Showing 60001 words to 63000 words out of 165545 words
suga abin kushewa a samu nayi, sai basu ganiba, dan saima wata ƙiba data ƙara masa cikar zati da kwarjini ya ƙaro.
Sai suka koma faɗin, ba dole ya narko ƙibaba yanacan yanacin daɗinnsa ya bar Rumana anan cikin wahala daga fara da mai sai wainar filawa.
Karaf sai zance a kunnen Umm-Ruman data fito ɗauraye filet ɗin da zaici abinci.
Kanta kawai ta girgiza tana mamakinsu ta koma ɗaki abinta dan gulma ta rufe musu ido basuko farga da itaba.
Koda Umm-Ruman ta koma ɗaki sai ta ɗauki turaren tsinke ta sake kunnawa, duk da dai da safema ta kunna, kuma Alhmdllh ƙamshin ya kama ɗakin saboda nacin saka turaren da takeyi ga firishina ta haɗawa da yaya maryam ta kawo mata mai ɗan yawa, tanata ɓoyen abunta sai kaɗan- kaɗan take sakawa har turaren wutarma, na tsinkenne dai kullum saita kunna saboda da yawa aka kawo mata su..
Tana ƙoƙarin kunna fitila saboda duhun magriba da garin yayi Ahmad ya shigo ɗakin da sallama, Amsawa tai ba tare data juyi ta kallesa ba saboda kunya, duk da tasan akwai jallabiya a jikinsa kuwa.
Batai auneba taji hucin mutum a bayan, cikin ɗan hanzari ta juyo, Ahmad dake tsaye a bayanta ya miƙa hannu zai ɗauki robar mai dake saman madubin, gefe Rumana ta matsa, duk da hakan kuma jikinsa na taɓa nata saboda lungun wajen baida girma sosai.
Baice da ita komaiba, duk da ya lura da yanda taketa zare idanu, ya ɗau mansa ya zauna abakin gadon danya shafa, ganin taƙi wucewa ya ɗago fararen idanunsa ya ɗan kalleta.
Saurin raɓashi tai ta fice, ya bita da kallo kawai yana girgiza kansa.
Tana alwala a bakin rijiya yazo ya wuce zai fita massalaci, ta shaƙi ƙamshin turaren daya saka tana binsa da kallo, sosai taga canji daga garesa, sai taga kamar an wani canja matashi, dan yanda jikinsa kawai ya murje zai baka amsar tafiya tayi riba.
Da wanna tunanin ta shiga ɗaki itama ta kabbara salla.
Ana idar da sallar magriba sai gashi ya dawo, a bakin gado ya zauna dai-dai tabarmar data ɗora kayan abincin, waya yakeyi, dan haka ta matso ta fara zuba masa abincin a filet, harta kammala zubawa yana wayarsa, sai dai idonsa na kanta kamar ya samu talabijin, dukda tanajin yanda idonsa ke yawo a jikinta tunɗazun ita bata yarda ta kallesanba.
Kauda kwanikan tayi gefe yanda zaiji daɗin sakewa a wajen sosai, ta yunƙura da niyyar ta miƙe kawai babu zato taji ya ruƙo mata hannu, kafin ta gama tantance gaskiyar lamarin ta tsinci kanta ɗare-ɗare bisa cinyarsa.
Kasa magana tayi dan matuƙar al'ajabinsa, ga jikinta sai wani yamm yakeyi, Ahmad ya ajiye wayar gefe tare da kallonta sosai, yanda yake kallon fuskarta babu wani alamun jin ba daidaiba ne ya sakata kasa jurewa ita, gashi fuskarsa sam babu walwala, kamar dai yanda ta saba ganintane acan baya.
Hannu ya saka ya ɗago da haɓarta yana ƙoƙarin zare hijjab ɗin, bata hanashi ba, dan batagama fuskar yin hakan daga garesaba, sai sake matse hannayenta take waje ɗaya illahirin jinin jikinta na gudu cikin kowacce jijiya da sauri.
Ya ajiye hijjab ɗin saman gadon ba tare daya tankaba, goshinsa ya ɗora saman nata, mutuniyarku saita sake ruɗewa, cikin in ina tace, “Ya..ya a...b in ....cin za..i zai huce fa�?.
Ahankali ya furta “idanma ya huce bakece kika ja ba?�?.
Babu shiri ta ɗago idanunta sai suka afka cikin nasa, dan har yanzu goshinsa nakan nata, hancinsu gab da juna suna musayar numfashi, hakama bakinsu babu wata tazara duk da ita Rumana taɗan duƙar da kantane ba kamar yanda nasa yake daret ba.
