Showing 36001 words to 39000 words out of 165545 words
dan ALLAH kuma kubar biye musu, shima Mudan ɗin zan masa magana yabar shiga harkarta, tunda bata da kunya, duk yanda yake tunanin da da yanzu akwai banbanci�?.
“Humm su dai suka banbanta da son zuciyarsu ɗan albarka, indai duniya ce kuma gasu gata nan, wanda ma bai zoba jiransa takeyi, wanda kuma duk yasai rariya yasan zata zubda ruwa, ni lalacewar wannan aurenma tsakaninka da yarinyarnan alkairine, dan kuwa na lura duk halin uwarsu ta kwashe, kuzo ku haihu kanaji kana gani ƴaƴanku su tashi ba tarbiyya, yanzu kuwa ALLAH yay maka sauyin alkairi, gidannan kaf babu mai cewa ga halin Umm-Rumana na banza, hakama uwarta, duk fitinar Gaje tayi ta barta, tunda ita dai ba tanka mata zataiba saboda haƙuri da kawaicin da ALLAH yay mata, dan haka ka kwantar da hankalinka akan yarinyarnan, insha ALLAHU wataran sai kace gwamma da akai hakan�?.
Idon Ahmad a lumshe duk yana jiyo nasihar Ayyahn sa, wannan itace shawarar da kowa ke bashi, tare da faɗin gamma da akai, shidai jinsu kawai yakeyi, dan bazasu gane yanda Samina ta mallake dukkan zuciyarsa bane, yasan kozai shekara kwatanta musu irin mugun sonta da yayma zuciyarsa dabai bayi ba fahimta zasuyiba, gaskiya so bai masa adalciba, da yasan a haka wannan soyayyar tasu zata ƙare da ya roƙi ALLAH mutuwa kafin wannan lokacin, kawai dauriya ya keyi, dan mutane karsu kallesa mara zuciya ne kawai, amma ko yanzu Samina ta yarda zata zauna dashi zai saki Umm-Rumana ya sake auren Saminar.
Humm, turƙashi Ahmad, lallai zuciya batai maka adalciba kam.
_________________________
Anayin Sallar la'asar Ayyah tacema Ahmad ya tafi gida ya kwanta, dan su Fa'iza ma sun dawo anbar Rumana ita kaɗai.
Badan ya soba ya fita Sufyan ya kaisa gida yauma a mashin ɗin.
Rumana na sharar ɗakin Ahmad ya shigo.
Yanda ya shigo kawai yasata gane babu lafiya.
Matsawa tai gefe ya shigo, tai masa sannu.
Hannu kawai ya iya ɗaga mata ya haye saman gado hannunsa dafe da kansa ya kwanta.
Cikin damuwa ta kwashe sharar data tattara a ƙofar ɗaki, taje ta zubar ta dawo.
Ya lulluɓe har kansa da bargo, hakan yasa ta zauna ta zuba tagumi kawai tana kallonsa, tausayinsa na sake kamata...
A wannan halin tajiyo sallamar Sufyan, leƙowa tai suka gaisa, yace mata yazone da likitan da zai duba Ahmad.
Izinin shigowa ta basu, koda suka shiga saita fito ƙofar ɗakin ta basu waje.
Zuwa wasu mintuna Sufyan ya leƙo ya kirata, shiga tai ɗakin, saita iske za'a ɗaurama Ahmad ɗin ƙarin ruwane ashe, ƙusa suke nema da zasu rataya ledar ruwan.
“Aiko Yah Sufyan babu ƙusa a ɗakinnan, amma bara na tambayi maman Ama... Ko za'a samu�?.
Har zata fito Sufyan yace, “Kinga bartama, bara mugwada ko tsahon zaikai jikin mirror ɗinan�?.
Gwadawa sukai sai sukaga yama kai, hakan yasa suka ratayeshi acan, sai da ya fara shiga jikinsa komai yay dai-dai sannan suka fice bayan likitan ya nunama Rumanan yanda zata saka ɗayan idan wannan ya ƙare, dan leda biyu za'a saka masa.
Suna fita sai kawai rumana ta zauna ta hau rusar kuka.
Ahmad na jiyota sama-sama, sai dai baice mata komaiba har barci ya kwashesa mai ƙarfi.
Har magriba ruwan bai ƙareba, saboda a hankali suka sakashi, alwala tayo tazo tai salla, bayan ta idarne ta tashi ta saka masa ɗayan ruwan kamar yanda suka nuna mata, duk da dai a tsorace tayi komai, lokacinne kuma Maman Ama.. Ta sake shigowa danta dubashi.
