Showing 159001 words to 162000 words out of 165545 words
dan Mudan ne tsaye akan komai har aka gama.
Gidajene guda uku jere da juna, na Ahmad, saina Mudan, sai Abu kuma.
Anguwar sabuwar anguwace, amma kuma dai ta cika da gine-gine sabbi, sai dai babu hayaniya sosai da yake ba kowane ya gama dawowaba, amare ma sunfi yawa a anguwar.
Tunda suka shigo gate ɗin gidan baƙi da kwalliyar gold a jiki Umm-Ruman ta saki baki tana kallon gidan, bawani ƙato bane amma kuma an masa gini mai ƙayatarwa.
Ta kalli Ahmad dake murmushi, gira ya ɗaga mata tare da kashe mata ido yana kama hannunta cikin nasa.
Bata iya cewa komaiba tabisa, hakama yaran binsu sukai suna tsallen-tsallensu.
Mudanseer ya buɗe ƙofar shiga falon yana faɗin, “Kowa ya shigo da addu'a, musamman ke Umm-Ruman dan dagake babu wata a gidanan harma dana Saudiyya�?.
Dariya suka sanya, Ahmad yace, “Amma Mudan kai ɗan bukulune, baƙin ciki kake naƙaro amarya?�?.
Sosai suke dariya yanzu banda Ruman dake ƙoƙarin ƙwace hannunta tana cika, Ahmad yay saurin sake damƙewa yana dariya da faɗin, “Kinga gimbiyar mata wasa nake, ai kishiya ko a mafarki babuke babu ita�?.
Nanma dai dariyar sukayi, banda su Haysam da tuni sun shige cikin falon da gudu sun ɗare kujeru.
An gyara falon tsaf, komai an saka a gidan, dan haka suka shiga zagayawa ko ina, a ƙasa akwai ɗakin Rumana sai ɗakin baƙi saina yara, akwai kuma wani anyi ƙofarsa ta fita can waje shima dai na yaranne idan sunyi girma, sai kicin da kafin ka shigesa akwai dani farko.
Kasancewar falon babbane an shirya kujerune har kashi uku a cikinsa, dolene tsarin ya burge mai kallo.
Sai ƙafar bene da zata kaika can sama inda ɗakin boss Ahmad yake, kafin ɗakin akwai falo guda biyu da kuma wani ɗakin bayan nasa.
Gaskiya gidan yayi ƙyau matuƙa, gashi an zuba komai masha ALLAH, Ruman ta rungume Ahmad tana hawayen jin daɗi, yau sune da gidan kansu bayan wahalar haya da sukai na tsahon shekaru har a ƙasar da ba tasuba.
Dariya Ahmad yakeyi, ya jata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Haba Gwal ɗina, minene abin kuka kuma anan?�?.
“Dolene nai kuka Yaya, UBANGIJI yay mana sutura kashi-kashi da baki bazai iya faɗaba, muna godiya a garesa irin wadda bata yankewarnan a saman harshe, Yaya kayi Surprise ɗina wlhy, koda wasa ban taɓa kawo hakan cikin rainaba�?.
“Dolene mu godema ALLAH Ruman, zakuma mucigaba da gode masa har ƙarshen numfashinmu, naso na faɗa miki batun gidan amma sai nace bara dai na bari idan mukazo ƙya gani insha ALLAHU, munrigada munyi yawa yanzu, idan mukace zamu zauna acan zamu takura musu muma mu takura, shiyyasa da Mudan ya samu fili nima sai nace ya bincika mana, to sai aka dace aka samu harma na Abu, a hankali mukaita ginawa ana hutawa har gashi an kammala cikin amincin ALLAH�?.
Daɗi yasa Rumana sake rungume Ahmad.
Ya dungure mata kai da faɗin, “Nima ai na rama ne, kina tare da new baby na amma shine ban saniba ko?�?.
Dariya sosai Rumana keyi, ta kama hannunsa ta ɗora saman cikinta, “To kayi haƙuri Yayana, ai gashinan kaji yanzu, ya kamata ace kafin kowa ya ringa sanin inada ciki kaine zaka fara ganewa, amma koda yaushe sai an faɗa kake ganewa�?.
“To ya na iya, nidai fa naji gimbiyar ta ƙara ɗanɗano, amma sai ban ranfoba�? yay maganar a cikin kunnenta.
Fuskarta ta ɓoye a ƙirjinsa suna dariya, shigowarsu Haysam yasa suka saki juna.
Gida suka koma a ranar, sai a washe garine suka dawo gidansu gaba ɗaya bisa rakkiyar ƴan uwa da abokan arziƙi, kowa nata yaba gida da tsarinsa, sai dare kowa ya kama gabansa aka barsu su kaɗai a gidansu, Zainab dai ta maƙale wajen Gwaggo akan itafa tana can sai idan zasu komane.
