Showing 87001 words to 90000 words out of 165545 words
safe inna Mari ta jefoma Samina tambaya a bazata.
“Anya Samina wannan mijin naki akwai zaman lafiya a tsakaninku?�?.
Da mamaki Samina ta kalli inna mari, “Inna miyasa zakimin wannan tambayar?�?.
Sosai Inna mari ta kalli Saminar, “K ƴarnan barmin wani ɓoye-ɓoye, fito fili ki faɗi damuwarki kafin ki koma malam ya maido miki shege akan layi, kafin ƴan bakin ciki da sa ido su farga�?.
Ajiyar zuciya Samina tayi tana ɗauke kanta ba tare da ta faɗi abinda suke bukatar jinba, bawai bata son faɗar bane, kawai dai tana tsoron faɗarne maganar cikinta ya shigo, kuma inhar zata faɗar sai wannan labarin ya shigo.
Suma ƙyaleta sukai basu sake magana akaiba har kwanaki uku da dawowarta.
A hakanma basuga ƙeyar Ma'aruff a gidanba, gashi tabar wayarta acan gidanshi, kayama da take buƙatar a kawo mata tanaji tana gani sai haƙura tayi.
A kwana na huɗune Inna mari tai shirin zuwa wajen malaminsu, Samina catai zata bita, batai musu ba suka shirya suka tafi tare.
Aiko ranar yini guda a wajen malamin suka yisa, ya haɗo mata abubuwa sosai akan Ma'aruff, na binne-binne da wanda zata bashi yasha ko yaci a abinci.
Mama gaje kuwa a can gidansu Ahmad catai Samina ta koma gidanta, harshi baba Yusha'un abinda tace dashi kenan.
Babu wanda ya damu da bin ƙwaƙwƙwafinta, dan kowama tasa ta ishesa a ɗakinsa.
_________________________________
Tsawon kwanaki huɗu Yah Ahmad na haushi dani akan kawai na tambayesa zuwa duba Yaya Samina, wannan abu nasa ya daɗe yana bani mamaki.
A ranar cikon ta huɗun ina cikin gyara kayana a drawer sai ga kira ya shigo min, bamma kawo shiɗin bane na zata ko Yah Mudan ne.
Ganin sunansa na yawo ɓaro-ɓaro a waya sai mamaki ya kamani, cikin hanzari na ɗaga saboda tana gab da tsinkewa.
A sanyaye nai sallama dan shi yayi shiru da ga can.
Yanda ya amsa da ɗan dama sai naji sanyi a raina, na tambayesa ya kasuwa da jama'a?.
“Alhmdllh, ya jikin naki?�?.
Da ɗan murmushi a fuskata nace, “Na samu sauƙi ai Yayanmu�?.
Daga can Ahmad ya lumshe ido kewarta na cigaba da zungurinsa, cikin sanyin muryar datai kwana biyu bata jiba daga garesa yace, “Yanzu mikikeyi?�?.
Daɗine ya kamani, nai murmushin da nakeji a jikina yayi tasiri a garesa, ƙasa na kuma maida muryata nace, “Ina gyaran kayane Yayana�?.
Yaɗan sauke numfashi kaɗan daga can, “Sannu da ƙoƙari�? ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Tunda nace yauwa sai mukai shiru mu duka, nice na katse shirun da cewa, “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH na ɓata maka rai ranar, insha ALLAH bazan sakeba�?.
“Ya wuce�?.
Ya bani amsa a takaice, daga nan muka sake yin shirun na wasu sakwanni kafin ya kuma kauda shirin namu da cewar, “Ki zaɓa cikin gidajen su Yaya Maryam ina kikeason zuwa?�?.
Wani daɗine ya kamani, cikin zumuɗi nace, “Ko gidan Yaya Maryam ɗinma yayi�?.
“Ki shirya sai su Salima su rakaki gobe idan ALLAH ya kaimu kimata yini, saura kukai har dare acan�?.
“Na gode Yayanmu, insha ALLAH zamu dawo da wuri�?.
Yanda ya jiyo tana zumuɗi sai tausayinta ya kamashi, amma sai bai nuna mataba yay mata sallama akan idan ya koma gida zai kirata, yanzu yana kasuwa ne, kafin ta bashi amsa ya yanke wayar.
Sosai naita zumuɗin wannan fita, su Salima na zuwa na gumtsa musu bayani, dariya sukaita min, niko ban damuba dan ni kaɗai nasan daɗin da nakeji, tunda akai aurenmu ban taɓa zuwa gidan kowaba a cikin yayyenmu, aiko tun a daren na gama kimtsa hatta kayan da zan saka saboda tsabar zumuɗi.
