Showing 15001 words to 18000 words out of 165545 words
tara da shi�?. Yana maganarne yana laluben aljihunsa.
Gwaggo da tun ɗazun tana saurarenau bata tankaba ta katseshi da faɗin, “Kabar kuɗinka, kai Abu kaje ga gawayi can lungun ɗakin Yaya na kashe jiya kayi masa gugar dashi, dama saboda ku aka fara tarashi kwa rage cacar kuɗin sayen tunda iccen yana bada rushi sosai�?.
Murmushi Ahmad yayi har haƙoransa suka bayyana, a hankali yace, “Mun gode Gwaggonmu�?.
Shiru tayi bata amsa masaba, shima sai ya miƙe sim-sim cike da kunya yay mata sallama ya fice.
Abu ya danne dariyarsa da ƙyar, danshi Gwaggon tasu da Yayansu dariya suke bashi a kullum, sai kace wasu surukai.
Gwaggo da tasan shakiyancinsa ne ya motsa ta ɗakko mafici tana kai masa duka, da gudu ya fito a ɗakin yana dariya.
Ahmad yana gaban kejin kajinsu tsugunne Sadiya tazo zata fice riƙe da kwanon langa babba, tai masa sannu tana ƙoƙarin wucesa.
Kiranta yayi, hakanne ya sakata tsayawa tana juyowa gareshi, “Na'am Yaya nazone?�?.
“A'a karki zo�? yay maganar cikin gatse yana zaro ɗan tsakonsa sabon ƙyankyasa daya mutu daga kejin.
“Yi haƙuri Yaya�?.
Baice mata komaiba sai da ya miƙe, “Mi zaki sayo muku?�?.
“Yaya ƙosai Baba yace, na ɗari da hamsin�?.
Bai bata amsar maganartaba ya lalubo ɗarin aljihunsa ya miƙa mata, “Amshi wannan kije Mudan na fanfo ki amshi ɗari a hannunsa saiki sayo, shi kuma baban ki maida masa kuɗinsa�?.
“To Yah Ahmad mun gode, ALLAH ya kara buɗi na alkairi mai albarka�?.
“Amin�? ya amsa akan laɓansa, ya ɗauke kansa daga sadiya yana ƙwalama Zainab autarsu kira.
Babu ɓata lokaci ta iso hannunta riƙe da tsintsiyar da take sharar tsakar sashensu.
“Idan kinzo shararnan ki sharo cikin kejin nan, wannan ɗan tsakon a wullasa masai karna dawo na iskesa anan wajen, sanan a wanke kwatanniyar agwagi a zuba musu sabon ruwa�?.
“To yaya�? ta amsa a ladabce.
Ficewarsa yay ba tare daya sake amsawa ba.
Majalissar abokansa yaje inda suketa bikin karya kumallo, wasu da koko wasu da shayi dai dai ƙarfinsu, sai indomie da ƙalilan ɗonsu sukeci da aka dafo daga wajen mai shayi.
Zama yay yana miƙama kowa hannu suka gaisa, duk sukai masa tayi, amma sai ya girgiza musu kai, nanfa suka hau masa ƙorafi akan hakan.
Murmushi kawai yayi, danshi babu wanda yasan yana azumin idan ka cire Ayyah, ko Gwaggo idan ba taga Ayyah nata ƙoƙarin haɗa masa abin shan ruwa ba bata cika sanin yana azuminba.
Text message ya shiga tafa ma Samina da ƴar ƙwaƙur din wayarsa, yanayi yana ɗan murmushi harya kammala ya tura mata sannan ya maida wayar aljihu yana fuskantar hirar da abokan nasa keyi mai kama da santin abincin da suke lodama cikinsu.
__________________________________
Samina na tsaka da cin indomin data sayo wajen mai shayi da tea ɗinta mai kauri ta tsinkayo shigowar saƙo a wayarta vivo ƙarama da Ahmad ya siya mata dan karta gani wajen tsaranta, jawota tai daga ƙasan filo ta buɗe saƙon.
Murmushi tayi saboda abinda saƙon ya ƙunsa, sai kuma ta taɓe baki tana ajiye wayar gefe.
Har yanzu dai zuciyarta bata sama mata matsayaba game da zaɓin da ya dace tayi, Ahmad ko Ma'aruff?, sai dai wani gefen na kawo mata kutsen wata shawara mai sakata ban tsoro akan Yah Ahmad.
