Showing 9001 words to 12000 words out of 165545 words
dake riƙe dashi a ɗakinta data amsa itama daga cikin ɗakinta.
Ya gaida Gwaggo data gama zuba ruwan harta ɗora a tiren data shirya abincin babansu tana shirin ɗauka zuwa ɗakinsa, sau ɗaya ta amsa ta ɗauki tiren tai gaba abinta, yaɗan bita da kallo yana kauda kansa a lokaci ɗaya.....
Ayyah dake fitowa ta katsesa da faɗin, “Ɗan albarka ka dawo?�?.
Murmushi yay mata yana ƙarasawa gabanta da cewa, “Eh Ayyah na, ina yini?�?.
“Lafiya lau ɗan albarka, kaga tashi ga abincinka nan yau miyarka nasaka akai dole a gidannan, maza kaci karya huce, ga manshanu nan dana soya maka ɗazun�?.
Cikin faɗaɗa fara'arsa ya miƙe yana faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi Ayyah na, ya jiƙan malam ya ƙara muku nisan kwana da lafiya�?.
Amin ta faɗa ita da ƙannensa.
Baba dake daga can ɗakinsa duk suna jinsu shi da gwaggo, ba yaune suka fara ganin hakanba, dan soyayyar Ayyah da Ahmad ALLAH ne kawai yasan iyakarta, amma ba mutumba, inhar ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba itace ta haifesaba.
Saman tabarmar da ƙanwarsa Sadiya ta shinfiɗa masa ya zauna, tuwone na jar masara dayaji dahuwa ta ma'iya, sai miyar tafasa da akayita da gyaɗa sai ƙamshi takeyi, ya buɗe kwanon langa ɗan ƙarami da manshanun ke a ciki ya zuba, tare da barbaɗa yajin daddawa da shikuma ke a robar cingam.
Laumar farko daya kai ya lumshe idanu saboda daɗin da miyar tayi, Zainab dake ajiye masa ruwa tai ƴar dariya ciki-ciki, “Yah Ahmad kaji miyar ta haɗu ko?�?.
Idanunsa ya buɗe ya ɗaga mata kai kawai batare da yace komaiba.
Ayyah dake ƙoƙarin kunna redio ɗinta tai saurin faɗin, “To akku, ki tashi masa akai yaci abincinsa cikin salama�?.
Baki Zainab ta kumbura tana barin wajen, hakan yay dai-dai da shigowar Mudanseer ƙanin Ahmad ɗin.
Sallama yay suka amsa, ya ajiye ledar hannunsa gaban Ayyah yana cewa, “Ayyah gashi nan inji Yaya Maryama, tace gobe insha ALLAHU zama tazo gidan�?.
“Karma tazo�? Ayyah ta faɗa rai a jagule.
Ɗago ido Ahmad yay ya kalli Ayyahn, kafin ya maida kan Mudanseer dake ƙoƙarin zama kusa dashi.
“Miya faru kuma da Yaya Maryaman?�?.
“Yaya abinda kasani kullumne dai, faɗa suka sakeyi da kishiyarta shikuma jakin ya daki yaya maryama ɗin, amma sai batazo ta faɗaba tai shiru, sai ɗazunne Inna Haule tazo da zancen gidannan�?.
Shiru Ahmad yay kamar bazai tankaba, ya tsame hannunsa daga abincin da yakeci yana ture kwanon silbar gefe, miƙewa yake shirin yi Ayyah tace,
“Ɗan albarka dama ka zauna kaci abincinka, itafa ta zaɓama kanta wannan rayuwar, mizaisa ku zauna kuna ɓata ranku a banza, maza koma ka zauna ka karasa ci�?.
Komawa yay ya zauna, danba tarbiyyarsu bace jayayya da maganar manyansu, Mudanseer ya ɗauki ruwan dake gaban Ahmad yasha tare da wanke hannunsa, cikin kwantar da murya yace, “Yah Ahmad babu tayine? Bayan ga ƙamshin manshanu inaji ya cikan hanci ɗan gatan Ayyah�?.
Hararsa Ahmad yayi, amma baice komaiba, hakanne ya saka Mudanseer ɗin yin murmushi ya saka hannu suka cigaba dacin tuwon, wanda a yanzu Sam Ahmad baya wani ci sosai saboda damuwar halin da ƴar uwarsa take ciki................✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(4)*
.............Har suka kammala babu wanda ya sake magana, Ayyah natajin redionta, su Zainab kuma na Assignment ɗin makaranta.
