Showing 57001 words to 60000 words out of 165545 words

Chapter 20 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

382

wayar yakamata tazam mai saka mata idanu akan wayar, kodama bata da ita ki saka mata ido tunda akwai ta ƙawaye.
Tanan suke shiga yanar gizo su haɗu da ƴan iskan facebook, ko istagram, ko litatafan batsa dake yawo a kowacce irin kafa ta yanar gizo, ko ƙawa ta sakata a group da sunan group ɗin matan aure wanda idonsu ya rufe basajin tsoron ALLAH duk abinda yake haramun shine abun kallonsu, wanda yake haramun shine abin furtawarsu da jinsu a zuwan wai koyan rayuwar aure, ke wane kidahumancin ya baki tunanin sai an ɗakko shaiɗancin tsiraicin wani kin ganine zakisan yanda zaki rayu da mijinki?, wlhy matan aure kaiconku da wannan wawancin mai toshe ƙofofin hasken zuciya da kashe gani.
Ƴammata da yawa daga shiga irin waɗannan groups suna canja suna komai ke fara tabarɓare musu, idan k uwa baƙya bibiyar lamarinta daga haka sai kiga komai da kika gina ya tarwatse.
Wlhy kuzama masu kulawa kafin ku riski ranar kuka da nadama akan ƴaƴanku, domin sai ALLAH yay miki tambaya dalla-dalla akan tarbiyyarta.
Wannan sakacin ne ya hana Mama gaje fahimtar komai akan Samina har Ammin su Umm-Rumana ita ta lura, ba ƙaramin ruɗani ta shigaba, sai dai tana tsoron tace wani abu aga zaƙewarta.
Samina kuwa kwanciya tai wahala ta sakata barcin dole, bata tashi farkawaba sai bayan sallar magriba, agaban mama gaje ta dafa ruwan zafi taje tai wanka dashi ta sake gasa jikinta kamar yanda taga ana cewa a novels, koda ta fito sama-sama taci abinci ta sake kwanciya, kobi takan kayan da mama gaje ta baza a ɗakin bataiba saboda ita tasan wahalar da taci kafin ta samo kayan.

Haka Samina taita jiyyar jikinta har kwana biyu, ko ɗaga wayar Ma'aruff batayi idan ya kirata saboda haushinsa da takeji, amma taji daɗin yanda ya nuna damuwarsa a kanta, sai turo mata massegea yake kamar hauka, wannan yasa a cikon kwana na huɗu ta kulasa.
Yako kalailayeta da daɗaɗan zantuka ranar, haryaci galaba a kanta tafito makaranta taje Office ɗinsa ta samesa, acan yakuma lallaɓata ya ƙara na biyu, ranarma taci kuka dan tasha wahala, amma daya lallaɓata da mayaudaran kalamanasa saita goge hawayenta saboda ta yarda dashi.
Tun daga wannan ranar ya maidata kamar wata matarsa, a gefe kuma yanata sakar mata kudi itada ƙawayenta suna shirin biki. Sati na biyu da kauda mata martabarta aka kawo lefenta daga gidansu ma'aruff akwati ashirin da huɗu cif, tare da katuwan jakkuna uku manya-manya, ɗaya na babanta, ɗaya na Mama gaje, ɗaya na danginta.
Ranar dai kam su Ayyah sunsha kallo, sun kumasha gori wajen mama gaje da danginta, ƴan anguwa kam ai kamar sa fasa gida kallon kaya, harda ƴan gayyar soɗi, dan ko su Maman Ama sai gasu sunzo ganin ƙwaf daga jin su Salima na sanarma Umm-Ruman cewar gobe za'a kawo lefen Yaya Samina.
Shine mutanenku sukai shiri Rumana bata saniba sukazo wai yimata kara tunda ita har yanzu bata fara zuwa gidaba baba Yusha'u ya hana, yace tai zamanta har Ahmad ya dawo ya bata izinin hakan, makaranta kawai take fita, shima kuma jarabawama suke zanawa ta ssce.
Ranar su Nafy ƙawayen Samina haka sukaita yawo da wannan lefe a social media, yayinda ya tadama ƴammata da yawa hankali da fatan suma sai an musu irinsa koma wanda ya fisa.
Harda masu takaicin inama sune, irinsu Kausar.
Koda sukaje suna bama Rumana labari tasha mamaki, dan ita bama ta kawo can sukajeba, amma sai batace dasu komaiba akan hakan dukda taji haushi.


