Showing 135001 words to 138000 words out of 165545 words

Chapter 46 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

404

Tafiyar Ahmad ta gama kankama, zai fara yin gaba kafin yaga abinda ALLAH zaiyi game da iyalinsa da yakeson su bishi, yana tare da damuwa game da karatun Zainab data fara za'a datse mata, dan bazai yuwu su koma can su kaɗai su zaunaba, amma da yay shawara da su baba sai sukace aje da Abu can porthercout ɗin sai ya zauna dasu Rumanan har aga abinda ALLAH zaiyi.
Kowa yayi na'am da wannan shawara.
Tare sukai shiri suka koma port, suka sake barin ƴan gidansu da kewa, kowa kuma nabin Ahmad da addu'ar fatan alkairi da ɗunbin nasara.
Duk jarumtarsa sai da ya share hawaye, dan yanaji a ransa kamar bai zama lallai ya sake ganawa da wasunsu ba, koshi ya mutu, kosu wani ya mutu.

Wannan tafiyar harda Abu aka yita, hakan yasa Ahmad da Umm-Ruman suka zauna a baya, Abu da zainab kuma na gaba dan shata ya ɗauka wannan karonma.
Sun isa gidansu da sukaima yajin sati biyu, a ranar da suka isan dai babu abinda suka iya tsinanawa saboda jigata, dan wannan tafiyarma tiɓis su Rumana suka isa, hatta da Abu kansa dan shima bai taɓa doguwar tafiyaba irin haka.
Haysam kam wannan karonma ragal yake yaronnan, sai dai yayi barci ya farka.

Washe gari kasancewar Abu ba mutum mai ganda ba da taimakonsa Umm-Ruman ta gyara ko ina ya ɗauki haske, Ahmad kam ma tunda safe ya fice gidan, bai dawoba sai yamma tare da Happy.
Duk da Rumana tayi mamakin ganinsu taren sai batace komaiba, ta tarbeta da mutunci kamar yanda ta saba, sai da suka shiga ɗaki Ahmad ke sanar mata anan Happy ɗin zata kwana.
Murmushi kawai Rumana tayi batace dashi komaiba, ya riƙo hannunta yana tsatstsareta da idanu.
“Naji bakice komaiba?�?.
“To Yaya mizance? Tunda da dai ga ɗakin Zainab basai tai kwanciyarta ba�?..
Baice komaiba ya sake mata hannu, ta fice shikuma ya bita da kallo kawai yana girgiza kai, akan laɓɓansa ya furta “Kishi kenan Gwal?�? babu mai bashi amsa, dan haka ya taɓe baki kawai.

Washe gari ranar tafiyar Ahmad, bayan ya gama kimtsawa suka rankaya domin masa rakkiya a motar daddyn Happy da sukazo.
Kallo ɗaya zakaima Umm-Ruman kasan ta ƙwaɗi kuka a daren jiya, shi kansa Ahmad wannan tafiyar jiyake kamar yayta kukan, Haysam nata barcinsa har suka isa Airport ɗin.
Zaman da baifi na mintuna talatinba aka fara sanar da shela akan matafiyan, nanfa ran Umm-Ruman ya sake dugunzuma.
Ahmad dake zaune kusa da ita ya sauka yay durƙuso a gabanta tare da kama hannayenta duka cikin nashi, yau ko kunyar Abu da Zainab baijiba.
“Haba Babie R ki daure Please, insha ALLAHU kuma nan bada jimawaba zaku bini, saboda inason ku kasance kusa dani yasa na zaɓi ƙasar saudia domin yin karatunnan koda aka bani zaɓi, saboda inason yarana su tashi da cikar burina, insha ALLAH bazan ɗau lokaciba zaku matso kusa dani kuma kinji, ki kulamin da Sadaukina, idan kuma nayi ajiyar ƙanwarsa anan itama a bata kulawa�?. ya ƙare maganar da shafa cikinta
Kanta ta ɗaga masa tana share hawayenta da murmushi a lokaci ɗaya, ya miƙe tsaye tare da sumbatar goshinta yana saka mata albarka shima da murmushi shinfiɗe a tashi fuskar.
Barin gabanta yay yaje ya sumbaci Haysam dake barci a bayan Zainab, itama ya kuma mata gargaɗi akan karatu.
Ya matsa yayma su Momyn Happy sallama yana sake musu godiya, sai ga Happy na hawaye, badan tasan bayaso ba da babu abinda zai hanata rungumeshi.
Ya bama Abu hannu shina yana sake jaddada masa ya kula sosai, cikin girmamawa Abubakar ke amsawa yayan nashi, tare da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara.
Harya tafi ya dawo wajen Umm-Ruman da duk suka miƙe tsaye ya rungumeta, dole Abu da Zainab sai ƙasa sukai da kansu.
Jin sunansa da aketa ambatane ya sakashi sakinta ba tare dayace uffnba ya juya ya fita.
Momyn happy tazo ta rungume Rumana a jikinta tana lallashi, da ƙyar suka samu tai shiru.