Ahmad ne ya fara tashi, bayan ya wanke hannu ya shiga ɗakin Ayyah, kusan mintuna biyar sai gashi ya fito hannunsa ɗauke da ƙananun kaya, dukda ya zama saurayi har yanzu kayansa na ɗakin, dukda kuwa sunada nasu ɗakin a ƙofar gida, takalman daya fita dasu ya ziro hannu ya ɗauka ya maidasu cikin ɗakin, sannan ya saka silifas ɗinsa dake gefe a wanke.
Ficewa yay daga gidan batare daya cewa kowa uffanba.
Ayyah taɗan rage sautin redio ɗinta tana kallon Mudanseer dake kwashe kayan da sukaci abincin.
“Mudan banso kayi maganar yarinyarnan gaban ɗan albarka ba, yanzun nan saiya saka abun a ransa kasandai halinsa�?.
“Wlhy nima Ayyah sai bayan na faɗa na gane nayi kuskure, dan sai sauke ajiyar zuciya yake�?.
Ayyah tai shiru cikin damuwa.
Ahmad kuwa yana fita ɗakinsu dake a soro na farkon fita daga gidan ya shiga, ya canja kayansa kafin ya ciro wayarsa da screen ɗin yay rugu-rugu saboda azabar lalacewa yashiga neman Number Samina, harta yanke ba'a ɗagaba, ya sake kira a karo na biyu nanma babu amsa.
Bai gajiyaba ya cigaba da kira, sai da yay mata kira na takwas ne ta ɗaga kamar a fusace.
Sautin kiɗan daya jiyo yana tashine yasakashi saurin faɗin, “Wai Samina kina nufin har yanzu baku koma gida bane?�?.
Guntun tsaki ta saki yanda bazai jiba, daga can tana murguɗa baki da harar wayar, “Ai yanzu zamu tafi�? ta faɗa a cinkin sanyin murya dan tsabar munafunci.
Kansa ya dafe yana gyara zama akan yololuwar katifar barcinsu, “Haba Samina, kinsan kuwa ƙarfe nawa yanzu? A matsayinki na mace ace kina waje har kusan sha ɗayan dare? Kina nufin da anan gidan kike zakikai wannan lokacin baki dawo bane? Koma shiyyasa kika tafi can ɗin danki samu lasisin yin yanda kikeso?!!�?. Ya ƙare maganar a tsawace.
Sosai ta firgita, jikinta na ɓari cikin in ina ta shiga fadin, “To yaya amma kuma ni ba wani abu nakeyi mara ƙyau ba fa, Nifa wlhy wannan bin ƙoƙwanton da abokanka suka koya maka bana sonshi, ni dai subar haɗani dakai gaskiya, ahaka kake tunanin zamuyi aure babu yarda a tsakaninmu?�?.
Leɓensa na ƙasa yaɗan ciza yana cewa, “K banason iskancifa, ni kike faɗama wannan banzar maganar...?�?
Batama bari ya rufe bakinsaba ta katse wayar ta koma cikin rawa.
Innalillahi kawai ya shiga ambatawa da ɗunbin mamakin Samina, anya kuwa itace ma ta ɗaga masa wayar nan? To amma ai muryartace, kansa ya dafe cikin tsagwaron mamaki da damuwa.
Har Mudanseer ya shigo Ahmad bai saniba, Mudanseer dake tsaye kansa ya sake maimaita kiran sunansa a karo na uku,
“Yah Ahmad!!�?
Aɗan firgice ya buɗe idanunsa dake a rine da duhu, tashi yay zaune sosai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, “Mudanseer yaushe ka shigone?�?.
Zama Mudan yay kusa dashi cikin damuwa, “Yah Ahmad tunfa ɗazun na shigo, inata maka magana amma baka ko motsaba, halan zancen Yaya Maryam kasaka a ranka, kokuma yauma gimbiyar taka tayi wani tutsun?�?.
Guntun murmushi Ahmad yay yana kallon ƙanin nasa, yaɗan taɓe baki yana ɗage kafaɗu, cikin ƙoƙarin kauda maganar Samina yace, “Mudanseer, dolene halin da yaya Maryam ke ciki ya dameni, bansan miyasa ta kafe akan wannan rayuwarba, inajin takaicin yanda a kullum mijinta ke mata dukan kayan wanki amma bazata faɗaba, shin wai ita wane irin sone har haka a tsakaninsu da bazata rabu dashi ba�?.
