Showing 150001 words to 153000 words out of 165545 words
tazo ko hutu, weekend ɗinma hanata wani lokacin Ahmad yakeyi.
________________________________
A kwana a tashi shekaru sukaita shuɗawa tamkar almara, kafin wani dogon zango abubuwa da yawa sun faru.
Bayan shigewar shekaru huɗu da tai dai-dai da cika shekarun su Rumana bakwai a saudiyya, Ahmad kuwa takwas.
A yanzu yaransu uku duk maza, dan cikin da Rumana ta sake haihuwa shiɗinma dai namiji ne, wanda yaci sunan Baba Ilyasu shima, suna masa alkunya da suna *_Abu-Turab_*, sosai yanzu Rumana ke sha'awar ƴar budurwa, musamman idan Subayya tazo musu weekend, wato yarinyar Gaddafi.
Abubuwa da yawa sun faru na cigabansu, karatunsu da duk suka kammala har Zainab, tare da gurbin aiki da ma'aikatar tace man fetur ta ƙasar Saudiyya taba Ahmad, sam baiso hakanba, dan ƙasarsa shima yake burin zuwa yayma hidima, amma sun ko dage suma sai yayi musu aiki na adadin wasu shekaru kafin su sallamesa.
Da farko yayi takaici, amma da Gaddafi yay masa nasiha akan ya ɗauki hakan shine mafi alkairi a rayuwarsa sai hankalinsa ya kwanta..
Da kuma ya sanarma Baba duk suka sanya albarka a cikin lamarin.
Rumana ma sun kammala karatunsu, amma tanason cigaba saboda daɗin da yay mata, hakama Zainab ta kammala, tanason cigaban dai itama, amma Ahmad yace saita samu miji ya aurar da ita inma zai aminta da cigaba da karatun nata.
To da yake akwai wani abokin karatunta da suke lobewarsu, ɗan asalin ƙasar Eygpt, amma haifaffen nan Saudiyya ne, mahaifiyarsa kuwa ƴar asalin ƙasan Nageriya ce, sunansa *Akeem*, sai kawai ta gabatar dashi garesu.
Ahmad da Rumana sun masa tarba ta mutunci, sun kuma yaba da yaron. sai dai Ahmad yace sai yayi bincike a kansa, idan yaga babu wata damuwa zai kai maganar gida kafin a yanke hukunci.
Daga nan suka fara shirin zuwa Nageriya ganin gida a karo na farko, wanda yay dai-dai da taron bikin Mudanseer da za'ayi.
A yanzu kam kowa yaga Umm-Ruman yasan na gaba yay gaba na baya sai labari, ta ko ina ta zama cikakkiyar mace kamila wadda a kowane irin taro zata iya bugar ƙirji ta kira kanta macen, balle a tsakaninnan da take ɗauke da wani yaron cikin maƙale a mararta, duk da dai ita kaɗai ta fahimci tana da kayanta, dan ko Ahmad taƙi sanarmawa.
Haysam ɗan saurayin yaro abin sha'awa da so ga kowa, a yanzu yanada shekaru takwas da wasu watanni a duniya, yaro mai matuƙar hazaƙa da haƙuri, sam bashi da kwaramniya, ɗabi'un ƴaƴan farin dai na tare dashi.
Sai Abu-Talib manyan ƙasa, kamaninsa da Haysam sun sake fitowa matuƙa, a yanzu yana da shekara biyar da wasu watanni shima a duniya, akwaishi da wayo ga ƙiriniyar masifa, jan faɗa da rashin barin saita kwana kam ai ba'a magana, akwai zuciya irin ta mahaifinsa tattare dashi sosai, dan a hallaya kam ba'a cewa komai wajen gadon Abbunsu, shima ALLAH ya bashi hazaƙar karatu, ga ƙulafucin iyaye, ko yaya Abbunsu bai dawo gida da wuriba yata tambaya kenan, “Ummie ina Abbunmu? Yaushe zai dawo? Ko miyasa bai dawo ba? Kira manashi a waya muji ya taho?�? wani lokacin tun tana jurar bashi amsa har taji haushi tai masa banza, idan kuwa Zainab ta kira waya lokacin tana makaranta aka bashi su gaisa yata mata rigima kenan akan ta dawo gida, sai dai taita lallashinsa har a rabu lafiya.