Da daddaren ma ya kirani, duk da dai sama-sama yanzunma muka gaisa naji daɗi, koba komai dai inaji a jikina ya daina fushi dani.
Ƙarfe goma mun gama shiri, ko nace na gama su Fa'iza da suka je gida su faɗa nake jira su dawo mu wuce, sai kallon agogo nake ina zuba tsaki, aiko basu dawoba sai kusan goma da kwata, sunsha harara kamar idona zai faɗo.
Sukaita zubamin dariya, ban kulasu ba muka fito na kulle ɗakin, Mama Ama ce kawai a tsakar gidan, kausar na ɗaki inaga dai jikin nata babu daɗine, ganin takalmin mijinta yasa mukaima maman Ama salama kawai muka fice abinmu, duk da neman zance da take na tambayar “Su amarya yau kuma ina aka nufa?�?.
Banko bata amsaba bayan murmushi da cewar “Zan ɗan fitane saimun dawo�?.
Muna fitowa su Salima ke faɗin, ”Wai ita matarnan bazata canjaba?�?.
Suma ban basu amsaba, muka tare Napep dai sukai ciniki sannan muka shiga.
Farin cikin da nai na fitar sai muka iske mafiyinsa a wajen Yaya Maryam, gaba ɗaya ta gama rikicewa da murnar ganinmu, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Gashi dama ita kaɗai muka iske a gidan kishiyarta wai tayi tafiya zuwa Zamfara biki.
Sosai ranar na tsinci kaina a farin ciki, domin na yini cikin ƴan uwana munsha zuminci, Yah Ahmad ma ya kira suka gaisa da Yaya Maryam har take masa faɗan wannan karon baizo gidanta ba harya koma.
Bansan wace amsa ya bata ba, naga dai ta kalleni tana dariya da faɗin, “Zahiri kuwa ɗan ƙanina�?.
Munsha yini cir, sai kusan biyar muka baro gidan, inaji ina gani muka biya ta ƙofar Gidanmu su Salima suka shiga suka ɗakko abu sukazo muka wuce amma ni sai dai kallo, sai da naji hawaye sun cikan idanu, banda aure waye ya isa maka katanga da gidanku? sai lokacin da akaso kaje.
__________________________________
Haka rayuwar taci gaba da shuɗawa, wasu abubuwan na wucewa wasunsu na biyo baya, wataran masu daɗi wataran saɓaninsu.
A wannan yanayin Samina ta koma gidan ma'aruff bayan sun masa shiri na musamman daga wajen malaminsu, tsafi gaskiyar maishi, a cewarsu sunga canji daga Ma'aruff ɗin, dan kuwa da kansa ma yazo ya buƙaci komawar Saminar.
Da farko ta tirje wai ita jan aji saboda taga yana lallaɓata, sai da Inna mari tai mata kaca-kaca akan ta zauna shirme ta lalata komai.
Aiko babu shiri ta dawo hankalinta ranar da yazo da dare ta shirya suka koma.
Tunda ta koma gidan ba'ace babu daɗiba, dan kuwa dai tana samun kulawa fiye da da, sai dai bai fasa shan giyarsa ba balle neman mata, yawan dukantane dai ya bari sai idan ya nemeta ne taƙi saboda warin giyar da bataso shinefa zai lakaɗa mata duka ya kumayi abinda yakeso koda ta ƙarfine, daga ƙarshe kuma yay mata wanka da amai mai uban wari.
Data lura gardamarta ke kawo irin waɗannan matsalolin saita fara sauke rawar kai koda yazo a bugen idan ya nemeta bata hanashi kanta, haka za'ayi tana toshe hanci, babu zancen jin daɗi ko farin ciki daga gareta, kawai ta miƙa kantane ya samu biyan buƙata dan gujema buyaginsa.
Sannan kullum safiya bayan sunyi breakfast sai ya bata ƙwayoyin hana ɗaukar ciki tasha a gabansa yanzu, idan tai gardama tasha mari kuwa, kuma tilas tasha.
Wannan abu na tadama Samina hankali ainun, su da sukeda burin ta haihu dashi amma shi shine yake gudun hakan?.
Ta rasa hanyar da zata ɓullowa al'amuran, tana son faɗama su Nafy tana tsoro saboda gargaɗin da Inna mari tai mata akan riƙe sirrinta ga ƙawaye.
Gefe ga tsangwamar dangin miji, ko wata sabga ake ya kaita gidansu komawa take kamar wata mujiya a cikinsu, babu mai mata kallon arziƙi, to ana harkar masu kuɗi ita talaka ɗiyar talaka wane damar hura hanci gareta?.