“To ni wlhy Yah Ahmad nama kasa fahimtar wannan al'amarin nasu, kaga kuwa yanda yaji mata wani mugun ciwo a hannunta�?.
Babu shiri Ahmad ya miƙe tsaye yana faɗin, “Ciwo kuma? Amma ta zauna bataje asibitiba?�?.
“Wlhy batajeba in gaya maka, sai da naje na tasata gaba ƙyamis ɗin Shamsu, dama kuɗin ɗinkine ɗazun Farida ta kawo ina jira ka dawo na baka sai Ayyah taimin aike wajen yaya Maryam ɗin na iske halin da take ciki�?.
Cikin tsagwaron takaici Ahmad ya jingina da bango yana lumshe idanu zuciyarsa na masa wani irin zafi, tsawon mintuna uku suna a haka kafin ya fice daga ɗakin yabar Mudanseer shima da nasa tunanin.
Shagon da suke ɗinki ya buɗe ya shiga, ta kowanne fanni ya rasa abinda ke masa daɗi, da ɗan hasken screen ɗin wayarsa yay amfani wajen haskawa ya nemo fitilar da suke kunnawa a shagon idan babu wuta, da yake suna cajinta da hasken rana ne, tayi ƙau da haske saboda ranar da aka zuba yau.
Ya sagalata jikin ƙusar da suke ajiyewa ya zauna a kujerar da tazama tasa, dan babu mai hawa wannan keken sai shi.
Ɓacin ran da yake cikine yasashi duƙufa kan aikin wasu kaya daya yanka tun jiya da hantsi, ɗinkin yake amma sam zuciyarsa bata wajen, tana can a tunanin Samina, ganinfa bazai iya daurewa ba saiya ja tsaki yana take keken ya tsaya da aiki, wayarsa ya ɗauka ya sake kiranta, ƙin ɗagawa tayi harta tsinke, ya ajiye wayar a wani yanayi.
Kamar zai haƙura sai kuma ya dai sake kira, tana gab da tsinkewa ta ɗaga.
Kafin yayi magana tace, “Na koma gida, harma na kwanta barci Hubby na, dan ALLAH kayi haƙuri ɗazun wayarce ta mutu ashe babu cajine�?.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke murmushi na neman kuɓce masa, Murya a sanyaye yace, “To sannu da zuwa�?.
“Uhumm�? ta faɗa daga can.
Shiru sukayi su duka, jin hakanne yasa Ahmad cewa “Kiyi barcinki sai da safe, nima ɗinki nake ɗan ragewa�?.
Kamar bazata amsa ba, sai kuma tace, “Ɗinki a daren nan Yah Ahmad?�?.
Murmushi yayi mai sauti saboda jin daɗin nuna kulawarta gareshi wadda ta daɗe batai hakanba, yace, “To Samie na ya na iya, na kwance ai baiga gariba�?.
“Hakane Yah Ahmad, amma dai kaje ka kwanta kaima, sai da safe�?.
“Nagode My Samie�? yay maganar a hankali tamkar mai raɗa.
Itako daga can baki taɗan taɓe tana ajiye wayar da maida hankalinta ga Ma'aruff sabon saurayin da tayi yau a hotel ɗin da sukaje wajen kamun ƙawarsu, shine ya kawota har gida a mota, koda suka iso sai suka zauna hira bata fitaba duk da kuwa dare yaja, dan kusan sha biyu ma.
Kallonta Ma'aruff yay yana ɗan ɓata fuska, “Shi kuma wanene wannan?�?.
Ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi da wani fari, “Karya dameka, yayana ne�?.
“Yayankine amma kika nuna damuwarki a kansa harda kashe masa murya?�?.
“Wannan duk farfaganda ce dan a rabu lafiya�?.
Shiru yay baice komaiba, ganin hakan yasa ta ɗakko masa wata hirar.
Da yake shima ɗan duniyane sai ya basar da zancen suka ɗora hirarsu.
______________★★★★___________
Ahmad kam kalaman Samina ne suka ɗan sanyaya ransa, ya jingina da bango yana lumshe idanu, shi kansa baisan iya adadin son da yakema Samina ba, bashi da burin daya wuce a yanzu ya mallaketa matsayin matarsa ta aure.
Yayi zurfi a tunani ya tsinkayo muryar Baba na faɗin, “Amadu! Kai Amadu shin barci kakeyine a shagon wai?�?.
