Showing 96001 words to 99000 words out of 165545 words
Rumana tai masa barka da zuwa ya amsa yana zama da tsokanarta.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗauki tiren data shiryama Ahmad abinci takai gabansu tana gaida Sufyan ɗin, koda suka gaisa saitai yunƙuri durƙusawa zata zuba musu abincin.
Ahmad dake latsa waya yana saurarensu ya ɗago ido ya kalleta, a hankali ya furta, “Jeki abunki zamu zuba�?.
Yanda fuskarsa babu walwala yasa bata musaba tama fita domin yin alwala.
Lokacin data shigo harsun fara cin abinci, sallarta ita dai ta kabbara, koda ta idar saita fita tabarsu sunacin abincin suna hirarsu.
Koda suka kammala ma tare suka sake ficewa daga gidan Sufyan nata mata santi, ita dai murmushi kawai takeyi kanta a ƙasa har saida suka fice.
Ta tattare kwanikan ta fita dasu danta wanke, tana wanke-wanken suna ƴar fira da Kausar data fito take shan iska a ƙofar ɗakinta, Maman Ama dai bata gidan tana gidan maman Aysha.
A haka tazo ta samesu, kawai sai gani sukai ta ɓata fuska, ko zato take gulmarta sukeyi? Bata san su firar tasuma akan haihuwar Kausar ɗin bace..
Tunda Rumana taga yanda tayi saita miƙe abinta dama ta gama wanke-wanken ta koma ɗaki kawai.
★★★★★★
Yauma anayin sallar isha'i Ahmad ya shigo gidan, ledar daya sayo musu kayan fruits ta amsa tana masa sannu da zuwa, kwalliyar datai yakebi da kallo dan ta mata ƙyau, itama ta lura da kallon da yake mata tun shigowarsa.
Ta katsesa da faɗin, “Yaya a haɗa ruwan wanka?�?.
A taƙaice yace, “Uhm�?.
Sai da takai masa har banɗaki sannan ta dawo ta sanar masa, ya miƙe ya cire kayansa ya saka jallabiya ya fita.
Kafin ya dawo ta saka fruits ɗin a filet mai ɗan girma, tana fiddo masa kayan da zaisa ya shigo.
Da taimakonta ya shirya dukda dai ita takasa sakewa dashi yanda ya kamata har yanzu, sosai takejin nauyinsa, abinda yasa take daurewa saboda ta lura yana son tattali, nuna kulawarta a garesa sosai ke sakashi sakin mata fuska tana ganin fara'arsa, a ganinta ta wannan hanyarne zata cusa masa sonta a rai koda bata samu kwatankwacin abinda Samina ta samuba na soyayyarsa, itama ta samu wani yanki a ciki.
Sai dai abinda Rumana bata saniba shine tuni tayi mamayar da Samina batai koda kwatankwacinta ba a zuciyar gwarzon nata, kawai dai bai furta baneba.
Yau ɗinma bai ɗaga mata ƙafaba, danshi dai ji yake ta sake canja masa fiye da wancan karon, shiyyasa baya gajiya da ita.
Rumana dai kam dauriya kawai takeyi, dan batajin daɗin jikinta sam, da safe kuwa luɓus ta tashi harda su zazzaɓi, to dama can ba isashshen lafiyarne da itaba shikuma yazo ya sake nuƙurkusarta.
Duk yanda yaso kuma suje asibiti tace ita kuma a'a, har sai da yakai da zazzaga mata masifar dabai niyyaba, sai kawai ta saka masa kuka.
Abin nan ya bama Ahmad haushi, dan baiga abin kuka a wajen ba shi dai.
Ƙyaleta yay yama shirya ya fice daga gidan dan jiya bai kammala uzirirorinsa ba shida Sufyan.
Yau ɗinma tare suka tafi da Sufyan ɗin a mashin ɗinsa.
Sai dai duk abinda yakeyi zuciyarsa nakan Rumana daya bari kwance duk da haushin data bashi.
Rumana kuwa kusanma sha biyu sai taji ta ta dawo dai-dai, sai dai ciwon jikin da Ahmad ɗin ya haddasa matane kam bai bartaba.
Abincima ta tashi tayi sannan ta gyara jikinta.
Lokacin da Ahmad ya shigo gidan sai ya isketa da su khadija ƙanwarta sun kawo mata kayan sana'arta da akayo daga can.
