Showing 18001 words to 21000 words out of 165545 words
daga shi sai best da boxer, baiyi auneba yaji jawaye masu ɗumi nabin kumatunsa.
Wai yau shine akan idonsa yarinyar da ya gama ɗorama buri ta shige motar waninsa ba shiba, bayan yaji a ransa tabbas taga kiran da yay mata a waya taƙi ɗauka.
Gaba ɗaya kansa ya kulle game da Samina, ya rasa wane kalar tunani zaiyi ko zaiji sassauci.
Bai motsa daga wajenba har aka kira sallar zuhur, ya tashi daƙyar ya fice bayan ya saka jallabiya a jikinsa.
Suna idar da salla ɗakin ya sake dawowa ya kwanta, nanma dai tunaninsa ya ɗora daga inda ya tsaya, bai sake fitaba sai da la'asar tayi, an idar da salla ya sake nufo gida, zamansa ke da wuya a bakin katifarsu Sufyan ya shigo ɗakin da sallama.
Hannu ya bashi sukai musabaha, kafin ya zauna a kusa dashi gefen katifar,
“Abokina ba tunani ko ɓacin rai akanta ya kamata ka sakama ranka ba, ɗaukar mataki da gaggawa kafin abun yay nisa shine yafi dacewa da kai, bansan miyyasa a kullum kake maida kanka ragon namiji akan Samina ba, ka riga ka sakema yarinyarne da yawa shiyyasa har take iya kawo maka waɗannan salon rainin wayon tamkar ba kanuwarka ba, ni dai yanzu da zakaji da ka shareta kawai, kaje ka samu su baba da maganar aurenku, gara ko hayar ɗaki ɗayane ka kama, tunda dai gwargwadon iko kana samun taro da kwabon da zaka iya riƙeku koda ba'a samu komai baja-baja ba, kaga saita karasa karatunta a cikin gidanka hankalinka kwance�?.
Sosai shawarar Sufyan taima Ahmad daɗi, ya kuma gamsu da ita ɗari bisa ɗari, godiya yay masa akan hakan, daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa akan maganar yaya maryam, Sufyan ya kara masa shawara game da Samina kuma.
A haka Mudanseer ya shigo ya samesu, gaidasu yayi ya ajiye kayan hannunsa ya fice zuwa cikin gida saboda azabar yunwar da yakeji.
________________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad na zaune a ƙofar ɗakin Ayyah yana buɗa baki, sai dai rabin hankalinsa nakan wayarsa, da alama dai akwai abinda yake tsumayen gani, amma yaƙi ya shigo......
“Ɗan albarka wai bazaka ajiye wayar nan kayi buɗa baki bane?�?.
Murmushi Ahmad yayi yana ajiye wayar gefensa, ya cigaba da cin alalar da Ayyan tai masa dan buɗa bakin, sai dai zuciyarsa sam babu daɗi, yau gaba ɗaya da ɓacin ran SAMINA ya yini a ransa, ya kuma tura mata massege akan ta dawo gida yau ɗinnan sai dai har zuwa yanzun bata shigoba, ya kirata kuma wayar a kashe.
Yana cin abincin yana sauraren hirar ƙannensa dake daga can gefensa a ƙofar ɗakin barcinsu, sai Ayyah da Gwaggo dake a ƙofar ɗakin gwaggon suna cin tuwo suma
Shigowar saƙo a wayar tasane ya sakashi saurin ɗaukarta har jikinsa na rawa, ko da ya buɗe saƙon sai yaga abokinsane Sufiyan yake masa “Please call me�?, numfashi ya ɗan sauke a ɓoye, zuciyarsa duk a cunkushe.
A kullum canji yake sake gani da ga ɗabi'un saminar sa, baisan mike shirin shigoma duniyar jin daɗinsu ba sam? Sai a yaune ya fahimci inda matsalar take ashe.
Haka dai ya gama buɗa bakin zuciya duk babu daɗi, duk ƙaunarsa da alala sai gata yau batai masa wani daɗi ba.
Ruwa ya ɗiba ya ɗan watsama jikinsa, yazo ya shiga ɗakin Ayya ya ɗauki kayan barci ya fita zuwa ɗakinsu na zaure.
Canja kayan yay ya fice waje wajen abokansa. Acan ya iske Sufiyan, sai da ya gaisa da kowa sannan yaja hannun Sufiyan suka koma gefe.
“Sufiy ya akaine? Naga kamin Please call me ne?�?.
Kaɗan Sufyan ya sauke numfashi yana cije baki, “Abokina wlhy akwai matsalane?�?.