Sai Abu-Turab, ɗan gatan Aunty zee kenan, autan Ummie kuma, duk da dai Ahmad yace shi autansa kam akwai yayu kamar shida a gabansa ma kafin yazo, dan haka da sauran aiki Rumana ta sake zage damtse😅, a yanzu shima yana da shekara Uku da wasu wattani a duniya, shima dai akwai wayon, sannan babu ragi, dan faɗa shi da Abu-Talib kullum ne babu fashi, kowa yana fama da zuciya, shima dai akwa wayo, ga surutu a bakinsa ko tsuntsun akku ya shafa masa lafiya, shifa komansa a rayuwa Aunty Zee, ko abu ya samo aunty Zee ce mai ɓoye masa, idan abun daɗi yaci ya rage zaije ya ɓoyema aunty zee ɗinsa, shima dai suna shirin sakashi makaranta kwannan nan, dan Islamiyya kawai yake zuwa, so Ahmad yake sai sun dawo ganin gida sannan a sakashi.
Sai uwar ƴaƴa Zainab, ta zama budurwa cikakkiya, asalin ƙyawun runawan nan na ɗawainiya da ita, hakan yasa take ɗaukar hankalin ƴaƴan larabawan nan, dan irin fatar su Ahmad tana da birgewa ga ko farar fatane, Zainab akwai tsiwa, amma hakan bai hanata tashi da nutsuwa ba, dan Ahmad da Rumana basuyi wasa da tarbiyyar Zainab ba, da iyayensu suka danƙa musu amana, a yanzu haka tanada shekaru ashirin cif a duniya, ga yanayin garin ya karɓeta, tako ina ta zama cikakkiyar mace abin buƙatar kowanne ɗa namiji.
Sai fa mai gayya mai aiki, Alhajin ALLAH, kamilin namiji kainuwa dashen ALLAH, wato dai angon Umm-Ruman nake magana Amadidin Ayyah Abbun Haysam da su Abu-Talib, yayan Zainaba kuma ba😉, lallai Ahmad kam yanzu ya kama ƙasa, bawai a dukiya nake maganaba, a cigaban rayuwa mai albarka da buƙatar dukkan namijin ƙwarai, dan dukiya dai ba itace mutunci ba, har yanzu Ahmad ba hamshaƙin mai arziƙi bane, yana rayuwarsane a tsaka tsaƙi, cikin rufin asirin ALLAH, zai iya ɗaukar dukkan ɗawainiyar iyalinsa harma data danginsa gwargwadon iko, sai dai bai tara ƙazaman kuɗaɗen dake jibge a bankunaba, sannan bai tara motocin da suka cika harabar gida ba, har zuwa yanzu bai da gidan kansama, dukda dai ya shirya wani gagarumin surprise ga Umm-Ruman wanda bai taɓa sanar Mataba koda a labari.
A yanzu haka an bashi gida da motar hawa a wajen aikisa, sannan za'a ɗauki nauyin karatun yaransa biyu, wato dai Haysam da Abu-Talib, ranar da wannan abin alkari ya riskesu har hawaye Ahmad yayi, yama rasa yanda zai kamanta farin cikinsa, UBANGIJI ya masa komai a wannan rayuwar, dan ko ilimin da ya azurtashi dashi kaɗai ya isar masa abin alfahari duniya da lahira.
Ga matar ƙwarai da ALLAH ya bashi, wadda tasan darajarsa da mutuncinsa, ga ƴan yaransu abin sha'awa da birgewa ga kowa, ya sauke nauyin buƙatun ahalinsa masu yawan gaske musamman akan karatun ƙannensa masu tasowa, ga harkar kasuwancinsu kullum sake haɓaka take shi da Gaddafi, hakama na wajen Nura komai yana tafiya Alhmdllh.
