
Itama babu jimawa sai ga wani cikin, nanma dai Ahmad yata murna tamkar ya goyata, inda itakam bataso cikinnan yanzuba kodan karatunsu da ya ɗauki zafi yanzun, amma sai bata nunaba ta godema UBANGIJIN da ya bata, dan inharma Ahmad ya fuskanci hakan daga gareta lallai zasuyi uwarwatsine kawai..
Haka dai ta cigaba da rainon cikin nan, da sauƙi shi bai cika bata wahala ba, sai dai yawan son abu mai sanyi da takeyi.
Zainab ma ta cigaba da karatunta a sashen lafiya a wata makaranta dake Riyadh, dan haka acan take zaune gidan wani abokin Gaddafi balarabe ne shima da matarsa ɗaya da yaransu biyu, su ƴan asalin ƙasar Saudiyya ne, yanzu idan ka ganta wajen su Rumana weekend