Sai da jirgin su Ahmad ya lula sannan suka bar airport ɗin, har gida su Dadyn Happy suka maidasu sannan suma suka wuce.
Umm-Rumana ta shiga ƙunci akan tahowar Ahmad porthercout balle barin ƙasa baki ɗaya, ranar har Haysam saida ya shaida tana fushi, dan ƙiri da muzu taƙi bashi nono sai tea sukaita banka masa da abinci.
Ƴan gida sunata kiranta harda amare su Fa'iza, sanda suke waya da Ammi saita saka mata kuka, Ammi ta yanke wayar kawai.
Haka ma baba kuka taitai masa, shidai ya allasheta da kalamai masu daɗi akan tabi mijinta da addu'a ba kukaba, kalaman babane suka sanyaya ranta harta daina kukan..............✍�?





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_64244456G_*



..............Ahmad an sauka ƙasar saudi-arebia, ƙasa mai tsarki, mahaifar MANZON ALLAH (tsira da amincin ALLAH su ƙara tabbata a gareshi), wajenda ɗakin ka'aba yake, gari mai farin jini da tarin al'umma, mai tarin ni'ima da burin zuwa ga kowa.
Jirginsu ya sauka a filin jirgin birnin Dhahran, Baisha wata wahala ba saboda haɗashi da yaron ogansa daya koya masa sana'ar ɗan kunne da akai tunkan ya taho, shima yana karatu anan ne, sai dai shifa ustazu ne na gaske, dan yana karatune ɓangaren islamic, an kwankwaɗi madarar ilimi sosai, sai dai muyi fatan ALLAH ya bada ikon amfani da shi, da amfanar da sauran al'umma.
Kasan cewar an tura masa hoton Ahmad shima kuma Ahmad ɗin yana da hotonsa sai babu wahala suka gane junansu.
Cikin al'ada irin ta larabawa suka rungume juna kafin suyi musabaha kamar yanda ustaz ya nuna yafi buƙata, kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi shinfiɗe, bazasu gaza sa'annin junaba, dan shima ɗin dai kwanan nan akai masa aure aka turo masa matar nan.
Suna riƙe da hannun juna har lokacin Ahmad yace, “Muh'd Gaddafi Umar ko? Idan banyi mantuwa ba�?.
Murmushi yay masa shima yace, “Hakane abokina, kaima Ahmad Hamza Rabi'u.
Ahmad yay ƙaramar dariya yana jinjina masa kai, abinka da masu ilimi, sai suka sake da juna dandanan kamar sun daɗe.
A gidan Muh'd Gaddafi Ahmad ya samu masauki, inda akai masa tarba ta mutunci da bazai taɓa mantawa ba, duk da amaryar Muh'd na fama da laulayin ciki haka ta shirya musu liyafa, Saudia taima Ahmad ƙyau, musamman birnin Dhahran da ya sauka, jinsa yake a yau tamkar wani sabon mutum, har suka iso gidan Gaddafi idonsa bai daina kalle-kalle ba.