Maman Ama na fita Abu ya shigo gidan da sallama, maman Ama dake ƙoƙarin fita ta amsa masa tana bashi hanya ya shigo,
“To, abun ya kai harda ƙarin ruwa kenan?�?. Abu ya faɗa yana ajiye kwanikan hannunsa
Rumana ta share hawaye tana faɗin wlhy kuwa Yah Abu, ni tsoroma nakeji kar wani abune ke damunsa ba'a saniba, garama akaisa asibiti tunda dai wannan ba likita bane babba�?.
“Karki damu Umm-Ruman, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu akaga jikin yaƙi daɗi ai gara aje asibitin, ga tuwo nan inji Ayyah, bara naje na sanar musu dan basusan an saka masa ƙarin ruwa ba�?.
Kai kawai Rumana ta iya ɗaga masa.
Ya fice da hanzarinsa, ita kuma ta koma ta zauna ta zuba tagumi.
Koda aka kira sallar isha'i da ƙyar ta iya tashi tayi, tana ƙoƙarin ninke abin sallar tajiyo sallamar matan gidansu, da sauri ta amsa tana ɗaga labule, ganin da gaske sune sai daɗi ya kamata, sai da suka gaisa da maman Ama sannan suka shigo ɗakin.
Ayyah ce da matan baba Iliyasu, Gwaggo da mama gaje da Ammin ta ne basu zoba.
Tabarma ta saka musu suka zauna, ta durƙusa ta gaishesu, suka tambayeta mai jiki tace da sauƙi.
Ta miƙe ta zubo ruwa a kofi ta kawo musu, Ayyah tace, “Rumana waye ya saka masa ruwan?�?.
“Ayyah tare da yaya Sufyan daya kawosa sukazo, leda biyune, da ɗayan ya ƙare shine na saka ɗayan kamar yanda suka nunamin�?.
“ALLAH ya ƙara afuwa�? suka faɗa kusan a tare.
Sun daɗe a gidan sunata jajanta abun, har Mudanseer ya shigo da baƙar leda a hannu, shima har cikin ɗakin ya shigo suka gaisa da Rumana, ya tambayeta jikin Ahmad ɗin yana ajiye ledar hannunsa.
“Ga wannan kananzir ne tun ɗazun yace na kawo shaf na manta wlhy, saboda ɗinki ya ɗauke hankalina, kawo risho ɗin a haɗa�?.
Miƙewa Rumana tayi ta ɗakko kwalin ƙaramin risho da su Fa'iza suka kawo ta ajiye gabansa, buɗewa yay ya fiddoshi daga ciki, ƙaramine amma yanada ɗan ƙyawunsa, suna nan zaune harya gama zira lagwanin ya haɗa komai yasa kananzir ɗin, sai da yaga tankin ya cika ya miƙa mata sauran yana faɗin, “Sai ki adana wannan ko�?.
Amsa tayi cikin girmamawa kamar yanda aka koyar dasu ga dukkan yayyensu.
Su Ayyah suka miƙe suna faɗin bara su wuce kar dare yayi, idan ya tashi tai masa sannu.
Tamkar Rumana zatai kuka haka taji, ta rakasu har soro tana share guntun hawayen da suka cika mata ido.
Umma tace, “Haba Rumana miye abin kuka anan, kowa da haka ya fara kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya dai da haƙuri da juna�?.
“Amin�? Ayyah ta amsa, Umma babba kam baki taɗan taɓe tana wani mosan mugunta, kusan dai ƙawar mama gaje ce.
Ayyah na kallonta amma tai kamar bata ganiba suka fice, Rumana ta koma cikin gida tana share sauran hawayenta.
Zama tai suna ɗan hira da Mudanseer, dan dama can shi yana sake musu ba kamar Ahmad ba, sannan mutum ne mai yawan barkwanci ga kowa. Shine ya sakata dole taci tuwon da Abu ya kawo, sannan yace ta bashi tukunya da ruwa ya dafa musu ruwan zafi, idan Ahmad ya tashi sai kawai ta juye masa yay wanka tunda ALLAH yasa akwai filas.
Tashi tai ta ciro tukunya daga kayanta, ta ɗauraye ta zubo ruwa ciki ta kawo masa ƙofar ɗaki inda ya maida risho ɗin yana ƙoƙarin kunnawa, ta ɗauko filas ɗin shima ta wanke dan su Fa'iza duk suka kawoshi tare da risho.
“Bara naje na dawo kafin ruwan yayi�? Mudan ya faɗa yana ƙoƙarin fita.
To ta amsa masa, shikuma ya fice.