To yazam ma zaman su Haysam ba sosai ananba, sai aka bar Umm-Ruman da Ahmad kawai, suma wani lokacin can gidan suke yini.
Suna kwana na tara da dawowa Ahmad yaje gidan Alhajin nan na anguwarsu da suka taɓa haɗuwa a saudiyya dansu gaisa yay masa godiya bisa alkairin da yayma su Baba, da kuma tsayawa da yay akan ginin gidajensu, dan shine yay tsaye akan komai har gyaran gidansu saboda sana'arsa kenan saida gidaje.
Alhaji yayi farinciki da wannan ziyara tasu Ahmad, sun kuma karramasu karramawa ta mutunci da girmamawa, sannan ya bama Ahmad dama akan ya ɗauki mota a gidan yaje yay amfani da ita har su tafi, dan baikamata yayta yawo a motar hayaba.
Ahmad yayi godiya da wannan karamci, ya amshi key ɗin da Alhajin ya basa suka koma gidama a motar daya bashin aro.
Satinsu biyu cif da dawowa baba ya zaunar da Ahmad akan maganar Samina, da kuma halin da mama gaje ke a ciki na taɓin hankali, dan yanzu lamarinta ya sake turewa sosai, zata zauna taita surutai tana faɗin tsiyatakun da sukai ita da inna mari, wani lokacin kuma saita haɗa kwanaki batai maganaba, sai dai kallon mutane da idanu.
Ahmad yaji tausayinta sosai, ya kuma aminta zaije ya fiddo Saminar kafin a shiga hidimar bikin su Mudanseer.
Washe gari kuwa tamkar yanda yay alƙawari haka ya shirya shida Mudan da Abubakar da baba ba tare da kowa ya saniba suka nufi prison iɗn da aka saka Samina.
Acan suka tadda Alhaji Hamisu dazai taimaka musu tunda shiɗin sanannen mutumne kuma mai jama'a.
Koda suka iso prison ɗin, Ahmad da Alhaji da babane kawai suka shiga, akabar Abu da Mudan a mota.
Suna nan zaune kusan awa ɗaya da wasu mintuna sai ga Ahmad ya fito ransa a ɓace, ya buɗe baya ya shiga ba tare daya cema su Mudanseer komaiba, sai dai bai rufe murfinba ƙafafunsa duk suna waje ma.
Suma yanayin da suka gansa a cikine ya sakasu yin gum da bakinsu basu iya cewa uffanba.
Suna nan zaune babu mai cema ɗan uwansa komai har kusan mintuna talatin sai ga baba da Alhaji sun fito.
Sam Ahmad baiko ɗago kaiba dukda yaji takun isowar su Baba wajen, yanata danna waya abinsa.
Baba yace, “Sannu sarkin zuciya, Amadu wai sai yaushene zaka rage wannan zafin nakane haka? Daga magana sai kayi fushi ka fito?�?.
Murmushi Ahmad yay yana ɗago gansa zaiba baba amsa, sai idonsa karaf akan Yamusashshiyar tsohuwa mai kama da Samina.
Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da yace, “Baba wannan ɗinfa?�?.
Baba yay murmushi mai ciwo yana kallon inda Samina ke tsaye kanta duƙe a ƙasa tana hawaye, ya kalli su Mudan da suma sukai mutuwar tsaye suna kallonta sannan ya bama Ahmad amsa da cewar “Ƙanwarkuce Samina�?.
A cikin matuƙar firgici sukace, “Samina fa Baba?!!�?.
Ƙasa ta durƙushe tana wani irin kuka maiban tausayi da cin zuciya.
Baba yace, “Kunga kushiga mota muje kunji, wannan ba maganar nan baceba, ɗiyata tashi bar kukannan haka ya isa kinji�?.
Kasa tashi Samina tayi, sai da Baba ya taimaka mata sannan ta miƙe daƙyar, ita da Baba suka shiga mitar Alhaji, Ahmad kuma dasu Mudan suna a motar Mudanseer ɗin.
Babu wanda ya iya sake tofa komai har suka isa gida, kowa sai saƙawa da kwancewa kawai yake a cikin ransa, gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi musamman ma Ahmad da sam bai taɓa kawoma kansa ganin Samina a wannan yanayinba, yanda yay matuƙar tsanarta sai tausayinta ya rage wani kaso a ciki.
Abu kam kasa daurewa yayi saida ya share hawaye saboda tausayin ƴar uwar tasu, ko iyayensu da suke tsoffi sunfi Samina ƙyawun gani a ido.