Ya ɗanji sanyin ganinta haka, amma sai bai sakar mata fuskaba.
Yaran suka gaidashi itama tai masa sannu da zuwa, duk amsawa yay a dake har ita ɗin.
Da kansa ya ɗiba ruwa ma ya tafi wanka baice ta haɗa masaba, koda ya fito ta gama shirya masa abinci, su Khadija kuma ta basu aikin data kauda hankalinsu suka dawo waje.
Ganin yaƙi kallon ko inda ta ajiye abincin sai ta daure tace, “Yaya ga abinci�?.
Kamar bazai tanka ba, sai kuma ya juyo yaɗan. kalleta ya ɗauke kansa, “Na ƙoshi, ke da baki da lafiya kuma waya aikeki yin abinci?�?.
“Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya, naji sauƙi, dama kuma bawani yayimin zafi bane zazzaɓin�?.
Bai amsata ba, dukda ta bashi tausayi, ya canja kayansa, da alama dai wanima wajen zai sake fita.
Sai da ya kammala tsaf sannan ya zauna ya buɗe abincin data ajiye, matsowa tai tana jin sanyi a ranta da zaici, ta zuba masa, tana ƙokarin komawa gefe yace, “K kinci?�?.
“Naƙoshi�? ta faɗa kanta a ƙasa.
Cokalin ya ajiye yana yunƙurin mikewa, “Cin nawa baida amfani kenan�?.
Saurin katseshi tai har tana dafa masa hannu, “Yi haƙuri yaya Please zanci wlhy�?.
Sai da ya zuba mata harara sannan ya koma ya zauna.
Daga ƙarshe dai a tare sukaci abincin sannan ya fice yana faɗa mata bara yaje baba na jiransa zasuje wata gaisuwa.
A dawo lafiya tai masa.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻a: https://youtu.be/N2nbw8zn9Jk
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(31)*
...............Cikin sauke ajiyar zuciya Umm-Ruman tace, “Kai Yah Ahmad ko daru�? idan ƴan arziƙin sukazo ayi, idan ƴan tsiyarne ya koma mata Ahmad ɗin data sani a gida.
A cikin kwana biyun nan dai kam ya bala'in maida kansa busy, hankalinsa bai samu zama waje ɗaya ba sai da ya haɗa kan duk abinda yake buƙata sannan.
A daren jiya malam ya tashi da mura ta rashin jin daɗin jiki, abunka da jikin tsufa, zuwa safiya sai abun yaso yin ɗan tsanani, tunda safe sukai kiran Ahmad koma barci bai tashiba kiran ne ya tadashi.
A gurguje yay brush ya canja kaya ya fice.
Tunda ya fita Umm-Ruman tai tagumi kawai tana ma kakan nasu addu'ar samun afuwa.
Ahmad na zuwa basu ɓata lokaciba asibiti suka wuce, shi da Mudan sukai ta shigi da fici saboda sune dai manyan ƴaƴa maza a gidan, iyayensu kuma ba karatu sukaiba, suma kuma suna bukatar a taimaka musun.
Dukansu dasu akaje asibitin, amma dai su Ahmad ɗinne keta kai da kawo har aka bama Malam gado sannan sukaɗan samu nutsuwa.
Rumana tun tana jiran dawowar Ahmad harta fara damuwa sosai, ta gyara ko ina dai tayi musu breakfast, sai dai ta kasa ci.
Tana zaune jugum har kusan ƙarfe ɗaya sai gashi ya shigo, jiki a sanyaye ta miƙe tana masa sannu da zuwa.
Ya kalleta yana ɗan lumshe ido ya jinjina mata kai kawai, dan jikinsa yayi luɓus saboda kai kawo da sukaitayi, ga yunwa na cin hanjinsa.
“Yaya ya jikin nasa?�?.
Kaɗan ya sauke numfashi yana zama a bakin gadon, “Da sauƙi sosai, sunata ƙara masa ruwane dan yaji ƙarfin jikinsa�?.
“Wayyo malam ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffarane�?.
Da amin Ahmad ya amsa yana miƙewa ya fara cire kayansa, hakanne ya saka Rumana fita danta haɗa masa ruwa.
Tana dawowa shi kuma ya fita zuwa bayin, koda ya fito yaga ta ajiye kayan shayi sai ya kalleta da mamaki.
