Showing 42001 words to 45000 words out of 165545 words

Chapter 15 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

385

dai komawa nai ciki na zauna inda na taso, kallo ɗaya kuma naima fuskar Yah Ahmad na fahimci yaji haushin abinda matar tayi.
Ni dai bance komaiba, kamar yanda shima bai tankaba ya cigaba da cin tuwonsa.
Bayan ya kammala yace na bashi ruwan wanke hannu.
Muƙewa nai na ɗebo a madaidaiciyar roba na kawo masa ya wanke, na fita naje na zubda, matar data roƙi ruwa ta bani kofina tana sake godiya.

Yanda naga ya ƙwanta da wurine na fahimci akwai damuwa, dan kuwa dai nasan ba barci yakeba tunanine kawai, kuma bazai wuce akan yaya Samina ba.
Haka kawai yau sai naji raina ya sosu, amma saina danne na maida kun nena ga ƴan kawo amarya daketa ƙoƙarin tafiya.
Zuwa wani lokaci gidan yay tsit, fita nai nayo alwalar barci na dawo ɗakin, na tura ƙofar na rufe da addu'a a bakina, na raɓa ta gefensa na haye gado nai kwanciyata.
Banma san lokacin da shima ya tashi ya kimtsa ya kwanta ba, ni dai tuni na jima a duniyar barci.


Kamar yanda na saba da safe nai ƙokarin fara sharar tsakar gidan, lokacin Yah Ahmad ya koma barcin safe dana kula ya iya, kuma tunma yana gida dama yakan taɓa wani lokacin.
Dariyar da naji a bayana ya sakani ɗan waigawa, wadda nake ƙyautata zaton amaryace naga sun fito daga ɗakinta da angonta, kallo ɗaya zaka fahimci suna a cikin nishaɗi, tana ɗaure da zanine sai tawul data yafa, shikuma jallabiya yana riƙe da botikin ruwa.
Janye idona nayi daga garesu, sai da sukazo gittani ne na gaishesu.
Duk sun amsa min sannan suka wuce Bayi a tare, babuko kunyata suka shiga bayi suka rufo suna cigaba da dariyarsu ta nishaɗi.
Ni dai sharata kawai na cigaba dayi ba tare dana sake bi takansu ba har suka fito suka wuceni zuwa ɗakinsu tana masa shagwaɓa wai ya ɗauketa ya kai har ɗakinsu.
Tofa, yau naga abinda ya girmeni.
Na faɗa a zuciyata ina kwashe sharan dana tattara.
Daga haka na ɗiba ruwa na wanke bayi shima kamar yanda na saba, sannan na fara jan ruwa a rijiya na zuba a banbuna na ɗaki dana waje duk da dama ina da ruwan.
A lokacinne maman Ama ta fito, muka gaisa na tambayi lafiyar yara ina ƙoƙarin shigewa ɗakina, dan na lura bakinta da magana sosai, niko banason wannan halayyar sam.
Ƙofar ɗaki na kawo risho ɗina kamar yanda na saba na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na juye a filas na saka ɗumamen tuwo shima, kwanikan dattin na zubasu a roba babba a nufina bayan mun karya saina haɗa duka nayi.
Ina gama ɗumama tuwo na juye a kula na kashe risho ɗin na zuba ruwan wanka abina.
Lokacin nake jiyo gulmar da Maman Ama keyi da mijinta daga kicin ɗinmu da ita kawai ke amfani dashi, danni tunda nazo gidanma ban taɓa koda leƙashi ba balle akai ga amfani dashi.
Kaina naɗan girgiza ina mamakin wai maza ma sun iya kananun magana, ni dai na wuce bayi nayo wanka nazo na shige ɗakina kawai.
Yanda kukasan mara gaskiya haka naita ƙumu-ƙumun saka kaya a cikin hijjabi, duk da nasan dai Yah Ahmad barcinsa ma yake, na gama ina tsaka da shafa mai ya farka, zaune ya tashi fusaka duk babu walwala, na ɗan saci kallonsa na kauda idanuna ina shafa kwalli a idona.
Tashi yay ya fita bayan ya ɗauki brush ɗinsa da ya sakama makilin akan madubi, hakan yasa na miƙe da azama nahau gyaran gadon, dan nasan maybe ya jima bai dawo ɗakinba, ilai kuwa harnai shara ma da sauri-sauri bai shigo ɗinba, sai da ina kwashe ƴar ƙurar dana tattarane ya dawo, matsa masa nai ya shigo ni kuma na fita zubar da sharan.
Koda na dawo bakina da nashi bai saɓa ba, nagama jera abincin a gabansa, duk da dai kulan tuwon dana ɗumama ne kawai sai filas ɗin shayi da kofi, sai ko guntun biredin jiya dake a leda da saurin sukarin da ya siyo gwangwani ɗaya, sai madara sacet uku nescafe guda uku shima duk a ledar.
Gani nai ya miƙe bayan ya ɗora idonsa akan ledar biredin dana ajiye, ya ɗauki wandonsa daya cire jiya ya ciri kuɗi ya fita.
Da kallo kawai na iya binsa, danni wannan halayyar tasa tana damuna bata damuna, abinda yasa nace haka dama can na saba babu wata shaƙuwa ta zaman hira ko abinda ya danganci hakan a tsakaninmu, nasan ko ba ƙaramin abu bane ace yanzu da wuri mun saki jiki wa juna da yanda naga ma'aurata nayi, abinda yasa take damuna kuwa shine kaɗaici, a gidan dai shi kaɗai nasani, ko yaya ina buƙatar sassauci daga garesa kodan nima naji sanyi a raina, na tabbata da aunty Samina ya aura da ba'aga haka daga garesa ba, dan bazasuyi kalar wannan zamanba saidai na farinciki fiyema da yanda naga amarya da angoncan yau.........
“K wai tunanin mi kikeyi haka?�?.
Maganarsa aɗan zafafe ta katseni daga dogon tunani na, bansan ya dawoba sam wlhy, ina fiki-fiki da idanu nace, “Ba komai�?.
Banza yaymin bai tankaba, hakan yasa nima na shiru na fara ƙoƙarin haɗa masa shayin da akema shan dai-dai ruwa kawai.
Nasan tunda akwai tuwo bazai ci biredi ba, dan haka na saka masa tuwon na tura gabansa, niko na haɗa tea ɗin nasha da biredin daya rage, na ɗan ɓalla a wanda yaje ya siyo saboda wancan guntune.

