Showing 45001 words to 48000 words out of 165545 words

Chapter 16 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

364

Bayan malamin islamiyyarmu ya taɓa bamu wata ƙissa da MANZON ALLAH ke wanka da *Nana Ai'sha (R.A)*.
Zaram na miƙe saboda fitowar Yah Ahmad daga ɗaki, a duƙe na ƙarasa alwalar maman Ama na tsaye a kaina, tana jiran Yah Ahmad ya gotamu ta ɗora maganarta daga inda ta tsaya.
Da azama na bar wajen ganin ya nufi bayi, na faɗa ɗakina ba tare da na sake koda waiwayenta ba.
Gaskiya matarcan lamarinta na bani mamaki da ɗaure kai, shikenan kai bazaka damu da rayuwarka ba sai ta wani, dole nazo na roƙi Yah Ahmad komawa makaranta kodan gujema halayyar maman Ama ta son kafa da'irar gulma a gidannan.

Ina idar da salla ne na fara kimtsa kayan danaga ya kammala yankawa, sai biyu suka rage bai taɓaba, na tattare ƙyallayen na saka a leda suma na share ɗakin dan ya samu wajen cin abinci.
Ranar dake a tsaye tasaka garin ɗaukar wani mugun zafi, da ace ina da dama kayan zan cire nasha iska wlhy.
Haka dai na gama shirya masa abinci a tabarma na ɗauki kofi ina zuba ruwa, bisa tsautsayi na ɗan zubar, wanda na gama zubawa na ɗauka nakai gaban abincin nasa, sannan na dawo ina duba tsumma danna goge wanda na zubar.
Abinka da sabuwar leda, ashe na ɗan ɗisar da mangyaɗa a wajen sanda nake girki, koda na goge wajen kuma ban lura da nanba,, ga ruwa ya zuba, ina ɗora ƙafata da dube-duben inda ruwan ya zuba kawai naji na tafi gaba ɗayana, sai gani ƙasa.
Fashewa nayi da kuka saboda wani azabar zafi daya ratsa ƙashin ƙafata da ƙuguna.
Sosai nake kuka dan na kasa tashi, bansan yaya akai kunnen maman Ama ya jiyoniba, sai gata ta shigo jiki na ɓari tana tambayata lafiya?.
Ganina ina kuka rike da ƙafa da hannu ɗaya, ɗayan kuma na riƙe ƙugu ya sakata faɗin, “Faɗuwa kikayine?�?.
Kaina kawai na iya ɗaga mata ina cigaba da kukana, takai hannu zata taimaka min danna miƙe sai ga Yah Ahmad yay sallama ya shigo.
Da mamaki ya kalli maman Ama ɗin sannan ya kalleni fuska babu walwala, “Miya faru?�?.
Maman Ama ta buɗe baki zata bashi amsa nai saurin katseta....
Kuka na kuma saka masa wanda ni kaina nasan harda taɓara nace, “Faɗuwa nayi�?.
Hannuna dake cikin na maman Ama ya kalla, ba tare da ya kalleta ba yace, “Barta kawai zan tada ita�?.
Koda ta sakeni a zatona zata fita, sai naga matarka ta gyara tsaiwa tana kallonmu sai kace wasu tv ɗinta.
Wannan abu da Maman Ama tayi ya zafi Ahmad a zuciya, dan haka da gayyar cusa mata baƙinciki ya rungumi Umm-Rumana ya ɗagata cak zuwa saman gado, tunda ya fahimci matarnan muguwar ƴar sa ido ce.
Aiko tamkar ya sani, dan tsayawa tai taga yaya za'a kwashe, daga ita har mijinta sun fahimci Ahmad bai taɓa taɓa Rumana ba, har gulma suke akan hakan, wai baya son Rumana hankalinsa nakan Samina har yanzun.
Wani irin zaro idanu tayi na tsagwaron mamaki, maimakon ganin hakan ya sakata fita saita sake maƙalewa.
Rumana kuwa tunda Ahmad ya ɗauketa jitai hawayen sun gudu saboda tsabar al'ajabi, sam bata kawo hakan a ranta ba, jitai kawai jikinta na wata irin tsumar tsoro, dan a rayuwarta hakan shine na farko gareta.
Ya kwantar da ita a gadon sai dai rabin jikinta na saman jikinsa, a hankali yace, “A inane kika buge?�?.
Hawaye Rumana ta matso da suka cika mata idanu, ta nuna masa ƙafarta, ƙugun kuma kunya takeji shiyyasa ta kasa nuna masa dukda nan yamafi ƙafar buguwa.
A mamakinta sai gani tai ya tura hannunsa cikin rigarta ya shafa ƙugun yana faɗin, “Shinan bakison a taɓane ragguwa?�? ya ƙare maganar da matsa wajen.
Jikin Rumana har rawa yake ta ƙankame Ahmad ba tare da ta shirya hakanba, ga wani siririn kuka data sakar masa na jin zafi, bai bartaba yanata matsa wajen yanda ƙashin zai saki.
Ita ko ta ruƙunƙumesa tamkar zata koma masa ciki. Dauriya kawai Ahmad yakeyi, amma gaba ɗaya jinin jikinsa yamutsawa yakeyi ta kowacce kafa, tsigar jikinsa yanda ta tashi ya saka kowanne gashin jikinsa fitowa ta ɓularsa. Karo na farko a rayuwarsa da ƴamace ke a jikinsa kwance, abinda ya jima yana kissimawa da Samina kawai, a yau sai ga saɓanintace kwance a jikin nasa. Kasancewarsa gwanin kamewa yasa baka fahimtar yana a mawuyacin hali koda a fuskane, saima kalmar Sorry da yaketa ambatama Umm-Ruman a hankali yana cigaba da murza ƙugun�?.
Saɗaf-saɗaf maman Ama ta fice a ɗakin wani abu na tokare mata maƙoshi, dan ita gani tai soyayya suke a gabanta kawai.
Duk yanda Ahmad yaso daurewa ya kasa, hakan yasashi zamewa ya kwanta yana saka Rumana sosai a jikinsa, wai shinan duk azuwan gyarane, taƙi tsayawa ya matseta, wannan damar Rumana da azabar matsa gurin ciwo ya isheta ta kuma mannema Ahmad sosai tana kuka da roƙonsa dan ALLAH ya bari hakanan, akwai zafi sosai.
Sam shi baima san tanaiba kam a yanzu, dan ɗiff kunnensa ya toshe, salon yanda yake matsa mata wajenma kawai zai baka tabbacin ya fara canja tasha ne.

