Showing 102001 words to 105000 words out of 165545 words
ƙofar gidan nasu sai yau, to lallai yana zargin kamar mijin Samina ne kenan?.
“ALLAH ya ƙyauta�? ya faɗa a zuciyarsa yana ajiye tunanin gefe guda dan ba damuwarsa bace. Napep ya tare musu suka shiga.
Rumana da idonta ke cike da barci ta kwantar da kanta akafaɗar Ahmad, kaɗan ya juyo ya kalleta, idanunta lumshe suke, hakan saiya kuma fiddo ƙyawunta sosai, ga kalar hijjab ɗin data saka ya kuma fiddo da ƙyawun fusakar tata ainun.
Hannu yakai ya shafa kumatunta a hankali, ta ɗan buɗe idanun nata tana kallonsa, nasa idanun ya lumshe mata shima yana faɗin, “Karkiyi barcifa fa, banida ƙarfin ɗaukarki�?.
Fuska ta kumbura dama can haushinsa takeji yasa Ammi ta tada ita, dan tace ace ya barta ta kwana kuma Ammi ta hauta da faɗa dole ta taso.
Kansa yaɗan jingina jikin nata yace, “Ni bana faɗa yau�?.
Murmushi tayi mai sanyi ta maida idanunta ta lumshe tare da riƙe nasa hannu sosai tana shaƙar ƙamshin turarensa na tun ɗazu dake manne da jikinsa.
Shima murmushin yayi idonsa akan hanya.
Shi dai mai napep yana daga gabane yana kallon ikon ALLAH ta madubi saboda fitilar daya saka a cikin napep ɗin dake haska su Ahmad.
Koda suka isa gida bayan sun biyashi kuɗin, bai wuceba har sai da suka shige gidansu, Mai Napep yace, “ALLAH ka haɗamu da masoyan ƙwarai, kana gamo da irin wannan masoyan ai tuni kake tada ƙayar baya a gidanku ai maka aure yasin�?.
Kunji mara man kai, sai kaje ka tada din😂⛹♀.
Ahmad ya amshi key ɗin ɗakin wajen Rumana ya buɗe, bata shigaba, hannu kawai ta zira ta ɗauki buta taje tayo fitsari sannan ta koma ɗakin, Ahmad na ƙoƙarin cire kaya ya tashigo, hijjab ɗinta kawai ta cire ta jefa saman gadon zata bishi ya riƙota.
“Daure muyi wanka saiki kwanta baki ɗaya kinji Babie R ɗina, maman kuma Babie na mai zuwa insha ALLAH�?.
“Yayah Please wlhy barci nakeji, nidai yau bazanyi wankanba�?.
Ya kula yau dai shagwaɓa takeji, sakata yay a jikinsa sosai suka zauna a bakin gadon a haka, cikin tausasa harshe yace, “Sorry Gwal ɗina daure kinji, zan saya miki sweet mai daɗi fa�?.
“Kai yaya, wannan wayone fa wlhy�?.
“Tab, waneni da yima Gwal ɗina wayo, ai kece Boss sai yanda kikeso za'ayi�?.
Da wannan lallaɓar ya samu yaci galaba akanta harya cire mata kayanta, ya haɗa ruwan wankan da kansa ya tasata a gaba zuwa bayi.
Ita dai da ƙyar tai wannan wanka, suka fito kowanne yay alwalar kwanciya barci da brush, wajen shirin barcinma sai da yasha daga da ita, dan bil haƙƙi da gaskiya barcine taf idonta, to yau bata samu tayi ko barcin safe ba balle akai gana rana.
Duk ƙwazabar Ahmad kam ai dole yau ya ɗagama Rumana ƙafa sukai barcinsu, shi harma tsoro yake karya koma can kuma baya samu hakan ya damesa, duk yanda yaso dauriya da asuba kuwa ai bata yuwuba, sai da yaɗan rage zafi sannan yajisa dai-dai.
Shafin sabuwar tarairaya Ahmad ya buɗe ga Rumana, ita kanta abun har mamaki yake bata, data motsa zaice inane ke mata ciwo? Mi take so taci ko ta sha?.
Abun na bata dariya ainun, idan taso tsokanarsa har langare nasa take, sai ta gama tsurar dashi sannan ta dawo taita masa dariya.
