Showing 120001 words to 123000 words out of 165545 words
Tuni fuskar Ahmad ta canja, kansa a ƙasa yace, “To baba ina mijin nata?�?.
Murmushi baba yay idonsa akan Ahmad ɗin, “Amadu bar zancen kowa je kaima zumincin ALLAH�?.
Kai Ahmad ya jinjina tare da faɗin “To baba�?.
Cikin gidan ya shiga, dan ya saka a ransa sai matarsa ta fara ganinsa kafin wata shashashsa.
Umm-Ruman na saka kaya ya shigo, dan fitowarta wanka kenan, jaririn kam barcinsa yakeyi shima an masa wankan tunda farar safiya.
Bata juyoba tadai amsa sallamarsa, tana ta ƙoƙarin jan zip ɗin rigarne sama yaƙi tafiya, ashe wani zarene ya shige ciki.
Ahmad ya matso kusa da ita tare da ɗora hannunsa bisa nata, baice komaiba ya janye natan yaja zip ɗin, sai dai shima bai wuceba, jansa yay ya koma ƙasa sannan ya duba, ganin zarene yaɗan ranƙwafo yasa haƙori zai tsinke, maimakon ya tsinke zaren sai ya kama busa mata iska a gadon baya.
Babu shiri Rumana ta juyo tana fuskantarsa..
Ɗagowa yay shima yana wani kallonta idanu a narke,
“Kai Yaya, haka ake sa zip ɗin?�?.
Ransa a dagule yake da aikin da baba ya sakashi, hakan yasa sam fuskarsa babu walwala, sai ɗanyatsa da yakai ya lakaci hancinta yana ɗage mata gira ɗaya.
Kafin ta samu damar magana ya jawota ta manne da jikinsa, dukansu suka sauke ajiyar zuciya, zip ɗin yaja yay sama yana mata magana a cikin kunne.
“Babie R mizan samu?�?.
Yanda yay maganar kamar akwai damuwa a maƙoshinsa ne ya saka Rumana janye jikinta daga nasa ta ɗago ta kallesa.
Murmushi tayi dan duk alamominsa ya nuna mata yanada damuwa, batace komaiba ta ɗora hannunta a ƙirjinsa tana gyara masa wuyan rugarsa da cire wani zaren ɗinki daya maƙale a surfanin, ta koma kan hularsa itama ta gyara mata zama da ƙyau, shidai kallonta yake kawai.
“Zumana kayi ƙyau, sai kace wani sabon ango?�?.
Kaɗan ya murmusa yana ɗora duka tafukan hannunsa a fuskarta, ya matso da goshinsa kan nata yana faɗin, “Gwal ɗina ni angone mana, angon ƙarni Abu Haysam �?.
Murmushi Rumana tayi, ta sumbaci laɓɓansa tana lumshe idanu, tace,
“Hakanefa Zumana, yanzu daga nan sai ina kuma?�?.
Guntun tsaki yayi yana cire goshinsa daga kan nata, “Share kawai babie R�?.
Batace masa komaiba harya ƙarasa inda Haysam ke kwance a babban gadon Ayyah yana barci, an naɗesa cikin kaya masu kauri ruwan hoda, harda showal ɗin da yake ciki, kaɗan ya janye showal ɗin ya sumbaci goshin yaron, “Sadauki na kai baka da aiki sai barci? Har yanzu kaƙi naga idanunka, ko duk jarumtarce?�?.
Dariya Rumana dake kallonsu da saurare tayi, hakanne ya saka Ahmad juyowa yaɗan kalleta.
Ta ɗauke kanta tana faɗin, “Jarumta ko ragwantaka�?.
kafin ya samu bata amsa Ayyah ta shigo ɗakin da kunun da aka damawa Rumana.
Hakan yasashi ɗauke kansa ya maida ga Haysam.
Ayyah tace, “Ɗan albarka ga yaro can Sufyan ya turo ya kiraka�?.
Saida ya sake sumbatar Haysam ya gyara masa rufar kamar yanda ya gani sannan yace, “To Ayyah na, sai na dawo�?.
Addu'a tai masa itama, ya nufi hanyar fita yana amsawa cike dajin daɗi, sai da ya kama labule sannan Rumana tace “ALLAH ya tsare�?.
Juyowa yay ya kalleta, yay mata ƙaramar harara, itakuma tai masa gwalo.
Ida ficewa yay yana murmushi.
