Showing 48001 words to 51000 words out of 165545 words
da yi mata, hakan ya ƙara saka izza da dagawa a zuciyar mama gaje da Saminar kanta, kullum cikin yima Ammin su Rumana da su Ayyah habaici ake, haka zasuyita ciye-ciyen kayan daɗi gaban su Ammin Rumana, amma ko guntu ba'ai musu tayi.
Duk abinda ke faruwa baba Yusha'u ya sani, ya taɓa ma Samina faɗa sau ɗaya akan shiga motar Ma'aruff, amma sai malam Rabi'u mahaifinsu yace karya ƙara ya sakama Samina da uwarta ido kawai. Saboda a randa yay maganar tujara sosai Mama gaje ta zubar a gidan, har su malam ɗin sai da ta zaga babu kunya babu jin tsoron ALLAH.
Komai kuwa a kunnen Ahmad dake gidan yazo gaida su Ayyah ya faru, ƙala bai ceba akan zancen, daga ƙarshema ya baro gidan kawai.
Zuwa yanzu takai karatun Samina ya fara walagigi, dan bata da burin daya wuce Ma'aruff yazo ya ɗauketa a mota su more rayuwarsu da shan minti, hakan yafiye mata zaman aji muhimmanci.
Kowa ya kawo ido ya zira mata, yayarta Bintu da iya kishiyar kakarta Inna mari ne kawai ke faɗama Saminar gaskiya, sai dai sam batama saurarensu, saboda a yanzu duk mai faɗa mata gaskiyar kallonsa take maƙiyinta, mai baƙinciki da cigabanta kai tsaye.
Gefe kuma zugar su Nafy akan haduwar Ma'aruff na sake tunzurata da zuzutata a ƙaunarsa.............✍�?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(17)*
..............Harna fito alwalar magriba basu tashi a wannan hira ba, dan maman Ama ma tana kicin ne tana girkin dare.
Ni dai nai alwalata na shige ɗaki ina tsokanar Amatullah dake barbazamin duwatsu a ƙofar ɗaki tana wasa.
Basu tashi ba sai gab da isha'i, shima mijin kausar ne ya shigo, sai lokacin naji wai tana fadin ta shafa'a batai sallar magriba ba.
Ni dariyama ta bani, shiyyasa naɗan murmusa ina cigaba da azkar ɗina.
Yah Ahmad bai dawo gidanba sai goman dare, na tashi daga kwanciyar da nai ina amsa masa sallamar sa, ledar hannunsa ya ajiye idonsa a kaina.
“Yaya jikin?�?
Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa.
Nace, “Alhmdllh, ya mutan gidan?�?.
Shiru yay bai amsaba, harma na fidda rai dan na miƙe kawo masa ruwa sai na tsinkayo muryarsa yana fadin, “Lafiyarsu lau, suna gaisheki�?.
Murmushi kawai nayi naɗan rissina na bashi ruwan dana ɗebo.
Amsa yay idonsa akan ƙafata da nake ɗingisawa, sai da yasha ruwanne sannan yace, “Ki duba ledan nan akwai magani saiki sake sha, insha ALLAH zai saki gaba ɗaya�?.
Kaina na jinjina masa ina godiya, na tambayesa abinci yace ya ƙoshi, abincin da yaci ɗazun ya tsare masa ciki.
Shiru nai ban sake cewa komaiba, inason masa magana ko zaiyi wanka nima na gwada na ƴan gayu amma inajin tsoro, hakan yasa nai ɓan da bakina har muka kwanta.
_________________________
Haka rayuwar wannan gida ta cigaba da tafiya mana, inda nake ganin sabbin salon ɗabi'u daga matan gidan, dan a hankali dai maman Ama kejan kausar jikinta, kullum kuma babu fashi sai sunba junansu labarin maganin mata da sukai amfani dashi da dare, harma da gwargwadon aikin da yayi akan mazansu, gefe kuma maman Ama na zuge Kausar akan Uwargidanta, dan tanada kishiya a wani gidan da ban.
Lokaci ƙanƙani saiga amintaka mai ƙarfi ta ƙulle a tsakaninsu, inda kuma idan ɗaya na ɗaki yazama ina tare da ɗaya a waje kaji yana sukar ɗan uwansa da gulma.
Kamar yanda Yah Ahmad ya ƙwaɓe ni babu ruwana to haka naja kaina, iyakata dakin gama nace ALLAH ya ƙyauta kawai nabar miki wajen, koma kina cikin faɗar nasan dabarar da zanyi na bar wajen.