Cikin farin ciki suka tattara suka koma sabon gidansu da suka samu rakkiyar abokan arziƙi da suka tara anan ƙasar Saudiyya, ga kuma waɗanda suke kallo ƴan uwansu da basu da kamarsu, Gaddafi da matarsa Jiddah.
Gidane da ya amsa sunansa gida, ga motar hawa da dukkanin abin buƙata a ciki, su Abu-Talib sai tsalle suke an dawo sabon gida, ballema ga wani ɗan lambun hutawa a gefe da aka shirya wajen wasan yara a ciki, hakan ba ƙaramin ɗaukar hankalinsu yayiba ainun.
Anan dai cikin birnin Dhahran ɗinne suka sake samun wannan sauyin rayuwa, sun tare da sati guda suka shirya zuwa makkah domin yin Umrah ta kwanaki goma.
Duk da kuwa basusan adadin Umrah da sukaiba a rayuwarsu cikin shekarun da suka tsinci kansu a saudiyya, aikin hajji kuwa tunda sukazo saudiyya basu taɓa fashin yinsaba duk shekara, tanan nema suke haɗuwa da ƴan ƙasarsu harma da waɗanda suka sani jefi-jefi, dan akwai wani Alhaji ɗan anguwarsu da Ahmad ɗin ya taɓa gamo dashi, lokacin Ahmad na cikin tsananin rayuwa da neman kuɗin karatunsa har neman taimako ya taɓa zuwa wajen Alhaji, amma a wancan lokacin sai ALLAH bai cida Alhajin nan ya taimaki Ahmad ba, Ahmad ya baro gidan da ɓacin rai saboda korar kare da matar Alhajin tai masa, sai gashi yau kwatsam sun haɗu a saudiyya, shi Alhajin ma bai gane Ahmad ba, amma shi Ahmad ya ganesa, dan haka ya gaishesa kuma ya bashi sani, duk da bai tuna masa da wancan batunba yadai kwatanta masa gidansu. Cikin ikon ALLAH kuwa Alhaji ya gano mahaifin Ahmad ɗin harma da abinda ya taɓa masa a wancan shekarun.
Bayan an kammala aikin hajji kafin lokacin komawarsu Ahmad ya ɗaukesa ya kaisa har gidansa, suka karramashi da tarba ta mutuntawa, hakan ya sosa zuciyar Alhaji har ya gaza haƙuri yayta neman gafarar Ahmad, murmushi kawai Ahmad ɗin yayi yace dan ALLAH subar zancen ya wuce, kowa kuma ai yasan ajizanci na ɗan adam.
Sosai Alhaji yaji daɗin wannan karamci na Ahmad, da ya koma gida Nageriya kuwa har gida yaje yayma su baba alkairi ya kuma basu labarin karramawar da Ahmad yay masa a saudiyya, yayta bama mutane labari kuwa, tun daga wannan lokacin zuminci ya ƙullu tsakaninsa da su baba mai ƙarfi, har takai ya ɗauki su baba su duka ya ɗorasu akan wasu harkokins, dukda basuyi karatun bokoba bazasu cutuba wajen tafi dasu.
“Wannan ma nasarace da Ahmad bazai taɓa mantawa da itaba a rayuwa�?.💪🏻😌
Bayan kammala Umrah suka koma Dhahran, kwanakinsu takwas da dawowa suka kammala shirinsu na tafiya ƙasarsu ta haihuwa tsaf, Zainab da Umm-Rumana sai murna suke, suko su Haysam dai suna murnar za'aje anguwane kawai, amma basusan ainahin inda za'aje ɗinba, dan Haysam ya manta da Nageriya kasancewar sanda suka barota bashi da wani cikakken wayo............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
..............Ɓangaren Ma'aruff abubuwa sam babu daɗi tsakaninsa da Mufida, dan tun bayan barin Samina gidan suka dawo gida zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu saboda videos ɗin da aka fidda na abinda ya faru tsakaninsa da Samina.
