Showing 132001 words to 135000 words out of 165545 words

Chapter 45 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

391

akwai kuma wani sabon malami da sukajiyo zasuje mata wajensa, daga mufidan har Ma'aruff ɗin sun kusa maganinsa.
Samina ta ɗanji daɗi, dan haka ta koma ɗakinta da ɗan ƙwarin gwiwa.


__________________________________


Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan kuwa lokacin bikin su Salima yazo, ana saura kwanaki huɗu su Rumana suka taho kano.
Cike suke da ɗoki tamkar waɗanda akaima gafara, wannan karonma dai sunsha wahalar ita da Zainab, Haysam kam abin mamaki ko gezau yaronnan, hakan yasa Ahmad yayta musu dariya akan Haysam ya fisu ƙarfin jini.
Sosai gida ya kacame da murnar zuwan su Umm-Ruman, kowa yana mamakin dunbin canjin daya gani a garesu cikin watanni takwas kacal, musamman ma Umm-Ruman data fara zama matar manya, ga Haysam ya zama ɗan saurayi, hakama Zainab ta ƙara girma.
Umm-Ruman nata addu'a akan kar Ahmad yace su tafi can gidan, sai bayan magriba takeji wajensu Fa'iza akan ai an kwaso kayanta daga can gidan, akwai wani ɗan fili a lungun su Iya an haɗesa da wani ƙaramin ɗaki, Ahmad ya gina musu ɗaki a wajen, yanzu haka kayansu duk suna can.
Duk da taji sanyi a ranta sai kuma taga da kunya, yanzu kenan gaban iyayensu zasu zauna ko yaya? Koda yake tana ganin dan dai ba zama zasu rinƙa yiba yanzu shiyyasa.
Bayan isha'i kuwa Ayyah ta kora Rumana can.
Ɗakine guda ɗaya, sai dai babba dan yafi ɗakinsu na gidansu Maman Ama, wannan kuma yayi musu ƙaramin banɗaki na wanka a ciki, sannan anja katanga a gaban ɗakin babu mai ganin wani suda su Iya.
An jera kayanta duka anan, ɗakin yay ƙyau sosai.
Juyowa tai tana kallon Ahmad daya fito daga bayi, yay murmushi yana faɗin, “Surprise Babie R�?.
Jikinsa ta faɗa tana dariya, “Wlhy da gaske kuwa ka shammaceni, yaya koda wasa baka taɓa sanarmin mun baro gidancanba�?.
Bayanta ya shafa yana faɗin, “Ai dama nace sai kinzo ƙya gani, na gaji da ganinki cikin magulmatan matancan ne, duk da dama dai yanzu ma ta ƙare, tunda ko bamu baroba ba zaman garin mukeba�?.
“Hakane Yayanmu, amma gaskiya wannan dabarar tayi, kaga kuɗinma hayar ai sun isa su kare mana wata lalaurar, ɗakin yayi tsari da ƙyau sosai�?.
“Da gaske?�?.
“ALLAH kuwa yaya�?.
“Kinga kuwa malam ne ya kawo wannan shawarar wlhy�?.
“ALLAH sarki tsoho mai ran ƙarfe, wlhy hakan yayi, ALLAH ya sanya alkairi�?.
“Amin gwal ɗina�?.

Har washe gari su Rumana suna amsar ƴan sannu da zuwa da ƴan ganin ƙwaƙwaf..........✍�?


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_43M_*



.............An tsunduma cikin hidimar biki da Ahmad keta samun ALLAH shi albarka, dan kuwa ya taka rawar gani sosai, shine yayma amare kayan ɗaki na gado, ya kuma ajiye isashen abincin da akaci gwargwadon ƙarfinsa, sannan ya danƙama Gwaggo kuɗaɗe masu dama itama akan taima Fa'iza siyayyar kayan kicin ta hannun ƙanwarsa Raheenatu.
Iyayensa suma dai sun ɗauki girman sun tattara sun bashi, dan shine ya bada auren ƙannen nasa.
Hakan ba ƙaramin ƙayatar da mutane yay ba, Ahmad kam sai yaji kamar yay kuka, dan abun ya masa girma da yawa.
Bayan kammala ɗaurin aure mata suka cigaba da hidima a cikin gida, amare dai suna ɗakin Umm-Ruman, sunsha ƙyau harsun gaji.
Gida cike da mutane, anata kaikawo da taya juna murna, inda abokan wasa suka saka Mudanseer a gaba da magana akan saura shi.
Shiko da ko budurwa baida sai abun yayta bashi dariya, duka nawa yake da za'a ishesa da wani zancen aure, Yah Ahmad yaushe yay aurenma duka-duka, shima sai ya shana sosai kafin yayi.