Basa iya riƙe sirrinsu, kowacce cikin zayyanema ƴar uwarta halin da take ciki suke, hatta da abinda sukaci da dare idan miji yaɗan sayo saisun bama juna labari, wani lokacinma na lura da biyu akeyi saboda ni, sai kuma lamari yaso juya akala kan maman Ama, dan kuwa dai Kausar tafi zaƙewa akan sayayya irinta ƙwalam da naƙulashe da mijinta ke mata, dan da safe har sauran naman kaza ko tsire ko balangu ake kasowa a filet ni da maman Ama duk dan mugani, tun ranar farko Yah Ahmad ya takan birki akan amsa, dan haka na bama Kausar amsa da ni bama nacin nama kwata-kwata, sai ta koma bama Maman Ama kawai, itako maman Ama zata amsa taci amma hakan na sakata baƙin ciki, dan zakiga tanata fushi da kawomin sukar Kausar wai tana badawane dan ace ta fimu jin daɗi wajen miji, nidai bancewa komai.
A kwana biyunnan kuma sai naga itama maman Ama ta fara ɗabi'ar kaso abu ta bamu wai a zuwan tsarabar kasuwa baban Ahmad yazo dashi, itama dai bana amsa saboda gudun ɓacin ran Yah Ahmad.
Ƙiri da muzu sai gulmarsu ta koma kaina, yayinda a gefe kuma suke kishi da juna, ni lamarin nasuma dariya ya koma bani, duk da sun gimeni amma idonsu na kaina, ni kuma bawani abu gareni na nunawa a garesu ba, tunma danazo gidan inaga sau uku nasan naci nama, biyu nama ɗaya kifi, suma duk na abincine da ake saye bai kuma wuce na ɗari biyu.
Zuwan da yaran gidanmu ke yawan yine yake ɗaukemin kewa, muyita hirarmu a ɗaki, sai kuma sukace na fara musu wani abu na saidawa kamar alawar madara ko aya ko iloka da makamantansu.
Banyi musuba nace su bari idan Yah Ahmad ya dawo zan sanar masa, idan ya amince to zan ringa yi musu.
Tun daga wannan ranar na fara sana'ar abubuwan yara, dan kuwa Yah Ahmad koda na gaya masa sai bai musaba, ya bani dubu ɗaya da ɗari biyar yace nayi jari, godiya nai masa sosai.
Abun har yayta bama Ahmad mamaki, domin kuwa yakan tuna Samina da kuɗi kaɗan kansata tayi fushi, idan ta tambayesa 3k ya bata 2500 aka tai haƙuri bashi dasu, to ranar kam sai tayi fushi dashi akan 500 da babu koda zata amsa 2500 ɗin kuwa, sai idan ya cika mata ɗari biyar ɗinne zasu dawo dai-dai.
Amma yau gashi ya bama Umm-Ruman 1500 kawai matsayin jari tanata masa godiya kamar ya bata 100k.
Yaji daɗin hakan sosai, musamman ma da yaga ta bada himma akan sana'ar, dan kuwa gida ta aika dasu Ammi ta sai Gyaɗa da aya aka soya aka ƙullo daga can, ƙannenta suka ɗauki wata sauran aka aiko mata nan gidan saboda yara masu shigowa.
Akan wannan sana'a ba ƙaramin dariya Kausar da maman Ama sukayiba, acewar Kausar ita yanzu ai bata da time ɗin wata sana'a, yaushe ma ta gama morar amarcinta da har zata takura tunaninta wajen wasu ƙulle-ƙulle.
Maman Ama kuwa tace ai ita bama zata iya sana'ar naira biyar ba, domin sana'ar yarace.
Rumana dai batace komaiba, sai ma murmushi da tai musu kamar yanda ta saba.
Duk kuma wannan abun da suke Ahmad na ɗaki kwance yana jiyosu, su kuma basuyi tunanin yana nanba, dan da takalmansa ya shige ciki bayan ya dawo sallar juma'a, lokacin da ya shigo duk suna cikin ɗakunansu.
Koda Rumana ta shigo ɗakin baice mata komaiba game da maganar, dan shima takaicin abinda Samina ta masa yau ne a gidansu ya sakashi zuwa ya kwanta.
______________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad ya fita zuwa gidansu, dan tun dawowar da yay bayan sallar juma'a bai sake fitaba sai da zaiyi sallar magriba, daga nanne kuma bai komaba har akai isha'i ya wuto nan.
Ƙannensa dake cin abinci a ƙofar Ayyah duk suka gaishesa.
Amsa musu yayi cikin rashin sakewa, hakanne ya sakasu fahimtar yana cikin damuwar abinda ya faru ɗazun har yanzun kenan.
