Showing 69001 words to 72000 words out of 165545 words
Dariya sosai Rumana takeyi, Abu ya fice shima yana tasa.
Zama Rumana ta gyara taci kazarta tai nak tana lumshe idanu, ta ɗora da maltinar da aka sakko mai sanyi kunnuwanta a mimmiƙewa sama, rabonta dacin nama harta manta lokacin, sai taji wani ƙaunar yaya Ahmad na girmama a ranta, sauran ta ajiye gefe tai kwanciyarta a tabarma kamar yanda ya buƙata.
________________________________
A gidan su Ahmad kam bikin dai daga danginsu ƴan shema babu wani armashi, dan inna marwa ce kawai da iyalanta sai sukazo, sai maza da zasuzo ɗaurin aure gobe, dangin mama gaje ne kawai suketa zuwa, waɗanda da yawansu kasan da biyune, dan sai habaici suke kala-kala, amma babu wanda ya kulasu hatta da Ammin su Rumana.
Koda Ahmad yazo gidan saida ya shiga har sashen ya gaida Ammin su Rumanan, aiko dangin mama gaje da ƙawayen Samina da ita kanta saminar tamkar zasu cinyesa da kallo, kowa ya gansa yansan hankalinsa a kwance yake, gashi yau shar yake da ƙyallin angwanci na gaske, fuskarsa ta sake yin wasai abin son kallon kowa ba tare da kaso ya gusa daga gareka ba.
Shikam koma kallon basu ishesa ba ya fito zuwa sashensu, dan sashen su iya ya fara shiga dama suka gaisa.
Bayan ya gaisa dasu Gwaggo da Ayyah su Fa'iza sukazo duk suka gaishesa, sai satar kallonsa sukeyi saboda ƙyawun da yay musu, su baba dai duk sun fice wajen nema.
Ɗakin Ayyah ya shiga suka buɗe kayan da yazo dasu aka fiddama kowa tsarabarsa a gidan gwargwadon bajintar da ya nuna ta ƙarfin aljihunsa.
Amma abin birgewa kowa aka bamawa sai murna yake da nuna jin daɗinsa, sunata jera masa godiya.
Koda ya shiga ɗakin gwaggo ya ajiye mata kuɗi sai cewa tai “Ita Yaya ka batane�?.
Kasa haƙuri yay saida ya kalleta, yasan Ayyah ta wuce gaban raini a garesa, kuma duk abinda ya siya musu tare ya sai musu, kuɗinma ya bata itama, amma saiya ɗan ƙarama Gwaggo wani abu matsayinta na mahaifiya, duk da yasan halinta dakamar wahala ta amsa, dan itama Ayyah idan su yaya maryam sukai mata alkairi inhar babu na Gwaggo bata amsa, sai dai idan ta raba musu dai-dai........
“Magana nake maka ka zauna kana kallona�?.
Murmushi yayi yana duƙar da kansa, yace, “Eh Gwaggo na bata�?.
“To ALLAH ya saka da alkairi, ya ƙara buɗi na alkairi�?.
“Amin ya rabbi�? ya faɗa cikin jin daɗi sosai.
Daga haka sake dawowa yay wajen abokansa ya basu tasu tsarabar, yaɗan zauna suka taɓa hira bayan sun dawo sallar zuhur, ya jima sosai a wajen suna shan shafta irin tasu ta abokan da suka shaƙu tun ƙuruciya kafin ya tashi shi da Sufyan su nufi shago dan yanason yanka ɗinkin Rumana ya samu kafin dare ya haɗa mata.
Yana aikinsa suna hira da bama juna labarin yaushe gamo...........✍�?
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏼: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(23)*
............Kusan ƙarfe biyar na yamma Rumana na bakin rijiya tana ɗibar ruwa Ahmad ya shigo gidan da sallama.
Ita da Kausar dake wanke-wanke a wajen ne suka amsa, maman Ama dake kicin tai zumut ta fito sai kace mai jira dama.
Rumana bata yarda ta kallesa ba tace, “Sannu da dawowa�?.
Ahmad da ya ja birki a gabanta ya amsa yana binta da kallo ƙasa-ƙasa, ko damuwa dasu Kausar baiyiba.
Ledar hannunsa Rumana ta miƙa hannu zata amsa, ya riƙe bai bataba, sai ranƙwafowa da yay wajen kunnenta yana magana ƙasa-ƙasa,
“Sai kin kalleni tukkuna ko kuma na ɗauke ki gaban ƴan sa idon nan har ɗaki�?.
Babu shiri Rumana ta kallesa cikin zaro idanu da mamakinsa.
Gira ɗaya ya ɗaga mata yana kashe ido murmushi shimfiɗe saman fuskarsa.