Da suka iso gidanma Samina kasa fitowa tayi a motar saboda kunya da matsananciyar tashin hankali da damuwar da take ciki, taso ace anbar rayuwarta ta ƙare a jail, dan tana jin kunyar haɗa idanu da mutane musamman jama'ar gidansu, tasan dukda tsahon shekarun data ɗauka mutane bazasu gaza tunawa da ta'asar data aikataba a baya, kuma bazasu gaza yin zunɗentaba, sannan babu abu mafi ɗaga mata hankali a yanzu irin ganin Ahmad da tayi.
Baba ne ya kamo hannunta ya fiddota, kasancewar yanzun ƙofar gidan nasu yazama wata ƙaramar kasuwa yasa idanu sukayo musu ca, dukda babu wanda ya gane Saminar saboda fita hayyacinta da tayi.
Lokacin da zasu shiga gidan sai kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi, wanda yaso ɗaga hankalin su Ahmad fiye da wanda tayi a baya.
Raɓasu yay ya shige abinsa tamkar abun bai damesa ba, hakan yasa baba ya bisa da kallo yana girgiza kai kawai, yasan Ahmad idan har ya tsani abu tofa ya tsanesa kenan sai kuma ta ALLAH kafin ya sake waiwayensa.
Da lallashi ya samu Samina ta shiga gidan, kai tsaye sashinsu ya wuce da ita, hakan yasa su Gwaggo da sukasan da zuwa ɗakkotan suma hankalinsu ya tashi matuƙa.
Gwaggo ta kama hannun Saminar ta saka a jikinta itama tana hawaye, hakama Ayyah kuka takeyi, iyama da Abu yaje ya kira ganin Samina ya matuƙar ɗaga hankalinta.
Sauran matan gidan babu wanda yasan mike faruwa, sai su Haysam dake gidan da sukai tsaye suna kallon Samina, Abu-Turab ma zuwa yay bayan baba ya ɓoye yana kuka wai tsoron Samina yakeji.
Baba yay murmushi tare da ɗaukarsa yana lallashi, “Haba Iliyasu minene abin kukan to, wannanfa ba abin tsoro bace innarkace kaji�?.
Noƙe kafaɗa Abu-Turab yayi yana sake ɓoye fuska a jikin baban.
Baba ya sake yin murmushi yana shafa bayansa.
Ruwan wanka Gwaggo ta haɗama Samina, kasancewar jikinta babu ƙwari sai iya ta shiga danta taimaka mata.
Wanka sosai na haƙiƙa iya taima Samina, kasancewar ruwane mai zafi sosai sai taji daɗin jikinta, har kanta sai da iya ta wanko matahi tas, sai ga Samina an fito daɗan fasali, dukda bilicin ya rigada ya gama lalatata, dukya lalata mata fata ya maisheta tamkar wata tsohuwa, ga wahalar datasha a jail.
Ɗakin Gwaggo aka kaita, zainab ta bata kayanta ta saka, sannana aka kawo mata tea tasha dan hanjinta ya wartsake.
Tana cikin shan shayinne Ahmad daya fita ya shigo gidan, magana yayi akan Saminar ta fito Mudan ya kaita asibiti dan a duba lafiyarta.
Kowa yay na'am da hakan, dan haka Samina na kammala shan shayin da kaɗanma ta iya sha Zainab ta kamota suka fika fito.
Asibiti mai ƙyau Mudan ya kaita bisa Umarnin Ahmad.
Shikuma ya ɗauki Abu-Turab daya maƙale masa suka tafi gida.
Koda yazo gidan bai faɗama Rumana komaiba, sai Abu-Turab ne ke sanar mata yaga ojuju a gidansu Baba.
Ta ɗauka shirmensane kawai, dan haka tai dariya ta share zancen, amma sai Abu-Turab yayta maimaitawa maganar, hardai ta ƙosa ta tambayi Ahmad dake cin abinci yana saurarensu ƙarin bayani.
Kamar bazai tankaba yacigaba dacin tuwonsa, sai da ya gama tsaf yamaje ɗakinsa yayo wanka ya dawo sannan yake sanar mata Samina ce fa da suka ɗakko a jail Abu-Turab ɗin ya gani.
Dukda Rumana bataga Samina ba yanda Ahmad ke bata labari saida tayi hawaye.
Shiko ya tsaya kawai yana kallonta da mamaki, to miye abin kuka anan? Kuma tunma bata gantaba, idan ta ganta kuma sai yaya kenan?.
Baki ya taɓe yana ɗauke kansa gefe, hakan sai ya bama Rumana haushi, dan a ganinta itama bai kamata Ahmad ɗin ya cigaba da riƙe Samina ba har yanzu, yadace ace ya yafe mata komai ya wuce kawai.