“A'a baba�?. Ahmad ya faɗa da sauri yana miƙewa tsaye.
A ƙofar shagon yaga baba tsaye, “Sannu baba, wani abu kake buƙata?�?.
“A'a babu komai, na fitone zan rufe gida saina leƙa ɗakinku naga Mudan ne kawai a kwance, shiyyasa nai tunanin ko kana nan, nakumaji ba ɗinkin kakeba ashe?�?.
Shafa kansa yay yana faɗin, “Eh wlhy baba, ɗinkin dai na fara sai kuma allura ta karye na tsaya sakawa, ashe babu mai ƙyau a shagon ma sai mun nemota da safe�?.
“To ALLAH ya kaimu, ka rufe kaje ka kwanta hakanan, kanaji jiya sai da ɓarayi suka shiga gidan Alhaji mamman�?.
“Wlhy kuwa baba, haka nima nakeji ɗazun da safe, ALLAH ya rufa mana asiri to�?.
“Amin ya rabbi�? baba ya faɗa yana juyawa gida.
Komawa cikin shagon Ahmad yay ya kashe fitilar sannan yazo ya rufe shagon ya koma cikin gida bayan ya rufe gidan.
Uzirinsa ya shiga bayi yayi, yay alwalar barci daya sabarma kansa kafin ya nufi ɗakinsu.
Mudanseer na ɓararraje a katifarsu yana jan nasharin barci, Ahmad ya shinfiɗa abin salla a gefe yana girgiza kai, salla ya tayar yay sha'i da wutiri, bayan ya kammala yay addu'oinsa ya cire rigar jikinsa dan sam baison kwanciya da kaya takura masa sukeyi.
Da ga shi sai boxer ya kwanta, bayan ya tura Mudanseer gefe da ƙyar saboda shima dai ƙatonne masha ALLAH.
Bargonsa yasa ya rufe jikinsa ruf har saman kai, dan komai zafi saiya lulluɓa yake iya kwanciya, sannan komai sanyi saiya cire kaya yake iya barci.
★★★★★★★★
Iya na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tana jiran taga ta inane Samina zata ɓullo.
Inna mari kuwa babu ruwanta, tuni ta shige ɗaki tai kwanciyarta tana shaƙar barci.
Sai wajen sha biyu da kwata sabon saurayin Samina yay haramar tafiya, ya kalleta ido cikin ido yana wani narkesu a cikin nata.
Hakanne yasaka tsigar jikinta tashi, tai saurin janyewa ƙirjinta na wani irin bugawa, tabbas batajin magana, amma har yanzu rawar kanta bai taɓa sawa ta yarda wani namiji ya taɓa aikata mata wani abu mara ƙyauba koda runguma kuwa, duk da kuwa tana jin sha'awa sosai irin wadda kowacce mace mai lafiya kanji a lokacin da takai shekarunta.
“Babie zan tafi, amma babu abinda zan samu�?. Yay maganar cikin raɗa kuma a saitin kunnenta.
Matse jikinta tayi kaɗan, muryarta naɗan rawa tace, “Yallaɓai kamar mi kenan?�?.
Wani mugun murmushi ya saki yana sake matso da kansa jikin wuyanta, sai da ya busa mata iska a wuyan kafin ya kai hanci yana shinshinar ƙamshin turarenta, cikin raɗa-raɗa ya sake faɗin, “Komai ma na samu inaso babie�?.
Yanda gashin jikinta ke miƙewane yasata ɓalle murfin motar ta fice ba tare data shiryama hakanba, ya bita kallo da idanunsa da suka fara rinewa yana murmushi, “Babie akwai wayo, shikenan na gode ga wannan kiyi amfani dashi wajen kwalliyar gobe�?.
Kamar bazata amsaba sai kuma ta ƙyalla ido taga yawan kuɗin, wani irin taji a ranta, tai azamar miƙa masa hannu tana faɗin, “Nagode sosai, amma kamar sunyi yawa ka rage�?.
Wata siririyar dariya yayi mai sauti yana dukan sitiyari kaɗan, ya maido kallonsa gareta har sannan da sauran dariyar a fuskarsa, “Babie nawanema waɗanan kuɗin da har kike tunanin sunmiki yawa? Ai ƙyauta bata yawa, yanzunma dan babu kuɗine a jikina shiyyasa, kinga shiga gida sai da safe�?.
Kanta kawai ta iya ɗaga masa, ta wuce sim-sim kamar wata munafuka.