Ai da ɗan gudu Rumana tabar wajen itama tana murmushi.
Dariya ta bama Ahmad, dan haka yayi kaɗan har haƙoransa na bayyana, “Yarinya idan na ɗaukar miki ruwan nan akwai tara�?. ‘Ya faɗa daɗan ƙarfi yanda Umm-Ruman dasu maman Ama da ke hangame da bakuna duk suka iya jinsa�?.
Ruwan ya ɗauka ya nufi ƙofar ɗakinsu har sannan baibar murmushinba, yayi kuma tamkar baisan dasu Kausar a tsakar gidanba.
“Sannu barewa�? ya faɗa yana ajiye ledar hannunsa idonsa akan Rumana data kawo masa ruwa.
“Yaya barewa kuma?�? tai maganar a ɗan shagwaɓa.
Haɗawa yay da hannunta da ruwan ya riƙe yana tsareta da idanunsa masu hasken tsiya, musamman ma yau da yake tare da farin ciki babu sirkin komai a cikinsu, har wani ƙyalli sukeyi, “Eh mana, tunda kin gudo kin barni da waɗancan matan gidan naku masu shegen sa ido�?.
Rumana tace, “Yaya sune basu da aikinyi ai, ni basa gabana balle halinsu�?.
“Da kyau Babyna haka nake sonki, kizama maiyin rayuwa dan kanki badan wani shashasha ba, ashe dai kema A ce�?.
Kauda kai Rumana tai gefe tana dariya, shi ba'ace masa A ba sai ita.
Hannun nata da ruwan ya haɗa yakai bakinsa, sai da yasha ruwan sosai ya janye yana sauke numfashi.
Tausayinsa ya kama Rumana, dan ta lura dama ƙishin yakeji, kofin ta ajiye ƙasa ta juya zata fita yace, “Zo mana�?.
Dawowa tai da baya, zata durƙusa gabansa ya riƙota ya zaunar kusa dashi.
“Yaya jikin naki?�?.
Ƙasa tai da kanta tana murmushi da wasa da yatsun hannunta, “Yaya babu wata damuwa, komai Alhmdllh�?.
“Da gaske?�?. ‘Yay maganar ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa�?.
Yanda yayin sai da tsigar jikin Rumana ya tashi kuwa, ta ɗaga masa kanta kawai dan ta kasa magana.
Hancinta yaja kaɗan yana faɗin, “Ashe matar tawa ba ragguwa bace�?.
Yanda yay maganarne da jan hancin nata ya saka Umm-Ruman ƙyalƙyalewa da dariya tana rufe fuska. Shima murmushi yayi, dan sosai yakeson ya ganta cikin farinciki, baya ƙaunar ganinta a takuren nan sam......
Ita ko yanda yau ya sake mata sai takejinta daban, tanaji a ranta ashe itama dai mace ce, ba kamar yanda su maman Ama ke nuna mata sun fita ba........
Ganin tayi shiru Ahmad ya kamo hannunta yana faɗin, “Tunanin mi kuma?�?.
“Ba komai Yaya, dama cazan miza'a dafa�?.
“Babie R waya faɗa miki amarya mai martaba irinki na girki a wannan ranar? Ai sai kinyi sati kina hutawarki, hidimata kawai zakikeyi�?.
“Babie R�? ta maimaita sunan a zuciyarta, sai kuma tai guntun murmushi, shima Ahmad dake kallonta murmushi yayi yana lumshe idanu.
A waje kuwa tunda su Rumana suka shige Kausar data rakasu da muguwar harara tace,
“Hum sabon sallo wai tusar liman bayan sallame salla�?.
tai maganar cikin hura hanci.
Maman Ama ta tare numfashinta da faɗin, “Ai wannan ya wuce sabon sallo sai dai bariki, shikuma a neman kuɗin abinda ya ƙaro ilimi kenan?�?.
Kausar ta ajiye sosan da take wanke-wanke ta miƙe da ƙyar saboda ciki tana jan tsaki, “bokon za'a nuna mana a yanzu, aiko bazamu ɗauki ƙananun iskanciba, sai dai in gaba zasu ƙara sayi a wani gidan amma ba nanba�?.
“Kausar faɗi ki ƙara da wayyo, dan baza'a lalata mana yara ba kuwa da watsewa�?.
Su dai kaɗai suke banbamin hassadarsu, Rumana ma batasan sunaiba, tana can cikin sabon shauƙi da yayanta da a yau yazo mata da sabon salon sabuwar rayuwa mai tsafta da riƙe zuciya.