“Kina nufin zama kikai jirana baki karyaba?�?.
“Yaya banji yunwa bane shiyyasa�?.
Baice komaiba ya ɗauke kansa, ya kimtsa ya fita massalaci domin gabatar da sallar zuhur.
Itama Rumana abinda tayi himmar yi kenan, bai kuwa jimaba sai gashi ya dawo ɗauke da ɗanyan indomie a leda.
ledar ya miƙa mata yana faɗin, “Tashi ki dafa wannan�?.
Amsa tai cikin girmamawa, kafin ta kammala yaɗansha tea dan yunwa yakeji bata wasaba, koda ta gama da ƙyar ya sakata taci abincin, ya lura batason cin abinci yanzu, ga wani tsarce-tsarcen yawu daya lura tanayi a kwana biyun nan.
Bai dai ce mata komai akan hakanba yace dai ta shirya suje asibitin ta duba malam.
Taji daɗi sosai, ta shirya tsaf ta kawo hijjab ta saka, maman Ama na tsakar gida suka fito, sai da Rumana ta kammala rufe ƙofarta kafin tace mata saisun dawo kakansu aka kwantar a asibiti.
Addu'ar samun lafiya maman Ama tai musu tanabin Rumanan da kallon ƙurilla, itafa saima taga kamar mai ciki.
Tsaki taja tana faɗin, “Toni bandama abuna waye yay cikin? matar da ko namiji bata taɓa saniba ta ina zata samo ciki?, inaga dai dagaske maganain ƙibar sukasha ita da mijin�?.
🤣Maman Amar mu ta mutunci kenan, ido bai gani baki ya ƙyalle saiya tofa, ALLAH ya gyara mana ke da masu irin halinki🤸🏻♀😂 .
Rumana tayi mamakin ganin ashe da mashin ɗin Sufyan Ahmad ɗin yazo.
Sai da ya hau ya tada sannan ya kalleta ganin tayi tsaye tana kallonsa kamar ta samu tv,
“Kona wuce ne?�? Ya faɗa manyan idanunsa a kanta.
Da sauri ta ƙaraso, dole sai da ta dafa bayansa sannan ta hau.
A zuciyarta take faɗin, “gaskiya roba-roba inba mijinkaba ai baida daɗin hawa�?, to diba yanda duk ta koma jikinsa, ballema ita matsoraciyarnan dama.
Babu mai cema ɗan uwansa uffan har suka isa asibitin.
Samina dake jikin motar Ma'aruff da ALLAH ya ɗorata a kansa ya kawota duk da dai akwai manufa a ransa, dan soyake yakai yarinyarsa gida suɗan huta, shiyyasa ya ɗakkota da kansa ya kawota gida kamar yanda yay alƙawari, sai dai suna zuwa aka sanar musu malam na asibiti, duk matan gidanma basu daɗe da tafiya ba sai yara kawai.
Da kansa yace tazo ya kaita asibitin itama, idan ya ajiyeta sa dawo gida da ƴan gidan nasu, da daddare kuma zai dawo ya ɗauketa.
Wani sama taji kanta kuwa, shiyyasa akai shiri na alfarma, yanzu haka sun shiga sun dubo malam ɗinne tazo rako Ma'aruff da zai wuce.
Tun shigowar mashin ɗin su Ahmad akan idontane, gabanta yay wata irin faɗuwa zuciyarta sai fatt-fatt take da masifar ƙarfi.
Ma'aruff dake magana batajiba ya kalli inda tabi da kallo kamar idonta zai zubo ƙasa.
Akan Ahmad dake faka mashin ɗin ya sauka, Umm-Ruman ta dafa bayan Ahmad zata sauka shida baima san su Samina nayiba ya ɗan juyo ya kalleta yana faɗin, “Babie R karki karyani fa�?.
Murmushi mai ƙayatarwa Rumana tayi, ta ƙarasa sauka tana bashi amsa,
“Oh Yaya, da nice fa yanzu kacemin raguwa�?.
Shima saukar yay yana murmushi da ƙoƙarin ajiye mashin ɗin da ƙyau, ya juyo yana ɗan ranƙwafowa ya lakaci hancinta da faɗin, “Yo ai ragguwarce�?.
Yanda Rumana ta ɗan ɓata fuska a shagwaɓe ne ya bama Ahmad dariya, dan haka yace, “Zaki wuce mu tafine ko saina ɗaukeki?�?.
Baya ta matsa tana masa harar wasa, ta tofar da yawun daya taru mata a baki kaɗan tana fara tafiya.
Hannu ya kai zai riƙota tai wani ɗan taku mai hanzari kamar zata ruga.
Dariya Ahmad yayi har haƙoransa na bayyana, yace, “ALLAH zan kamakine Yarinya�?.
Wannan kalma tashi karaf a kunnen Samina da Ma'aruff dake binsu da kallo kamar idanunsu zasu faɗo ƙasa.
Sukam su Ahmad ma basu lura dasu ba har suka shige.
Ma'aruff ne ya fara taɓe baki yana faɗin, “To shi wannan faƙirin yaushe yay ƙiba haka? Ko shima sha ka fashe ɗin da mata ke sha ya sha?�?.
Banza Samina tai masa, dan ita kaɗai tasan sukar da takeji a zuciyarta, badan ta baro handbag ɗinta wajen mama gaje na a ciki da wlhy bazata koma ba.
Shiko Ma'aruff Umm-Ruman ce ta tafi da zuciyarsa, harya kasa haƙuri sai da yay ma Samina tambaya, “Wai dama wannan aka aura masa?�?.
Guntun tsaki Samina tai, a taƙaice tace, “Uhm�?.
Babu zato taji Ma'aruff yace, “kai amma ƙyaƙyƙyawa da ita, wlhy tama fiki ƙyau da nutsuw....�?
Sai kuma yay shiru bai ƙarasaba ganin kallon da Samina tai masa a hargitse.
“Kinga malama daina watsomin waɗanan idanuwan, indai nine ma kinga tafiyata, kice ina gaidashi shida ƙyaƙyƙyawar matarsa dan ALLAH�?.
Hawayene kawai suka shiga sakkoma Samina a kumatu, wanda ita kanta batasan na minene ba, da ƙyar ta iya tsaidasu tabi bayan su Ahmad, dukda tsantsar kishin Rumana daya doki ƙirjinta bazata iya daurewa ba sita sake ganinsa ko zataji sassauci.
Su Ahmad kam tunda suka shiga iyayensu mata duk suka zubama Rumana ido, sukam basu fahimtaba, cikin girmamawa duk suke gaishesu daga Rumanan har Ahmad.
Tsagwaron farin cikine ya bayyana a fuskar Ayyah, hakama Gwaggo da Ammi sai dai su sun shanye a zukatansu, su dai su Yaya maryam sun kasa ɓoye farin cikinsu duk da hasashe suke ba tabbatarwa sukaiba, Mama gaje kuwa zuciyarta sai gudu take da sauri-sauri.
Ahmad da Rumana dai suka shiga inda Malam ke kwance danta dubashi, barci yakeyi, shi kaɗaine a ɗakin har yanzu kuma ana saka masa ruwa, likatanne yace duk su fito dan ba'ason ana masa yawan hayaniya.
Basu jimaba a ɗakin suka fito, Ahmad ya nufi wajen likita dan yaji ya ake ciki yanzu?, ita kuma Rumana ta zauna wajen iyayensu mata da yayyanta.
Lokacin Samina ta shigo, dan haka Rumana ta gaisheta da bata haƙuri akan rashin zuwa dubata da bataiba, tace alokacin itama batajin daɗine.
Cikin ɗan taɓe baki Samina tace, “Karki damu�? daga haka taja bakinta tai shiru.
Itama Rumanan sai bata sake cewa komaiba, su Ayyah ma duk suna saurarensu amma babu wanda ya saka baki.
Tashi Samina tai ta nufi office ɗin likita wai bari taje taji yaya ake ciki? Babu wanda ya tanka mata sai mama gaje, dan tunda tazo asibitin taketa nuna isa ita adole matar mai arziƙi, har cewa tai za'a canjama malam asibitin iya tace a'a nanma ya Isa, Ahmad nata iya bakin ƙoƙarinsa hakanma su ya wadatar.
Yanzu kuwa data tsiri zuwa Office ɗin likita kowa ya fahimci Ahmad ta hango ya shiga ƙila.
Babu kuma wanda ya tanka mata akan hakan.
Yanda Rumana ta kasa zama taketa fita zubda yawune ya saka amaryar baba iliyasu tai magana cikin murmushi,