Ƙasa ta sake maida idanun dan bazata jura kallon cikin nasaba, cikin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace, “Yaya ni kuma?�?.
Ahmad da muryar Rumana ta saukar masa da kasala yace, “Uhum mana, ke haka aka koya miki tarbar miji ne? Wata shidda bama tare amma sam banga wani murnar ganina ko kewata a tare da keba�?.
Karon farko da kanta ya kasa ɗaukar kalamansa, domin batai tsammanin wannan furucin daga garesa ba. Saita kasa bashi amsa, wasa dai taketayi da hannayenta dake bisa cinyarta, itako tana saman tasa zaune ko nauyinta bayaji.
Hannunsa dake zagaye da ƙugunta ya janye ya kamo hannayenta da taketa cuɗawa waje ɗaya.
Sosai jan lallen da akai mata wanda ya gaurayu da zanen baƙi yayma choco fatarta dake kama da tasa ƙyau, ya janye kansa daga goshinta yana sauke sassanyan numfashi tare da murza yatsun hannun nata duka cikin hannayensa.
“Tunda bakiyi murna da dawowar tawa ba, ɗagani na koma inda na fito�?.
Da sauri ta girgiza kanta idonta na cikowa da ƙwalla “ALLAH yaya ba haka baneba fa, nayi murnar dawowarka mana�?.
Tsura mata ido yay, yanda idanunta suka kawo ruwa suna fidda wani ƙyalli saboda hasken fitilar sun ƙayatar dashi, ɗan yatsa ya ɗora kaɗan ya dangwalosu yayinda suka gangaro kaɗan saman furkarta, “Har yanzu kina nan a shashasharki dai?�?.
Baki Rumana ta kumbura kaɗan wai ita dole taji haushi ya cemata shashasha.
“Haushi kikaji?�?
Yay maganar cikin kunnenta yana sunsunar dokin wuyanta dake kamshin khumrar data shafa.
Da sauri ta sinne kai ƙasa, jikinta na ɗaukar ƙyarma saboda sabon al'amarin da yakeyi mata.
Baki yaɗan taɓe yana saka hannu ya ɗago haɓarta suka kalli juna, “Oh jan ajine komi?�?.
Kasa jure kallon tayi tana janye idanunta, “A'a kawai dai banyi zaton dawowar taka bane ba yanzu�?. Tai maganar cikin sarƙewar halshe.
Karon farko yayi murmushi har haƙoransa na bayyana, ya yunƙura tare da miƙar da ita shima ya miƙe, harkan tabarmar suka isa hannunsa riƙe da nata, ita dai ji take tamkar ta tsilla da gudu, sai da suka zauna sannan ya saki hannun nata, yakai hannu ya jawo filet ɗin abincin gabansa ya faraci ba tare da ya sake cewa komaiba.
Rumana dai na zaune duk a takure, addu'a take ALLAH ya kawo mai belinta yanzun nan, sai dai addu'ar tata bataci ba, dan kuwa har ya kammala cin abinci babu wanda ya shigo, sai motsin matan gidan da suke jiyowa daga tsakar gida.
Shikam Ahmad yanacin abincine idonsa akanta, musamman ma ƙushinta data gama tsole masa idanu tun shigowarsa gidan, amma da yake jarumin dakewane bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba.
Ya kammala cin abincinsa tsaf sannan yasha ruwa yana yin hamdala, dai-dai nan aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.
Wayarsa ya ɗauka yay kiran wani da taji yana ambata da Nura, kusan mintuna biyu suna wayar sannan ya kashe, miƙewa yay tsaye yana zira wayar cikin aljihun jallabiyarsa, “Bara naje salla, daga can zanje gidan dan bamu gaisa dasu baba ba�?.
Kan Rumana a ƙasa tace, “Saika dawo a gaishesu�?.
“Uhum�? ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.
Sai da Rumana ta jiyo fitarsa daga gidan gaba ɗaya sannan ta sauke numfashi tana murmushi, ta kalli hanunta sosai da yasha murza a nasa ta lumshe ido, wai yau itace bisa cinyar Yah Ahmad zaune ɗane-ɗane, yana mata magana cikin taushin murya da sanyi.
Duk da tasan ba sonta yakeba hakan ba ƙaramin daɗi yay mataba, salla ta miƙe ta gabatar sannan ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage a filet ɗin tana mai jin wani tsagwaron nishaɗi...
★★★★★★
Koda aka idar da sallar isha'i Ahmad gidansu ya nufa, inda ya samu damar gaisawa da kakanninsa da iyayensa maza, waɗanda yayi mamakin baiji sun rufeshi da faɗan rashin dawowarsaba, dukda yayi tsammanin hakan kuwa, ko baba baice dashi komaiba akan hakan.