Har maman Ama taje ɗakinta sai ta kasa daurewa, tsabar hassada nacin ranta ta kasa zaune ta kasa tsaye, maganin zafi ta ɗauka ta dawo ɗakinsu Umm-Rumana, tunda ta ɗaga labule taga yanda suke mai makon ta koma da baya sai catai “Yauwa ga maganin zafi kozata shafa a wajen insha ALLAHU zai saki�?.
Yanda tayi maganar da ƙarfine ya dawo da Ahmad hayyacinsa, ya buɗe idanun da suka canja launi da ƙyar, kafin ya yunƙura ya tashi zaune da Umm-Ruman a jikinsa, ita tanata shashshekar kukane, shiko sai ajiyar zuciya yake saki a jere kamar jaririn dake neman abinci bai samuba.
Fuskarsa mugun tamke yakai dubansa ga maman Ama, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda yasan muryarsa zata iya fallasa tsantsar buƙatar dake a tare dashi a halin yanzu.
Maman Ama ta ajiye musu maganin zafin gefen gadon ta fice kamar gaske, amma saita maƙale a bakin ƙofa.
Umm-Ruman ta raba jikinta da nashi tana share guntun hawayenta, murya a matuƙar shaƙe yace, “Sannu, kawo ƙafar muga itama�?.
Rumana ta marairaice idonta na sake cika da ƙwalla, “Yaya dan ALLAH ka bari na huta sannan, ALLAH akwai zafi�?.
Kansa ya girgiza yana kamo ƙafar, “Waya ce miki idan aka barshi anjima bazakiji zafinba, saima kinfiji fiye da yanzu�? ya ƙara maganar yana matsa ƙafar itama.
Nanma ta ɗanyi kuka tana rirriƙe masa hannu saboda ƙafarma ta ɗan bugu, sai da ya tabbatar ta matsu sosai ne ya sauka a gadon, jakkarsa ta kaya ya buɗe ya fiddo maganin zafi, dan ko kallon wanda maman Ama ta ajiye baiyiba, a ƙafar ya fara shafawa kafin ya kalli Rumana cikin ɗan ɗaure fuska yace, “Juyo bayan ki ɗaga rigan�?.
Cike da jin kunya Rumana tabi umarninsa, shiko yay mursisi yana shafa mata a wajen. Bayan ya kammala ya miƙe tsaya yana cewa, “Kwanta kiɗan huta na minti biyar maganin ya shiga wajen sosai�?.
Babu musu ta kwanta tana gyara rigarta, shiko ya ajiye man zafin saman mirror ya koma saman tabarmar ya zauna.
Yunƙurawa tai zata tashi tana faɗin, “Bara na saka maka abincin�?.
“Barshi zan zuba kawai�?.
Yay maganar yana buɗe kular abincin.
Dole Rumana ta koma ta kwanta, Ahmad kuma ya zubama kansa a binci a filet ɗin da Umm-Ruman ta ajiye.
Sai ya samu kansa da yawan kallonta, kaɗan-ƙadan idonsa sai ya kai gareta.
Rumana kuwa barcin wahala ne yay gaba da ita ba tare da ta shiryama hakanba.
Maman Ama dataji shiru sai ta kama gyaran murya, da faɗin, “Sannu amarya kinji�? Ahmad duk yana jinta, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita, jin anƙi bata amsa taja ƙafafunta ta koma ɗaki.