_________________________________


Baba ne ya gindayama Ahmad sharaɗin ya tabbatar yazo gida anyi bikin Samina dashi, tunda shine namiji babba a gidan bai ƙyaitu ace baya nanba.
Dukda baiso hakaba dole yabi umarnin baba, tunda yanzu dai Alhmdllh, duk da bawasu maƙudan kuɗi ya samuba babu laifi tafiya tai riba, dama kuma ya gama shirinsa tsaf.


★★★★★★

Umm-Rumana duk da bata da tabbacin zuwa gidan bikin haka ta wanke kanta Salima ta yarfa mata kananun kitso, suka kawo ƙawarsu har gida tai mata ƙunshi mai ƙyau, haka kawai ta tsiri juya fasalin ɗakinta.
Tako tsare su Fa'iza suka tayata, komai suka canja masa muhalli ya koma kamar wani sabon ɗaki, aranar kuma su Samina ke shirya fatin ƙunshi a wani haɗaɗɗen hotel tsadajje.
Su Fa'iza duk sun gudu sunbarta ita kaɗai a gidan, dan haka bayan tai wankanta tai kwanciyarta tana kwasar barcin gajiyar aikin da sukayi.


★★★★★★

Ƙarfe kusan huɗu su Ahmad suka iso cikin garin kano, ya jigatu sosai saboda tafiyar dare sukayo, tun a tasha sukai sallama da Nura da shima yazo ganin gida, ya loda kayansa a napep ɗin da yay shata suka nufi gida.
Ƴammatane danƙam da ƙofar gidansu, ga galla-gallan motoci sun jeru domin kwasarsu zuwa wajen kamu.
Mai napep ya samu ɗan wajen maƙalewa yay fakin.
Kallo ɗaya Ahmad yayma motocin ya ɗauke kai, dan koba a faɗa masaba dai yasan ƴan bikine.
Yana fitowa idon Mudan dake ɗinki a shago ya sauka kansa, cikin matuƙar mamaki ya fito, dan babu wanda yasan da dawowar Ahmad ɗin sai baba.
“Yah Ahmad!�? Abu ya faɗa da ƙarfi shima tare da sakin butar da ya ɗeboma Mudan ruwa daga cikin gida, sheƙawa yay da gudu ya koma dan kai rahoto.
Kafin kace mi yara sun zagaye Ahmad anata murnar ganinsa suna kwasar kaya zuwa cikin gida, hakan ne ya sakashi farin ciki, inda kuma hankalin ƙawayen Samina ya dawo kansa, dan kuwa su Nafy tuni sun fara rattafo labari akan da shine zai auri Samina ai.
Da yawansu ƙyawunsa ya ɗau hankalinsu, sai dai sunce rashin ƴan canji ya kwafsa masa.
Ahmad da baisan mi sukeba tuni ya nufi cikin gida riƙe da hannun Mudan suna dariyar tsokanar da mudan din ke masa akan yayo ƙiba kamar ba shiba.
A ƙofar soro sukai karo da Samina da taci ado cikin wani arnen farin les, ƙawayensu kusan biyar na tare da ita, da alama dai zasu fita ne domin a kaisu wajen kamun.
Kallo ɗaya Ahmad yay mata ya ɗauke idanunsa yana cigaba da murmushinsa da ya ƙara haska choco color ɗin fatarsa mai ƙyalli ta asalin rumawa.
Haka kawai Samina ta samu kanta da faɗuwar gaba, tuntuɓe tayi zata faɗi ƙawayentan sukai saurin tarota, da kallo ta bisa har suka ɓacema ganinta, sosai taga ya canja mata duk da ma babu kwalliya tare dashi, dan wandon jeans ne da t-shert mai gajeren hannu a jikinsa, duk rigar ta yamutse alamar sunsha zaman mota.
Siririn tsaki taja tana faɗin, “Ɗan wahala kawai�? a fili.
Mutum biyu a ƙawayen nata da sukasan komai suka kwashe da dariya kuwa, suma idonsu a kansa, sai daifa harga ALLAH sun yaba da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar.
A cikin gida kam an rikice da dawowar Ahmad, harma ya rasa sannu da zuwar wazai amsa, ƴan uwansa da yaran anguwa duk sun zagayesa, kunsan yaro dason adawo daga tafiya a bashi tsaraba koda ta biredi ce😂.
Fahimtar hakan da Ahmad yay ya sakashi jan ledar biredi ɗaya ya miƙama Sadiya data ajiye masa ruwa yace ta raba musu.
Aiko kowa yana samu aka bashi sai ya fita cike da ɗoki kai rahoto gidansu.
Bakin Ayyah gaba ɗaya yaƙi rufuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, Gwaggo kuwa babu mai cewa ga yanayinta, sai dai cikin ranta ita kaɗai tasan sanyin da takeji na dawowar Ahmad ɗin.
Bayan yasha ruwa suka gaisa da mutanen da suka shigo ƴan biki masa sannu, wasuko dai ƴan son ganin ƙwaƙwaf ne.
Bayan an gaggaisa suka fita, shima sai ya samu gaisawa da nasa iyayen da ƙannensa.
Yana shirin kishingiɗawa a tabarmar da aka shimfiɗa masa Ayyah tace, “Ɗan albarka badai anan ba, maza tashi ka wuce wajen matarka ka huta acan�?.
Cikin shagwaɓa ya narke murya yana faɗin, “Kai Ayyah na, nifa kamarma kin daina sona nake gani?, yanzu abincimafa kince bazaki bani naci ananba�?.
“Aiko wlhy ban baka, gashi dai zan zuba a kwano auta tazo ta bika dashi gida kaci acan, maza tashi, baiwar ALLAH ai tayi haƙuri ƴarnan�?.
“To Ayyah zan tafi, amma ki bari mu gaisa da baba to�?.
“A'a idan ka dawo anjima kwa gaisa, dan malam ma baya nan kusa yaje Dawanau ne�?.
Dole Ahmad ya miƙe domin bin Umarninta, jakkar kayansa kawai da jakka ɗaya da leda ya ɗauka, sauran kayan kuwa duk nan aka barsu a ɗakin Ayyah kamar yanda yace su Sadiya su shiga dasu.
Shi kuma Mudanseer ya ɗauka kayan ya fito ƙofar gida domin tarar napep.
Su Samina amare har an wuce, sai abokan Ahmad dake jiran fitowarsa.
Nanma fa wata sabuwar murnarce ta sake kacamewa a tsakanin abokan amana tun ƙuruciya, da ƙyar Ahmad ya ƙwaci kansa akan zaije ya kimtsa ya dawo.
Ya shiga napep ɗin da mudan ya saka masa kayansa suka wuce.