Tashi tai ta bar masa falon tana kuka, shiko ya bita da kallo harta haye sama sannan ya sauke numfashi yana girgiza kai da murmushi, irin ita mai ƴar uwarnan ko.
Duk binciken da Doctor yayi baiga wata matsalaba tattare da Samina, sai olsa kawai dake damunta, sai zazzaɓin cizon sauro da jininta daya hau, saiko tashin jin ƙarfin jiki.
A take suka bata gado, aka saka mata ƙarin ruwa.
★★★★�?
Kwanan Samina uku a asibiti, tana samun dukkan kulawa ta musamman, dan dukkan abinda ake buƙata Ahmad tsaye yake akai, hatta da abincin da likitan ya bada shawarar a ringa maba Samina haka Rumana kullum ke ƙoƙarin dafawa akaima Samina, dukda dai Ahmad ya hanata zuwa dubata asibitin, a cewarsa saita gama fushin dashi sannan.
Ganin dai da gaske ba barinta zaiyi tajeba saita sakko daga haushinsa da takeji ta bashi haƙuri.
To aranar da yamma yace ta shirya yakaita su duba Saminar.
Taji daɗi, ta shirya tsaf cikin baƙar abaya ta larabawa tare da naɗa kanta da gayalen jallabiyar, tayi ƙyau sosai, har Ahmad yaji kihin barinta ta fita a haka.
Da dai tai masa ƴar shagwaɓa sai kawai ya haƙura suka tafi.
Acan suka iske su Zainab dasu Haysam suma Mudan ya kaisu.
Sosai hankalin Samina ya tashi da ganin ƴaƴan Ahmad da Rumana, da yanzu itace a wannan matsayin, amma gashi son zuciya ya jata takai kanta ga hanyar data gaza ɓillewa, tayi kuka sosai tamkar zata shiɗe, Rumana ta rungumeta a jikinta tana lallashi da tabbatr mata komai ya wuce dan ALLAH tabar kuka, ta ɗauka hakan matsayin ƙaddara kawai.
Ahmad na ɗakin amma ko kallo basu ishesa ba, daga ƙarshema ya fita hannunsa riƙe da Abu-Turab zuwa wajen likita.
A ranar aka sallamesu da daddare, sai kuma lokacin sauran ƴan gidan sukasan da dawowar Samina har Baba Yusha'u, yako tubure Samina bazata zauna a gidanba, anyi lallashin duniya yaƙi sauraren kowa hatta iya.
Fahimtar da sukai ransa a ɓacene yasa baba yace Ahmad ya tafi da samina ta zauna a gidansa harsu shawo kan baba Yusha'u, dan yanzu yana cikin fushine zai iya furtama Samina dukkan abinda yazo bakinsa.
Sam Ahmad baiso hakanba, amma sai yaga Umm-Rumana na ɗokim ita, hakan datai ba ƙaramin haushi ta bashiba, dan haka yasa Mudan ya kaisu gida akan shi akwai inda zaijene.
Rumana sarai ta fahimci dankar ya ɗauki Samina ne, amma sai batace komaiba ta barsa, dan ita lamarin Ahmad ma yanzu al'ajab yake bata, idan ya riƙe abu a rai ya riƙesa kenan, kafin ya sakko asha fama.
Ɗakin baƙi na gidan aka bama Samina, Rumana ta ɗeba wasu kayanta ta bata, dukda sun mata yawa haka taketa zundumawa, tsakaninta da Ahmad kuwa ko kallonta bayayi, idanma ta gaishesa sau ɗaya yake amsawa ya ɗauke kansa, idanko tana falon ƙasa shi baya zama, hakan na masifar damunta, dukda tana nan maƙale da mugun sonsa da yafi na baya yawa tasan yamata nisa a yanzu, danshi mijin ƙanwartane, ƙanwar tatama uba ɗaya, ko matan duniya sun ƙare tasan bata isa kida kallo ga Ahmad ba a yanzun.
Wani lokacinma da gayya yakema Umm-Ruma wani abun a gabanta, aiko hakan yana zafarta a rai, dan takanci kukanta sosai.
Kamar wasa zancen gitowar Samina ya fara zagaye bakunan mutane, da biyu ake zuwa ganinta gidan sai dai a iske batanan, wasu sukance ɓoyewa take, wasu kuma suce tana gidan inna mari ne wajen babarta.
To koma dai miye abin tsegumi bai ƙarewa a bakunan mutane.
An shiga hidimar bikin su Mudanseer, wanda ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure Ahmad ya ɗauki su Rumana sukabi jirgi sai porthercout, ashe ita batasan Happy ce amaryar Mudanseer ba.
Wannan al'amari ya ɗaure kan Rumana, to a ina Happy suka haɗu da yah Mudan haka?.