Yakance babu komai i zai rama wataran, ta ɗauka yanzu itace a ciki shine a kwana, amma wataran zata dawo kwanar shi kuma ya koma ciki.
Dole rayuwarsu ta burgeka, babu sanyi gaba ɗaya, sannan kuma babu zafi mai tsanani.
Wataran ai farin ciki wataran saɓaninsa.
Inda ƴan gidansu abin ke ƙona musu rai, dansu UBANGIJI kan nuna musu farin cikin su Umm-Ruman ɗinne kawai.
Ɓacin ransu kuma suna ƙoƙari dannewa su shanye abinsu a cikin rai da cikin ɗaki, tunda ALLAH yayo Ahmad ɗin bamai hargagi ba, koda ɓacin ranne ya shigo cikin sanyi ake yinsa babu wani faɗa ko cacar baki a ciki.
_________________________________
Samina kuwa bayan wucewar su Ahmad ta jama Ma'aruff tsaki saboda kallon ƙurullar da yake binsu da shi, aiko yana juyowa ya daddage ya ɗauketa da maruka har biyu.
Da ƙarfin masifa ya turata mota ya rufe yana faɗin yau sai ta san ta masa tsaki wlhy.
Wannan abu kuwa duk a idanun abokan Ahmad dasu Mudan dake shago ya faru, sai yaran dake wasa a wajen, sunema suka kai labarin wannan mari cikin gida.
Baiko yi kaffara ba suna shiga cikin gidan ya hau jibgarsa ita kuma tana zaginsa da ja masa. ALLAH ya isa.
Sai da yay mata lilis da duka sannan kuma ya afka mata, taci wuya a hannunsa, dan yau ko aman da yay matama kasa tashi tai ta wankesa.
Washe gari kuwa labarin marin Samina yayta yawo cikin anguwa, Mama gaje taita masifa da cewar ƙaryane, kawai an sakama Samina idone anason ganinta cikin bala'i kuma baza'a ganiba, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu.
Babu wanda ya kulata a gidan har taci ta tsire, sai daga baya ta kira Samina dan tasan tabbas da Ma'aruff bai mari Saminar ba da wannan zance bai fitoba.
Aiko Samina ta fashe mata da kuka, tare da zayyane mata dukan daya kara mata ma da suka ido gida.
Mama gaje tace, “Bar ɗan iska ai daga wannan karon dai ta ƙare, kedai kiyi duk yanda malam yace zaici ubansa ne matsiyaci, kuma zan koma zuwa gobe dan wancan cikin na shegiyar can baza'a haifesa ba, Ahmad bai isa samun ƴaƴaba har saikin samu Samina�?.
Daɗi sosai yakama Samina, dan dama da baƙin cikin cikin nan ta fito Ma'aruff ya ƙara mata da haushin kallonsu Ahmad ɗin shine ta ƙare da cin duka a wajensa.
Washe gari duk da wuyar da taci a hannunsa sai da ya tsareta tai masa breakfast, yana fita aiki kuwa ta ɗakko abubuwan da malam ya bata ta fara ƙoƙari yin duk yanda yace tayi daki-daki.
Tsafi gaskiyar maishi, tun daga wannan lokacin Samina tace taga canji, dan yanzu kam ta sake kama Ma'aruff a hannu, koda giyarsa ya sha baya dukanta, sannan duk abinda ta tambayesa yimata yake, idan rashin kunyarta ta tashi kuma ta zuba masa gwargwadon iko baya iya ce mata komai.
A yanzu dai ta gama da matsalar ma'aruff kamar yanda ta faɗa, cikin jikin Rumana ne taget dinta na gaba, dan tayi alƙawarin sai yabi rariya, kuma da ga shi Umm-Ruman bazata sake ɗaukar waniba sai dai a lahira idan anayi.
Ni dai bilynku nace, “Hummm�?.☹️😏
_____★_★_____★_★______★_★______
A wannan karon kwanan Ahmad tara ya juya, da zai tafinma sai da akasha daru shida mutuniyar, dan kuka taita masa ranarma, shi dai ya samu ya lallaɓa ya gudu yana jin ƙaunarta na mamaye duk illahirin gaɓɓansa da jijiya.