___________________________________
Sun iso station ɗin su da baba da baba Ilyasu, ganinsu tsaf-tsaf ya saka akai musu tarbar mutunci.
Sun musu bayanin wadda sukazo fiddawa.
Ogan ya bama ɗan sanda ɗaya umarnin fiddo Samina, sannan aka bama Ahmad inda zai saka hannu.
Ƙinyi yay sai da baba yay masa magana, fuskarsa babu walwala yaja buk din tare da ɗaukar biron da aka ajiye masa, dai-dai nan aka fiddo Samina.
Babu ɗankwali a kanta babu takalmi, tayi wani ziru-ziru ga ƙananun ciwuka da taji lokacin da suke faɗa da Ma'aruff.
Akan Ahmad dake rubutu ta fara sauke idanunta, wani sama numfashinta yayi da ƙyar ta fisgosa, sai maimaita sunansa take cikin zuciya, ya ajiye biron yana tura buk ɗin gaban ɗan sandan tare da yima Samina kallo ɗaya ya ɗauke idanunsa yana sake tamke fuska.
Ƴan sandan sun mata gargaɗi akan ta kiyaye gaba, dan tana dai gani dangin mijinta duk da sunada arziƙin da waya kawai zasu iyayi a fiddata amma sukazo har station ɗin suka fidda ɗansu ita suka barta.
Ita dai kanta a ƙasa, saboda kunya da baƙin cikin Ahmad yanajin sirrinta.
Shiko tamkarma baisan anaiba, ya ɗauke kansa daga garesu baki ɗaya yana danna wayarsa daya ciro a aljihu.
Koda aka sallamesu shine farkon fitowa ma, lokacin da suka fito suma jingine da mashin suka iskesa yana waya da Happy data kirashi.
Zuciyar Samina sai sake tsitstsinkewa take, gaba ɗaya Ahmad ya canja mata a komai, ya rikiɗe ya zama wani hamshaƙin namiji.
Ita dasu baba napep suka shiga, Ahmad da Sufyan kuma suka hau mashin dan daga nan inda suka fito dominsa zasu wuce, su baba kuma su wuce da samina gida.
★★★★★★�?
Tunda suka fito daga Napep ƴan anguwa dake kai kawo jefi-jefi da yara suketa kallon Samina, ta shige gida tana rufe fuska da mayafi.
Da Mudan taci karo a soro ya fito daga sashensu, ya bita da kallon mamaki harta shige sashinsu itama.
Ƙaramar dariya yayi ya ida ficewa yana faɗin, “Ankusa fara wasan kenan�?. dan dama yanajin sanda baba kema Yah Ahmad bayanin zuwa su amso Samina daga station.
Mama gaje da batasan hidimar da akeba ganin Samina kawai tai ta shigo, ta ajiye robar hannunta dake ɗauke da kayan miyar da zata ɗora abincin rana tana kallon Samina.
Ammi ma dake wanki daga ƙofar ɗakinta da kallo tabi Saminar harta shige.
Hakanne ya saka mama gaje jan tsaki tana faɗin, “To kurwarta dai kurr wlhy, wannan kallon ƙurulla har ina�?.
Ammi dai batace komaiba ta cigaba da wankinta, mama gaje na ƙoƙarin bin bayan Samina baba Yusha'u daya shigo gidan ya dakatar da ita a zafafe.
“Ina wannan lalatacciyar? Maza zoki fitarmin daga gida, wlhy su Yayanma su suka fiki da sukaje suka amsoki daga wajen ƴan sandan, ai ni sonai yanda mijin naki da danginsa suka barki acan suma su barki ki ƙare rayuwarki a kulle, ki fito nace ki fitarmin a gida ko�?........
Fitowa Samina tai tana hawaye, dai-dai nan su baba da suka biyo bayan Baba Yusha'u suma suka shigo suna masa magana.
Sai dai sam yaƙi sauraren kowa, ya kafe akan Samina saita bar masa gida.
Wannan ƙaramar hayaniyace ta fargar da sauran jama'ar gidan harma da maƙwafta da katangarsu ke jingine da gidan nasu Ahmad.
Hankalin mama gaje ya tashi saboda jin fallasar da Baba Yusha'u ke musu a bainar Nasi, dan faɗin komai yake babu rufi, su Ayyah duk sun shigo an haɗu anata bashi haƙuri, amma sai sake jerama mama gaje ALLAH ya isa yake akan ɓata masa rayuwar ƴa datai, yakuma tabbatar mata wlhy badan ƴan uwansa da iyayensa da suka hanashiba da tuni ta tsufa a gidansu itama.