Waɗannan matsalolin ne suka tarumata akai ko ƙibar kirki balle murjewar kwanciyar hankali bataiba, ga dai gida iya gida da kayan alatu amma babu wadataccen kwanciyar hankali a cikinsa.
Wani lokaci idan Ma'aruff ya tafka mata wata tsiyar takan ji a ranta da Yah Ahmad ne hakan bazata faruba sam, har kuka takanyi akan hakan duk da bataji a ranta har yanzu ta aikata ma Ahmad ɗin ba daidaiba.
★★★★�?
Ga Umm-Ruman kuwa tanajin sabbin abubuwa a jikinta, musamman son kaza da jin bata sha'awar kaza, yawan barci da saurin fushi, lokuta da dama shi kansa Yah Ahmad ɗin sukan haura sama ta waya, yakanyi mamakinta tunda tun fil azal yasan batada kwaramniya balle akai ga rashin kunya gana gaba.
Tayi wata irin murjewa, fatarta kuwa tai luff har ƙyalli take, sannan tai haske sosai kamar yanda su Maman Ama ke yawan gulmarta yanzu akan wai bilicin takeyi.
Shirmen ƙuruciya baisa Rumana ta fahimci wasu abubuwan da takeyi da sukai canji ko mata nisa a yanzu ba, da abun ya fara tsamari saita koma danganta hakan da wai shawara ke damunta😂.
Wata hikima ta UBANGIJI kuma sai ALLAH ya toshe ji da ganin Kausar da maman Ama akan fahimtar komai daga halin da Rumanan ke ciki.
Koda yake ita dai Kausar ma lafiyace ta mata ƙaranci, to maman Ama ma dai da alama laulayin sabon ciki takeyi, dan yanzu ko zamanma basa yawanyi sai lokaci-lokaci, shima zakiji gaisuwace sama-sama kowa ya samu waje ya kwanta.
Wannan yanayin ne ya kawoma gidan su Rumana yawan shiru, inba su Ahmad da Amatullah ke wasaba, gasu dai matan gidan babu mai ƙarfin yin wani motsi mai girma.
_________________________________
Ga Ahmad komai yana tafiya Alhmdllh, sai dai ƙalubalen kasuwa na yau da kullum, wataran a samu yanda akeso wataran saɓanin hakan, amma ko dai yaya ba'a rasa na abinci Alhmdllh.
Zuwa yanzu ya shiga wata na uku da dawowa, tun yana yawo da ƙaramar kwaba har ya ƙara neman babba data fita, sai kuma ga ɗan waje dukda bawani mai yawa bane, dan alfarma wani yay masa ta hanyar alhaji yaɗan bashi gaban shagonsa yake jingina kwabar, shi leda yake sayarwa mai shagon.
Hakan ba ƙaramin cigaba yazoma da Ahmad ba, dan yana ganin hasken zama wajen sosai.
Bayason ya cika wata uku baimaje gidaba, dan haka ya fara tunanin zuwa anan kusa kodan cika alƙawarin da yayma iyayensa, ga kewar matarsa kuma a gefe na cinsa a kowacce magudanar jini.
Ranar wata lahadi ya koma gida da wuri saboda kansa dake masa ciwo, gashi irin wannan ranarma kasuwar zakaga duk shiririta tafi yawa saboda masu garin ranar komai yakan tsaya ne agaresu a irin wannan ranar, magani yasha ya kwanta, da yake masu gidan sun fita ziyara basu kai ga dawowa ba daga sai shi kaɗai a gidan.
Da ƙyar ya tashi yay sallar magriba, sai lokacinne masu gidan suka dawo, tashi yay ya buɗe musu gate suka shigo da motarsu, ya tsaya har suka fito.
Gaisuwa sukai cikin girmama juna, dan matar tana son Ahmad sosai, tana kuma ƙyautata masa duk da ba addini ɗaya suka fitoba ba kuma yare ɗayaba, hasalima ko zo zan kasheki bata saniba da yaren hausa, UBANGIJI ne dai kawai ya haɗa jininta da Ahmad ɗin, sai kuma ƙyawunsa dake ɗaukar hankalinta, (kunsan ƙabilun nan dason abu mai ƙyau☺️).
Ciki suka shige shi kuma ya zauna a ƙofar ɗakin mai gadi da yake kwana dan yasha iska saboda zafi.
Wayarsa daya samu ya sake saya yaketa danne-danne a cikinta, yana a wajen har kusan takwas.
Ganin lokacin Salla yayine saiya miƙe ya koma ɗaki yay sallar isha'i.
Tun yana cikin sallar yakejiyo kukan yarinyar iyayen gidan nasa sama-sama, babanta sai ƙoƙarin lallashinta yake amma taƙi daina kukan.
