Showing 126001 words to 129000 words out of 165545 words

Chapter 43 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

368

Ita dai batasan yanaiba, ta gama komai yanda ya dace dan yace dagasu sai kayan sawa zasu tafi, sai ɗan abinda ba'a rasaba da Rumana ta ɗauka.
Gab da magriba suka bar gidan tana jaddadama su Kausar kalmar a yafi juna.
A fili dai sunce suma a yafe, amma ƙasan zukatansu tamkar zasu kama da wuta haka sukeji, sunajin baƙar hassada akan wannan tafiya ta Umm-Rumana, ita kanta ta fahimci yaƙe kawai suke mata da dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. Duk da ita sai takejin wani iri babu daɗi saboda sabo............✍�?





_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻a: *_41_*



.............Washe gari suna idar da sallar asuba motarsu ta tashi, Rumana sai share hawaye takeyi, Zainab kam ko a kwalar rigarta murna taketayi, su kaɗaine a motar dan shata Ahmad ya ɗauka duk da kuɗin daya kashe hakan yafi musu sauƙi, dagasu sai kayansu, direba da Ahmad a gaba, zainab da Rumana da Haysam a baya.
Kuka sosai Rumana takeyi haka ƴan uwanta, duk dauriyar Ammi sai da tayi hawaye itama, tunda motar ta wuce gidan sai ya koma tsit, kowa yanajin kewarsu a ransa, dan Ahmad ya zama wani jigo abin alfaharinsu.
Mama gaje kuwa babu abinda kecin ranta sai baƙin ciki, ko fitowa ba taiba lokacin da kowa ya fito ƙofar gida har iya domin ganin tafiyarsu.
Babu wanda ya damu da lamarinta, sukabi yaransu da addu'ar fatan alkairi sudai.

Sunyi tafiya mai nisa Rumana tana kuka, yayinda Zainab barci yay gaba da ita, dama Haysam tunda suka taho shi barcinsa yakeyi.
Ahmad da direba ma ba wata hira sukeba, saboda hankalin Ahmad naga Rumana, itama dai barcinne ya saceta.
Ajiyar zuciya a Ahmad yayi kaɗan, yana maijin tausayinta na tsigota da yay daga cikin dangi, bashi da wata mafita bayan wannan, duk da kasancewarsa ƙaramin ma'aikaci yanada ƙyau ya maida hankalinsa ga aikinsa tuƙuru, gashi karatu yakeson komawa, zai sake zama busy sosai, kuma koba komai yana buƙatar jinta a kusa dashi, itama karatun ya keso ta koma kafin yara su fara mata nauyi.