“Matsala kuma Sufiy? Akanmi to?�?.
“Wannan banzar yarinyar mana Sha'awa, wai ni zataima rashin mutunci akan ɗan uwanta na legas ɗinnan yazo wajenta?�?.
Cike da mamaki Ahmad yace, “Itama Sha'awar abinda ta daukarma ranta kenan? Wai miyasa zukatan ƴammatan yanzu mafi yawansu sukafi karkata akan kuɗi da mai kuɗine abokina?�?.
“Wlhy kuwa Ahmad, gaskiya bazan iyaba mace ta zauna tana zubamin iskanci, ya isa hakanan, wannan karon na barta har abada...�?
Da sauri Ahmad ya katseshi da faɗin, “Haba Sufyan karkace haka mana, kaimafa kasan Sha'awa na sonka, ɗazunfa kaine ka gama fahimtar dani akan Samina, ƙilama kayi kuskuren fahimtar tane........�?
“Ahmad kuskuren fahimta fa kace? Sam babu wani kuskuren fahimta akan batuna, Please kai daine kake neman kasa fahimtar tawa�?.
“Kaga yi haƙuri abokina, wlhy na fahimceka, yanzu kabar komai a hannuna zan sameta, idan munji dalilinta bashi da muhimmanci sai kawai ka barta, amma nikam wannan abu yana bani mamaki na ƴammatan wannan zamanin, su kawai idan kaga suna kwantarma saurayi kai da nuna tsantsar ƙauna yanada wasu wakilai masu farar fuskane (kuɗi) a banki?, mafi yawancinsu haka halinsu yake, ƙalilanne na gari masu son mutum domin ALLAH, Shin suna mantawa da cewa su waɗan nan masu kudin da rarrafe suka tashi suma?�?.
“Ahmad mubar zancennan, wlhy ƙaramin ɓacin rai kawai yakeyi, ai kai bakace hakaba, domin kuwa kayi sa'a, duk waɗannan banzayen halayyar sam Samina bata dashi, son gaskiya take nuna maka bawai wata abar banza dukiya ba, ko ganin da mukai mata ɗazun sai daga baya na zauna ina nazari akai, maybe ma ba abinda muke tunani bane akanta wlhy, naga rankane ya ɓaci kawai shiyyasa na sake barinka ka huce akan maganar�?.
Ahmad da zancen Sufyan yay masa daɗi yay murmushi, dan yanason yaji ana yabon Saminar sa a koda yaushe.
Cikin abokansu suka koma suka zauna, daga nan fira ta ɓarke a tsakaninsu, duk da dai Ahmad yayi gum, sai maida hankalinsa da yay wajen cigaba da neman layin Samina.
Amma har lokacin kwanciya yay kowa yay yunƙurin tafiya gidansu bai sameta ba, a wannan daren da ƴar damuwa ya kwanta, garama jiya daga baya taɗan sanyaya masa ransa..............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(7)*
.............A ɓangaren Samina kuwa shopping Ma'aruff ya fita da ita, sun shiga cikin shoprite inda Samina ta rikice, dan bata taɓa zuwa ba, sai dai tanajin labari wajen su Nafy, tuni kanta ya nema kwancewa, dan sai tagama kamar ba'a kano take ba.
Ma'aruff dake taku ɗai-ɗai cikin ƙasaita irinta masu ji da dukiya ya bama Samina umarnin ta zaɓi duk abinda takeso.
Sam bata cutar da kantaba, tako ware ƙwanji tana lodar kaya iya son ranta, shiko yana biye da ita yana kallo tamkar ba kuɗinsa zai biya da kayan ba.
Ta ɗauki kaya sosai sukaje wajen biya, ATM ɗinsa kawai ya miƙa ya koma gefe, aka gama cirewa aka saka musu a leda, ɗaya daga yaron shagon ya ɗauka ya bisu mota dashi.
Daga wajenma ba gida ya kaitaba, wani gidan gona sukaje, wanda take ƙyautata zaton yana da alaƙa dashi, wajen yayi ƙyau, dan an gyarashi na musamman domin hutawa.
A kujeru suka zauna, inda Ma'aruff da kansa ya fiddo musu ice-cream ɗin daya siya musu da gashashshen kaza.
Da farko dai Samina taɗan noƙe baza taciba, wai ita kunya, amma da taga zataima kanta buƙulu tuni ta fara kai lauma harma tana neman zarta Ma'aruff ɗin.
Shi abunma dariya yaso bashi, amma sai ya fuske abinsa.