Abinda ya bani mamaki koda muka gama karyawa yau bai fitaba, zamansa yay a gidan, sai ma waya da ya ɗauka ya kira Yaya Mudan ya kawo masa wasu kaya zai yanka a gidan.
Ni dai ƙala banceba, sai dai zuciyata nata zungurata akan nai masa maganar wanka.
Na daɗe ina mulmula maganar kafin da ƙyar na iya fiddata, “Yaya ko zakai wanka tunda akwai sauran ruwan zafi a filas?�?.
Shiru banji ya amsaba, hakane ya sakani satar kallonsa, sai naga ashe ni yake kallo shima, jinai duk na daburce, dan kallon dai irin na kinma samin idon nan ne, to amma ya zanyi tunda nai suɓutar baki.
Banyi zatoba naji yace, “Haɗa ruwan�?.
Ai zumbur na miƙe kamar dama a ɗofane nake, ina kallonsa ya kauda kai yana murmushi, da alama dai yanda nake a tsoracene ya bashi dariya shima.
Duk da ya kauda idonsa kar naga murmushin naji sanyi a raina sosai, dan na jima banga hakan daga garesa ba.
Ina dawowa daga kai masa ruwan na haɗa wanke-wanke na fice abina gaban rijiya.
Ina ƙoƙarin farawa yazo ya gittani ya shiga bayi.