Bai jimaba sosai ya dawo da leda a hannu, ya miƙa mata tare da buɗe tukunyar, ruwan nata ƙoƙarin tafasa ne, dan haka ya buɗe murafan filas ɗin ya matso dashi kusa. Yana tafasowa kuwa ya kwashe sa, sai da ya cika sannan ya miƙa mata bayan ya rufe, ya kashe risho ɗin ya ɗako da kansa ya maido mata ɗaki.
“To Umm-Rumana bara naje gida dare ya farayi, idan ya tashi ki tabbatar dai yasha magani, amma ki haɗa masa tea yasha zaiji daɗin jikinsa, ALLAH ya ƙara afuwa, da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo naga yaya ya tashi, idan munga babu wani canji sai aje asibiti ALLAH ya rufa asiri�?.
Kanta ta ɗaga masa, ji take kamar tace ya tsaya karya wuce shima, amma bata da ikon hakan, tana kallo ya fice ya barta ita kaɗai sai Ahmad daketa barcinsa dan Mudanseer ya cire masa ƙarin ruwan tun ɗazun saboda ya ƙare.
Tun tana kallonsa harta fara gyan gyaɗi, ahaka Ahmad ya farka kusan ɗayan dare ya ganta, ɗakinsu buɗe ga hasken fitila ƙau saboda sabon batiri dake a ciki, idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta, sai ta bashi tausayi, an haɗata da aikin da sam bai dace da itaba.
Bargon ya janye ya sakko daga gadon, yaɗanji ƙarfin jikinsa saboda ƙarin ruwan da aka saka masa.
Motsin saukarsa ya saka Rumana buɗe idanunta, cikin ɗan rikicewa take masa sannu, ya amsa murya a dushe.
Buta ya ɗauka ya fita, itama saita miƙe ta fara zuba ruwan sanyi a botiki kafin ya fito taji idan zaiyi wankan, a haka ya fito ya sameta, kanta a ƙasa tace, “Yaya Ko zakayi wanka?�?.
Kamar bazai amsa ba sai kuma yace, “Inason yi amma akwai sanyi�?.
“Ruwan ɗumine ai�?
Kallonta yayi sosai, ganin haka yasata saurin cewa, “Eh ai Yah Mudan ya kawo kananzir ɗin, shine ya dafa maka�?.
Janye idonsa yay akanta yana jin ƙaunar ƙanin nasa, da hannu yay mata nuni data haɗa masa, ya miƙe ya hau cire kaya.
Da sauri ta fita da ruwan takai masa bayi, a tsakar gida suka haɗu yana sanye da jallabiya, ta wuto shikuma ya shiga bayin,
Tea ɗin ta haɗa masa kamar yanda Mudan yace tayi, ta shimfiɗa abin salla ta ajiye shayin a gefe da biredi, sai ƙwai da Mudan yasa aka soya masa shima ta juye a filet ta rufe.
Ahaka ya shigo ya sameta, ya ɗauki buta ya sake fita, babu jimawa ya dawo, sai da ya kulle ɗakin sannan ya ƙaraso, Rumana na gefe zaune kanta a ƙasa ya tada salla.
Kafin ya ƙarasa ramuwan sallar magriba da isha'in har Barci ya fara kwasar Rumana a wajen, ta riga da ta saba da barcin wuri.
“Ki tashi kije ki kwanta�? nutsatstsiyar muryarsa ta daki kunnenta.
Buɗe ido tayi da sauri tana gyara mayafinta, ta ɗaga masa kai tana ɗan matsowa gabansa, buɗe shayin tai da ƙwan ta matsar gabansa sosai,
“Su Ayyah sunzo dubaka da Umma ƙarama da Umma babba, hakama yah Sufyan yazo sake dubaka baka tashiba�?.
“Na gode�? ya faɗa a hankali.
Shayin ya ɗauka ya fara sha saboda yunwa yakeji dama, Rumana ta miƙe ta ɗakko ledar magungunansa ta ajiye gabansa, tabarmar data kwanta jiya ta ɗauka zata shimfiɗa a ɗayan lungun gadon tunda Ahmad na zaune inda ta kwana jiya sai ya dakatar da ita.
“Ki hau gadon ki kwanta�?.
Yanda yay maganar a dake tasan babu zancen musu, sai dai jikinta har rawa yake kaɗan, taya zata iya kwana dashi bisa gado ɗaya?.
Kamar mai tsoron a saceta haka ta ɗofana a bakin gadon ta cure jikinta waje ɗaya.
Ahmad na kallonta baice mata komaiba, ya gama shan shayinsa yasha magani da ƙyar, Rumana dayake ta juya masa baya batasan hidimar da yakeba.
Ya daɗe zaune a wajen har barci ɓarawo ya sace Rumana dake kwance a ɗofane.