Su Rumana duk suna a sashensu Ahmad anata hidima, saboda girma da ake bama Baba Hamza sai yazam kamar komai anan akayi, sannan ma Ahmad shine ya ɗaura auren, ga kuma dangin Gwaggo dana Ayyah, can ɓangaren su Salima sai yazam dangin mamantane kawai da abokan arziƙinta, ƴan shema kuwa duk suna a sashen su Samina, amare da ƙawayensu na sashen su iya inda su Umm-Ruman suke yanzu suma.
Rabon da taga Ahmad tun kusan goma na safe, ko wankama ba anan yayiba, ɗibar kayan yay ya fita tunda safen.
Bayan kammala ɗaurin aure kuma Mudan ne ya fita da abincin abokansa da yace ta ɗiba ta ajiye. Sai Abu daya aiko ya amshi Haysam shima.

Samina ta shigo sashen, duk ta rame, sai farin bilicin daya maidata kamar wata aljana, tunda aka fara hidimar bikin nan sai yanzu ake ganinta a gidan, dan bata leƙoba ko sau ɗaya sai yau.
Tunda tazo kuma suna ɗaki ita da su mama gaje, sai da binta yayarta taje ɗakin kaima su Inna mari abinci take mata faɗa akan ita bazatazo ta gaisa da dangiba, bayan anata tambayarta.
Kamar bazatazo ba, sai dai mitagani oho mata ta taso ta fito.
Sai yauƙi take ita a dole matar mai kuɗi duk da kallo guda zakai mata ka fahimci rayuwarta a wajige take, sai dai idonta na sauka akan Umm-Ruman saita raina kanta, dan ita taƙama da sutura kawai takeyi.
Amma Umm-Ruman murjewar jikinta da ƙyawun data ƙara shine babbar amsar dake nunama duk mai kallonta tanajin daɗi, sannan tana tattare da tarin kwanciyar hankali a gidan aurenta.
Shigowarta abokan wasa sukai mata ca da maganar ai su sun zata batazoba ko tayi nauyi ɗan baba ya hana.
Sosai maganar ta soki ƙahon zuciyar Samina, cikin yaƙe kawai take gaisawa da mutane.
Koda ta iso wajen yayunta ta gaisa da kowa amma banda Rumana, koda Rumanan ma ta gaisheta da ƙyar ta amsa mata.
Ko a jikin Umm-Ruman, dan a halin Samina ai babu baƙonta kuma.
Duk yanda Samina taso barin wajen hakan ya gagara, dole ta zauna kodan neman ɗebe kewar damuwarta a hirar da ƴan uwanta keyi cikin kwanciyar hankali abinsu.
Sukam hankalinsu kwance suke hirarsu da dariya, har Rumana data nunama bata damu da abinda Saminar tai mataba sam.
Shigowar Ahmad dake ɗauke da Haysam a kafaɗa yana barci ya sakasu kallonshi su duka.
Yayi masifar yin ƙyau cikin dokakkiyar shadda kalar ruwan ƙasa mai duhu, sai maiƙo take da ɗaukar idanu, hular kansa ma dai kalar shaddar, hakama takalmasa, babu wanda zai kallesa yace Ahmad ɗin nan ne daya jigatu a soyayyar Samina, komansa ya sake canjawa, sai wani annurin kwanciyar hankali fuskarsa ke fiddawa musamman saboda gyaran da sajensa yasha.
Cikin tsokana wasu daga cikin iyaye ke faɗin ga “Uban amare ga uban amare�?.
Murmushi kawai yake faman yi, saboda masu maganar duk yayun Ayyah da Gwaggo ne da ƙannensu.
Samina da tun shigowarsa idonta ya sauka a kansa tai ƙasa da kai tana haɗiye wani busashshen yawu mai kauri, gashi Rumana kusa da ita take zaune, sai ma an wuceta za'a kai ga Rumanan.
Shiko da idonsa ke kan matarsa yace, “Haba Gwal, kina ganinmu bazaki taso ki tarbemu ba?�?.
Dariya su Yaya Maryam suka saka musu, Ruman dake murmushi ta miƙe ta nufoshi.
Samina da zuciyarta tai duhu da baƙin ciki ta maimaita sunan “Gwal�? a zuciyarta da Ahmad ya kira Umm-Ruman dashi ko kunyar mutane baijiba, da ƙyar ta iya maida ƙwallar data cika mata idanu tana satar kallonsu ta gefen idanu.
Rumana kuwa data isa garesa hannu ta miƙa masa danta amshi Haysam ɗin, amma sai ya girgiza mata kai da ƴar harara,
“Haba Babie R wanda ke barci za'a ɗauka? Ko dai goyo�?.
Ɓata fuska tai cikin marairaicewa tace, “Yaya goyo kuma? Salon ya ɓatamin kwalliyata�?.
Sosai yay murmushin da har haƙoransa suka bayyana, cikin ƙasa da murya yace, “Duk kwalliyar da bani akaimawa ba ai bata da wani amfani Gwal ɗina, kuma ina kishin duk wanda zai ganta koda matane�?.
Karaf maganar a Ahmad a kunnen Samina, saboda a kusa da ita suke, ji tai tamkar ta fasa ihu, da tasan zai shigo wajen nan da bazata taɓa zuwansa ba, Ahmad ɗinta data girma da soyayyarsa ne a gabanta yake furta kalami masu daɗi ga watanta ba itaba........
Wata ƙanwar Ayyah ce ta matso tana faɗin, “Ɗan gidan Ayyah kaga kawosa kaji�?.
Murmushi yayi yana miƙa mata Haysam da cewa, “A lallai yau ango zai more bayan uwargidansa�?.
Dariya tayi itama tana cewa, “ai bazanyi a batiba, idan ya tashi saina ranƙwashi kansa sau goma sannan, wane mijine haka babu kuɗin cefane babu ɗinki�?.
Dariya su Yaya Maryam suke musu da kare Haysam ɗin.
Yayinda Umm-Ruman da Ahmad suka koma murmushi sudai.

