Showing 75001 words to 78000 words out of 165545 words

Chapter 26 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

386

gidanta yaje sai sunyi.
Ta girmesan amma tsiran bawani baneba, shiyyasa hakan ke bashi haushi.
Su Yaya Maryam nata musu dariya Rumana ta shigo, ya zubama kan Sakina ranƙwashi yay saurin nufar hanyar ƙofar gida yana faɗin Rumana ta samesa a waje.
Sosai yanzu kowa ke musu dariya har Ayyah da Gwaggo, dan kuwa Sakina taji zafin ranƙwashin nan sosai.
Ya tsaya mana inba tsoroba, kuma zata kamashi saita rama.
Ita kanta Rumana abun nasu ya matuƙar bata dariya, dan haka tabisa da kallo tana murmushi.
Sallama taima su Ayyah dasu Yaya Maryam ɗin ta fita, lokacin anata hayaniya a ƙofar gida da abokan ango, dube-duben inda zataga Ahmad takeyi, duk da kuwa ƙofar gidan akwai hasken wutar nefa da aka kawo.
Jin an kama hannunta tai saurin juyowa, ganin Yah Ahmad ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali, baice mata komaiba yaja hannunta suka bar wajen.


★★★★

Duk da Ahmad ya lura da fushin da takeyi sai ya shareta kamar bai fahimci abinda take jima haushin ba, lokacin da suka shigo gidan shiru dan kowa ya shige ɗaki ya kwanta, Ahmad ya buɗe musu ƙofa suka shiga.
Kayan jikinsa ya rage itako Rumana ta samu waje ta zauna tanata kumbura fuska.
Baibi takanta ba ya haɗa ruwan wanka ya tafi yowa, har ya dawo ɗakin tana a inda ya barta, murmushi yayi kaɗan yana girgiza kai, yasa tawul ya goge ruwan jikinsa ya shiga shirin barci.
Sai lokacin itama ta miƙe ta ɗeba ruwan ta fita, da kallo kawai ya bita amma uffan bai ce ba.
Itama dai wankan tayo, lokacin data shigo harya kwanta, sai dai ba barci yakeba waya yakeyi, Rumana ta kalli agogon ɗakin sannan ta kallesa, duk da bataji da wa yake wayarba hakan ya bata haushi, tako sake tsuƙe fuska waje guda.
Duk abinda take Ahmad na lure da ita, ta kammala mutsu-mustun shirinta tazo gefen gadon nesa dashi ta kwanta a takure.
Dai-dai nan ya ajiye wayar shima, matsowa yay tsakkiyar gadon ya jawota ta dawo jikinsa.
Hancinsa saman dokin wuyanta yana hura mata iska yace, “Kodai mu koma ne kima amaryar zaman ɗaki?�?.
Tasan baƙa ya faɗa mata, dan haka tai shiru, murya a shaƙe ya sake faɗin, “Dake fa nake magana�?.
“A'a�? ta faɗa tana ƙanƙame jikinta saboda abinda yake mata da hannunsa a cikin jiki.
Bai sake magana ba sai sabon salo daya canjama kwanciyar tasu.

“Yau ɗinma dai babu sauƙi�? cewar Umm-Rumana a zuciya tana share hawaye bayan ta gama gurzuwa a hannun jaruman mazaje.
Da taimakon Ahmad yau ɗinma ta kimtsa jikinta tanata masa kuka, da yake kukan da biyune harda haushin ƙin barinta ta kwana gida sai na yau ya nema finma na shekaran jiyan, shi dai Ahmad idanuma ya zuba mata, sai dai a ƙasan ransa yanajin tausayinta dan shi kansa yasan shiɗin bana wasan yara bane, tunda yana a ganiyar ƙuruciyarsa ne, kuma yanzunma aka fara wasan🤭.
Yanata lallashinta ta sigar shafa mata baya har barci ya kwashesu a haka su dukansu.

★★�?

Washe gari Ahmad na gida har azahar bai fita ko inaba, hakanne ya saka Rumana fahimtar itama dai bazataje ko inanba kenan.
Bataga fuskar tambayaba kuma dan haka tai shiru da bakinta sai haushi dake cinta a zuciya.
Bayan anyi sallar azhar ɗinne Zainab da Ni'ima ƙanwarta sukazo, taɗanji daɗi, dan kayayyakin bikine wanda Ayyah ta haɗo tace a kawo mata, a wajensu takejin ai suma su Yaya Maryam duk sun tafi gidajensu ma, gidanma sai iya dangin mama gaje ne kawai da suke shirin zuwa buɗar kai gidan Samina.