Asiri yana ɗawainiya da Ma'aruff sosai, hakan yasa yake masifar tsoron Mufida, a lokacin taso ƙwarai da gaske su rabu, sai dai iyayenta suka tsawatar mata saboda akwai wata manufa a ran mahaifinta, duk da mahaifinta ƙanin maman Ma'aruff ne bashi da wani buri da ya wuce ya mallake company ɗin su Ma'aruff ɗin, bayan rasuwar mahaifin su Ma'aruff yaso ya tattare dukiyar yaran ya riƙe a hannunsa akan shi ne zai kula musu tunda dai mahaifiyarsu macece.
Amma sai sam taƙi aminta da hakan, dan gudun kar a salwantar da dukiyar marayu, a lokacin shi ma'aruff yana Germany yana karatu, ya kammala degree ɗinsa na biyu zai tafi na uku ne ta matsa masa akan ya dawo gida dole, yabar karatun wanda yayi ya wadatar.
Badan Ma'aruff yasoba ya dawo Najeriya, daga nan ta danƙa masa dukiyar a hannunsa, shi kuma sai ya gyara company mahaifin nasu na yin takalma kawai aka cigaba da harka.
Wannan al'amari yayima mahaifin mufida ciwo a rai, amma sai ya danne, kullum dai yana neman hanyar da zai mallaki dukiyar har zuwa yanzun, bayan auren Samina da Ma'aruff ya fahimci ƴar uwarsa bata ƙaunar matar ɗansa, dan haka yayta sake tunzurata a ƙiyayyar Samina, yana cusa mata son haɗa zuminci tsakanin ɗiyarsa da Ma'aruff.
Tun abin bai tasiri ga maman su Ma'aruff ba har taji ta aminta saboda basu barsu hakaba, dan bin bokaye wajen maman mufida lamarin sai dai gyaran UBANGIJI, hatta da videos ɗinnan ƙanin Mufida ya sakesune da gayya saboda Samina ta barma ƴar uwarsa gidan, tunda shima yasan dukiyar Ma'aruff mahaifinsu ke ƙulafuci, idan kuma an samu shine zai mora tunda shine namiji babba a gidansu.
Rikicin dake yawan faruwa tsakanin Ma'aruff da Mufida ne ya nema fara susutar dashi, dan sai shan giyarsa ta ƙaru fiye da da, da yake ALLAH ba azzalumin sarki bane sai kuma ya koma begen Samina, da yasha yay ɗaɗil sai yayita ambatar sunanta a cikin shirmen surutansa na maye.
Maman Ma'aruff sam batasan mike faruwa ba, tana can ta saki baki akan tunda Ma'aruff ya rabu da Samina maƙiyiyarsu shikenan ya samu salama a rayuwarsa kenan, yanzu zasuyi zama na arziƙi da ƴar uwarsa.
Sai dai hankalinta ya fara tashine ganin kusan sati uku Ma'aruff bai zo inda takeba, al'halin baya iya kwana uku baizo gidanba.
A lokacin ta danne abin a ranta da tunanin ko ruɗanin tsiyar da Samina ta tafka musune bai sakesuba, tare da videos ɗin dake yawo yakema kunyar zuwa gidan.
Kwanaki sun sake shuɗawa, har kusan sati na shidda babu Ma'aruff babu dalilinsa, ranar wata asabar sai gashi yaje gidan, hankalinta yay masifar tashi da yanda ta gansa, dan ya rame sosai yayi baƙi.
Zaunar dashi tai tana jera masa tambaya akan mike damunsa?, amma sam ya kasa faɗi mata komai, ganin bazai sanar mataba sai ta haƙura, dan a tunaninta dai wancan abunne ke damunsa har yanzun.