Mama gaje fa taji babu mafita sai kawai ta saka kuka, wai Baba Yusha'u dai dama ya shirya cin zarafintane.
Abu dai ya nema yin tsamari har sai da iya ta shigo sashen ta tsawatar sannan.
Baba Hamza kuma yace, Samina ta zauna har sai Ma'aruff yazo sun nuna masa kuskurensa sannan ta koma.
Da wannan aka kashe maganar kowa ya fito, Mama Gaje da Samina suka shige ɗaki ransu a dagule.
“Keko Samina miya kaiki wajen ƴan sanda?�? Mama gaje ta faɗa hankalinta a tashe.
Kuka Samina ta sanya tana kallon mama gaje, ta shiga zayyanema mama gaje duk abinda ya faru, harma abinda basu saniba dangane da shan giya da Ma'aruff keyi.
A matuƙar firgice mama gaje tace, “Samina giya fa?�?.
“Wlhy da gaske nake mama�?.
Kasa magana mama gaje tayi, tasaka hannu bibbiyu ta rabga tagumi kawai tana kallon Samina.
Yaya bintu dake tsaye daga ƙofar ɗaki basu saniba tai murmushi mai ciwo, “Wannan shine abinda na hango miki Samina, ni nasan bai zama lallai ki samu abinda kike hangenba ɗari bisa ɗari kodan girman butulcin da akaima Ahmad, farin ciki shine abin buƙatar ɗiya mace a gidan miji ba dukiyaba, mama kun tafka babban kuskure wlhy, ku........�?
“K binta ki kiyayeni wlhy!!!�?.
Mama gaje ta faɗa a matuƙar tsawace.
“K wace irin wawuyace mara kishin ƴar uwarki, ni nasan yanda Ma'aruff kesan Samina wlhy sai dai idan asiri akai musu, kuma ba kowa bane sai dai wannan annamimin yaron Ahmad ko baƙar dagarcan (Amin su Rumana take nufi), suna baƙin cikin ta fisu ta wuce da saninsu, shine suka ƙulla mata dan tarasa zaman lafiya a gidan aurenta�?.
Murmushi kawai Bintu tayi tana girgiza kai, tace, “Wannan shine ake kira da suna *GUDU DA WAIWAYE....* mama, gashi tun ba'aje ko inaba harya fara kawo muku *mugun zato*, ina Ahmad yaga wani lokacin ma Samina asiri balle Ammi da abinda yake gabanta kawai takeyi, abinda ta zaɓane ALLAH ya bata kawai. Godiya ya kamata kumasa dan a yau ɗinma kuɗinsa ya saka ya fiddota, badan mahaifinsa ba kuma sai dai ta dawwama a hannun ƴan sandan�?.
Tana gama faɗa ta fice abinta tabar musu ɗakin.
____________________________________
Anta ƙananun magana akan wannan al'amari daya faru da Samina, harda masu ƙara gishirima a kai, tana ji tana ganin shigowama sashen su Ahmad taga jariri ya gagareta, saboda ƴan barka masu shige da fici.
Lamarifa ya taru yayma su mama gaje yawa, ga baƙin cikin haihuwar Rumana, ga tashin hankalin abinda ya faru da Samina, ga surutan mutane dake tashi harda abindama ba ayiba.
Sunason fita wajen malaminsu baba Yusha'u yace konan da zaure Samina ta fita inhar ba mijinta yazo gidanba to tabar gidan kenan har abada, itako mama gaje inhar ta fita to abakin aurenta.
Dan randa inna mari tazo barkane yaji suna ƙulla yanda zasuje wajen malam su sanar masa abinda ke faruwa, musamman ma a kan aikin Rumana da basuga ya wani ciba, tunda gata daram ita da jaririn ta, ga ruɗanin daya ɓillo a cikin auren Samina wanda su basu san da shiba.
Ranar da Umm-Ruman ta cika kwana biyar da haihuwa, Samina nada uku a gidan sai kawai akaga su yaya maryam da akwatina guda huɗu set guda kenan, sai kuma babba guda ɗaya kalarsa da ban da ƴan tarkace irin na jarirai.
Tofa, kallo ya koma sama, aka gama shigo da kaya kafin a tattara zuwa sashen su Rumana akai a dire, dan gwaggo da Ayyah harma da baba dama duk sun gani sunkuma san da shirin.
