Showing 108001 words to 111000 words out of 165545 words
da yakeji a ransa na cikin jikinta, a ganinsama tayi ƙarama da ɗaukar cikin, amma yasan UBANGIJIN daya basu shine zai bata ikon haihuwa lafiya.
Yama su baba maganar tafiya da Rumana amma sai sukace ba yanzuba, ya bari ta haihu dan bazai yuwu ace sun tafi tana cikin wannan halin hakaba, balle cikin nama fari, kowa zaiso ta haihu a gida cikin danginta kodan itama ta samu kulawa.
Baiyi musu da suba ya haƙura duk da bai soba, ya tattara ya koma bayan randa ya cika sati guda.
A wannan tafiyarma sai da tai masa kuka, haka dai ya gudu ya barta.
Tun daga sannan duk ƙarshen wata sai Ahmad yazo gida, wani lokacin yay kwana uku, ko huɗu harma sati yakanyi.
Duk zuwan da yay kuma saisun tsinci kayan haihuwa sun ajiye a gidan yaya Maryam, hakan yasa ƴan gidansu Rumana su Maman Ama ke dariyar gatsatsa, wai gadai Ahmad ya canja amma su basuga wani canjiba, koɗan kayan haihuwar da akan siya a yadda na haihuwar fari basu ganiba ga Ahmad.
Bai iya komaiba sai zaryar dawowa gida saboda fitina na cinsa.
(Kusan har yanzu basusan ya samu aiki ba ƙabayen😹).
🤦🏻♀kuji masifa, bayan da sunce masa lagwani😏😂🤣.
Duk da Umm-Ruman takan jisu wani lokaci bata ko kallonsu, ita dai fatanta a kullum ALLAH ya bata ikon zama dasu da zuciya ɗaya, ya kuma hanata yimusu ƙƴashi ko hassada a komansu.
Duk da wannan abun da suke mata haka zaki ganta da ɗiyar Kausar maƙale wani lokacin, dukda tana fama da kanta har goyata take su fita cikin gari wani lokacin, ta kama hannun Amatullah ga Surayya babyn Kausar kuma a baya.
Akwai randa taje gidansu Ayyah taita mata faɗa akan wannan gangancin goya Surayyan, takuma tabbatar mata karta sake ɗaukama kanta wannan rigimar, ta bari har ALLAH ya sauketa lafiya sai tayi koma miye.
To tunma daga ranarne taɗan ɗaga ƙafa da goya Surayyan, amma hakan baisa tayi fari a idon Kausar ba balle taji kunyar zama yi da ita.
Tun farko dama bata saka lamarinsu a rantaba balle yanzunma ya dameta, harkokin gabanta kawai take da ƴar sana'arta data samu karɓuwa sosai, sai ko rainon cikinta da a kullum take addu'ar fitowarsa duniya lafiya.
___________________________________
Daga Samina har mama gaje sun saka a ransu aikin da Ahmad ya samu ba wani na kirki baneba, harda cewa ƙilama ƙaryane anayine kawai dansu, rashin ɗaukar abun da muhimmanci ya sakasu ƙin saka abun a ransu, sai cikin Umm-Ruman ne kawai yafi zame musu damuwa.
Ranar wata juma'a Samina ta shirya zuwa gidan Umm-Rumana kamar yanda malaminsu ya bata Umarnin ta fara shige mata tundaga sannan, dan cikin Umm-Ruman ya shiga watan haihuwa.
Taci adonta cikin kaya na alfarma, dan kuwa rantsatstsar doguwar rigace da taji adon duwatsu ta saka, komai nata dai ya kasance na matan manya, dan zuwa yanzu ƙawayen data ƙara masu rawar kai irinta sun sake wayar da ita fiye ma da da, ɗaukar kanta take sama sosai, balle gashi Ma'aruff yana a tafin hannunta ne sai yanda takeso za'ayi, uwarsa kanta da ƴan uwansa duk ta bi dasu babu mai mata kallon banza yanzun, shiyyasa take musu rashin mutuncin da duk suma sukai mata a baya, matsalarta dai kawai cikin datake ta zuba ido ya shiga saboda Ma'aruff ya daina bata magani yanzu bulum kakeji babu ko alamarsa, taje asibiti likita ya tabbatar mata cewar lafiyarta ƙalau, abin na tada mata hankali, dan babu abinda tafi buƙata sama da ɗaukar cikin ma'aruff a yanzu, a ganinta haihuwar da zatai dashine zai ƙara mata lasisin mallakar dukiyarsa, dan mahaifinsu ya rasu tuni, kuma ma'aruff ɗinne kaɗai namiji a gidansu, shiyyasa ya tashi cikin gata bana wasaba, duk dukiyar ƙannensa tana wajensa shi yake juya musu, dan Company ɗin ba nasa bane shi kaɗai, shaye-shayen da yakene ya saka duk yarinyar da ya nema auren ke lalacewa, ga neman mata ko bunsuru ya shafa masa lafiya.