_________________________________

Ko wacce amarya tana saka daren farkonta a jerin tarihin daren tunawarta koda takai tsufa saboda muhimmancinsa a gareta, sa ɓanin Samina daya zame mata daren baƙin ciki da wahaltuwar ciwo, da safe tashi tai tamkar wadda aka tsamo daga bakin kura, tayi wujiga-wujiga cikin azabar ciwo, ga kukan wahala datasha idanu sunyi luhu-luhu.
Har lemon tsami sai da ta samo daƙyar a kicin ɗinsu tasha amma bataji yanda takeso ba, sai da taɗan samu kanta kaɗan harta sami damar gyara jikinta tai wanka, bataga ko ƙeyar ma'aruff ba a gidan kuma bataji motsinsa ba sam, gashi koɗan abincin da akan kawo daga gidan surukai washe garin kai amarya ita babu wanda ya kawo matashi.
Ƴar kazar amarcin da ango yake kawowa nanma bata sameta ba a daren jiya.
Komai ya dagule mata ta kowanne fanni, har zuhur bataga kowa ya leƙotaba ga yunwa ga damuwa ga ciwon mara, falo ta dawo ta kwanta cikin kujera tana hawaye, a lokacinne taji ana ƙwanƙwasa ƙofa.
Tashi tai bayan ta ciri tissue dake saman center table ɗin falon ta goge hawayenta taje ta buɗe, ƴan uwan mahaifiyartane da sukazo buɗar kai.
Matsa musu tai suka shigo tana musu sannu da zuwa, su dai sai binta suke da kallo.
Duk da sunsha mamakin ganinta ita kaɗai a gidan sai basuce komaiba, yanda akasan amarya da farin jini sun zata kodai dangin mijinta sa iske wasu a ciki, duk da dai sun kula ƴan gayune kowa rayuwarsa yake babu ruwansa data wani, kuma yanda mijin nata yake firi-firi babu alamar kunya a idonsa ma ya hana kowa raɓarsu.
Yanayin da suka ganta wujiga-wujiga basu kawoma kansu tana cikin damuwa baneba, ca suke kawai dai angone ya mori amarcinsa musamman lura da yanda take tafiya da sukayi, ita kuma ciwon marane ya sakata tafiya a dudduƙe😣🤭.
Bata iya faɗama kowa halin da take cikiba har suka gama hidimarsu bayan la'asar sukai shirin tafiya, a lokacin kuma motar ma'aruff ta shigo cikin gidan.
Ya fito daga mota sai wani tsume fuska yake tamkar baiga waɗanda suke a gidanba, kamarma zai wuce bazai gaidasu ba sai kuma dai miya gani oho masa, ya tsaya ya gaishesu cikin rashin girmamawa ya wuce abinsa.
Wannan abu kuwa ya saka kowa a cikinsu yaye baki suna binsa da kallo harya shige, ita kanta Samina abin ya sosa mata rai.
Su dai duk sun tafi zuciya a saɓule, yayinda wasu suka gumtsi abin faɗa da yaɗawa kuwa.

Samina na shiga falon taci karo da Ma'aruff tsaye yana cika yana batsewa, harara ta zuba masa tana jan tsaki zata wucesa.
Baice mata komaiba ya fisgi hannunta ya jata ɗakinsa saikace wata abun banza, saman gado ya wurgata kawai ya afka mata.
Sosai Samina taji warin giya a jikin Ma'aruff, hankalinta yay matuƙar tashi, duk da a buƙace take dashi sam batajin daɗin yanda yake mu'amulantarta yanzu, ga warin giya ya addaba ma, tsabar baisan abinda yakeba kuma danna mata bakinsa kan nata, yunƙurin amai samina ta fara tana kuka wiwi, Ma'aruff ya cire bakinsa jin zatai masa amai yako kaftama fuskarta mari.
Kuka mai tsuma rai Samina ta saki, dama gashi da mugunta yake kusantarta saboda baisan ina hankalinsa yakeba, kuka take tana roƙonsa yayi haƙuri, ta tuba.
Cikin maye yace, “Ba ke kike buƙatata tun jiyaba, dan uwarki kin samu ma shine zakimin yanga�? ya ƙare maganar yana sake kafta mata marin daya sake gigitata.
Yana samun nutsuwa kuma ya kwarayo mata amai a jiki mai azabar wari ya koma gefe yana sauke numfashi...............✍�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(25)*