Tun fitar Ahmad ta farko neman kuɗi, yaɗan fara zuwa da kaya yana ajiyewa ɗakin baba acewarsa zai haɗama Rumana lefen da ba'ai mataba, hakan yasa duk zuwan da zaiyi sai yazo da wani abu yaɗan yadda, ranar da suka karɓo Samina fitar da sukai akwatina suka sayo suka kaisu gidan Yaya maryam, dama acan yake tara kayan haihuwa, waɗanda ya tara anan kuma kullum idan zata wuce gida saita ɗauki wasu ta tafi dasu, a haka aka fidda kayan daya tara a ɗakin baba.
Ba wani uban kaya na fariyya Ahmad ya danƙara a akwatunanba, amma dai Alhmdllh ya cancanci yabo, dan kuwa ko maƙiyi yaga wannan lefe dolene ya yaba, ga kuma kayan barka na jariri da kayan ƙamshi na al'ada da iyaye mata kan haɗa Ayyah ta haɗasu rankakakaf, sai ɗan akuya gasashshe na al'ada shima na ƙauri da baba yayi.
Mama gaje na tsakar gida su Sakina suka shiga, Samina kuwa tana wanka.,
Suka sauke akwatina a ƙofar mama gaje saboda aima Ammin Rumana irin kawaicin nan, a baɗini kuwa harda son ƙularwa ga mama gaje da Samina.
Aifa nan dangin Ammi dake gidan suka shiga callara ghuɗa.
Su Yaya Maryam dake tayasu suka shiga musu bayani, Sakina tace, “Waɗan nan kayan barkane na al'ada da kowa ya san wajibine yima mai jego idan ta haihu, musamman ma haihuwar fari, waɗannan akwatina kuwa saƙone daga Ahmad, yace a faɗa muku kayan lefene na Umm-Ruman da baiyiba a baya, ga sunan ayi haƙuri dai babu yawa�?.
A take waje ya sake kacamewa da sabuwar ghuɗa.
Basu jira mama gaje ta fara buɗewa ba, hakan ne ya saka mama gaje da ƙirjinta ke lugude kamar zai fito yin tsaki, ta fara sakin maganganu akan duk barikin dai da za'ai na banzane, dan ko kama ƙafar lefen Samina dai wannan lefe baiyiba.
Babu wanda yabi takanta, dansu ba yawan bane matsalarsu, albarka suke fata, da bajintar da Ahmad ya nuna ba tare da kowa yayi zaton hakanba.
Tuni gida ya kacame, maƙwaftama sunata shigowa ganin kaya.
Samina data fito wanka ta samu ta raɓa ta shige ɗaki tana haɗiyar zuciya.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻. *_40_*
*_GDW_*
...........Haka aka shiga hidimar biki ba'a sakata cikin kowacce sabga, to ganin angonma yafi komai mata wahala a gidan, dan tun randa ya kawo mata invitations ɗinnan bata sake ganin ƙeyarsa ba.
A danginta kuwa babu wanda yaje mata kara, dan mama gaje sun rufe sunƙi sanarma kowa za'aima Samina kishiya, sai a shanun ƴan talla jama'a ke jiyo labarai suna kawoma ƴan gidan gulma.
Yanda bata faɗaba babu wanda yay yunƙurin zuwa balle ya nuna mata yasan ma halin da ake ciki.
Ansha hidima ta alfarma, dan yanzune kam a kaima Ma'aruff auren gata kamar yanda danginsa suke faɗa, ranar asabar bayan kammala gagarumar dinner ɗin da har gidan tv suka nuna aka kawo amarya ɗakinta.
A lokacin Samina tana cikin wani hali, dan kuwa duk taga wannan shagali a tv, yanda Ma'aruff yake rawar ƙafa da washe baki, da yanda danginsa ke ɓarin dukiya kamar ba wahala sukai suka taraba ba'ai koda kwatankwacinsa a nata bikinba, hakanne ya sakata zaman dirshen a kafet tasha kukanta..
Duk yawan ƙawayen data tara babu wanda ya tuna inda take balle yazo, hatta dasu Nafy bata ganiba balle sababbin datai na yanzun.
Har ƴan kawo amarya suka kammala ghuɗe-ghuɗensu da arerewarsu Samina na zaune a wajen ta zuba uban tagumi abin tausayi.
Kafin wani lokaci gidan ya koma yay tsit, tun tana tsammanin shigowar Ma'aruff harma ta fidda rai, dan yanayin shirun da garin yayi sai haushin karnuka ya tabbatar mata dare ya