Daga can ƙarshen tabarmar da suke zaune ya zauna, a haka Ayyah ta fito daga lungun Baba ta sameshi..
Da damuwa sosai a fuskarta tace, “Ɗan albarka dama kana nan?�?.
Kansa ya ɗago yana kallonta, ya girgizashi kaɗan yana faɗin, “A'a Ayyah, ai tun tafiyar da nai ɗazun ban dawo ba, yanzu ma nazo wajen baba ne�?.
“To lafiya dai ko?�?.
“Lafiya lau Ayyah, magana kawai nakeson muyi, amma inaso ma ace kema kina wajen�?.
“Shike nan tashi muje ai yana ciki�?.
Tashi yay tsaye, Ayyah na gaba yana biye har lungun baba dake zaune a ƙofar ɗaki saman tabarma, kwanika na gefensa da alama abinci ya gama ci, dan hannu ma yake wankewa lokacin da suka shigo.
Zama sukai suka jirashi ya ƙarasa, ya ajiye butar yana fesar da ruwan bakinsa da ya kurkure, sannan ya jawo da baya ya zauna sosai.
Gaishesa Ahmad yayi, ya amsa cike da kulawa yana tambayarsa Rumana.
“Tana lafiya baba, tace ma a gaisheku�?.
“Muna amsawa, amma lafiya na ganka haka kamar mai fama da ciwo?�?.
Kan Ahmad a ƙasa yay murmushi, murya a sanyaye yace, “Lafiyata lau Baba, kawai dai yanayin garinne�?.
“Amadu yanayin gari kokuwa abinda ka kasa yakicema ranka?, bara na faɗa maka gaskiya, inhar baka cire yarinyar nan da halayenta a ranka ba bafa zaka zauna lafiya cikin salama ba, ka cire duk wani abun da ya faru ko yake faruwa a gidannan ka fuskanci matar da ALLAH yay maka zaɓi madadin son zuciyarka, Ahmadu idanfa kai saken da yarinyar nan Rumana ta farajin ciwon wannan shirmen naka har taso guje maka wlhy zakayi *GUDU DA WAIWAYE....*, kasan kuwa da ga karshe iyakarka mugun zato, amma baka da karfin ɗaukar mataki, ina saka maka idone kawai dan naga iya gudun ruwanka, to na lura bamai sanin zuru bane kai, yanzu abinda akace yarinyar nan ta maka yau a gaban saurayi da mutanen anguwa idan kai da mai zuciyane bai cancanci ka ɗauke kanka daga gareta ba har abada?........�?
“Ayi haƙuri dai malam, ai kowa yasan yanzu hankalinsa baya a kan Samina, sai dai mu tayasa da addu'a kuma, kasan dama irin wannan fitarsa a rai sai dai a hankali�?.
“Kayya Ruƙayya, ke dai bar lamarin shirmen wannan ɗan naki, inda har bai saka abun a ransaba ai da yabar damuwa da lamarinta, ya kuma tashi ya nema ma kansa mafita ko�?.
Ahmad da kansa ke a ƙasa yace, “Baba kuyi haƙuri ku gafarceni, yanzu ma haka nazone da wata mafitar, fatana dai ta zama mai amsuwa a gareku�?.
Baba yace, “To babu laifi, muna saurarenka�?.
Sai da Ahmad ya kuma luliya maganar a zuciya kafin yace, “Baba dan ALLAH inason a bani izini na bar garinnan�?.
“Kabar gari kuma? To zuwa ina kenan?�?.
“Duk inda ALLAH ya rubuto mani, inason fita nema ne kawai, bawai dan anmin gorin rashin arziƙiba, ba kuma dan ban godema ALLAH da sana'ar da ya baniba, hakan zaisa zuciyata mance komai dai insha ALLAHU�?.
Baba dake jinjina ka sa yace, “Banƙi ta taka ba, amma dai abin dubi anan ita matar taka fa? Duk auren naku kwanansa nawa? da za'ace ka tafi wani waje ka barta, sai naga kamar akwai wauta�?.
Shiru Ahmad yay, dan haka baba yace, “Jeka tsakar gida ka jiramu, amma ka turo mani Suwaiba�?.
Ahmad ya amsa da to yana miƙewa ya fita, da kansa ya leƙa ɗakin gwaggo ya sanar mata kiran baba.
Batace dashi komaiba ta kashe redion da takeji ta tashi ta fito amsa kiran.