Yanzun kam har ɗaki ya shiga ya samu gwaggo ya sake gaisheta, duk da bata sake masaba sai da ta jero masa tambayar ya hanya da sauransu.
Yaji daɗin kulawarta, dan haka ya amsa yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a.
Ba tare data kallesa ba tace, “Kai yanzu nan kana ganin abinda kayi mai ƙyaune? Ka tafi kabar ƴar mutane har tsahon wata shidda? Kana ganin inda badan gida bane iyayenta zasuyi shiru su zuba mana idanu?�?.
“Nasan ni mai laifine Gwaggo, amma dan ALLAH ku gafarceni, wlhy inda ALLAH yay zaman nawa mai nisane, sannan harna kwashe kusan watanni uku bana fuskantar komai a sana'ar tawa, saboda bada jari najeba, lokacin ko kuɗin motar dawowa aikine a gareni, amma insha ALLAHU bazan sake kwatanta hakanba, kuma ALLAH ya huci zukatanku, itama zan bata haƙuri na kuma nema gafararta�?.
Shiru gwaggo tayi kamar bazata amsashi, sai kuma zuwa can tace, “Shikenan, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, abu na gaba shine karnaji wani abu daban agareka cikin hidimar bikinnan, babu ruwanka da sabgar yarinyarnan komi zasuyi, ka kama kanka ka kama girmanka, suma su Mudanseer ka sake gargaɗinsu akan karnaji karna gani�?.
“Insha ALLAHU gwaggo an wuce wannan wajen yanzu, babu wani abu saɓanin mai daɗi da zakiji, ni yanzu babu wani abu daya shafeta da yake a gabana sam�?.
“Hakan ya fi�?.
Gwaggo ta faɗa a taƙaice, daga nan shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake cewa uffan a cikinsu, shi dai Ahmad badan hirar ta ishesa bane, haka ita gwaggon, tadaiyi shirune saboda dama tun fil azal babu irin wannan sabon na doguwar hira a tsakaninsu.
Kusan mintuna biyar saima ta miƙe ta fice tabar masa ɗakin gaba ɗaya.
Sassanyan murmushi yayi yanajin ƙaunar mahaifiyar tasu cikin ransa, maimakon tace ya tashi yaje, shi yaga ta koresa shine ita ta bar masa ɗakin dan kar ace ta saka ɗan fari a ɗaka suna hira.
Kai shikam bazai yarda Rumana taima ƴarsa ko ɗansa na fari wannan abunba gaskiya, dan kuwa akwai cutuwa, yanzu shi badan gwaggon ta samu Ayyah mai ƙyaƙyƙyawar zuciya ba da yaya kenan?.
Miƙewa yay yaje ya haye gadonta ya kwanta kamar yanda yakeyi a ɗakin Ayyah.
Gwaggo dake tsakar gida tana ƴan kaye-kaye saboda ganin hadari sai zuba ido take taga ya fito amma shiru, gashi Ayyah na sashen baba saboda yau itace da girki, yaran kuwa duk sun fice wajen kamu sai Zainab kaɗai a gidan itama tana sashen su Samina.
Ɗakin ta dawo dan taga mi yakeyi a ciji da bazai fito ya tafi gidaba gashi har goma tayi, dan taskar labaraima akeyi a redio.
Sosai mamakin ganinsa saman gadonta ya kamata, dan sam koda yana yaro ba ɗabi'arsa bace hawar mata gado, sai da ɗakin Ayyah.
“Kai lafiyarka kuwa? Wace irin ɗabi'ace wannan?�?.
Dariyace taso kufcema Ahmad dako motsi baiyiba, amma sai ya daure ya haɗiye da ƙyar yana faɗin “Oh gwaggo bakiso na hau sai ƴaƴanki kawai su Mudan? To nima ai suna hawa gadon ɗakinmu idan sun shiga shiyyasa na rama, kuma wlhy ki tambayi Ayyah kiji�?.
Ayyah dake tsaye bakin ƙofa ta kwashe da dariyar shaƙiyancin Ahmad, “ALLAH ya shiryeka ɗan albarka, ammafa kamin dai-dai, maza ka rama mana kuwa muma hawar mana gado da ƴaƴanta keyi ehe�?.
“Yauwa Ayyah ta, shiyyasa kike burgeni akan faɗar gaskiya�?.
Harara Gwaggo ta bankama Ahmad tana cije baki, “Tashi ka fitarmin a ɗaki fitsararren banza kawai�?.