Bayan sunci sunsha aka kaisa inda zai kimtsa ya hutama ransa, yakoji daɗin hakan dan hutun yake buƙata dama sosai, sai dai koda ya kwanta sai tunanin ahalinsa ya hanasa rintsawa, ya tabbata yanzu Rumana nacan cikin damuwa har yanzu, tafiya iya porthercout kawai ta saka kanta a matsananciyar damuwa inaga yabar ƙasarma baki ɗayane, ko Haysam zaiyi kuka in bai gansaba oho.
Yata tunane-tunane kafin barci ya sacesa.

Rayuwar gidan Gaddafi ta birge Ahmad sosai, dan ya fahimci akwai tsantsar ƙauna a tsakanin ma'auratan da soyayya mai tsafta, hakan sai ya tada masa nasa tsumin akan tashi gimbiyar da a yanzu ta zama wani sashi na rayuwarsa, sai murmushi yake saki tare da ƙara jin ƙaunarta da begenta mai tsanani.
Ya ƙanƙame filo a ƙirjinsa yana sauke nannauyan numfashi tare da rumtse idanunsa da kiyasto Baby R ɗinsa a yanayin da yazame masa sirri mai daraja da mutuwace kawai zata iya masa shamaki da tunawar.


_________________________________

Kwanaki Biyu Rumana na a sukuku da ita, kafin kuma ta saki jikinta ta koma normal, dan Ahmad ya kirata a ranar da Safe da wayar Gaddafi, tayi farin ciki sosai kuwa, yanda yake bata labarin kansa a saudia sai taji kamar tai tsuntsuwa ta ganta acan.
Su Zainab ma duk sai da ya gaisa dasu, hakama Haysam an saka masa wayar yanaji hayaniyarsa duk da shi yaron baisan anaiba ma.
Gidama Ahmad ya kirasu dan su sami kwanciyar hankali, aikam duk sunji daɗin hakan sosai, sunata jifansa da addu'oin fatan alkairi.
Cikin jin daɗi da tsantsar kewarsu yake amsawa har yanajin ƙwalla ta taru masa a idanu, ahalinsa suna da muhimmancin da bakinsa bazai iya furtawaba a rayuwarsa, yana addu'a rabbi ya azurtashi da halalinsa mai albarka da zai tallafi rayuwar sauran ƙannensa masu tasowa, suma su sami ilimi wadatacce kamarshi, ba dole sai na boko ba, na addini shine jagaba akan komai, shine kuma ake ribantuwa dashi a duniya da lahira, dan haɗuwa da Gaddafi ya sake tada masa kwaɗayi akan son sake zurfafa ilimin addini a rayuwarsa, sannan yanama ƙannensa sha'awar hakan suma.



___________________________________



Duk wani shigi da fici na karatun Ahmad da taimakon Gaddafi da yasan gari yayisa, sosai jami'ar *_King Fahd University of Petroleum & Minerals_* ta ƙayatar da Ahmad, ya zama ɗan ƙauye a cikinta, “kaga gini tamkar ba hannune yayisa ba malam Gaddafi?�?.
Gaddafi dake kallon Ahmad yay murmushi yana mai sake bin makarantar da kallo shima, yace, “Ai Birnin Dhahran yana cikin manyan birane na duniya masu ƙayatarwa, shiyyasa da yawan Universitys da sauran makarantu dake wannan birnin zaka samesune a ƙawace, birnin da fadar saudiyyarfa yake kenan, kasanko ai dole komai na cikinsa ya ƙawatar�?.
Ahmad ya sauke numfashi yana faɗin, “Lallaikam, cigaban da ya gagari namu ƙasashen kenan, kowa da ga aljihunsa saina ƴaƴansa da iyalansa ya sani, ALLAH ka azurtamu da jannatulfirdausi maɗaukakiya�?.
“Amin ya rabbi abokina�?
Gaddafi ya faɗa yana maijin takaicin al'ummarmu da suka dauki zalunci ƙaramin abu da bazai taɓa komai na rayuwarsuba, balle ya ragesu, sun manta da inda ake biyan zalunci komin ƙanƙantarsa da ayyuka, ranar da kowa ayyukan yafi buƙata ruwa a jallo, ranar da in baka da ayyukan kwarai a taskarka zunibin wanda ka zalunta za'a ɗiba a maka maka (Ya rabbi ka rabamu da rufaffiyar zuciyarda shaiɗan ke gadinta, ka azurtamu da ganin gaskiya komai dacinta garemu, ka hanamu zalintar duk wanda ALLAH ya haɗamu zama dashi koda ba'amuhalli dayaba, ka hanamu hassada da ƙyashi wa kowa, ka hanamu ƙuntata zuciyar kowa a rayuwarmu, ka hana maisan ƙuntata mana samun nasara a kayinmu😭🙏🏻).
Har suka isa gida suna cigaba da tattauna matsalolin ƙasarsu ne da suka baro.