A haka ta kammala cin abincinta ta fiddo kwanikan, inda su Iya suke ajiye wanke-wanke takai ta ajiye, ta nufi ɗakin kakarta inna mari dan bata labari akan abinda ya faru jiya.
Inna Mari na tsakar ɗaki zaune tana juya wani turmin zani mai ƙyau Samina ta ahiga.
Zama tai gefenta tana fadin, “Inna wannan zaninfa?�?.
“Uhhm, wlhy Samina Haire ce ta aiko dashi jiya da daddare, wai sotake na cigita mata ko akwai mai saya, itama ɗanta yayo mata shine zata sayar saboda fatara ta isheta, nikuma badan karna ɗaukarma kaina rigimaba dana saya na ajiye saboda fitar sunan ƴar uwarki binta, na huta kinga�?.
“Eh kin kawo shawara Inna, to ki ɗauka kawai�?.
“Kijiki da wani zance auta, idan na ɗauka da shekarun tsohuwarki zan biyata?�?.
Dariya Samina tayi, ta karkace gefe tana kwanto kuɗin data raba uku wanda Ma'aruff ya bata ta ɓoye sauran tazo nunama inna mari kashi ɗaya, ta ajiye gabanta.
Sosai inna mari ta firgita, cikin ƙwalalo idanu tace, “Samina! Ina kika samo waɗanan maƙudan kuɗin haka? Kar dai sata kika far......�?
“Inna sata kuma? Dan ALLAH daina min baki mana, sabon saurayi nayi jiya ɗan masu kuɗi, shinema ya kawoni har gidanan, yakuma bani w aɗanan kuɗin dubu biyar dazai wuce�?.
“Kai dan ALLAH jikallena da gaske?�?.
“Wallahi kuwa Inna�?.
“Tofa, kice arziƙin yazo Samina, lokacin cin moriyar haihuwa yayi, yanzune mijin aure dai-dai dake ya iso gareki�?.
“Hummm�? kawai Samina ta faɗa.
Itako inna mari ta ƙule da murna harda ringume Samina, atake ta cire dubu ɗaya taba Saminar wai ta kashe, ta ajiye dubu uku kuɗin zani, ɗaya kuma ta saƙe cikin zaninta tana faɗin “Wannan kayan kicin zamu fara saye, dan yanzu sune ƙaryar, muma dolene asamu a jerin lissafi, ballema gidan daya dace a tarama kayan kicindin ƴan gaske zakije�?.
Ita dai Samina murmushin yaƙe kawai take iyayima inna mari, tanaso tace abama mamanta nata tanaji tsoron jarabar Inna mari.
Yanzu da bata ɓoye wasuba ko mama gaje inna mari bazata tunaba, amshesu zatayi duka.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*GW*
*(6)*
..............Ahmad na barin majalissarsu shago ya shiga, ya samu ya ida haɗa rigar wandon jiya da ya fara cikin kuzarinsa, yana shirin Fita Mudan ya shigo cikin shirin makaranta.
“Yauwa Mudan ka fito?�?.
“Eh wlhy yaya, gara naje dan yau text gareni, amma zan dawo da wuri insha ALLAH�?.
“Masha ALLAH, idan ka rigani dawowa to dan ALLAH kai ƙokarin haɗa kayancan nasu Jamila, banason suzo gobenma bamu kammala ba mu sake saɓa alkawari, nima zan ɗanje wani wajene, bansan kuma ko zan dawo da wuriba gaskiya�?.
“To yaya babu damuwa, amma ta gama biyan kuɗinta kuwa?�?.
“A'a gaskiya bata gamaba, Ƙawarta dai ta kammala, amma ka duba littafin da ake rubutawa zakaga nawa kuɗinta ya rage, karka bata kayannan saita fara danƙa maka kuɗi�?.
“Angama insha ALLAHU yaya, ga sauran kuɗin jiya na wajen Faridan, dubu ɗaya da ɗari uku na taɓa na maganin Yaya Maryam�?.
“Barsu a hannunka, bani dai ɗari biyu kawai a ciki, saika bama su Ayyah kudin cefane, dan na lura yau baba sai a hankali bashi da kuɗi�?.
“Eh wlhy kam naji yana faɗama Gwaggo yanzu data aika yaba auta kuɗin sayo omo�?.
“To ka basune?�?.
“Nabata naira ɗari ta sayo ɗan babban nan ƙila yakai ko jibine�?.
“Okey babu damuwa, kaje karka makara nima wanka zanje nayi na fitan, a dawo lafiya, ALLAH ya bada sa'ar text�?.