Sun ɗan taɓa hira, inda yayta mata tambayoyi a fakaice game da kanta, itako taita basa amsa kanta tsaye.
Kusan awa biyu suna wajen, kafin yace ta tashi ya kaita wajen bikin.
Sai da suka biya ta gida ta ajiye shopping ɗin da yay mata, sannan ya kaita wajen bikin inda su Nafy sukaita ihun ganinta, bai tsayaba yaja motarsa yay gaba ya barta anan tunda bashi da alaƙa da bikin nasu.
Yauma sun raƙwashe sun ƙwalle abinsu, ansha hidima sosai, dan sosai Samina ta manta da wani Ahmad, acan aka kusa kwana wajen dinner ɗin, sai gabannin asuba suka tashi, gidan amarya aka kaisu suka karasa kwana.
Samina bata tashi ganin massege ɗin Ahmad ba sai da safe.
Dukda taji tsoro sai da ta taɓe baki, tana mamakin yanda yake bata umarni tamkar wani mijinta.
Kashe wayar tayi gaba ɗaya dan karma ya kirata, basu bar gidan amaryaba kuma sai yamma da akayi buɗar kai sannan suka wuce gida.
Koda Samina ta dawo gidansu inna mari bata zaunaba, kayanta ta haɗa waje ɗaya bayan ta ɗibar musu abin ci a cikin kayan da Ma'aruff ya saya mata, ana sallar isha'i ta baro anguwar zuwa anguwarsu..
_____________________________
Ahmad da bai samu barci sosaiba a daren jiya yau sai ya daɗe kwance bayan sun dawo sallar asuba.
Har takai Ayyah ta fara cigiyarsa saboda ya saba shigowa shi da Mudanseer da safe gaidasu, amma yau har kusan sha ɗaya babushi babu alamarsa, Mudan ne kawai ya shigo ya gaidasu da safen ma.
Ayyah ta aika Zainab auta ɗakin su Ahmad dan taga ko lafiya, dan tata jiran ko Mudan zai shigo ko Abu, amma babu wanda ya shigo a cikinsu.
Zainab tayi sallama kusan huɗu babu amsa, dan haka ta tura ƙofar cikin sanɗa ta leƙa kanta, kwance ta hango Ahmad a katifarsu ya lulluɓa da bargo har saman kansa, sai fuskarsa daya bari a buɗe kawai.
Komawa tai da baya ta sake rufe masa ƙofar, taje ta sanarma Ayyah.
Gwaggo na jinsu amma batace komaiba, sai Ayyah dataketa ƙorafi akan kodai bayajin daɗine, ganin Gwaggo taƙi saka baki yasata jan zani ta saka a kanta ta fita zuwa soron.
Koda ta shigo ɗakin kaɗan taja bargon daga saman kansa ta ɗora yatsunta a goshinsa, zafi rau kansa, hakanne yasata fahimtar bayajin daɗi kenan.
Sanyin yatsunta da yaji a kansane ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar.
Ganin Ayyah ce ya sashi ƙoƙarin tashi zaune, da sauri tace,
“A'a, kaga yi kwanciyarka ɗan albarka, dama baka da lafiya shine ko Mudan baizo ya sanar mana ba?�?.
Cikin magana da ƙyar Ahmad yace, “Ciwon kaine kawai Ayyah, Mudan kuma baisanma bana jin daɗiba�?.
“Ai ciwon kai ya wuce ace masa kawai ɗan albarka, sannu kaji, bara na saka maka ruwan wanka a wuta, saika daure ka tashi ka watsa ruwan ka karya kumalo sai kasha magani�?.
Fuska ya ɓata sosai, dan bayason magani sam, sanin hakane yasa Ayyah cigaba da lallashinsa har ya yarda zai watsa ruwan.
Ayyah ta fito a farko, shikuma yana bayanta dafe da kai suka fito daga ɗakin, da Samina dake fitowa daga cikin gida sukaci karo, Ahmad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa.
Sai Ayyah ce kawai ta amsawa Samina gaisuwar da take yimata.
Ayyah tace, “Ɗiyata ashe kin dawo?�?.
Kan Samina a ƙasa tace, “Eh Ayyah, jiya da daddare na dawo�?.
“ALLAH sarki, to yaya jikin Inna Mari ɗin?�?.
Sai da Samina ta saci kallon Ahmad da ya raɓasu zai wuce tankar bai santaba sannan ta bama Ayyah amsa da “Jikinta Alhmdllh, taji sauƙi shiyyasama na taho, amma Ayyah yah Ahmad kuwa lafiya yake?�?.