Cikin kwanaki kaɗan komai ya kankama na karatunsa, Gaddafi ya ɗaukesa sukaje har makkah yay addu'oi ɗakin ka'aba na neman nasara da haske a dukkan al'amuransa, makkah ma ta ƙawatar dashi ainun, yay ziyarce-ziyarce sosai kafin ya fara zuwa makaranta, shine har Madina bisa jagirancin Gaddafi dai.
Aiko Alhmdllh, dan tunkan ai nisan zango yafara cin karo da hasken, dan kuwa yanda ya kamata yana fahimtar karatun da yazo dominsa.
Satinsa biyu a gidan gaddafi ya samu wajen zama shima, hakan yasa ya tattara ya koma can, gashi abin jin daɗi kusa da makarantar.
Kwaɗayin son faɗaɗa ilimin addini dan amfani da damar da ALLAH ya bashi, ya sakashi ma Gaddafi maganar son komawa makaranta, sosai Gaddafi yaji daɗin wannan al'amarin, kuma Ahmad ya birgesa, babu bata lokaci nanma ya shiga shigi da fici har Ahmad ɗin ya samu shiga wata islamiyya ta dare da aka buɗe domin magidantan da basu da lokacin kai da rana da irinsu Ahmad da karatu ke cinyema lokaci, nanma dai Ahmad ya fara karatunsa cike da nasarori kuma ya maida hankali dan kuwa masu iya magana sunce gemu baya hana ilimi.
Kullum da dare sai yayi waya da iyalinsa, Rumana taita masa shagwaɓar da ke tada hankalinsa dajin buƙatar son ta matso kusa dashi.
Haka kwanaki sukaita jaa, abubuwa nata faruwa, inda kafin kace kwabo Ahmad ya ja watanni huɗu da tafiya, tun yana ƙaraminsa mutum ne shi mai zuciyar nema, hakan yasa ko a ƙasar ta saudia bai zauna ya dogara da karatunba kawai, dukda duk watan duniya albashinsa na shiga asusunsa, wanda aciki yake fidda hidimar iyalansa da ahalinsa.
Shawara ya nema wajen Gaddafi akan son fara yin wani abun, Gaddafi yay murna da wannan zuciya ta Ahmad, nan take ya bashi shawara ƙyaƙyƙyawa kuwa, da taimakonsa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe duk da dai na Gaddafin sunfi suka fara kasuwanci, dan dama shi Gaddafin yanayi.
A lokacin da Ahmad yake watanni na goma sha ɗaya sai dai muce Alhmdllh, dan kuwa dai-dai gwargwado yasamu rufin asirin da zai iya maido su Rumana nan, babu ɓata lokaci yasa aka fara musu shirin tahowa harda Zainab, Abu kuwa anan porthercout ɗin yasa ake nema masa admission, dan dama yana zuwa wajen Nura tare suke zama wajen sana'ar kayan yarinsu Ahmad ɗin.
Randa Ahmad ke sanarma Rumana suyi shirin tafiya kano tayi farin ciki sosai, dan tafiyace dake nuni da sun tafi kenan daga can jirginsu zai ɗaga zuwa saudia.
Harda Abu suka taho kanon, amma shi zai dawo ne tunda komai na karatunsa ya gama kammala.
Sosai Rumana kum taji kewar Port, zuwa yanzu kuma babu inda Haysam baya zuwa da ƙafarsa, yayi wayo sosai har magana yakan ɗan dagula duk da bata fita da ƙyau sosai, ta kuma yayesa ba tare da kowa ya saniba hatta da shi Ahmad ɗin kuwa..
Kowa yayi farin ciki da wannan zuwa nasu, sai dai banda irinsu mama gaje da har yanzu suka kasa samun mafita balle damar cutar dasu.
Haysam ɗan dangi, kowa sai ɗaukarsa yake da jinjina saurin wayon yaron.
Dukda Rumana taɗan rame saboda rashin mijinta a kusa hakan bai hanata sake yin ƙyauba, fatarta sai ɗaukar idanu take.
Wannan zuwan bata zaunaba, ta shiga ziyarce-ziyarcen dangi dayin sallama, itace har katsina wajen Fa'iza dake fama da cikin da har ya fito, da alama dai kusan lokaci ɗaya suka samu ita da Salima ma, duk da sun huta sosai sunci amarci kafin ALLAH ya kawo cikin.
Fa'iza tayi farin ciki matuƙa da zuwansu, ranar sunsha hira sosai, suka kwana suka hantse washe gari da yamma suka taho suka barta cike da kewarsu.
Wannan karon ta samu har tsohon gidansu taje domin gaida su Maman Ama, sai dai tayi rashin sa'a ta iske maman Ama bata nan, wai tayi yaji saboda faɗa da sukai da mijin akan zai ƙara aure ya faffale fuskarta da maruka.
Kausar kawai ta iske sai waɗanda suka kama hayar ɗakin da suka zauna yanzu, sosai Kausar ta ruɗe da ganin yanda Umm-Ruman ta sake canjawa, tamkar ba ita bace ta zauna a gidan nasu, gashi ta girke ta zama mace sosai, keko shekara kusan biyu kenan basuga junaba, tun arba'in ɗin Haysam da gashi yanzu yana takawarsa.
Duk sai Kausar ta raina kanta, tanatama Rumana Gulmar maman Ama, ita dai Rumana bata tofa tataba sa ALLAH ya ƙyauta da tace, da tagama abin zai wuce makaɗi da rawa tai musu sallama ta taho, ta barsu da tafa hannaye na mamakin wai yanzu Saudia su Rumanan zasu koma?.