Sau biyu ana saka masa ranar aure amma yana lalacewa saboda rashin mutuncinsa, wasu kuma saiya gama lalata musu rayuwa saiya gudu bazasu sake ganinsa ba, idan ma sunsan inda yaken kosun kawo ƙara gidansu a banza, mahaifiyarsa ca take ƙaryane, sharri akaima yaronta baya shan giya, abinda yasa bata saniba ma'aruff baya shan giya sai dare, dayasha kuma gida yake dawowa, da safe kafin ya fita ta sakeshi, to inba tare kake dashiba har barci bazaka san yanayiba, gashi komai da taku yake kayansa, hakan yasa ko ita Saminar bata taɓa saniba.
Sannan ita kanta Samina da shirin yaudararta yaje, daya samu abinda yakeso ya gudu, sai dai kuma su Mama gaje sun masa DAURIN GORO bai saniba, dan saka malam sukai yay ram dashi a hannu akan tilas ya auri Samina.
ALLAH kuma sai ya amsa musu akayi auren dama yake da alamar tambaya saboda cikin da taje dashi a jikinta.
Cikin takunta na gayu ta fito daga ɗakinta tanata zabga ƙamshi, Ma'aruff na kwance a doguwar kujera yana kallo, ya kalleta da mamaki dan shidai baisan zata fitaba.
“Ina zuwa haka?�? ya faɗa cikin tsareta da idanu.
Saboda tasan tsiyar data shirya masa saita zauna tana murmushi, “Wlhy so nake naje na duba sister ɗina Umm-Ruman, ance batajin daɗi ne Sweet�?.
Jin ta ambaci sunan Rumana sai ya washe baki da faɗin, “Wai kina nufin mutuniyata?�?.
Dukda maganarsa ta zafeta sai ta danne itama tana murmushin tace, “Tabbas ita kuwa, ai nama manta ka santa�?.
“A to bari kawai na shirya muje tare, tana wane asibitine?�?.
“A'a ba asibiti takeba tana gida�?. Samina ta bashi amsa zuciyarta na mata zafi.
Babu yanda ta iya ta yarda suka tafi tare, ita ke tuƙa motarma saboda tunda ta sameshi a hannu ta tilastashi ya koya mata mota, duk kuma motarsa datai mata ita take hawa a gidan dukda ya bata wata ƙarama.
Cayay su biya ta shoprite wai suma Rumana tsaraba, Samina bata musaba kuwa suka biya, sayayya ta tashin hankali taga yanayi, itafa lamarin guy ɗinan mamaki yanzu yake bata, tama rasa yanda zata fassara manufarsa akan Rumana, tunda dai shi ai ba mahaukaci bane yasan tanada aure, kuma ƙanuwarta ce uba ɗaya.
Uffan batace dashiba ya gama kwasar duk abinda ya tare gabansa yaje ya biya suka tafi.
Sai da ta kira mama gaje a waya ta sake nata kwatancen gidan sannan, da suka isa ma Ma'ruff cayay dashi za'a shiga gidan, sai da Saminar tace bazai yuwuba, tunda basu Rumanar bane kaɗai a ciki akwai ƴan haya bayansu, ya zauna a mota kawai zata saka Rumana ta fito su gaisa.
Badan yasoba ya haƙura, ita kuma ta kwashi kayan daya takura mata ta shiga cikin gidan.
Umm-Rumana na zaune a ƙofar ɗakinta kan tabarmar data shinfiɗa dantasha iska, aya da Ammi ta soyo take ƙullawa, maman ama na bakin rijiya tana wanke-wanke, sai Kausar daketa kaikawo daga ɗaki zuwa kicin tana dahuwar naman kai anama su Rumana iyayi, hira sukeyi, duk da ma dai maman Ama ne da Kausar ƙarfin hirar, sai anyi abun dariya Rumana kanyi, sai kuma jefi-jefi takan saka baki itama.