“Amin yayana abun alfaharina�?.
Madan ya faɗa cikin ƙarajin ƙaunar ɗan uwan nasa.
Ahmad baice komaiba ya kulle shagon ya fita zuwa cikin gida.
Sannu yayma su Ayya dake a tsakar gida suna cin ɗumamen tuwo ita da gwaggo a kwano ɗaya.
Ayyah ce kawai ta amsa masa, gwaggo kuwa ko inda yake bata kallaba.
Ruwa ya ɗiba a botikin ƙarfe yazo zai sake wucesu.
Ayyah dake binsa da kallo tace, “Ɗan albarka badai da ruwan sanyi zakai wankan ba?�?.
Ruwan ya ajiye yana murmushi, “Dashi zanyi Ayyah, sauri nakene shiyyasa, kuma ai rana taɗan fara zafi babu sanyin sosaima�?.
“Hakane, amma kuma mura nake tsoron kartai maka kamun kisan mummuƙe�?.
Kafin ya samu bata amsa Zainab da Fa'iza suka sanya dariya saboda zancen Ayyah na ƙarshe.
Cikin harara ya kallesu, hakanne ya sakasu yin tsitt suna haɗiye dariyar da ƙyar.
Ƙwafa kawai yayi ya ɗauki ruwansa yana faɗin, “Karki damu Ayyah bara na watsa�?.
Harya fito da ga wankan su Ayyah na tsakar gida zaune, shiga ɗakin Ayyah yay ya shafa mai acan, ya shirya cikin yadinsa ruwan ƙasa da Abu ya goge masa, yayi ƙyau sosai, yana tsaka da taje kansa akai sallama a ƙofar ɗakin.
Amsawa yay yana juyowa saitin ƙofar, “Wanene?�?. yay maganar yana ɗage labulen.
Umm-Rumana dake tsaye cikin Uniform ɗin islamiyya ruwan madara kanta a ƙasa tace, “Yaya nice, dama Yah Sufyan ne yace na sanar maka yana jiranka�?.
Sakin labulen yayi yana faɗin, “Okey, kice masa ina zuwa�?.
Cikin ɗan risinawa ta amsa da “To�?.
“Umm-Ruman jirani mu wuce�?. ‘Fa'iza ta faɗa daga ɗakin Gwaggo tana ƙokarin jawo hijjab ɗinta da jakar makaranta�?.
“Kiyi sauri to, dan mun makara wlhy, nima harmun fita dasu Salima Yah Sufyan ya maidoni�?.
Fa'iza na fitowa Ahmad ma ya fito daga ɗakin Ayyah yanata ƙamshinsa mai sanyi.
Kusan a tare suka fita shi da su Fa'iza, suka wuce islamiyya shi kuma ya hau mashin suka bar anguwar shi da Sufyan da yake masa hirar su Fa'iza.
Ahmad da ke a bayan mashin ɗin ya ɗan daki kafaɗar Sufyan kaɗan,
“Kai malam ka isheni, kabar saka shirgina a cikin na yarancan kaji�?.
Sufyan yay ƴar dariya yana shiga lingun da zai kaisa gidansu Inna mari yana faɗin, “Oh bakasan shirgin yara sai na Samina ko? To ai baifi shekara biyu da rabi tabama su Umm-Rumana ɗinba itama, da yakema sunada girman jiki aiba komai zata nuna musu ba�?.
“Kai dai kasani alhaji�?. Cewar Ahmad yana ƙoƙarin sauka a mashin ɗin.
Sufyan dake ƴar dariya shima ya sauka yana kafe mashin ɗin.
Waya Ahmad ya ciro daga Aljihu yana ƙoƙarin kiran Samina, dan wani waje zasuje yace su biyo su duba Inna mari sai su wuce.
Kusan kira huɗu bata ɗagaba, yana ƙoƙarin hangen inda zai ga yaron da zai aika a kiratane wata danƙareriyar mota data gama ƙoshi ta faka a gabansu.
Daga Ahmad har Sufyan motar sukebi da kallon mamaki, wanda ke a ciki bai fitoba kusan mintuna uku.
Ɗauke kai Ahmad yayi da ga motar ya cigaba da neman layin Samina ko zata ɗauka, dan shi abinda kawai zuciyarsa ta bashi bata kusa da wayarne....
Cikin tsagwaron gayu Samina ta fito da ga ɗakin Inna mari, sai ƙamshi take zabgawa, wanda bai saniba bazai taɓa ɗauka ta fitone da ga irin gida nasu Ahmad ba.