Cikin barci naji muryar Zainab na faɗin, “Yaya Rumana ki tashi ga Yah Ahmad ya dawo�?.
Da ƙyar na iya buɗe idanuna saboda ba ƙaramin barci nayiba ashe, ganin Zainab zaune kusa dani ya tabbatar min da ba mafarkin dana saba yi bane.
Tashi nai zaune sosai, sai kuma na miƙe zumbur jin muryar Yah Ahmad dake amsa gaisuwar su maman Ama.
Kasa haƙuri nayi, na nufo ƙofa domin tabbatarma kaina.
Sai dai ashe ya kawo jiki zai shigo sai mukai karo harna bige kaina a ƙirjinsa, nai baya zan faɗi yay saurin ruƙomin hannu..............✍�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(20)*



...............Sassanyan numfashi na sauke jin ALLAH ya taimakeni bansha ƙasaba, sai dai jina a jikinsa saboda jawonin da yayi ya saka gabana faɗuwa nai saurin son matsawa bayan again.
Sakinta Ahmad yayi saboda ganin Zainab a ɗakin, shima jinta da yay jikinsa ba ƙaramin bugawa ƙirjinsa yayi ba, ya raɓa ta gefenta zai wuce murya na Rawa tace, “Sannu da zuwa Yaya�?.
Idanunsa ya ɗan lumshe yana ƙoƙarin zama a bakin gadon, ya ɗago ya kalleta sosai murya ƙasa-ƙasa ya amsa da “Yauwa, kema sannunki�?.
Ruwa Umm-Ruman ta ɗibo a kofi bayan ta ɗauraye, ta kawo gabansa ta ajiye tare da durƙusawa tana sake masa sannu da zuwa, tana a duƙen take gaishesa cikin girmamawa.
Daƙyar Ahmad ke ƙoƙarin amsawa dan sosai Rumana ta canja masa, sai yaga ta sake girma, ko dan dai kafin tafiyarsa ba wani kallon ƙwarai yake mataba, sannan bata yarda ta zauna babu hijjab, yau ko ya rutsatane babu hijjabin.
Sanye take da siket da riga na wani yadi mai kama da atanfa, siket ɗin 8-fisis akai masa, hakan yasa ya matseta kaɗan daga sama ya buɗe sosai a ƙasa, ga rigar fitet ita kuma, sai hannunta ne daya buɗe sosai daga ƙarshe.
Mudanseer ne yay musu ɗinki, a lokacin har Ahmad ɗinma na faɗan yanda Mudanseer yay wulaƙanta kayan da ɗinkin manyan gayu.
Yadin bai kai sun sami ɗan kwaliba, sai wani kalan suka saya, itako Rumana bata cika son ɗan kwali mai santsiba, shiyyasa ko yanzu gyalen jallabiyane ta yana akan nata, hakanne ya bayyana haɗaɗɗen kitsonta ta gaba, sai jelar da yake iya hangowa kaɗan idan ta duƙa saboda tanada tsahon gashi, kusanma duk yaran gidansu ALLAH ya basu suma harsu mazan.
Duk da yasha ruwa a gidansu baiƙi shan wanda ta kawo masaba, dan ganinta ya haddasa masa wani sabon ƙishirwan.
Yana cikin shan ruwanne Zainab ta miƙe saboda gargaɗin da Ayyah tai mata akan tai maza ta dawo karta zauna.