Kamar jirana maman Ama take sai gata itama ta fito dana wanke-wanken daga ɗaki tazo ta tsira kujera gefena ta fara.
Da farko tsokanar Amatullah na fara muna dariya, sai ta rage murya ƙasa-ƙasa tana faɗin, “Amarya anya kuwa wannan amaryar jiyan zamu dai-daita da ita? Babu wanda zaice gidanan ga yanda daren farkonki ya kasance saboda kunsan kanku daga ke har mai gidanki, amma ita jiya ihu taitaima mutane na rashin mutunci, ita ba budyrwa ba balle ace�?.
Sosai gabana ya faɗi jin ta ambaci daren farkona, gefe kuma ina mamakin wannan saka ido irin na maman Ama, wato ita idonta na kammu ashe akan taji yaya mukai daren farko? Tab anya kuwa zaman gidannan bazai canja saloba?.
Ban samu bata amsa ba naji motsi a bayanmu, da sauri na waiga sai naga Yah Ahmad ne, da alama dai yama ji duk mi maman Ama ta faɗa, dan wata uwar harara ya zabgamin yana ƙaramin tsaki ya shige ɗaki.
Innalillahi kawai na iya ambato a raina, na kai kallona ga maman Ama dake cigaba da zabga surutu ita koma lura da yah Ahmad ɗin bataiba......
“Amarya wai yanaga kinyi shiru....?�?
Murmushin yaƙe nayi ina girgiza mata kai, “Babu komai maman Ama, kawai dai banda abin faɗane, ni kitsoma nakeson naje, nasan kuma Yaya bazai barni naje gidaba, ko akwai maiyi anan kusa?�?.
Nai maganar domin kauda surutanta marasa ma'ana.
Tace, “Eh to sai dai nan gidan matar Ali, ta iya kitso kam sosai wlhy, dolene kikayi oga sai yayi biyan da bai shiryaba�?.
Nanma Murmushi kawai nayi, hakan kuma yay dai-dai da sallamar Yah Mudanseer daga soro. Na gane muryarsa shiyyasa na amsa masa ina faɗin “Ya Mudan ka shigo mana�?.
Ya shigo da sallama, ya gaida maman Ama ba tare da ya kalli inda muke ba ya shige ɗakinmu.
Nima tashi nai na zubar da ruwa dan na gama sai tukunya, itama a tsaitsaye nai wankinta na kwashi kayan nabar maman Ama a wajen.
A ɗaki na iske Yah Mudan suna hira da Yah Ahmad, sai tsokanarsa yake yana murmushi, nima ina shiga ya dawo da tsokanarsa kaina, dariya kawai nayi na ajiye kwandon wanke-wanken dana ɗora a tire ina gaidashi, a kuskure muka haɗa ido da Yah Ahmad dake duba littafi turamen zani kusan shida ajiye a gabansa.
Babu shiri na ɗauke kaina, shima sai ya ajiye buk ɗin yana kallon Mudanseer.
“Mudan zokaje can wajen kaɗanyo mana cefane kafin ka wuce, dan yankannan zai iya ɗaukata dogon lokaci ban iya tashi nayo ba�?.
“To yayana ɗan gidan Ayyah, angon ƙanwata Umm-Ru ma na�?.
Ya ƙarasa sunana da ɗai-ɗai saboda hararar da Yah Ahmad ya banka masa.
Fita yay yana dariya, Yah Ahmad yace, “Shashasha kazo ka amshi kuɗin�?.
Daga bakin ƙofa yace karka damu akwai kuɗi jikina, ƙanwata mi za'a sayo?�?.
Kallon Yah Ahmad nayi dan nima dai bansan mi za'a sayo ɗinba tunda ba taɓa tambayata yay ba idan zaiyo cefane shi, niko kullum abincina baya wuce taliya da mai da yaji saboda shegen kwaɗaina, sai shinkafa da wake, ko dafa duka.
Shima da ya kalleni sai ya janye idonsa ya maida ga Yah Mudan ɗin, shine ya lissafa masa abinda zai sayo, ya miƙa masa ɗari biyar yana cewa, “Ka ƙara da wannan tunda cefanen da yawa�?.
“A'a kabarsa yaya, akwai kuɗin ɗinki da yaron malam ya bani yanzun nan zanzo nan, bara naje na dawo�?.
Yah Ahmad ya maida kuɗinsa a aljihu, Yayinda Yah mudan ke ficewa shi kuma.
Ni dai duk ina zaune gefe ne ina saurarensu, tsarinsu na ƙara birgeni, dama can kowa yasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu.

“Zo nan�? na tsinkayo muryar Yah Ahmad.
Kallonsa nayi, dan banyi zaton dani yake ba ganin dai muna zaune ba wani nesa sosai da juna ba, yanda ya tsatstsareni da idanu yasa na miƙe zuwa gabansa na tsugunna.
Yace, “zauna da ƙyau�?.
Zaman kuwa nayi cikina na sake ɗurar ruwan tsoro.
Kallona yay sosai ko ƙyaftawa bayayi, ga fuskarsa babu alamun wasa yace, “Ina wasa da ke?�?.
Da sauri na girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla, dan bansan mi nayi ba, sai matse hannuwana nake cikin na juna.
Ya cigaba da faɗin, “Kinsan daga yau ɗinnan da nake miki magana, idan har na sake ganinki zaune da matarcan kuna wata doguwar hira bayan gaisuwa sai na miki shegen duka a gidannan, wato ma har labarin daren farko kika bata....?�?
Da sauri na girgiza masa kaina ina faɗin, “Wlhy A'a Yaya, ALLAH ban taɓa ba tunda nake�?.
“Ba gashi tana miki hirarba, ke har kinkai girman sanin akwai wani abu shi daren farko ga amarya daman?�?.
Hawayen da suka zubomin a saman fuska na share ina cigaba da girgiza kai dan na kasama magana.
Ahmad dake haɗiye dariyar yanda Umm-Rumana ta rikice da ƙyar ya kuma zazzaro mata idanunsa, danshi duk yana yine danya ƙwaɓeta da wuri karta saka kanta a wannan masifar ta shegen gulma, shiyyasa tunda suka tare a gidan ɗabi'un maman Ama basu masaba har mijinta, sam bayason mu'amularta da Umm-Rumana ɗin.
“Kinga daga yau, bama itaba, ko wannan da aka kawo jiya karnaga wata aminta ta haɗaki da kowace shegiyar mata ama anguwarnan ba gidannan kawai ba, inko hakan ta kasance kema kinsan sauran, tashi ki ban waje�?.
“Kayi haƙuri dan ALLAH Yah Ahmad, zan kiyaye insha ALLAHU, amma dan ALLAH ka yafemin�?.
Duk da ta bashi tausayi sai cayay kawai, “Ya rage naki�?.
Tashi Umm-Rumana tai ta koma gefe tana cigaba da sharar hawayenta.
Ahmad dake buɗe zani ɗaya zai fara yanka yace, “Wlhy kika bari Mudan yazo yaga waɗannan hawayen ko, saina sassafaki a ɗakinnan�?.
Babu shiri Rumana ta goge hawaye tsaf, sai ko ga Mudanseer ya dawo ɗauke da leda yellow mai layi-layi.
Yana ajiyewa ko zama baiyiba yace zai koma yana da aiki a shago, gashi zaije makaranta da yamma.
Godiya nai masa yay mana sallama ya fice.