Ya tafi da kwana biyu Kausar ta tashi da naƙuda a safiyar Laraba, ranar dai kam a asibiti ta kwana, su Rumana nata mata addu'ar sauka lafiya.
Tasha wahala sosai kafin ALLAH ya sauketa lafiya ta santalo ƴarta mace mai kama da ita.
Su Rumana na shirin tafiya dubota sai gasu sun dawo ma gida.
Daga ranar kuma aka shiga zaman bakwai, inda abin gutsiri tsoma ya samu ga maman Ama, dan duk abinda ba aima Kausar ba saita tanka, ita dai Rumana nata idone, sai idan dangin Kausar sun bukaci wani abu daga gareta ta basu, tanama ɗaki kwance tana fama da kanta, dan tunda Ahmad ya wuce sai yazam bata cika jin daɗin jikin nata ba, dauriya kawai takeyi tunda dai ba sharkaf take a kwance ba.
A haka aka kwashe kwanaki shida da haihuwar Kausar, inda kuma aketa shirin suna gobe idan ALLAH ya kaimu.............✍�?
Sai munzo cin rangam ni da Fans Kausar⛹♀
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(33)*
...............Ɓangaren Ahmad kam randa ya isa porthercout washe gari ya damƙama ubangidansa takardunsa.
Sosai kuwa Uban gidan nasa yay mamakin ƙyawun takardun Ahmad ɗin da yaba ƙokari basirar da ALLAH yay masa.
Happy ma tanata santi, dan yanzu itada Ahmad ɗasawa ake duk da yana shareta bai kuma shiga sabgarta, ko ɗan Assignment ɗinta ta kwaso shi take nufa, yana mata kodan darajar iyayenta, wani lokacinma ba Assignment ɗin bane haka kawai zata kwaso buks tace yay mata lesson.
Idan yanada lokaci yakan mata, idan baidashi kuma yace ba lokacinba, wani sa'inma waya zaiyi da Rumana sai yace mata lokacinsa na matarsane yanzu.
Ita sam bata aminta yanada mataba, gani take kawai dai yana faɗane danta bashi waje.
Kasuwarsa kuwa bai fasa zuwaba, yana zuwa kullum kuma Alhmdllh, dama dazai tafi Nura ya miƙama kayan shima yaɗan samu, koda ya dawo yanzun kuma sai ya bashi shawara akan mizai hana yazo shima ya koya harkar.
Nura bai musaba yayma Ahmad ɗin godiya, dan ɗan riƙema Ahmad ɗin da yayi a wannan tafiyar yaji daɗin harkar..
Tun daga wannan lokacin suka kuma kasancewa tare da Nura, dan har zuciyarsa yana son Nura, yana ɗaukarsane tamkar ɗan uwa na jini.
Ubangidansa tunda ya amsa takardunsa bai sake ce masa komaiba a kansu, shima kuma bai sake maganaba ya maida hankalinsa ga sana'arsa kawai.
Sai dai kuma yana fatan dacewa idan da alkairi a cikin aikin, idan babu alkairi ALLAH yama hana samuwarsa.
__________________________________
A wannan safiya dai gidansu Rumana da sunan babien Kausar suka tashi, da yake ƴan uwantane ke komai sai su Rumana suka zama ƴan kallo, sai dai ɗan abinda ba'a rasaba sukan taimaka, koda yake Rumana ce kawai a gefe, Maman Ama ai tuni tayi uwa tayi maɗaukiya, sai ƙara shigewa jikin Kausar ɗin takeyi, da kuma ta koma gefe ta zageta da gulma😹.
Ita dai na Rumana kallone.
An kira Sallar Zuhur Rumana dake ɗaki kwance tana fama da rashin daɗi jiki ta miƙe da ƙyar, ita dai bawai zatace ga inda ke mata ciwo baneba, amma sam jikinta batajin daɗinsa, nata salon laulayin kenan.
Sannu taima matan dake zaune a ƙofar ɗakinta ƴan uwan Kausar ɗin, duk amsawa sukayi suma da mata sannun.
Tana shiga bayi sai wata a cikinsu ke faɗin, “Kai amma ciki yama yarinyarnan ƙyau, jiba yanda ta murje tai haske�?.
“Wlhy kuwa Maman hafsa, nima dai tunda muka shigo naketa kallonta, ko gajiyama banayi da kallon nata�?.