Jin barci na neman sake ɗaukarsa saiya miƙe ya ɗakko filo daga gadon da bargo, jallabiyarsa ya cire ya kwanta akan abin sallar yana rufa da bargon duk da kuwa garin akwai sirkin shigowar zafi.
★★★★�?
Yau dai kam duk yanda yaso fita a gidan bayan sun gama karyawa hakan ya gagara, dan sosai ciwo ya kaishi ƙasa, daga ƙarshe dai sai da Rumana ta amsa wayarsa ta kira Mudanseer.
Babu ɓata lokaci yana zuwa suka wuce asibiti.
Sai ga zance kamar wasa ya zama babba, dan kuwa dai gado aka bama Ahmad.
Kowa ya tausaya masa, dan kuwa dai ansan ciwon abinda Samina tai masane ya kasa barinsa.
Samina ko koda taji labari ko a jikinta, dan ko sau ɗaya bata taɓa leƙa Ahmad asibiti ba har yagama kwanakinsa shida aka sallamesa ya koma gida.
Duk ya rame choco color ɗin fatarsa ta sake wani irin fayau, sai hancinsa da ya sake fitowa raɗau da manyan idanuwa.
Bayan yayi wanka da ruwan da Rumana ta dafa masa ya fito jiki duk babu ƙwari, su Ayyah duk suna daga waje zaune ya shiga ɗaki ya shirya, itama dai Rumana wajen ta fito ta zauna zaman jiransa.
Bayan ya kammala saka kayan ya kira Mudanseer daga cikin ɗakin.
Shiga yay, mintuna kaɗan shima Mudan ɗin ya leƙo ya kira Ayyah da Rumana.
Shiga sukayi, Rumana ta zuba masa abincin da Yaya Maryam ta kawo masa, duk da bayajin daɗinsa haka Ayyah ta takura masa tana basa a baki, sai da yaci fin rabi sannan ta ƙyesa, aka koma dagamar shan magani, dan kuwa da ƙyar yasha sa hardasu yunƙurin amai.
Ranar dai duk anan suka yini sunata tarairayarsa, sai gab da magriba duk suka tafi aka barsa shida Rumana kawai.........✍�?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo
*(14)*
.............Shuru ɗakin yayi bayan tafiyar su Ayyah, babu wani sabo a tsakaninsu na shaƙuwa tun can baya, sai dai girmamawa irin ta yaya da ƙanwa da kowa ya sani, yayanma irin wanda ake shakka sosai ɗinnan.
Umm-Ruman tana zaune da ga kan tabarma inda ta idar da salla ta zabga tagumi, gaba ɗaya kewar gidace ke addabarta, musamman ma yau da duk ƴan uwanta suka kasance a gidan tare dasu.
Ahmad kam yana daga can ɗayan gefen kwance saman sallayar da shima ya idar da salla, dan rashin ƙwarin jiki ya hanashi tashi yaje massalaci.
Yanayinsa zaka kalla kawai shima kasan tunanin yakeyi, dan ya ƙurama silin ɗin ɗakin idone ko ƙyaftawa bayayi, gashi sai taunar lip ɗinsa na ƙasa yakeyi da haƙori.
Kiran sallar isha'i da aka ƙwalane a masallacin kusa da su ya saka Ruman miƙewa ta fita, Ahmad kam ko motsi bai yiba.
Koda ta dawo tayi kamar zata masa magana amma sai ta fasa ta kabbara sallarta, harta idar bai dawo hayyacinsa ba, ta sauke numfashi a hankali, cike da tausayinsa ta matsa gabansa,
“Yah Ahmad!�?
Shiru nanma bai motsaba, ta sake kiran sunansa kusan sau uku shiru, dole ta miƙa hannunta zata ɗan bugi filon daya jingina jikin Wadrobe ya saka kusan rabin bayansa da kansa, amm sai a mistake hannunta ya gogi kafaɗarsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yayinda Rumana kuma taja hannunta da sauri tana cusashi cikin hijjabi, jikinta sai tsuma yakeyi, sai kace wadda ta taɓa wani mugun abu.
Kallonta yayi da idanunsa da suka canja kala, ga ramar da yayi ta fito sosai saman fuskarsa, “Lafiya dai?�?
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa.
Rumana dake ƙoƙarin matsawa baya cikin in ina tace, “Dama salla har an idar wasu masallacin�?.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai, bai ce mata komaiba ya fita ya sake ɗauro alwala.
Koda ya idar ɗinma zaman shurun suka koma, a haka mijin maman Ama.. Yay sallama a ƙofar ɗakin, tashi Ahmad yay yafito suka gaisa yana sake tambayarsa yaya jikinsa?.
Cikin mutuntawa ya amsa masa akan da sauƙi, kowa ya koma wajen iyalinsa...
Yau ɗinma dai