..............Samina ma aman ta shiga kwararawa.
Ma'aruff ya tashi zaune da ƙyar yana faɗin, “Kai wai k dan uwarki amai kikemin ma a ɗaki? To aiko saikin shanyeshi shegiya sauran titi, ƙilama bani kaɗai kike baiwa ba�? ya ƙare maganar yana kai mata wani bahagon bugu.
Dan wuyama Samina yanzu kasa kukan tayi, babu ko ɗigon tausayinta a ranshi ya tashi yashiga lakaɗa mata duka, ta ƙwaci kanta da ƙyar zata gudu, yace wlhy idan ta fita sai ya mata mafiyinsa tazo ta gyara masa gado da ɗaki, uwartace zatazo ta goge wannan aman?.
Dole Samina ta tsaya dan duk a birkice take, ga tsoronsa ya kuma tasiri mata arai, tana kuka ta nannaɗe zanin gadon, shiko yana tsaye ƙyam a kanta da belt ɗin wandonsa.
Haka ta haɗa ruwan morping tazo ta tsaftace gadon zuwa tsakar ɗakin, Ma'aruff kuwa na tsaye a kanta, sai da yaga komai yay masa need sannan yace ta haɗa masa ruwan wanka, kuma saita wanke bayin, danshi ya kula wai batada tarbiya, toshi zai koya mata tasa a gidannan😂🤭.
Duk uban aikinnan da Samina keyi a bubbuɗe take tafiya saboda ɓarnar da Ma'aruff yay mata na afka mata, duk yanda yakeso haka tayi, tana hawaye harta kammala komai ta saka masa wankakken zanin gado ta feshe ɗakin da air parishioner.
Zata fice ya kuma dawo da ita, “K dan uwarki juyo bayanki, ubanwa zai wanke miki wannan zanin gadon? Zoki ɗauka karkuma kibari na tashi barci na ganshi da dattin nan�?.
Dawowa tai ta ɗauka ta fita dashi tana sharar ƙwalla.
Shiko yaja tsaki yana nufar ban ɗaki, koda yayo wanka zuwa yay ya kwanta abinsa, barci mai nauyi kuwa ya sacesa hankali kwance.

A ɗakin tama data koma kuka taitayi rurus, ga warin zanin gadon dana giyar daya goga mata ya addabeta, dole ta ajiye batun zaman kuka gefe ta miƙe ta hau wankin zanin gadon hanci a toshe, sai da ya fita fes ta ajiyeshi gefe itama ta fara tsaftace nata jikin, ta shiga ruwan zafi kozataji nutsuwa akan baƙar muguntar dayay mata.
A daren jiya ta wahaltu da buƙatarsa, sai gashi bata samu nutsuwar fitar abinda ya dametanba saima baƙar wahala data shawo, wahalar kuma ta mantar da ita buƙatar da take ciki gaba ɗaya.😣⛹‍♀

Tsakar gida taje ta shanya zanin gadon da ƙyar, ga yunwa nacin hanjin cikinta, ga damuwa, kayan cincin da aka kawo mata na gara wanda mama gaje tai bajintar yi saboda za'a kawo ƴa gidan masu kuɗi Saminar ta ɗiba, sai dai kuma tuno warin aman Ma'aruff da haɗa bakinsu da yayi ya faɗo mata a rai, saurin ture filet ɗin tai gefe saboda sabon amai da taji yana zuwa mata.
Kanta ta dafe tana hawaye da faɗin, “Nashiga uku ni Samina, wace rayuwace na jefo kaina a ciki?�?..
Bata da mai bata amsa dan haka ta cigaba da raira kukanta a falon.


“Masu karatu ban saniba ko kuna da amsar bata”💁🏼‍♀�?.