Maman Ama dake bayansu kaɗan tace, “Inafa ciki anan? Bilicin dai da shan maganin ƙiba�?.
Duk juyawa sukai suka kalleta da mamaki, babbar Yayar su Kausar tace, “Aiko dai maman Ahmad idanunku basu gane muku dai-dai ba, yarinyarnan babu wani bilicin da take balle shan maganin ƙiba, cikine wlhy....�?
Dai-dai Rumana ta fito daga bayi, hakanne ya sakasu yin shiru, sai dai fa idanun Maman Ama tamkar zai faɗo wajen kallon Umm-Rumana, ita da batasan sunaiba ta duƙa da ƙyar tana yamutse fuska zatai alwala, sai dai ta zubda yawun daya tarar mata a baki sannan ta fara.
Maman Ama ta kuma zaro idanu waje tana faɗin, “Kambu, yasin cikine kuwa, to yaushe akai hakan?�?.
Har Rumana ta gama alwala ta miƙe zuwa ɗaki kallonta Maman Ama take harma da wasu a dangin Kausar ɗin, dan wasu labarin yanda akai aurenta da Ahmad ɗin sukeyi ta dalilin bijirewar Samina.
Ita dai bama tasan sunaiba, ta shige ɗakinta kawai ta kabbara salla.
Masu himmar sauke farali a kan lokacine sukai himmar tashi suma, Rumana tai musu allura, tana cikin sallar mutum biyu suka shigo ɗakinta dan suyi anan, ciki kuwa harda ƙawar maman Ama wadda ta kasance ƴan uba suke da Kausar, dama can an ƙulla ƙawancen ne saboda gulmar Kausar.
Lokacin da Umm-Ruman ta idar ne su kuma sunayi, wayarta tai ring, dan haka ta jawota tana dubawa, tayi mamakin ganin Yah Ahmad, dan bai cika kiranta a irin wannan lokacinba saboda kasuwa.
Ɗagawa tai ta saka a kunne da yin sallama murya a sanyaye.
Shima daga can ya amsa cikin lumshe idanu.
“Gwal ɗina kin tashi kenan?�?.
“Lah yaya waya faɗa maka ina barci?�?.
“Zuciyata mana babie R, aina kiraki, tunda naga baki ɗagaba nasan barci kikeyi�?.
Murmushi Rumana tayi har yana jiyo sautinsa, “Tace kai Yaya, to yaya kasuwan?�?.
“Kasuwa gata nan munata bugawa, yaya baby ɗina da ƙarfin jikinki?�?.
Murmushi taɗanyi tana sake ƙasa da murya saboda ba ita kaɗai bace, tace, “Nidai ƙalau nake�?.
“Ai haka akeso Ruman, shi kuma babie na fa?�?.
Neman kauda zancen take ya katseta da faɗin, “Ruman nifa banson wannan kunyar, abinda akaimin ban yarda aima ɗana ba uhyim�?.
Rumana taɗan kalli yanda matan sukai kasare suna saurarenta dan sun idar, ƙasa ta kumayi da muryarta tace, “Yaya bafa ni kaiɗai bace�?.
“Owo keda waye haka?�?.
Shiru tai dan tarasa yanda zata faɗa masa ya fahimta, da kansa yace, “Okey yaufa kuna suna ashe?�?.
Rumana tace, “Uhm�?.
“Ayya to ALLAH ya raya, nima kewarki ce ta isheni, anjima na kira�?.
“Na gode yaya�?.
Bayan Rumana ta ajiye wayar tsabar son jin ƙwaƙwaf, ƙawar Maman Ama sai cewa tai, Amarya munfa gode, kema ALLAH ya saukeki lafiya muzo i war haka musha suna�?.
Murmushi kawai Rumana tayi kanta aƙasa, sai dai batace komaiba.
Suka sake mata godiya suka fito.
Itako alawa ta ɗakko ta saka a bakinta kamar yanda yanzu takeyi saboda batason tara yawun nan.
Ƙawar maman Ama taje har ɗaki ta sameta itama tana salla, tana idarwa ta juyo tana faɗin, “Ƙawata Yaya da gaskene cikinne?�?.
“Wlhy kuwa shine ƙawata, muna salla fa mijin ya kira, kinji kuwa yanda ake kashe murya kojin abinda take faɗa bamaji