Ahmad kuma bai barta ta sake ko leƙo waje ba har sai da aka kira sallar magriba ne ya fito riƙe da buta, a gaban idonsu yay Alwala, Umm-Ruman ta fito ta amshi butar, koda ya bata saiya matsa ya sumbaci gefen kuncinta na dama yana faɗin, “Saina dawo babie na�?.
Duk da kunya ta gama rufe Rumana haka ta daure saboda ganin yanda aka zubo musu idanu, itama cikin sanyin murya tace, “ALLAH ya tsaremin yayana�?.
Fita yay yana murmushi, itako ta shige bayi abinta batako kalli sashen su Kausar da suka sake cika da baƙin cikiba.
Koda ta fito kowacce ta shige ɗakinta, Rumana tai dariya a zuciyarta da faɗin, lallai aiki ya sameku.
★★★★★★
Sai da akai isha'i ya dawo gidan, yazo musu da abinda zasuci, sannu Rumana tai masa, ya amsa yana zama a tabarmar dake shinfiɗe yana faɗin,
“ALLAH yasa da ruwan zafin wanka a gidan nan?�?.
“Eh akwai, a zuba ne?�?.
“Eh to barsa naci abinci first�?.
Tace, “to�?.
Tare sukaci suka ƙoshi, duk da dai Rumana najin kunya, shiko ko'a jikinsa kai tsaye yake komansa babu wani risini, sai yanzun take sake yarda da maganar mutane dake faɗin mutum mai shiru-shiru baida sauƙi idan yaso abu, duk da ba koda yaushe ya cika fara'a ba bata damuba, dan itama ba fara'arce da itaba.
Ruwan wanka ta haɗa masa ta tafi kaiwa, ta juyo zata fito sukaci karo dashi a ƙofar bayin, tsare hanyar yay ya hanata fita, cikin dauriya tace, “Yaya ga ruwan nan�?.
“Na gani ai�? ya faɗa yana jan hannunta, ya tura ƙofar bayin.
Da sauri tace, “Yay...�?
“Shiii bansan surutu�? yay maganar babu wasa a fuskarsa.
Dole taja bakinta ta kulle, tanaji tana gani ya cire mata kaya kamar yanda shima ya cire jallabiyar da ya sako kawai a jikinsa, babu shiri Rumana ta rufe idanu ruf, jikinta har tsuma yake saboda tsagwaron kunyar data mamayeta, mamakinsa ne ke sake girmama a ranta, wai dama haka Yaya Ahmad ɗinnan yake?.
Haka akai wannan wanka babu wani sakewa daga Umm-Rumana, suka fito yana riƙe da kayanta ita kuma botikin wankan.
A yanzun kam taji daɗi da babu ko ɗaya daga matan gidansu a waje, sai dai bata saniba mijin maman Ama ya gansu, jikinsa kuwa har ɓari yake wajen zuwa ya bama matarsa labarin abinda ya gani.
Lokacin da take leƙensu ta Window Ahmad na tsaye yana brush a wajen, ga iskar hadari data fara kaɗawa, Rumana ma fitowa tai domin yin brush ɗin, cikin zuciyarta tanajin daɗin canjawar yayanta, dama tasan tun can da shi mai tsaftane, ruɗanin Samina kawai daya sakama ransane ya nema susutar dashi.
Tana kammala alwalar barci isaka mai ƙarfi ta taso, cak Ahmad ya ɗauketa ita da butar yay ɗaki dasu suna dariya saboda tsorata da tayi wai catake iskarce tai sama da ita.
Kausar dake ƙoƙarin rufe ɗaki dan yau mijinta a gidan Uwargida yake tace, “Watsatstsu kawai�? Tana jan tsaki.
Ahmad kam sai da ya dire Rumana a tsakkiyar ɗakin sannan ya juya ya rufe musu nasu ɗakin.
Ko a wajen shirin barcinma dai Rumana nata muƙu-muƙu, a zuciyarta tana ƙunƙuni akan figaggar rigar da Ahmad ya ciro cikin kayansa ya bata wai ta saka, dan ƙyau rigar tayi ƙyau, sai dai dole kaji kunyar sakata a gaban wanda bake matuƙar ganin girma.
Kodata saci kallonsa sai taga ko'a kwalar rigarsa, shi boxer ma kawai ya saka ya haye gado a hakansa ya kwanta yana kallonta, dan yace idan ta gama tazo gabansa yaga yanda rigar tai mata.
Ita dai tasan inhar a haka za'a cigaba ta bani da Yah Ahmad a gidannan, tunda ta lura shi babu ruwansa da kawaici agaban kowa, duk abinda yazo masa a rai shi yakeyi.
Dole tabi umarninsa dan babu wasan jayayya a tsakaninsu, shiko ya ware ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, daga ƙarshe yajawota ta faɗo jikinsa ya mirgina tsakkiyar gadon da ita yana sauke mata tagwayen kisses.