Koda tazo ta zauna Baba yay mata bayanin komai da Ahmad yazo dashi, bata ce komai ba a kai, dama sunsan bazata ce ɗinba, sai Ayyah ce ta bama baba amsa da “Niko malam sai naga kamar babu komai insha ALLAHU, musamman dai da itama Rumana tamuce, kuma itama barinsa garin zai kawo mata salama harya fuskanceta, sannan kuma bamusan alkairi. da ke cikin wannan tafiyaba da yaketa ambato, amma duk hukuncin da ka yanke akan hakan mu masu biyayyane akansa, dan abinda ka hango mu bazamu hangosa ba sam�?.
Baba dake sauraren Ayyan ya sauke nannauyan numfashi, kafin yace, “Tunda har kun aminta da hakan kuma ai Alhmdllh, ni dai dama ba matsala bane, tun kuma maganar farko da kikaimin na sanar da su Iya, suma basuyi jayayyaba, sun dai ce na dakata har sai ya sake kawo maganar da kansa, to tunda yanzu ya sake maganar ai ina ganin sai kawai mu bisa da fatan alkairi ko?�?.
Cikin faɗaɗa murmushi Ayyah tace, “Hakane malam, mun kuma gode da wannan amincewa, sai aita tayamu da addu'a kuma�?.
“Addu'a ai dolece Ruƙayya, shi mai yara inhar da hankali jikinsa ai kuma isasheahen barci ya kare masa kenan, ALLAH dai ya cigaba da mana jagora da tsare mana su baki ɗaya�?.
Amin ya rabbi, Ayyah da Gwaggo suka amsa a tare.
Ayyah ce ta leƙo da kanta tai kiran Ahmad, dan haka ya tashi ya koma.
“Amadu mun amince kaje, amma da sharaɗi�?.
Ahmad ya ɗago yana kallon baba, don san jin minene sharaɗin.
Baba ya cigaba da faɗin, “Sharaɗin shine karka yarda dogon lokaci ya riskeka baka ziyarci gidaba, sannan inhar kai dawowar farko naga ka canja daga Amadun dana sani to lallai bazaka sake komawa ba�?.
“Baba na amince da dukkan sharaɗin, fatana dai kuci gaba da min addu'a�?.
“Za'a cigaba dayi insha ALLAHU, yanzu yaushene kake shirin tafiyar?�?.
“Eh to asan samuna insha ALLAHU ranar laraba, zanyi ƙoƙari na kammala dukkan ɗinkunan mutane dake hannuna, daga nan na damƙa komai a hannun Mudanseer, sannan inason itama Rumanan ta koma makaranta tunda sun kusa fara jarabawa, inaga hakan zai rage mata kaɗaicin�?.
“E lallai kayi ƙyan kai, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, duk da ni yanzu karatun bokon nan ma tsoro yake bani, to amma ita rayuwa ba'ai mata kuɗin goro, dan wani ya bijire dalilin hakan bazakai imani cewa kowama zai kasance hakanba, ALLAH ya cigaba da tsare mana ku baki ɗaya, yanzu kafin ka wuce saika sanarma su Iya duk yanda mukai, nima zuwa safiya zan shiga mu tattauna harma dasu Yusha'u akan batun�?.
“To Baba nagode ALLAH ya saka da alkairi, ya kara muku lafiya da tsahon kwana�?.
Su duka da amin suka amsa. Daga nan Ahmad yay musu sallama ya tafi, sai da ya shiga Sashen su Iya kankanninsa, bayan sun gama ɗan wasansu na jika da kaka ya zayyane musu komai, babu wanda ya musa a cikinsu, saima albarka da fatan alkairi da nasara sukaita saka masa, zuwa kusan sha ɗaya malam yace ya tashi yaje dare yayi haka nan.
_________________________
Lokacin daya shigo gida Umm-Rumana har tayi barci, hakan yasa bai tadata ba shima ya kimtsa ya kwanta, ya daɗe yana tunani kafin barci ya ɗaukesa.
Washe gari da safe suna karyawa ya sanarma Umm-Ruman maganar tafiyarsa, duk da tasan ba wata soyayya a tsakaninsu ɗan zaman nan da sukai shakuwa ta fara tasiri a garesu, hakanne ya saka duk sai taji babu daɗi.
Amma tayi farin ciki da yace zata koma makarantar ta, hakama islamiyya duk zata koma, dan bayason tanama zama a gidan balle ta koyi halinsu maman Ama.
Duk da ya gindaya mata sharaɗin saka dogon hijjab da niƙaf a makarantar hakan bai ɓata ranta ba sam.
A gaba ɗaya kwanakin da suka biyo baya na shirin tafiyar Ahmad ne, yay ƙokarin kammala ayyukan jama'a daya amsa, sannan yaje makarantar su Rumana yay maganar dawowarta da faɗar matsayinta na