Da ga Rumana har Zainab sun jigatu da wannan doguwar tafiya da basu taɓa riskaba a rayuwarsu, Haysam kam kuka yayta tsilalawa, musamman da lokacin da aka saba masa wankan yamma yayi, sosai ya rikice, Ahmad dai shi yayta taimaka mata, dan a gajiye take, ga kuma ruɗatan da Haysam yayi, dan bai taɓa mata makamancin kukan nanba da suna gida, yayi kukan dare kam sosai amma da yake Ayyah ce ke kwana dashi ita dai nata kallone, wani lokacinma sai yayi kusan rabin kukan take farkawa.
Iya galabaita dai kam sun galabaitu da wannan tafiya, dan ko abincin da sukan tsaya ci ita da zainab basa wani iya ci, Zainab amanta biyu ma ita.
Wannan yanayinne yasa Rumana bazasu iya ƙarar da komai da suka gani a hanyaba, ALLAH dai ya saukesu lafiya gabannin asubahi.
Gidane ƙarami da aka bama su Ahmad ɗin ƙananun ma'aikata su zauna, falone sai ɗakuna biyu a falon, babba guda ɗaya da kuma ƙarami da baikai girmaba, sai ko kicin da sito shima ɗan fit, kowanne ɗaki da bayinsa a ciki.
Ginin gwamnati ba ginine na mugunta ba, komai akanyisa da inganci, dan haka dolene gidan ya burge mutum, duk da dai kamar a kwatas suke, babu wata hayaniya kamarma babu mutane a wajen.
Ita dai Rumana ma bata kallon abubuwa takeba, burinta ta samu ta zauna ta huta, hakama Zainab data maƙale jikin Ahmad saboda rashin ƙwarin jiki, gashi ɗauke da Haysam a kafaɗa barcin wahala ya sacesa.
Nuni yay musu da su shiga ciki bayan ya buɗe ƙofar da key ɗin daya ciro a aljihu, har sannan Zainab na jingine dashi, Rumana tai gaba shikuma ya shigo da yaran, yayinda direban keta ƙoƙarin sauke musu kayansu.
Ɗan gidan ya sake birge Rumana, daɗinma da taji sune a can ciki jikin katanga.
Babu komai a falon sai wani kafet da aka shinfiɗa daga gefe akan tayis ɗin, dan haka suka zauna anan, zainab ma kwanciya tayi, Ahmad ya ɗorama Rumana Haysam a jiki ya fita domin shigo da kayan.
Sai da suka gama shigo dasu tas sannan ya fice domin yo salla tunda da massalaci a wajen.
Yacema su Rumana ma suje suyi sallar.
Da ƙyar ta lallaɓa Haysam ya kwanta ta miƙe, ɗakin daya nuna mata ta shiga, tabi ɗakin da kallo saboda akwai nefa, katifa ce kawai a ciki sai tarkacensa na kaya da abinda ba'a rasaba, sai ƙamshi ke tashi kuwa mai daɗi.
Ta nufi ƙofar da take ƙyautata zaton bayine, ilai kuwa shine, alwala tayo dan akwai fanfo, ta dawo ɗaƙin bayan taje falo ta ɗakko akwati ɗaya ta canja zani saboda ƙyanƙyamin na jikinta da takeyi.
Harta idar da sallar Ahmad bai shigoba, sai bayan kusan mintuna talatin garima ya fara haske sannan sai gashi da sallama.
Tunda yaga bata a falo sai ya nufo ɗakin, Rumana na ƙoƙarin cire hijjab ya shigo.
Kusan a tare suka haɗa baki wajen yima juna sannu, Ahmad ya nufi bayin yana faɗin, “Wanka ya kamata ki musu kema kiyi saina samo abin kari ku kwanta ku huta, dan na kula duk bakwa hayyacinku�?.
Da “To�? ta amsa umarninsa, ya saka musu hita a ruwa sannan ya fita zuwa kicin, dan yanada ƴan kayan abincinsa da yakan dafa wani lokacin.
Ƙamshin ƙwai kawai Rumana take jiyowa, amma sai bata leƙaba tazo ta tada Zainab da tai barci, da taimakonta zainab ɗin tai wanka, ta cire mata kaya a kayan sawarta sannan ta ɗauki Haysam shima tana cire masa.
Dai-dai nan Ahmad ya shigo da tire ɗan babba ya ajiye idonsa akan Zainab.
“Zainab yaya jikin?�?.
A marairaice ta kallesa tace, “Yaya naji sauƙi, barci dai nakeji�?.
“To bara ki karya saiki kwanta kinji ko�?.
Kanta ta ɗaga masa tana cigaba da saka kayan, Rumana ma na jinsu tana ƙoƙarin cirema Haysam kayan jikinsa.
Ganin ta miƙe Ahmad ya kalleta, “Zaki iya masa wankan kuwa Ruman?�?.
“Lah yaya zan iya, ai tun a gida ana sakani na masa saboda irin wannan ranar dama�?.
Kansa ya jinjina mata, ita kuma ta wuce bayin.
Tana farama Haysam wanka ya fara ƙwaɗa kuka, hakan yasa Ahmad miƙama Zainab shayin daya haɗa mata da sauri ya miƙe zuwa bayin, shi duk gani yake Rumana bazata iya wankanba.
Amma ganin tanayin dai-dai sai hankalinsa ya kwanta, da taimakonsa aka kammala ma Haysam wankan, tace yayi shima kafin ta shiryashi.
Bai musaba kuwa, itama saita fito.
Har ta gama shirya Haysam ta shayar dashi sannan ya fito, Zainab kam tuni ta gama karyawan ta kwanta barci yay gaba da ita, tashi tai ta shiga itama, ta barsa yana shiri.
Sai da suka kammala komai daya dace, suka karya suma sannan Umm-Ruman ta kwanta, Ahmad kam shiri yay ya fita ya barsu bayan ya kullesu ta baya.


★★★★★★�?