_________________________
Ɓan garen Samina kuwa sosai ganin Ahmad ya zauna mata a rai, duk da ƙoƙarin turesa da take a rai hakan ya gagara, yau daren ɗaurin aurenta da Ma'aruff amma Ahmad yazo ya cunkushe dukkan tunaninta, koda sukaje wajen party ɗin da suka shirya iyakar su ƙawaye da abokansa kasa sakewa tai, duk da shima Ma'aruff ɗin ta lura tunda aka fara hidimar bikin nan yaketa wani ɗaɗɗaure mata, abinda yasa batabi takansa ba saboda duk kuɗin data buƙata bata yake, abinda kawai ta kawo a ranta rashin son auren nasu da Mahaifiyarsa ta nuna ƙuru-kuru ne, dukda yana ƙoƙarin son ganin bata fahimtaba.
A yau kuma asabar aka wayi gari safiyar ɗaurin aure, gidan nasu ya cika saboda isowar ƴan shema, ga kuma dangin mama gaje na nan cikin gari da ƙawayenta sun ƙaru.
Bakajin komai sai ƙamshin girki da hayaniyar data cika gidan, dan girke-girke ake na garari, su dai su baba iyakar ƙarfinsu suka bada, amma mama gaje tace sunfi ƙarfin dafa wannan abincin a bikinsu, gefe ta ajiye kayan dasu baban suka bada ta fiddo tasu sayayyar, dama ta raba wasu ayyukan gidajen ƙawayenta.
★★★★�?
Kusan sha ɗaya na safe su Kausar ana tsakar gida ana sana'ar ta gulma, wata maƙociyarsu maman Aysha ta shigo suna mata gulmar Rumana sai ga Rumana da Ahmad sun fito cikin gayun daya nema zauta zukatansu.
Rumana na sanye da les ruwan makuba daya haska choco ɗin fatarta, an masa kwalliya da kalar ruwan zuma kaɗan, gashi Ahmad yay mata ɗinkin daya zauna mata sosai a jiki tamkar irin matan manyan nan dake ji da hutu, tasha awarwarayenta da sarƙa masu ƙyau da tsari, tundaga kan takalma zuwa mayafi da bag duk sabbine, Ahmad ma na sanye da sabuwar shadda ruwan zuma sai maiƙo take, ko angon sai dai ya nuna masa tsadar kaya amma ba tsarin kwalliya ba, ƙamshin khumran da Rumana ta shafa da turaren Ahmad ɗin sun gauraye sun bada wani ƙamshi mai tsayama maƙiyi a maƙoshi.
Yana riƙe da bag ɗin Rumanan a hannunsa sai leda mai ɗan girma baƙa itama, ta rufe ɗakin ta juyo suka haɗa ido suna sakarma juna lallausan murmushi, ido ya kashe mata ita kuma taɗan murguɗa masa baki.
“Ni ko?�?. Ya faɗa yana matsota.
Baya taja tana sassanyar dariya da gyara mayafinta, “Yi haƙuri ba kaiba�? itama ta faɗa a hankalin.
Ƴar ƙwafa yay ya nufi hanyar fita riƙe da bag ɗin da ledar ba tare daya bataba.
Ita kuma ta ƙarasa gasu maman Ama tana faɗa musu ta tafi wajen biki sai sun ƙaraso suma.
Da ƙyar suka iya amsa mata su duka har maman Aysha ɗin, ta kaɗa kanta ta bi mijinta suka rakata da harara.
Ba ƙaramin tsaya musu a rai wankan Umm-Ruman yayiba, dan ko makaho ya laluba yasan sunyi ƙyau sosai, kamar sune akema bikin.
A soro ta iske Ahmad tsaye yana jiranta, ya miƙa mata bag ɗinta, amsa tayi tana cewa, “Thanks yayana�?.
Baice komaiba sai kallo da yake binta dashi, shi kansa ganin matar tasa yake kamar ba itaba, dan kuwa ya kuma tabbatarwa jikin Umm-Ruman nason abu mai ƙyau, kamar yanda mutane ke faɗa akansa shima.
Cikin katse masa tunani ta miƙa hannu zata amshi ledar hannunsa, saiya janye yana girgiza mata kai, ya nuna mata hanya yana faɗin, “Ke kanki badan kar ace na cika rawar ƙafaba da ɗaukarki zanyi bazakisha wahala ba�?.
Gaba Rumana tai da sauri tana murmushi, yayanta wlhy yafi mijin novel ɗin da Samina ta tafka kuskure akan nemansa.
Duk inda suka gitta kallonsu akeyi, hakan kuma saiya zafi Ahmad a zuciya, ya tsaida musu napep suka shiga yana