“Uhm Yaya Rumana bara naje gida, Ayyah tace karna zauna saboda magriba ta kusanto�?.
Ji Rumana tai kamar ta hana Zainab wucewa, dan kallon da Ahmad ke mata duk ya sakata ruɗewa, kamar zatai kuka tace, “Ki zauna su Fa'iza su zo mana, ƙilama Yah Madan yazo anjima saiki bisa�?.
Zainab taɗan ƙwalalo ido waje tana fadin “Kai, Yaya Rumana ALLAH Ayyah dukana zatai, gara dai na tafi, gobe zan dawo�?.
Ahmad dai duk yana jinsu amma uffan bai ceba, yama ajiye kofin ruwan ya koma latsa wayarsa daya sake, dukda ba sabuwa bace tayi ƙyau dan batasha wahalaba sosai.
Hamsin Rumana ta bama Zainab, “Tunda kinƙin Zee shikenan, gashi saiki hau napep�?.
“Kima barshi Ayya naira sittin ta bani kuɗin zuwa da komawa, kin gani�? zainab ta ƙare maganar da nunama Rumana sauran talatin ɗin tana ƙoƙarin fita.
Ba yadda Rumana ta iya dole a gaban idonta zainab ta wuce.

Kanta a ƙasa tanata faman gyara gyalen danya rufe mata ƙirji ta maida hankalinta ga Ahmad da har yanzu bai daina latsa wayarba.
“Yaya a saka ruwan wankane ko zaka fara cin abincin?�?.
Ba tare da ya bar abinda yakeba yace, “Sakamin ruwan, dan zafi nakeji�?.
Da “To�? ta amsa, ta sanshi dason wanka da ruwan zafi dan haka ta ɗakko na filas data saba ajiyewa ta juye a botiki ta fita danta sirka masa.

Da sauri Maman Ama da Kausar da suka haɗa kai suna gulma a ƙofar kicin suka hau washe baki kamar gaske.
“A, Amarya barka fa ƴan tafiya an sauka lafiya�?.
Umm-Ruman ta amsa da “Yawa, ngd�?.
Tasan dai gulmarta sukeyi, tunda kullumne babu fashi, har maƙwafta surutu suke zuwayi akan wai Yah Ahmad ya watsar da ita tsahon wata shida yaƙi dawowa, ƙilama ya gudune, idan iyayenta sukaji zasuzo su kwasheta itada kayan tunda mai gidan haya dai ba lamuni zaiyiba idan shekara ta ƙare.
Yanzukam gulmarta suke akan wai ashe tasan mijinta zai dawo shiyyasa taketa ɓare-ɓaren gyara jikin tarbarsa, amma da suka tambayeta sai tace kwalliyar bikice.
Kausar harda cewa, “Yo kwalliyar iyakar fatar ido dai zata tsaya tunda ba wata uwa zai iya mataba�?.
Sosai maman Ama taita dariya da faɗin, “Wa yaga lagwani�? shinema Rumana ta fito ta ritsasu.

Sai da taɗan sake ɗauraye masa bayin sannan ta ajiye ruwan ta fito.
A ƙofar ɗaki ta iskesa zai fito, hannunsa riƙe da abin wanka da brush da ya sakama makilin, ta matsa ya wuce bayan ya ajiye takalman daya fiddo na silifas.
Aiko harya shige banɗaki su maman Ama na binsa da kallon ƙurilla, so suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login