Su Rumana ansha barcin gajiya, kusan kwana uku suna hutawarsu, abinci ma Ahmad ke sayo musu, bai kuma nema komai daga gareta ba duk da yana cikin tsananin buƙatar hakan.
Da yamma randa suka kwanaki na ukun sai gashi shida nura a mota da kujeru, dama ya daɗe da bayarwa ayi wajen wani kafintan bahaushe da suke kira malam na kano, yana irin sana'ar gwangwan ɗinnan ne, sai yazam yanada yara masu aikin kafinta, Ahmad ya sanshi ne sanadin Nura, malam na kano yanason ƴan uwansa hausawa, dan haka yake taimaka musu da abubuwa da dama, dan ya kuɗance da sana'ar gwangwan ɗin nan sosai, a hankali Ahmad yayta biyansa, yanzu hakama bawai ya kammala biyan bane, duk da kujerun ba wasu masu shegen tsada bane, dai-dai ƙarfi dai akayisu.
Mamaki ya kama Rumana sosai, ita dai tana kallonsu ne har suka gama tsara kujerun a falon, kafet din da yake ajiye da shi kaɗai a falon a ka maidashi tsakkiya, sai ƙaramar katifa da aka sakama zainab a ɗayan ɗakin itama, ya umarci Rumana akan ta maida mata kayanta duka a can.
Sun daɗe da Nura a gidan, dan sai dare ya wuce, da yake yanzu shine a gidan su Happy ya maye gurbin Ahmad tun lokacin da aka bashi gidan nan.
Da daddare bayan sun kammala hira da cin abinci zainab ta shige ɗaki wai barci takeji ita dai, Ahmad na zaune yana danna waya bai tankaba, sai ita da Rumana ke maganarsu dama can, sai idan ya gadama yake jeho tashi.
Haysam na goye a bayanta yana barci.
Bayan shigewar Zainab Rumana ta kalli Ahmad ɗin, “Yaya zakasha shayin ne yau? dan nima kwanciyar kam zanje nayi�?.
Idanunsa ya ɗago ya kalleta, ya ajiye wayar yana wani sake ƙanƙance idanu kamar wani bachaine.
“Eh kawo�?.
Ya faɗa kamar wanda bayason magana.
Tashi tai ta nufi kicin, babu jimawa ta dawo da kofin shayi yana tururi.
Koda ya amsa idonsa na kanta, ita dai ta ɗauke kai kamar bata fahimcesa ba.
Ɗaki ta nufa tana faɗin bara ta kwantar da Haysam kafin ya shigo. Da uhum ya amsa mata.
Koda ta shiga ta kwantar da Haysam a ƴar katifarsa mai net saita cire kaya ta shiga wanka, dukkan dabarun dasu Yaya Maryam suka ƙara mata karatu a kai shitayi kafin shigowar Ahmad, dan tasan yau dai batada mafita, wannan narke fuskar da yake faman yi yakai maƙurar da bazai iya ɗaga mata ƙafaba.
Kamarko tasan abinda ke ransa kenan, dan yana kammala shan tea ɗin tashi yay ya nufo ɗakin bayan ya kashe fitilar falon da fanka, dan basu da kayan kallo.
Isketa yay tanama Haysam addu'a, bai ce komaiba ya nufi bayi, ita kuma ta daka hijjab ta nufi ɗakin Zainab.
Itama tayi barci tuni, addu'a tai mata sannan ta gyara mata kwanciya ta fito.
Tana shigowa Ahmad na fitowa, yace, “Daga ina?�?.
“Addu'a na yoma Zainab�?. ‘Ta faɗa tana zama bakin katifarsu�?.
Baice komaiba ya ƙarasa shirinsa, ita kuma ta cire hijjab ɗin ta kwanta.
Sai da ya duƙa wajen Haysam ya zira hannu yaɗan shafa kumatu yaron yana murmushi kafin ya taso yana faɗin, “Sadaukina banda kukan dare yau, Ni da Mommyn filin daga zamuje�?.
Kallonsa Rumana dake daga kwance tayi cikin mamaki, sai dai harya kwanta ya sakata jikinsa bata iya cewa komaiba.
Ya hura mata iska a cikin kunne yana magana a hankali, “K idan ance yau ranar barcice sai ki yarda?�?.
Rumana taɗan ƙanƙame jikinta saboda tsigar jikinta data yamutsa gaba ɗaya, shi kansa jikinsa rawa ya farayi saboda tsananin kewarta da yayi.
A yanda duk sukai laushi zai tabbatar maka kowa kewar ɗan uwansa na damunsa, dan yau ajiye kunya Rumana tai ta tabbatarma yayanta da gaske shiɗin natane, kuma ya karɓu a gareta karɓa ta har abadan.
Hakan ba ƙaramin neman zauta Ahmad yayiba, dan baitaɓa zato daga Gwal ɗinsa ba sam, duk da ta jigatu ta daure domin ganin ya samu farin ciki daga gareta, kodan tarin alkairan da yayi mata kashi-kashi tun daga haihuwarta zuwa yau da bazasu lissafuba.
Bata samu kuɓuta daga garesaba sai da kukan Haysam ya tsaida komai, a gurguje suka tsarkake jikinsu tazo ta ɗaukesa ta bashi abinda yakema kukan.
Ahmad harda dungurema Haysam kai, wai baiji nasihar da yay masaba ashe😂.
Ita dai Rumana tai murmushi kanta a ƙasa dan taƙi yarda su haɗa ido saboda nauyin abinda ta aikata yau, shiko ko'a jikinsa, saima wata ƙaunarta ta musamman dake sake shigarsa ta kowacce ƙofar gashin jikinsa.
Da asubama bayan yay sallar asubahi sai da ya sake komawa filin daga injisa.