Barin wajen Ahmad yay zuwa ga iyayensa yana gaggaishesu, yayinda su kuma suke masa taya murnar an ɗaura aure, da ALLAH ya sanya alkairi, sai addu'a akan hidimar da yay.
Yaja wasu mintuna kafin ya dawo inda su Rumana suke, idonsa akan Umm-Ruman yace, “Gwal ɗina yunwa nakeji fa, a taimaka a bani abinda zan sakama hanjina, ke da Ayyah duk kun manta dani yau nikam�?.
Sosai Umm-Rumana kejin kunyar wannan Gwal da yake ambata a gaban iyayen da yayunta, amma yaya ta iya, tunda shi taga ko a jikinsa.
Miƙewa tai tana faɗin, “Yaya abincin gidannanfa duk ya zama saura, gashi bana tunaninma akwai tuwo duk sai shinkafa ta rage�?.
Yace, “Nikam shinkafarnan bana sonta gaskiya, bincika mani idan da fura ko ita sai na sha�?.
Amsawa tai da to, shi kuma ya nufi hanyar fita yana cewa idan ta samu ta bayar a kai masa yana waje wajensu Sufyan.
Ahmad na fita Samina ta miƙe tabar wajen, dan idan har tace zata cigaba da zama komaima zai iya faruwa da ita, dan bazata iya riƙe damuwarta ba.
Babu wanda ya damu da ita, kowa harkar gabansa yakeyi.
Rumana ta samo fura ta bayar aka kaima Ahmad ƙofar gida kamar yanda ya umarta.


★★★★★★★★


Bayan sallar isha'i aka shirya kai Salima ɗakinta, itako Fa'iza sai gobe idan ALLAH ya kaimu za'a nufi Shema da ita, daga can sai Katsina ta dikko ɗakin kara, dan can angonta zaizauna saboda acan yake aiki.
Salima ansha kuka kuwa, inda ta samu rakkiyar dangi da yawa saboda mijinta ɗan napep ne, sukazo kuwa gayya guda ɗaukar amarya, sai da kowa ya samu waje isashe kafin a saka amarya ita a mota a ɗinguma.
Umm-Rumana da ƙyar Ahmad ya barta wai zata kwasoma Haysam sanyi, ALLAH ya taimaketa Ayyah ta amshi Haysam ɗin ta goya hakan yasa ta samu damar tafiya.
Ɗan gidan Salima mai ƙyau ita kaɗai abunta, dan gidan kansane ba haya yakeba, aiko nan dangi aka shiga ƙananun magana akan ai abun ba'a dukiya bane zuciyace kawai, kowa yasan wannan habaici ana yinsa ne wasu Samina, wadda ita bama ta zoba tana gida abunta sai Binta ce taji zafin abun, sai dai tasan gaskiya mutane ke faɗa ai, tun barowar Samina wajen su Rumana tai zamanta sashensu bata sake fitaba, amma kowa ya ganta yasan tana cikin damuwa, dan har bayi ta shiga tasha kukanta, wani irin masifaffen son Ahmad takeji a ranta, musamman ganin datai masa yau shida matarsa da ɗansu, hakan ya kuma tada hankalinta, ɗan yaron mai ƙyau, da yanzu ita ta haifesa fa.
Mama gaje ta fahimci Samina tai kuka, sai dai bata da damar tambayarta saboda taron mutane.
Basu daɗeba aka kwasosu aka dawo dasu gida, sai kuma ALLAH ya kaimu gobe tafiya kai Fa'iza.