Da farko baki Ahmad ya taɓe saboda yarinyar bata sonshi, gata ƙatuwar budurwa amma idan tana taɓara saika ɗauka wata ƴar shekara bakwai ce.
Jin hayaniyar naɗan ƙaruwane ya saka Ahmad leƙowa dan yaga mike faruwa?.
Kuka ya iske Happy nayi rurus, iyayen duk sun rikice sunata lallashinta amma taƙi saurarensu, tayi zaune a ƙasa dirshan duk ta jefar da abubuwan jikinta irinsu gashi da abun hannu da takalma saboda tsabar rashin man kai.
Kamar zai koma sai kuma ya tambayi ko lafiya?.
Baban ne yayma Ahmad bayanin wai Assignment na makaranta aka basu, su kuma duk sun kasa koya mata tun jiya, saboda basu iya Mathematics ba, wanda kuma yake koya mata baya nan, shinefa take wannan shirmen.
Kai Ahmad ya girgiza yana mamakin wannan taɓara, yace idan bazata damuba tazo shi zai koya mata.
Da mamaki duk suka kallesa, itako yarinyar harda hararsa wai miya sani da har zai koya mata?, Hausawa ƴan arewa da basa karatu hauka zai koya mata ko?.
Murmushi Ahmad yayi kawai, bai kuma ce mata komaiba ya juya zai koma ɗaki abunsa.
Saurin tsayar dashi maman tayi sannan taima Happy magana da yarensu akan ta gwada bashi tunda yace zai iya ɗin.
Bai musaba ya dawo, gani yay Happy ta miƙo masa buk ɗin tana hararsa, fuska a ɗaure ya amsa danshi dama bamai son wargi bane tun fil azal, shiyyasa sam baya barin Happy taga fara'arsa, duk da tana masa kallon ƙasƙantacce bahaushe ɗan arewa da wahala ta kawosa yankinsu cin arziƙi.
Kallon Questions ɗin yay ya taɓe bakinsa, hannu ya miƙa mata ta bashi pen ɗin nanma tana hararsa, baibi takantaba ya amsa, zama yay a ɗan dandamalin da aka zagaye flowers ɗin gidan ya fara mata aikin.
Dukansu idanu suka zuba masa cike da mamaki, cikin mintuna sha biyar ya kammala mata shi tsaf cikin ƙwarewar Handwriting ɗinsa mai bala'in birgewa, ba tare daya ce mata uffanba ya miƙa mata buk ɗin yana tsashi tsaye.
Amsa kuwa tai tana kallo, da salon rubutunsa mai cike da nutsuwa ta fara cin karo, sai kuma aikin, baki buɗe ta ɗago ta kalli bayansa daya juya dan tuni yama bar wajen, jiki a saɓule ta maida dubanta ga iyayenta tana faɗin, “Mommy yayi fa�?.
Amsar buk ɗin sukai suma duk suka duba, mamaki ya kamasu, sam basu taɓa kawowa a ransu wai Ahmad yayi karatuba, kasa daurewa Dadyn yarinyar yayi yace, “Dama kayi karatu?�?.
Ahmad ya tsaya cak, sai kuma ya juyo ya kallesu yana guntun murmushi, yace, “Har matakin degree kuwa oga, ku a tunaninku Hausawa basa karatune? Kodan kunga muna zuwa yankinku neman na kanmu?�?.
Dukansu babu wanda ya iya bashi amsa saboda mamaki da kunyarsa, shiko ya juya abinsa ya shige ɗakinsa ransa na ƙuna saboda yanda aka ɗauki yarensa a ƙasarsa.
Washe gari saiga Happy har ɗakinsa cikin tsantsar farin ciki, ita da ke ƙyanƙyaminsa sai gata harda rungumesa, saurin tureta yay a jikinsa yana mata tsawar karta sake masa haka bayaso.
Farin cikin data take ciki ya sakata bashi haƙuri tana miƙa masa buk din data kwafi aikin da yay mata jiya.
Kamar bazai amsaba sai kuma ya amsa a yatsine yana jan ƙaramin tsaki.
Taci 100/100, ya ɗan taɓe bakinsa yana miƙa mata buk ɗin.
Ko haushi batajiba ta shiga bashi labarin itace ta taci ɗari bisa ɗari a kaf ƴan department ɗinsu.
Cikin halin ko in kula yace mata “Congrat�? a taƙaice ya ɗauke kansa.
Ita dai bata kula da basarwarsa ba ta sanar masa kiran da Dad dinta ke masa.
Binta yay suka shiga cikin gidan.