Tun daga wannan ranar abubuwa suka sake canjawa tsakanin Ahmad da Umm-Ruman, dan yanzu kam kaso mafi yawa daga kunyarsa ajiyeta take gefe sai sun gama ƙonuwa a soyayyarsu sannan ta maido ta ta lulluɓa, hakan nama Ahmad daɗi aynun, dan shi dama haka yafi buƙata.
Dolene zamansu ya birgeka, akoda yaushe cikin waya suke da ƴan uwa da abokan arziƙi da suka baro, satinsu huɗu a garin Ahmad ya ɗauki su Rumana ya kai har gidansu Happy.
Sosai sukaita mamaki, dan sufa da basu yarda Ahmad nada aure ba.
Aiko kamar su haɗiye Haysam dan so, yaron yay bala'in birgesu, dan haka Mummy ta sakasu sukaje wani ƙaton super maket taima Haysam siyayyar kaya masu ƙyau.
Wannan abu yabama Rumana mamaki, duk da ba wata hira tai da suba saboda su basajin hausa, ɗan turancin bakinta kuma baida yawan da zasuje doguwar magana, sai dai ta lura mutanen sunada kirki, Ahmad koda yazo yaga hidimar da sukai musu yayta godiya.
Sai dare suka koma gida, Happy tace sai tazo itama.


_________________________________


Tafiyar su Ahmad da kwanaki biyar Ma'aruff ma ya ɗauke Mufida suka tafi Honeymoon kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa, a cewarsa ƙila daga nan sa samo rabo.
Wannan abu yay masifar taɓama Samina zuciya, dan har sai da tazo gida.
Mama gaje taita lallashinta da ƙarfafa mata gwiwa saura kaɗan Ma'aruff yazo yay gurfane a gabanta yana neman gafara, ita dai tayi haƙuri ya gama rawar kan amarcin kawai.
Da wannan lallashin ta sama zuciyarta salama, sai lokacin taji labarin tafiyar da Ahmad yay da Rumana wajen aikinsa, sai taji zuciyarta ta sake dagulewa, babu shiri ta miƙe tana faɗin zataje gidan inna mari daga can saita wuce gidanta.



*_BAYAN WATANNI BIYAR_*


Zuwa yanzu abubuwa da dama sun faru na cigaba a wajensu Rumana, dan duk wata Ahmad ya amsa albashinsa zai ɗan tsintar musu abinda basu dashi a gidan ya saka musu, dan danan gida ya haɗe yay tsaf dashi, su kansu sunajin daɗin yanda komai ya zama ɗas a muhallinsa, a watani biyar ɗinnan zuwan Ahmad gida biyu yay kwana uku a na farko, na ƙarshen nan kuwa satinsama guda, amma banda su Rumana, hakan yayma iyayensa daɗi, dan ya tabbatar musu tafiya da iyalansa can bazaisa ya manta da waiwayarsu ba kenan.
A gefe kuma yanata shirye-shiryen komawarsa makaranta, hakama Zainab an sama mata wata secondary anan kusa da kwatas ɗin nasu, zata ringa zuwa da wata yarinyar maƙwaftansu da bata wuce sa'artaba, duk da dai ba hausawa bane kuma ba musulmai bane, amma basu da matsala dai, dan a hankali sukaita shiga jikinsu Rumana har sabo yay ƙarfi a tsakaninsu ana gaisawar mutunci, sai islamiyya da Ahmad ya samar mata sanadin ogansa na ɗan kunne, duk weekend take zuwa ita kuma.
Haysam kam kullum ƙara wayo yake, yanzu haka yana zama abinsa, da ɗan rarrafe duk da dai bai nunaba rarrafen, yaron ya ƙara ƙyau sosai da cikar haiba maiban sha'awa, kowa yagansa saiya tanka, dan haka Ahmad ya dage da tofe kayansa da addu'a, itama Rumana yakance tai masa.
Duk sanda zaije gida sai taji kamar tai tsuntsuwa ta bisa, sai dai babu dama, har ƙwalla takeyi, Zainab kam bata damuba, balle tana gaisawa dasu Gwaggo a waya akai-akai, ita daɗinma garin takeji sosai da sosai.


______________________


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login