Tunda Samina tai sallama duk suka zuba mata idanu, ita Rumana ma bata ganetaba da farko, dan Saminar tayi bala'in sake fari, takumayi ƴar ƙiba ba laifi, gashi ta toshe fuska da glasess baƙi.
Gidan su Umm-Ruman ko ina lailaye yake da suminti, sannan ba wani girmane dashiba da za'ace ya tara baƙar ƙazanta ko tarkace, ko ina tsaf yake abinsa, amma hakan bai hana Samina yin yatsine-yatsine ba.
Rumana ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin, “Lale marhabun da Yaya Samina, sannu da zuwa ki shigo�?.
Wannan furuci na Rumana ne ya saka su maman Ama fahimtar wacece, dan koda aka kawo Samina gidan a wancan lokacin ai maman Ama bata gantaba sosai, tunda ko kwana batai a gidanba, takuma canja sosai ma yanzun fiye da da.
Dan munafurci harda ce mata Hajiya Samina🤣.
Itako ta amsa tana sake ɗage musu kai tamkar wata matar shugaban ƙasa.
Ita dai Rumana tai mata iso zuwa ɗaki, ko zama basu gama yiba saiga Maman Ama da zoɓo da ruwan leda afilet, wai ta kawoma Samina.
Rumana dukda tasan salon annamimancine hakan bai hanata mata godiya ba.
Samina sai bin ɗakin take da kallo, a ranta tana tuna randa aka kawota cikinsa, ita koma kalar kayan gadon bata shaidaba dan bata tsaya kallon komai na cikinsaba a wancan lokacin.
Ita dai Umm-Ruman ta gaisheta da girmamawa kamar yanda ta saba.
Samina ta amsa cike da yanga tana faɗin, “Uwar biyu ashe kin kusa sauka haka?�?.
Murmushi Rumana tayi kawai bata iya cewa komaiba ita dai.
Samina ta harareta kaɗan tana taɓe baki, sai kuma tace, “Yah Ahmad ya haɗaki da aiki ya gudu ya barki, ai wasu mazan dama sam basu da tausayi, abinda kawai suka sani suma macen ciki su aje mata fara da mai suyi gaba, acan kuwa dadinsu sukeci su kiga sunyi ɓul-ɓul.
Rumana dai bata bata amsaba nanma, dan ta gama lura akwai cin mutunci a ciki.
Samina taci surutanta ta tsire sannan ta miƙe akan zata wuce, dama ta anguwar sukazo gittawa shine tacema mijinta bara ta shigo tayi zuminci tunda ita Rumana Ahmad ya hanata.
Rumana ta bata haƙuri akan itama zatazo insha ALLAHU.
“ALLAH yasa to, ga shinan ƙyaɗan sabunta kema inji hubbyna, kizo yana ƙofar gida ku gaisa�?.
Jimmm Rumana tayi tana tunani da kallon kayan, dan daga amsar kayan har fita gaisawa da mijin Saminar tasan zai iya zama matsala tsakaninta da Yah Ahmad.
Amma dan kada Samina taga kamar akwai wani abu a ranta saita zira hijjab ta fita, daga zaure ta tsaya Ma'aruff ya shigo suka gaisa, yanda cikin ya ƙarama Rumana ƙyau da murjajjen jiki sai Ma'aruff ya nema zaucewa, ɗan hegiyar sai haɗiyar yawu yake yana lashe laɓɓa, idonsa kam tamkar zai zazzago ƙasa saboda kallonta.
Itako bama tasan yanaiba dan kanta duƙe yake a ƙasa ko kallonsa ta kasayi, suna kuma gama gaisawa tai musu sallama zata shige gida, jikinsa har ɓari yake ya fiddo kuɗi ya bata amma sai taƙi amsa ta shige abinta.
Jiyay kamar ya jawota ya rungume a jikinsa, a fusace Samina ta fisgi hannunsa sukai waje.
Ƙwacewa yay tare da hankaɗata yana jan tsaki, dan yaji haushi sosai..........😝✍�?
🤸🏻♀Ɗan hegiya, wannan Gwal ɗin Amadidin Ayyah ce, ƙwalelekanka dan uwarka😏🥴😹⛹♀⛹♀
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(35)*
...............Koda Rumana ta dawo cikin gidan bata koma ɗaki ba, inda Samina tazo ta sameta a ƙofar ɗaki nan ta sake zama.
Su Kausar da suke zuba ido suga mi Samina ta kawo dole suka haƙura.
Su basu sanma Rumana ita neman mafitar da zata ɓulloma Ahmad takeba a cikin ranta, tasan ko giyar wake tasha bata isa tunkararsa da maganar zuwan Samina gidanba balle harda mijinta kuma sun kawo mata abu.