Cikin murmushi Ayyah tace, “ALLAH ya ƙara lafiya to, Ɗan albarka kuwa bayajin daɗi, nima yanzu nazo dubashi naga bashi da lafiya�?.
Muryar Samina na rawa ta shiga jero masa addu'ar samun lafiya, Ayyah kuwa na amsawa cikin jin daɗi.
Ahmad ko koda ya wucesu jiyake tamkar ya shake wuyan Samina saboda kishin dake cin ransa, ya gaida Gwaggo dake hada-hadar ɗora girkin rana.
Amsawa tai cikin satar kallonsa, dan muryarsa ta tabbatar mata bayajin daɗi, ta ɗauke kanta tana cewa, “Baka da lafiyane?�?.
Sai da ya kalleta, murya a sarƙe yace, “Kaina kemin ciwo�?.
“ALLAH ya sawwake�? ta faɗa tana shigewa ɗakin da suke ajiye kayan abinci.
A saman laɓɓa ya amsa yana binta da kallo, ya ɗan lumshe idanunsa yana jingina da katangar da aka zagaye sashen nasu da ita.
A haka Ayyah ta shigo ta sameshi
“A'a, tsayuwar mi kakeyi kuma anan ɗan albarka?�?.
Idanunsa ya buɗe a kanta yana sauke numfashi da buso iskar bakinsa, yace, “Babu komai Ayyah �?.
“To jeka zauna na haɗa maka ruwan saika watsa�?.
Umarninta yabi, yaje ya zauna a kujerarta dake ƙofar ɗaki ajiye.
Bayan ta haɗa ruwan Zainab tazo takai masa banɗaki.
______________________________
“Wai lafiya na ganki a sukuku? Bayan kuma ba haka kika fitaba�?.
Samina ta ajiye ledar omon data siyoma Mama gaje tana faɗin, “Babu komai mama, Yah Ahmad ne baida lafiya�?.
Shiru Mama gaje tayi bata tankaba.
Kishiyar mama gaje mahaifiyar Umm-Rumana da suke kira da Amma na daga bakin murhu tana haɗa wuta, tana jin uwar da ƴar, sai dai batayi ko tariba, saboda tun a daren jiya ta jiyo kalaman Mama gaje akan Ahmad tasan akwai matsala, dan agaban idonta Samina ta shigo da ledoji niƙi-niƙi a hannu, daga baya ta jiyo murnar da Mama gajen takeyi daga cikin ɗaki, har tana kushe ƙokarin Ahmad duk da wahalar dayay da Samina a baya, koma yake kanyi har yanzun.
Saminar ma batace komaiba ta juya ta zata fita, da sauri mama gaje tace, “Ina kuma zakije? Bayan nace ki wanke min zanin gadoncan dana jiƙa tun jiya�?.
“Mama ina zuwa�? Samina ta faɗa ba tare da ta saurari mamar tataba ta fice da hanzari.
Kanta tsaye sashen su Ahmad ta nufa, ta iske Gwaggo a tsakar gidan tanata aikinta na abinci, sai Sadiya dake taimaka mata da wasu ayyukan.
Gaisheta tayi, Gwaggo ta amsa da fara'a tana tambayarta yaushe ta dawo?.
Faɗa mata tayi jiya cikin jin nauyinta, Sadiya dake dariya ganin yanda Gwaggo da Samina kejin nauyin juna itama ta gaisheta.
Kafarɗarta Samina taɗan buga tana faɗin, “Baki da kunya yarinyarnan, ina Yah Ahmad yake? Koya koma ɗakinsu?�?.
“A'a yana ɗakin Ayyah, sun tsareshi ita da Iya yana shan magani, kinsan maigidan naki da magani tamkar jariri yake�?.
Dariya kawai Samina tayi, saboda Gwaggo dake a wajen bata iya bama Sadiya amsaba..
Samina ta leƙa ɗakinsu Sadiya, dan taga takalman Fa'iza, ciki ta shiga da sallama, Umm-Rumana da Fa'iza dake Assignment na islamiyya duk suka kalleta.
Da yake ta girmesu, kuma suna kallonta matsayin wadda yayansu zai aura sai suke bata girma sosai, gaisheta sukai, ta amsa tana ɓata fuska saboda ganin Rumana a wajen, dan mahaifiyarsu ta riga ta cusa musu ƙin kannenn nasu da suke uba ɗaya sosai.
Umm-Rumana ma saita maida hankalinta ga Assignment ɗin bata saka musu baki cikin hirarsu, dan tasan ƙaramin aikin