Aiko maman Ama na dawowa bayan kusan sati da zuwan Rumana da labarin zuwan Umm-Ruman ɗin Kausar ta tarbi maman Ama duk da a yanzu basa shiri anyi uwar watsi tuni, harda ƙara gishiri da magi😂.
Maman Ama taji takaici na rashin ganin Umm-Ruman, dan haka ta ɗau aniyar sai tazo har gida taganta tunda Kausar tace sai nan da sati biyu Rumanan zasu wuce.
Sai dai kuma an taki rashin sa'a, dan kuwa kwanaki huɗu da zuwa Umm-Ruman maganar tafiyarsu ta tashi, haka sukai sallama da ƴan uwa da abokan arziƙi, suna kuka itama tanayi sukai mata rakkiya airport ita da Haysam da Zainab suka lula abinsu.


__________________________________

*_SU UMM-RUMAN A JIRGI ZA'A BAR ƘASA🥴😹_*

Cike zuciyarta take da kewar ahalinta, gefe kuma na cike da farin cikin zuwa ga mijinta da tai kewa tsawon watanni takwas, tare da ɗunbin ɗoki zuwa ƙasar da kowa ke fatar ganinsa a ciki.
Ahmad na filin jirgin tarbarsu tun kusan awa ɗaya saura su sauka, yana cikin tsagwaron zumuɗi da baki ma bazai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login