*_Washe gari_*


Washe gari akai shirin miƙa fa'iza, tunda wuri aka gama kimtsawa, itama tasha kuka fiyema dana Salima, bayan an kammala mata faɗa suka ɗunguma zuwa shema, dan sai anyi biki suma a can yau zuwa gobe su miƙata cikin katsina su juyo.
Kaf su Rumana ba'abar kowaba dasu aka tafi, Samina ce kawai batajeba, a ranar ma ta tarkata kayanta ta koma gida, dan inhar tace zata cigaba da zama a gidan zuciyarta zata bugane idan tana ganin Ahmad.
Tarba ta mutuntawa suka samu a shema, dan auren zumincine da kowa ke murna dashi, anta musu hidima sosai kamar a goyasu.
Haysam ya nema takurama Rumana da kuka ta banka masa maganin da yasakashi dogon barci, dan ya hanata rawar gaban hantsi bayan itama tana buƙatar taɗan warwasa😂.
Faɗa yaya Maryam taita mata kuwa akan haka, ita dai tai tsit tunda tasan bata da gaskiya.

Sun kwana sun hantse washe gari aka ɗauki Fa'iza suka sake ɗunguma cikin Katsina, itama ɗan gidanta mai ƙyau kuma ita kaɗai, kowa yanata sam barka.
Salla kawai sukai aka ɗan gyagygyara mata waje, dayake aikin yawane dan danan suka kammala, ƴan shema sukai gida, ƴan kano suma suka nufo kano cike da kewa da fatan alkairi ga ƴar uwarsu.

Sai takwas na dare suka iso kasancewar tafiyar yamma lis sukayo, Ahmad na kwance a ɗaki duk yanajin hayaniyarsu, tunda ya dawo sallar isha'i yay kwanciyarsa saboda gajiyar hayaniya.
Rumana bata shigo ɗakinba sai kusan goma, dan batai tsammanin yanama gidanba, da yamma sunyi waya kafin su taho yake faɗa mata sunje wani waje shida Sufyan.
Sannu yay mata, ta amsa tana kwantar da Haysam dake barci kusa dashi, bata zaunaba ta faɗa wanka dan shi take buƙata fiye da komai.
Bayan ta fito tai sallolin da suka riskesu a hanya na magriba da isha'i, har lokacin Ahmad na kwance barcima ya fara ɗaukarsa bayan ya gama tattaɓe Haysam.
Tashi tai ta fita neman ruwan zafin da zataima Haysam wanka, dan tasan inma batai masaba saiya farka, kuma hanasu barci zaiyi tunda ta rigada ta sabar masa da wankan kullum kafin barci.
Ahmad ma baisan ta fitaba sai motsin dawowarta yaji, idanu ya buɗe yana kallonta har tazo ta ɗauki Haysam ta cire masa kaya.
“Bakijin akwai sanyi garin nan Ruman, kibarsa da wankan nan�? yay maganar muryarsa da alamun son barci.
Tsayawa tai daga ƙoƙarin zame wandon jikin Haysam, tace, “Yaya wlhy jiƙe yake da fitsari a panpas ɗinnan, sannan rabonsa da wanka tunda safe a shema da Yaya Raheenatu tai masa, komun kwanta zai tashemu da rigima anjima�?.
Numfashi ya sauke da fadin, “To kardai ki zuba masa ruwa bisa kai, dan mura zata iya kamashi�?.
Da to ta amsa tana miƙewa zuwa bayi.
Tana zuba masa ruwa a jiki ya hau mata kuka, bata kulasaba saida ta kammala tazo tai masa shirin barci, tea ta haɗa ta bashi, dan yarigada ya fara girman da har tsoro take yace zaisha nono, dayakema baida damuwa komai aka bashi ci yake, sai dai yasha ya ƙoshi sannan itama ta miƙe tana shirin barci, shi kuma ya rarrafa jikin Ahmad dake barci-barci ido biyu.


*_BAYAN KWANA GONA_*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login