Tana ma inna mari da iya sallama wayarta ta shiga ƙara, tsaki taja mara sauti, dan tasan dai bai wuce Ahmad sarkin naci ba, dan duk kiran da yay mata tana zaune tana kwalliyane, amma dan iya shege taƙi ta ɗaga.
Amma Ma'aruff na kiranta yace ya iso ta fito jiki yana rawa.
Sam idanunta bai kai kansu Ahmad ba, saboda suna daga bayantane, taku take ɗai-ɗai tamkar tazo filin gasar sarauniyar ƙyau ne, ƙamshinta kuwa tuni ya buɗe hancin Ahmad da Sufyan da ke binta da kallo baki buɗe tamkar sakarkaru.
Daga cikin motar Ma'aruff dake kallonta ya miƙa hannu ya buɗe mata murfin gefensa, a gaban idonsu Ahmad ta shige motar.
Wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare maƙoshin Ahmad ne ya wuce da ƙyar, yaso ya danne amma sai ya kasa, ya yunƙura cikin zafin nama zai je gareta Sufyan yay azamar ruƙo hannunsa yana girgiza masa kai.
Dole Ahmad ya haƙura ya zubama motar ido har tabar wajen, Sufyan dake ɗaukarsu video recording a waya ya sauke yana sauke numfashi kusan a tare.
Baicema Ahmad komaiba akan hakan, sai Mashin da ta haye abinsa ya tayar yanama Ahmad nuni da shima ya hau suje.
Har sukaje inda suke son zuwa babu wanda yay magana balle su ɗakko zancen Samina.
Sun isa wajen ƙawarsu mai suna Zaheedah, tare sukai karatu da ita, da farko catai tanason Ahmad, amma sai bai ɓoye mataba ya sanar mata yanada wadda zai aura tayi haƙuri.
Tayi fushi a lokacin, amma daga baya sai ta dawo kuma tace su zama abokai, badan Ahmad ya soba ya amince saboda matsawar Sufyan da Ameen, tun daga lokacin sai suketa zuminci, tare da taimakon juna akan karatu har ALLAH yasa suka gama.
Sun cigaba da zumincinsu, yayinda suke haɗuwa jefi-jefi dasu Ahmad ɗin, sai ko waya ita sunayi akai akai.
Tarbar mutunci suka samu daga wajen Zahidah, ta kaisu har falon baƙi dake a cikin gidansu, kafin wani dogon lokaci an cika musu gabansu da kayan ciye-ciye.
Sufyan ne kawai yaɗanci wani abu, amma banda Ahmad dake a zumi, wanda dole ya faɗa musu azumi yakeyi saboda fushi da Zaheeda tayi akan baici abin gidansuba.
Gaisuwa sukayi cikin mutunta juna, kafin su ɗora da hirar yaushe gamo, dan sun ɗan daɗe basu haɗuba.
Sun mata bayani akan abinda ya kawosu game da taimakon da zatai musu akan yaya maryam.
“Karka damu Shema, insha ALLAHU zan bada gudunmawata, domin gyaran aure aiba abin wasa baneba, amma ku yaya maganar naku auren? Musamman ma kai Shema da nasan akwai matar tamu a hannu?�?.
Murmushin yaƙe kawai Ahmad yayi, amma baice komaiba, sai Sufyan ne ya bata amsa da faɗin, karki damu, soon zakiji bayani mai daɗi insha ALLAHU�?.
Cikin faɗaɗa murmushi tace, “To ALLAH ya tabbatar mana, ya kuma kaimu lokacin�?.
Da amin suka amsa, inda Ahmad ƙoƙarin danne ɓacin ransa kawai yakeyi a wajen.
Kusan awarsu biyu a gidan sannan sukai mata sallama suka tafi, bayan ta haɗasu da leda ta kayan shan ruwan Ahmad. Da ƙyar suka amso, dan sai da ta ɓata rai sosai sannan.
Sufyan yaso su ƙara zuwa wani waje danya ragema Ahmad ɓacin ran da ya lura yakai ƙololuwa a ciki, amma sai Ahmad ɗin yaƙi yarda, yace su wuce gida kawai.
Sufyan na kafe mashin a majisarsu Ahmad bai zaunaba, hannu kawai ya bama su Salisu dake zaune su uku kawai suka gaisa ya nufi gida abinsa.
A ɗakinsu na zaure ya yada zango, da ƙyar ya iya zame kayan jikinsa ya zauna