A ranar ya wunine anan gidan, ba komai ya kawosaba kuma sai umarnin Mufida akan yazo ya ɗauka mata takardun company ɗinsu, to amma da yazo ya rasa hanyar da zaibi ya ɗauka, dan suna ɗakin mamansune, shikuma ba shiga ɗakin yakeba sai da dalili.
Har dare bai samu yanda yake soba, maman kuma ta sakashi ya tafi gida dole harda bada abu a kaima Afrah, tunda ita batasan dawan garinba.
Tunda ya shigo gidan Mufida taga babu takardun ta hausa da masifa kamar uwarsa, yay shiru kawai yana kallonta, daga ƙarshe ya koma bata haƙuri, amma taƙi koda saurarensa, ganin abin zaiyi yawa sai yay ɗan irin buɗe mata wuta ɗinnan wai ko zataji shakkarsa ta saurara masa, dan duk tsiya da zagin da take masa maigadi na jiyosu.
Aiko sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kunci yana kallonta da ɗunbin mamaki, “Mufida ni kika mara?�?.
“An mareka, ko zaka ramane?! Wawa da kai lusari, kana abu tamkar ba namijiba, ɗakko takardu su gagareka a cikin gidanku......�?
Raɓata yay ya wuce bai iya sake magana ba, ransa a ɓace ya shige sashen da Samina ta zauna, dukda har ya fara ƙura haka ya faɗa cikin kujera ransa na masa zafi, bai san miyasaba idan yana gaban Mufida bai iya komai a rayuwarsa, sai yabar inda takene zai dingajin ciwon abinda take masa, ya kai dubansa ga kwalaben giyar da ya baza a falon na Samina kaca-kaca, cikin rawar jiki ya miƙe, inda ya ajiye kwalayen giyar kusan biyar ya nufa, ya ɗakko biyu ya dawo ya zauna, ransa na masa zafi ya ɓalle ya hau kwankwaɗa.
Sai da ya jisa mankas sannan ya zube a wajen yana surutai da zagin Mufida tare da begen Samina.
★★★★★★�?
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa nata sake tsauri tsakanin Ma'aruff da Mufida, kullum tana aikashi ya ɗakko mata takardun Company ALLAH bai bashi ikon ɗakkowaba.
Yanda take matsa masa akan waɗannan takardu haka mahaifinta ke matsa mata itama.
Abu kamar wasa watanni suka shuɗe shekara ɗaya ta kusan haɗuwa, zuwa lokacin hankalin momin su Ma'aruff yakai ƙololuwar tashi da canjawar Ma'aruff ɗin, dan takai hatta da aiki yanzu Ma'aruff sai ya gadama yake zuwa, al'amuran Company sun fara taɓarɓarewa.
Ranar dai tai shiri da kanta tazo gidan, a lokacin Ma'aruff na sashen Samina yayi mankas da giya, da wannan damar Mufida tai amfani ta ƙalama Ma'aruff sherin wajen mahaifiyarsa, ta nuna dai duk wannan abu da yakeyi akan Samina na ne, nan take Mamansa tace ai asiri iyayen Samina sukaima Ma'aruff.
Aiko ta kira mahaifin Mufida ta sanar masa, koda yazo gidan shima sai ya nuna shiga tashin hankali kamar gaske, ya kuma zugata akan suje su saka ƴan sanda su kama iyayen Samina.
Babu musu ta yarda da wannan shawara, sukaje kuwa police station suka kai report, ƴan sanda sunji kuɗaɗe babu wani bincike suka nufi gidansu Ahmad, sai dai koda sukaje an sami akasi, dan a ranar su baba duk basa nan, suda matan gidan duk suna Shema wajen biki, su Mudan ne kawai a gida.
Koda ƴan sanda suka sanarma Mudan dake shago yana ɗinki abinda ya kawosu tsabar iya shegensa sai ya turasu gidan inna mari akan cewar ai iyayen Saminar yanzu sunbar gidan sun koma can.
Ƴan sanda babu man kai suka yarda😂, suka kuwa kwashi ƙafafunsu sai gidan Inna mari bisa kwatancen da Mudan yay musu.