Tasan hakan gagarumar matsala zai kawo musu wadda zai iya haɗa sati yana fushi da ita, idan kuma bata faɗaba yaji a bakin wani ai sai tafi shiga tara ma ba uku ba, to ita yaya zatai kenan?.
Ta ta saƙawa da kwancewa akan neman mafita tana cigaba da ƙulla ayarta, daga ƙarshedai zuciyarta ta bata wata shawara da ita kanta taji ta aminta da shawarar.
Kamar yanda ta yanke shawaran jiran Yaya Mudan yazo ta faɗa masa komai, sai gashi bayan sallar isha'i ya kawo mata fruits da kullum ya jura kawowa, ko wani ɗan abin kwaɗayi haka, idan kaga bai kawoba to baida kuɗine kokuma Ahmad ya dawo gari.
Lokacin da yazo su fa'iza basu kai ga zuwa ba, dan yanzu sukanje majarantar dare, sai an tashesu ƙarfe tara saisu taho nan.
Bayan sun gaisa da Mudan tai masa bayani komai da zuwan Samina da nuna masa kayan da suka kawo da ko buɗewama ita bataiba taga miye a ciki.
Hakan ya bama Mudanseer mamaki sosai, dan shidai yaji a ransa akwai wata manufa a zuciyar Saminar.
Yace, “Kin sanarma Yah Ahmad ne?�?.
Rumana ta riƙe haɓa tana faɗin, “Wai, Yah Mudan wlhy tsoro nakeji, shiyyasama na yanke shawarar faɗa maka idan zaka sanar masane to, dan nasan komu bamu faɗaba wani zai faɗa masa musamman matan gidannan dana san saisun sanarma mazansu, sukuma zasu iya faɗa masa, to maimakon yaji a wani waje yaji zafi gara musan abunyi, kasan Yayah nada zuciya akan abinda duk bai masaba�?.
Mudan ya jinjina kansa yana sauke ajiyar zuciya, yace, “Hakane kema kinyi ƙyan kai, yanzu dai bara na tafi da kayan, insha ALLAHU zan masa bayani a yanda zai fahimta, ki kwantar da hankalinki kinji, dan kina yanayin da sam ba'a buƙatar damuwa tattare dake�?.
Rumana tace, “To Yah Mudan nagode sosai�?.
Da zai wuce da kayan ya tafi, Rumana nata zuba ido taji Ahmad yay mata magana akan kayan nan ko zuwa Samina amma shiru, kuma kullum ne babu fashi sai sunyi waya, daga baya saita fara tunanin kodai madan bai sanar masa baneba?.
Kasa haƙuri tayi da Mudan yazo gidan ta tambayesa.
Ya tabbatar mata yako masa maganar, dan shinema yace abama Ayyah kayan ta ajiye a wajenta, kuma harsu Baba ma sunsan komai a kan maganar.
Rumana tayi matuƙar mamaki, amma sai itama ta share abun a ranta taci gaba da harkokinta.
Zuwan su Samina da sati ɗaya Ayyah tazo gidan da kanta, bayan sun gaisa tacema Ruman ta kimtsa kayanta insha ALLAHU nanda kwana biyu zata koma can gidan da zama har saita haihu, dan cikinta ya shiga watan haihuwa, bakuma zasu barta ananba ita kaɗai.
Hakan yama Umm-Ruman daɗi sosai, koba komai ta samu hutu daga su maman Ama.
Koda taima Ahmad maganar da suna waya sai yace mata ai yasan da komawar tata shima, hankalinta ya sake kwantawa sosai, a washe garin ranar kam sai su mama Ama sukaga tanata kimtse-kimtse su Salima na tayata, iya abinda zata iya buƙata kawai ta zuba a jakkuna biyu dan tsabar wauta🤣, sai kace ance ta tafi kenan.
Washe garin da zata wucene ta sanarma matan gidan, dan sai zuwa dare zata wuce, da safen dai su Fa'iza suka wuce da kayanta, wanan abu yama su maman Ama ciwo, sai dai kuma ya suka iya.
Da daddare kuma ta wuce ta basu filin gidan su warwasa da ƙyau🤸🏻♀.
___________________________________
Tunda Umm-Ruman ta dawo gidansu take sake ganin tattali da kulawa musamman wajen Iya da Ayyah, duk wani kulawa da mai ciki kan nema Rumana na samunsa, hatta