Ni dai Bilynku bani da🤩🤪⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀


★★★★

Ma'aruff bai farka ba sai kusan tara na dare, normal ya miƙe, yay wanka yay shirinsa mai nuna alamar na fitane, a falo yaci karo da Samina dake kwance a galabaice ko sallar la'asar, magriba, isha'i bata samu yinsu ba saboda rashin ƙarfin jiki, yunwa tacita ta cinye.
Tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, “Lafiyarki kuwa?�?.
Ganinsa cikin hankalinsane ya saka Samina tunanin roƙonsa kozai tausaya mata, ta miƙa masa hannu tana fashewa da kuka.
“Dan ALLAH ka taimakeni kar yunwa ta halakani�?.
Tsabar rashin mutunci irin na ɗan giya dan baisan yama aikata mata duk wancan abunba sai ya riƙota yana faɗin, “Wai dama bakici abinciba?�?.
Ganin ya amshi abun da muhimmanci Samina ta kuma langyare masa tana fashewa da sabon kuka, kwantar da ita yay yana miƙewa, “Kinga ina zuwa�?.
Samina ta bisa da kallo harya fice, batai zaton zai dawoba, dan kusan awa ɗaya sannan sai gashi da abinci ya kawo mata, shine ya tadata zaune ya fiddo mata daga leda ya bata, jikin Samina har rawa yake taga abinci, aiko ta fara masa cin hannu baka hannu ƙwarya kamar bata taɓa cin abinciba a duniya, tana gamawa ta miƙe da gudu xuwa banɗakin falon ta shiga yin amai saboda yunwar data gama cinye mata hanji.
Da kallo kawai Ma'aruff ya bita amma ko gezau baiyiba ballema ai tunanin zai bita ya taimaka mata.
Yana wajen zaune ta dawo tana tafiya da ƙyar da fidda huttan numfashi suma da ƙyar ɗin, kujerar ta koma ta kwanta.
Ma'aruff ya kalleta aɗan yatsine yace, “Lafiya dai ko?�?.
“Amai nayi�? tafaɗa a marairaice.
“Tofa, to ALLAH ya kiyaye, kibar zama da yunwa dan yanzu kinga sakamakon ta�?.
Da mamaki ta kallesa hawaye wasu na korar wasu, “Hakama zakace nabar zama da yunwa bayan kaine sanadin komi, jiya aka kawoni gidanka ashe abinda ka shirya min kenan Ma'aruff? Wannan shine sakamakon son danai maka da sadaukarwa?......�?
“K Samina kinga dakata min, mina miki mara ƙyau a gidannan, idan batun abinci kike baga komai nan a kicinba, miya hanaki shiga ki girka? Naga dai gidannan ba baƙonki baneba, idan kuma maganar daren jiya kike nima saikimin uziri, sam babu buƙatar abinda kike ƙulafici daga gareni a sannan, to tayaya kike tunanin zan iya mu'amulantarki yanda kike buƙata......?�?.
Cikin katsesa Samina tace, “Eh amma ai ka mu'amulanceni ta hanyar da bantaɓa maka zatoba, yanzu dama ashe kana shan giya?�?.
Tsaki yaja yana taɓe baki, “To miye dan ina shan giya? Rayuwatace fa, kuɗina, ra'ayina kuma, please karki kawomin wannan ƙananun maganar dan bazan ɗaukaba�?.
“Dolene na maka magana akan shan giya Ma'aruff, domin a sanadinta yau ka dubi yanda ka nema halakani, idan a haka zamu cigaba a gidannan watarana gawata za'a tarar, jiba yanda ka farfasa min jiki da duka, bayan rashin tausayin daka nuna mani da baida banbanci fyaɗe....�?
Kansa ya dafe, sai kuma ya ɗaga mata hannu yana faɗin, “Ya isa haka Please, kiyi haƙuri ni bansan na mikiba, kuskure aka samu�?.
Tsayawa kawai tai tana kallonsa hawayenta suna sake ƙarfin gudu.
Yace, “Kin tsareni da ido, banace kiyi haƙuri ba�?.
Koba komai taji ɗan sanyi a ranta, ta share hawayenta tana amsa masa da “Shikenan ya wuce, amma dan ALLAH Sweet wannan ya zama na farko na ƙarshe, dan ALLAH kabar sha kaji�?.
“Shikenan ya wuce, ki ɗauki ɗayan abincin sai ki sake ci kije ki kwanta, ni bara na fita saina dawo�?.
Da sauri Samina ta tashi zaune, “Sweet fita kuma? A wannan daren?�?.
Kamar bazai kulata ba, mikuma ya gani oho masa ya juyo ya kalleta, “Kinga bawani jimawa zanyiba zan dawo, akwai abinda zanyine, nima fitar ta zamemin dolene�?.
Kasa ce masa uffan tayi, sai baki da hanci data saki tana binsa da kallo harya fice.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login