Showing 3001 words to 6000 words out of 165545 words

Chapter 2 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

352

ya kwace ƴaƴansa.
Tunda kowa ya fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama Kawunsa Yusha'u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan ALLAH.
Da taimakon Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda Samina da Ahmad suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya.
A wannan karon Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake zuciyar kowa musamman Malam Rabi'u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma gidan ya sake ɗaukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici saboda yanzu akwai ƴaƴa a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu, musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba'a gidan ta tashiba.

A haka har Samina itama ta shigo sakandire ɗin dayake maza da matane a haɗe, hakan ya saka shaƙuwarsu ta sake ƙarfi mai ban mamaki, tana aji ɗaya yana aji biyar, amma ko yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan baban soyayya😂............✍�?




_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏�
*_Typing📲_*




*_🏃🏻‍♂️GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*(2)*


.............Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da kawa har abin ya fara rikiɗa yana zama soyayya, soyayyarma mai ƙarfi da shaƙuwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi da hukuncin UBANGIJI? Dole suka ɗauke idanunsu suka koma musu addu'a da fatan ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana'arsa ta saida yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda sana'ar ɗinkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari, dan haka yashiga wani shagon koyan ɗinki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ƙullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daɗewa zata fito wajensa su koma tare..
Ƴan shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ƙanana, badai za'ace za'ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad ɗin faɗa, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faɗan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita ɗan zagaya a ɓoye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa ɗaya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ƙwazo matuƙa.
Ayyah ta fasa ɗan asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken ɗinki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani ɗakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken ɗinkin, sai yazama shike ɗinkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar ɗinkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ƙwareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faɗawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da buƙatun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ƙyau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko ɗinkima sai yayi da gaske yake samu yaɗanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ƙaninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad ɗin da wasu ayyukan.


Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daɗi sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
Daɗin hakan da Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da ƴan uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake damƙa ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da alƙawarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan alƙawarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ƙasa saboda kunya.
Yayinda sauran ƴan uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daɗi, dankuwa koba komai zumincin ƴaƴansu zai ƙara danƙo da ƙarfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.

Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad ɗinba, idan kuma Ahmad yayi arziƙi dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.

Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya ɗinki yana kama ƴan kuɗaɗe sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na ɗiya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ƙara saka mata girmansa da ƙaunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad ɗintane kawai take kallo da gashin arziƙi, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ƙarshe a jami'a sai yake bata shawarar komawa karatu.

Lokacin suna zaune a ƙofar gidansune a shagon ɗinkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da ɗan murmushi ta dukar da kanta ƙasa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace, “Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuɗin ɗaukar nauyina?, kullum ana haɗa na masara da ƙyar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a ziri'ar mu kaf babu macen data taɓa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ƙannenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami'a ba nima nasani�?.
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace, “Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan ɗauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ƙila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu ɗan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a miƙamu daga ciki kowama ya huta�?.
Maganarsa ta ƙarshe ce ta sakata jan hijjab ɗinta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ƴar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace, “Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU�?.
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya haƙura ya ƙyaleta.
Daya shiga gidan suka haɗuma da sauri ta kauda fuska taƙi kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana ɗauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin haƙoransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haɗa ido da Samina data saci kallonsa.
Ido ɗaya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin ɗauke kai tana murguɗa masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaɗi da ƙarin kaunarta a ransa.

Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daɗi ya lulluɓe ta washe baki tana rungume Samina.
“Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ruƙayya, niko Ruƙayya ta rainar mini�?.
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ƙarshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya ɗagama ƙafa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.

Sai washe gari Ahmad ya samu saƙo a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daɗin hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ƙarfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaɗan samu madogarar da za'ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ƙarasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.

Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faɗi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ƙokari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daɗi.
Hakama iyayensu kowa yaji daɗi, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad ɗin yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran ƴan uwantama ƴammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.

Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuɗin shigarsa basu kai nauyin ɗukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuɗin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ƙarfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan ɓan garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ƙoƙarinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faɗaɗa neman kuɗin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan ɗinki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuɗin akuyar yaɗan sayo kayan su zare da wasu ƙananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan ɗan ɗebo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya ɗora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.

Da waɗannan sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ƙannensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree ɗinsa ya samu yay bautar ƙasa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana'oinsa na ɗinki da saida kayan ɗinki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faɗa sosai ya ƙware, ɗinkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ƴan kwalisa da ƴammata zaka samu ɗinkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan ɗinki yaɗan kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay ɗinkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.

Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu yasan suɗin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels ɗin hausa, rayuwar jin daɗi da dukiya da akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daɗi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiɗin dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da ɗaukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faɗin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
Haɗuwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali Ahmad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login