Haka na tashi na fidda cefanen, Yah Ahmad nata yankan ɗinkinsa da duk ya maida hankalinsa wajen. Sai da zan fita waje girkine yace nayi anan ƙofar ɗaki basai na fitaba.
Duk da nasan zafin wuta zai ƙarama ɗakin zafi haka nabi umarninsa tunda risho ɗin ba hayaƙi yakeba, kayan miya kawai na fita na wanko tare da ɗanyen kifi da Yah Mudan ya sayo mana a waje nazo ɗaki na niƙa a gireta, kifin kuma nai ƙoƙarin sashi a wuta danna ɗan tafasa da kayan ƙamshi na rage masa ƙarni.
Maman Ama kawai kake iya jiyowa a tsakar gida da yaranta, amaryarmu kuwa suna ɗaki sai dai kajiyo sautin dariyarsu.
Da yake girkin bawani mai yawa bane dan danan nagama girka mana shinkafa jalof, wadda a ido kawai dolene ta birgeka saboda aikin nutsuwa ne, na kwashe a kula gaba ɗayanta na gyara wajen kamar banyi komaiba.
Har lokacin kuma Yah Ahmad nata yankan kayan, sai lokaci-lokacine yake amsa waya idan an kirashi, nama lura mafi yawa abokansane ke tambayar lafiya? Sunga bai fitaba, saiko Customers masu amsar ɗinki ko masu kawowa............✍�?







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(16)*



.............Kiran sallar zuhur da akeyine ya saka koda na gama gyara wajen sai ban zauna ba, na ɗauki buta na fita.
Ina fitowa Amaryar jiya da mijinta suka fito daga bayi da alama wanka sukayo tamkar ɗazun da safe, harga ALLAH ban kawo komai a raina ba, saima sannun da sukaimin na amsa na shige banɗakin.
Na fitone idona ya sauka akan mama Ama dake leƙe ta Windown ɗakinta, sai dai ganin kamar na ganta ya sakata saurin sakin labulen, kaina kawai na girgiza, na zauna bakin rijiya ina alwala.
Sai ko gata itama zumut ta fito da buta a hannu, tazo gab dani take faɗin, “Amarya an tashi kenan?�?
Kallonta nayi da ƴar fara'a nace, “Ai dama ba barci nakeba, aiki nake yima a ciki�?.
Tai wata ƴar dariya idonta ƙyam akan jelar gashina, “Ai najiyo ƙamshi har nake zance da zuciyata akan yau kuma amarya a ɗaki ake girki? Ko kayan daɗi za'aci tunda naji ƙamshin kifi na tashi�?.
Nace, “A'a, kawai dai dan Yah Ahmad na gidane na zauna saboda na tayashi hira�?.
Buɗar bakinta sai cewa tai “Ku hirar kuke, wasuko da ranar ALLAH suna gado suna murzar juna, wannan matar inaga da bamu da maza a gidannan lallai da munsha kallo, aini yau naga bariki wai wanka da miji da tsakar rana�?.
Shiru nayi danni sam maganar tata tazomin a baibai, na farko dai ban gama fahimtar gundarin maganar ba, na biyu kuma bansan minene matsalarta da wannan amarya ba, miye laifi idan tayi wanka da mijinta?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login