Kasa daurewa Ahmad yay ya sakko yana dariyar yanda Gwaggo ta haɗe gabas da yamma kamar zata makesa, yayinda Ayyah ke tayashi daga waje tana faɗin, “Kaga fito kama tafi gida karta makemin kai daga dawowa�?.
“Aifa ganinan Ayyahna�?.
Gwaggo dai bata tanka musu ba, duk da tana jiyosu suna mata dariya a tsakar gida har su Fa'iza suka shigo.
Haɗe fuska Ahmad yay yana kallonsu, dukansu sunsha jinin jikinsu duk sai sukai tsaye suka kasa ƙarasowa.
“Daga ina kuke a wannan lokacin!?�?.
Tuni jikin Sadiya ya fara ɓari, hakama Salima uwar tsoro, sai Fa'izace cikin ƙarfin hali tace, “Yah Ahmad wajen kamu�?.
“Kamu?, har zuwa wannan lokacin da yake baku da hankali?�?.
Guri ɗaya duk suka cure saboda tsawar da yay musu.
Ayyah tace, ”Wlhy nima tun ɗazun abin ya dameni, babanku ma sai faɗa yakeyi, namazo ne nai maka maganar kozaka tura Abu yaje ya kirasune�?.
Sosai ran Ahmad ya ɓaci, yace, “Okey sabon iskancin da yazo muku a kai kenan saboda bana gidan?�?.
“Wlhy A'a yaya, dan ALLAH kayi haƙuri bazamu sakeba�?.
Mudan dake shigowa ta bayansu ya tallare ƙeyar Sadiya dake farko shima yana masifa, “Yah Ahmad karka wahal da kanka ai tun acan saida na basu maruka bibbiyu marasa mutuncin�?.
“Oh kace kainema kaje ka taho dasu?�? cewar Ayyah.
“Wlhy kuwa Ayyah, tun kusan takwas nake zuba idon ganin sun dawo amma shiru, har tara shiyyasa nai azamar ƙarasa ɗinkin danake nabisu har can, sun miƙe ƙafafu sam basuma da alamar tahowa�?.
Ƙwafa Ahmad da takaici ya isa yayi, ya nunasu su duka yana faɗin, “Wlhy daga yau wanima cikinku ya sake zuwa fatin saina kusa halakashi a gidannan, ƴan iska kuwuce kuba mutane waje kawuna kamar sheƙar angulu�?.
Da gudu suka shige ɗakin Gwaggo dake saurarensu daga ciki, babama duk yana jiyosu, ya kumaji daɗin yanda Ahmad da Mudanseer sukai musu, baida haufi akan tarbiyyar ƴaƴansa, koda baya numfashi su Ahmad garkuwar ƙannen sune.
Ganin iskar hadari ta fara tasowa Ayyah tace, “Ɗan albarka maza gida kafin wannan ruwan ya sakko kaji, ka gaida ɗiyar tamu�?.
Sallama yay musu ya tafi, bayan ya leƙa yayma su Iya ma sallama, wadda ta bashi wani abu a robar swan tana faɗin, “Ungo wannan ka kaima Rumana, tashashi yanzu kafin ta kwanta�?.
“To Uwargida ran gida za'a bata ta gode, amma minene haka kamar zuma?�?.
“To shugaban matambaya ba zuma bace, maganin shawarace da naji su Salima nata ƙorafin bata gajiya da kwanciya, shiyyasa na haɗa matashi kartazo wajen taron nan taita langaɓe-langaɓe, tasha kamar kashi ɗaya bisa huɗu�?.
Dariya Ahmad yayi yana cewa, “Oh kajimin iya, kina nufin matata raguwace dai kawai a fakaice?, karki damu nan gaba kaɗan ƙofar gidannan saita mata kasaɗan�?.
“Dako nayi farin cikin hakan ɗan ƙwal uba kawai, kaima ai gakanan ka ɗakko sanwar fara kiban kamar iliyasu�?.
Fita Ahmad yay yana dariya Malam dake kwance yana tayashi.
A waje yay sallama da abokansa dake shirin shigewa gidajensu, ya tari Napep zuwa gida saboda harma an fara yayyafi.
A lokacinne kuma motocin su Samina ke isowa, da alama dai lokacin aka tashi daga kamun nasu da yasha banban dana saura.
Dan kowa dai yasan da yamma ake kamu tare da dangin amarya, dangin mijima ƙalilan suke zuwa, to ita nata dangin mijin sunfi yawa, danginta ɗaiɗaikune iya ma ƴan uwan mama gaje ne, sai tarin ƙawayenta.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba