Showing 51001 words to 54000 words out of 165545 words

Chapter 18 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

372

matar aure a yanzu tunda makarantar ta ƴammatace, hakama islamiyyarsu yaje ya daidaita mata komai, acewarsa bazata shiga ta matan aure ba, mafi yawan makarantun matan sunfi maida hankali ga saida abubuwa da gulmae juna.
Daren da zai tafi ya zaunar da Rumana yay mata Nasiha sosai, tare da kafa mata shariɗɗa na zaman gidan, duk kuma abinda takeso ta tambayi Mudanseer zai kawo mata, sannan Fa'iza da Salima zasu dawo nan su ringa tayata kwana.
Taji daɗin zancen dawowar su Salima, dan har akan fuskarta sai da yaga haka, amma sai yay tamkar bai fahimceta ba.
Dama tun da daren yay sallama da kowa nasa, iyayensa kakanninsa abokansa dama duk wanda yasan suna huɗɗar mutunci dashi.
Dan haka yana dawowa sallar asuba ya shigo gidan bayan sunyi sallama da mazajen su maman Ama, jakkarsa daya zuba kaya kala uku kawai ya ɗauka, dan ko wanka baiyiba, sai kuma Umm-Rumana taji hawaye na zuba mata.
Tsayawa yay kawai yana kallonta, shi kansa baisan shaƙuwa ta shiga har haka a tsakaninsuba sai yau, ya tako a hankali zuwa gabanta, babu tsammani ya jawota jikinsa kawai ya rungume, ƙanƙamesa tayi tana mai fashe masa da sabon kuka, baice komai ba ya shiga bubbuga bayanta a hankali yana mai lallashinta ta hakan, ganin zata ja masa makara sai ya ɗago kanta ya sumbaci goshinta, murya ƙasa-ƙasa cikin kunnenta yace, “Haba Ƙanwata kuma amaryata, kimin addu'a kinji, amma ba kukaba, ALLAH yay miki albarka, insha ALLAHU lokaci zaiyi da zaki mallaki Ahmad da komansa, ke dai ki zama mai yawan haƙuri da yanayinsa na yanzu kawai�?.
Ƙara faɗawa jikinsa Rumana tayi tana wani kukan, yay murmushi mai sanyi yana janyeta a jikinsa, taimaka mata yay ta hau saman gado, ya lulluɓa mata bargo tare da ƙara sumbatar goshinta, yace, “Karki manta dani duk runtsi�?.
Abinda kawai ya faɗa kenan ya juya ya fita yana ja mata ƙofar.
Lokacin data jiyo ƙarar rufe ƙofar gidan sai ta kuma fashewa da sabon kuka mai cin rai da tsuma zuciya, tasan dai ba soyayya bace a tsakaninsu, amma tanajin wani ɗacin na wannan nisan nasu.

Ahmad kam Sufyan ya iske yana jiransa da mashin a ƙofar gida, dan haka ya haye suka ɗauki hanyar tasha.
Koda suka isa sai suka iske mota ana mata lodin zuwa garin porthercout, babu wani tunani aran Ahmad ya faɗa bisa shawarar Sufyan, motar dama dai ta gama cika, gurin mutum ɗaya ya rage rak, Ahmad na shiga suka tashi, har motar ta fice a tashar suna ɗagama juna hannu shi da Sufyan...............✍�?





_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(18)*



...........Taci kuka sosai harta godema ALLAH, dole masu iya magana suce sabo akema kuka ba mutuwa ba, harta fara jiyo motsin maman Ama da yaranta a tsakar gida ita batai ko yunƙurin tashiba, ahakama barci ɓarawo ya sake saceta, saboda jiya sun daɗe basu kwanta ba.
Gaba ɗaya barcin nata sai ya kasance mafarkin Ahmad ne.

Kusan goma Kausar ta fito daga ɗakinta zatayi brush, tabi tsakar gidan da kallo kafin takai dubanta ga maman Ama dake can ƙofar ɗakinta tana haɗa zoɓonta na saidawa.
“Yau gidan namu bai samu ƴar sharar safenba kenan? Ko gimbiyar tamu babu lafiya ne?�?.
Ƴar dariya Maman Ama tayi, taɗan taɓe baki cikin iya gulma tana faɗin, “Zaune dafa'an murar kwaɗo, inaga dai kewar tafiyar maigidace ta hanata fitowa�?.
“Yo ina mijin ya tafi?�? cewar Kausar tana matsowa kusa da maman Ama.
“Uhum wai neman kuɗifa, Kausar nifa wlhy mijin yarinyarnan sai naga tamkar bai taɓa riƙe biroba balle akai ga zaman aji, amma waifa nan inda yake digiri garai�?.
Cikin tsantsar hassada Kausar tace, “Yo digirin banza, maman Ahmad ai yanzu wannan ruwan dare ce, ALLAH ma yasa ko a ajin ba na ƙarshe yake ɗaukaba, ita da ba uwar wani abu ya taɓa mataba ma miye na damuwa dan ya tafi mtsooow�?.
Dariya sosai Maman Ama keyi, tace, Kijiki da wata magana, idan baiyi mai gaba ɗaya ba, kika sani ko yanayin ƴan kananun ayyuka, duk namijin dai da zai kwana da mace ɗaki ɗaya bai iya mata komaiba ai idan kaji gangami da labari, ALLAH sai dai idan bashi da lafiya ne�?.
“Nimafa nayi wannan tunanin wlhy, ko ogana da ina bashi labari cayaymin sai dai idan mijin baida lafaiya, amma wane lusarine za'a kawoma budurwa kamar wannan ya iya kallonta ya kauda kai kuma su kwana lafiya su tashi a ɗaki ɗaya�?.
“Kin daiji magana, wlhy hasashenmu duk ɗayane, inaga baida lafiya dai sai yake fakewa da damuwar dan waccan ta ƙisane�?.
Sosai suka kwashe da dariya, har suna haɗa baki wajen faɗin “Tamɓele kenan�?.

Duk wannan shagali da suke Rumana ma batasan sunaiba, barcinta take abinta.
Bata farka ba sai kusan sha biyu, ta tashi a firgice da mamakin barcin da ta sha, brush da buta ta ɗauka ta fito, Kausar da maman Ama na tsakar gida zaune, Kausar na tsifar kai daga ƙofar ɗakinta maman Ama kuma na tsince shinkafar da zata girka.
Su duka zubamata ido sukai tamkar yaune suka fara ganinta, Rumana ta gaishesu tana tambayar inasu Ahmad.
“Suna ƙofar gida, amma lafiya kuwa da barci har rana Amarya?�?.
“Lafiya lau maman Ama, kainane kawai kemin ciwo kaɗan-ƙaɗan�?.
“Ayya to ALLAH ya sauwaƙe�?. Mama Ama tai maganar suna kallon juna da Kausar kowanne na taɓe baki.
Kausar tace, “Amin, to Amarya ko dai mun samo baby ne?�?.
Murmushi kawai Rumana tai mata ta ajiye brush ɗin ta ƙoƙarin shiga bayi ta tsinkayo maman Ama nabama Kausar amsar tambayarta......,
“Hhhh kema Kausar akwaiki da son zance dai, kin taɓa ganin gonar da ba'a taɓa mata ko gewaya ba ta fidda tsirrai? Dama kin tsaya a abinda ta faɗa ɗin yafi�?.
Naɗan ciza leɓena dukda ban gama fahimtar zancen nasuba nasan akwai shaƙiyanci a ciki, yanda suka kwashe da dariya kawai ya tabbatarmin da hakan.
Sosai ƙyanƙyami ya kamata ganin bayin duk datti, dan bata tashiba baza'a samu wanda zai tsaftaceba, sai kace ita kaɗai ke amfani dashi, waje ta dawo tai brush ta koma ɗaki abunta.
Bata zauna ba ta hau gyaran ɗakinta, sai da ta kimtsa komai tsaf tayo shara ta goge ledan da ruwa da omo tasa turaren wuta sannan ta dawo sharar waje, har lokacin kuma su maman Ama ana zaune ai ana gulmar maƙwafta, wance tayi kaza wance tace kaza.
Rumana dai bata saka musu bakiba harta kammala sharar tsakar gidan taja ruwa a rijiya, tana ƙoƙarin fara wanke ƴan kwanikan da sukai amfani dasune mijin Kausar ya shigo gidan, gaidashi sukai ita da maman Ama.
Maman Ama na ganin Kausar da mijinta sun shige sai ta ɗakko boket tazo gaban rijiya ɗibar ruwa.
Dama ina kallon yanda take hararar ledar hannun mijin Kausar kamar idonta zai faɗo ƙasa.
Tana zira gugar ne take faɗin “Amarya bakiga mutuniyarki ana karya ƙugu su miji ya kawo cefane ba, batasan munsan komaiba yanzu, sai abinda kishiyarta tace miji keyi�?.
Murmushi kawai nayi amma bance uffanba, maimakon maman Ama taji haushi tai shiru itama sai ta cigaba da zaro zance akan Kausar, azamar kammala abinda nake nayi nabar wajen ina faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to�?.
Ina kallo ta bini da wata harara tana taɓe baki, na girgiza kai kawai na ɗauki ruwa da omo naje na tsaftace bayin sannan nazo na ɗiba ruwan wanka a rijiya.
Har lokacin kuma Kausar basu fitoba, maman Ama na zaune tana facing ɗin ɗakinsu tamkar mai hango abinda sukeyi a ciki.

Lokacin dana fito wanka sai haɗiyar zuciya take, harda dukan Amatullah.
Ni dariyama ta bani, na shige ɗaki abina inayin kayata a zuciya.
Ƙin fitowa nai, ina shirin ɗora taliya a ɗaki sai ga sallamar Zainab.
Ta shigo ɗauke da kwanon silba.
Cikin ɗokin ganinta nake faɗin, “Ga autar gwaggo ga autar Ayyah�?.
Itama dariyar takeyi da cewa, “Kai Yaya Rumana, sai kace wadda tazo daga legas�?.
“Lallai yarinya, kinsan kuwa yanda nakejin daɗi idan na ganku, daga ina haka?�?.
“Daga gida nake, Ayya ce tace na kawo miki wainar rogo da mukayi�?.
“Kai-kai kice yau daɗi kukeci a gidan malam ɗin?, duk ni kaɗai wannan?�?.
“Eh mana�? Zainab ta faɗa tana ƴar dariya.
Na kashe rishon ina cewa, “Aini to nama fasa dafa komai, wannan kam tama isheni�?.
Zainab data kwanta a tabarma tace, “Ai aunty fa'iza ma tace anjima zasu taho itada aunty Salima nan, tace karkiyi girki zasu yo muku taɓa ka lashe�?.
“To ALLAH ya kawosu lafiya�?.
Haka Rumana ta zauna taci wainarta ta rogo tai nak, sunata hirarsu da Zainab, har aka kira sallar la'asar sannan ta miƙe alwala, itama Zainab alwalar tayo sukai sallah, bayan sun idar ta bata naira talatin kuɗin napep da aya da gyaɗa tace taje gida kar a nemeta.
Godiya tai mata ta wuce, itako ta jawo littatafan makaranta ta hau dubawa.



_______________________________


Ahmad kam tunda suka ɗauki hanya ya jingina kansa da kujera yay shiru yana tunanin rayuwa da abinda ya zamo masa sanadin barowa gida, wani sa'in idan ya tuna rayuwar da sukai da Samina a baya sai yaji kamar zai yarda da maganar wasu mutane dakan ce asiri akai mata, sai dai wani sashe na zuciyarsa na saurin ƙaryata wannan magana, sai ya bijiro masa da ainahin gaskiya aka lamarin Samina ta gujesa ne kawai saboda burin banza da wofi da son duniya, wanda a wannan zamanin mafi yawan ƴammata shine yake ruɗarsu ya halakasu, wasu zaka samu da taimakon iyayensu, wasuko sun zubda tarbiyyar iyayen ne sun ɗauki ta ƙawaye ko samari, san zuciyane kawai kesa a zagi ilimin boko, amma wlhy bashi da alaƙa da lalacewar yaranmu, lalacewar kawai tafi yawa daga zuciya ko tarbiyya da dai sauransu.
Yayi zurfi a tunaninsa sosai, har sukai tafiya mai nisan zango dashi kansa baisan adadinta ba, sai da na kusa da shine ya taɓasa lokacin da suka iso wani gari aka tsaya domin yin salla sannan ya dawo hankalinsa.
Bayan salla suka sai abinci kamar yanda yaga abokan tafiyarsa nayi, dan duk inda ya saka ƙafa tarene suke da makwafcinsa da suka zauna kusa da juna.
Bayan sun dawo kuma sai ƴar fira ta fara shiga tsakaninsa da abokin zaman nasa, wanda yace shi sunansa Nura, shima dai neman arziƙi ya kaisa rayuwar garin porthercout.
Tun Ahmad bai sake masaba dai harya saki jikinsa kular da yay kamar Nuran baida yawan hayaniya, ahaka har suka isa garinna port gabannin asubahi.
Dole Ahmad yabi Nura masaukinsa da safe kamar yanda ya buƙata, dan kuwa inma yaƙi dai bashi da wajen zuwa, tunda ba kowa ya saniba balle yace zai nemeshi.
Masaukin na nura dai bawani waje bane face gidan biredi, inda sukan maƙala ƴan kayansu su wuce wajen sana'a, idan sun dawo su yada zango a ƙofar wani shago da ire-irensa su rage dare, zuwa ƙarfe goma su nufi gidan biredi su kwanta, asubar fari kuma za'a tashesu saboda za'a fara aiki.
Sana'ar kuma Nura Shu-shaina ce, dan haka koda Nura yayma Ahmad bayani sai bai jayayya ba yace shima zaiyi, tunda bada wani jari yazo ba balle yace, dama iya kuɗin motane, sai kuɗin da suka rage masa a aljihu naira dubu ɗaya da ɗari bakwai.
Da waɗannan kuɗinne Nura ya rakashi ya sayi ƴan abubuwan bukata da zai fara wannan sana'a, a ranar babu hutu suka fara zagayawa kuwa.
Ahmad yasha matuƙar wahala, duk da ya saba da wahalhalun talla ba irin wannan baneba, saboda banbancin gari da jama'ar garin, sauƙinsa ɗayama yayi karatu, shine ya taimakesa wajen furta magana da mutane, dan inhar kaji hausa to sai dai idan suna tare da bahaushene waɗanda suka kasance ƙalilan a garin kuma.
Sai yamma lis suka dawo yanata yaƙe, ga ƙafafunsa sai ciwo suke, harya yi aniyar cema Nura shi dai bazai iyaba, sai kuma wani tunani yazo masa a rai, idanma yace bazaiyiba to yanada jarin yin wata sana'arne bayan wannan? Wannan tunanin shine ya danne dukkan yunƙurinsa ya sama zuciyarsa haƙuri.
Hankalinsa bai kuma tashiba sai da sukazo kwanciya, yaga kowa na ƙokarin jera kwalin da zai kwanta, ƙwalla ne suka cika masa idanu, dukda kasancewarsu talakawa ko kwanan tabarma bayi yakeba sai ta kama, ko yaya dai sunada ƴar katifar barcinsu.
Shi aranarma sun manta basu sayo masa kwalinba, sai na Nura suka gitta suka kwanta iya ƙirjinsu kawai wai dansuji ɗan taushi, ƙafafu kuma na saman suminti, Ahmad da ya saba rufa zai iya barci sai gashi yau babu abin rufar, aiko duk yanda yaso yin barci kasawa yayi, ta ko ina babu daɗi, zuciya sai tuna masa matarsa da iyayensa harma da Samina take.
ƙarfe uku da rabi aka tashesu, har lokacin kuma Ahmad bai rintsaba, haka suka fito kamar awaki, kowa yaɗan samu waje a waje ya maƙale dan ya ƙarasa daren, wasuko basu kwantaba suka hau hidimar shirin fita kasuwa sai kace fataken dare.
Wannan ƴar kwanciya dasu Ahmad suka samu ƙofar wani shago ce ta jawo masa barci yaɗan figesa, sai da Nura ya tashesa da asuba da ƙyar.

Gaba ɗaya komai ya rikiɗema Ahmad, dukya fita hayyacinsa tamkar ma wanda baisan A ba, gaba ɗaya ya rikiɗe matsayin ɗan ciraninsa, kwanansa huɗu sannan ya samu damar kiran ƴan gida a waya.
Yaci faɗa wajen baba saboda ƙin kira ya sanar ya sauka da baiyiba, sai da yayta bama baba haƙuri sannan ya sakko.
An bashi ya gaisa da kowa, harda Mudanseer, yace masa yaje da dare ya kaima Rumana waya su gaisa.
Aiko kamar yanda ya buƙata da daddare ya kaima Umm-Ruman waya, lokacin su Fa'iza masu tayata kwana suna gidan. Gaisuwa kawai sukai ya tambayata babu dai wata matsala ko? kuma ta daina kukan?.
Ta faɗa masa eh tana haɗiye kukanta.
Daga haka bai ƙaraba yay mata sallama, itako ta mikama Mudanseer wayar.
Tun daga ranar bai sake neman Rumana ba, sai dai duk kwana biyu yakan gaisa da baba, idan yaga kuɗin zasu isa a haɗashi dasu Ayyah, idan bazasu isaba shikenan yace baba ya gaishesu kawai.
Tun Ahmad na jigata harya saba da sanar tasu, ya dake zuciyarsa sosai, komai ya zame masa jiki.
Kafin wani nisan zango sai ga wata ɗaya ta shuɗe babu labarin Ahmad balle dawowarsa, da yake yakanyi waya da Madan ya sanar masa ƴan kuɗin ɗinki da ake samu suna riƙesu har Rumana sai hankalinsa yakan ɗan kwanta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login