★★★★★★�?

Koda na farka bayan la'asar kaina kawai na gani a ɗakin, babu kayan da ya yanka, sai kular da abinci kawai ke ciki da kofin ruwa, filet da ƙaramin kofi da yay amfani dasu ma can na hangosu ya saka a robar da nake tara wanke-wanke.
Sakkowa nai daga gadon, dukda har yanzu ina ɗanjin zafin amma ba kamar ɗazunba, takarda dana gani saƙale a hannun kofin ruwan na zare ina warwarewa.

_Idan kin tashi kici abinci, ga maganinan kisha kuma._

Iya abinda kawai aka rubuta kenan a jiki, nai murmushi kawai, a raina nace da mijin Novel ne bazaije ko inaba saina tashi, ya bani abincin da kansa da maganin, ƙilama har wanka zai mini.
Ayyana hakan da nayine ya saka ni tuna yaya Samina, sai nayi saurin faɗin “ALLAH ka ciremin wannan ragon tunanin a raina, dan kuwa suma marubutan suna saka wani abunne kawai dan nishaɗi, wani abun kuma dan ƙara ilimi da gyaran zaman takewar aure, amma ga irinsu yaya Samina nan mai makon su duba abu mai muhimmanci su ɗauka a ciki sai suka ɗaura rayuwarsu bisa mara muhimmancin, na tuna randa naji tana faɗama mama gaje itafa auren irin mijin Novels shine burinta, kuma sai ta cikashi, maimakon naji mama gaje ta kwaɓeta sai cewa tai shi mijin novel ɗin yaya yake ne? Samina!.
Ina jiyosu Yaya Samina na bata labari tiryan-tiryan na wani littafi da take karantawa suna dariya.
Na girgiza kaina kawai ina murmushi, daurewa nai na fita ɗauro alwala.
Maman Ama dake jan ruwa a rijiya ta kalleni, sai naga kamar fuskarta babu fara'a, amma sai ban kawo komaiba, sai dai kuma maganar da tayice ta sakani kallonta.
“Oh ni Amarya sai yanzu aka tashi?�?.
Murmushi na mata, “Wlhy kuwa Maman Ama bansan barci ya kwasheniba, ashe har anyi sallar la'asar�?.
“Ina kuwa zaki sani, daga gyaran ciwo an koma soyayya, ni shiyyasama na fito na baku waje, dan naga kun manta dani a ɗakin. dama su maza idan kana amarya ai jinka suke kamar ƙwai a cokali, sai an fara haihuwa ɗaya biyu sai labari ya canja salo�? ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariya tana cigaba da faɗin, “Muma fa duk anmana mafiyin ma wannan tarairayar, shiyyasa da ake muku yanzu sai muga abun kamar maimaici�?.
Murmushi kawai na sake iya yi mata, nace, “ALLAH sarki�? kawai nai wucewata bayi.
Duk da Maman Ama ta girmeni, kuma rayuwar gidanmu ba irin haka bace, ba kuma wasu ƙawayene daniba bayan su Fa'iza na fahimci alamar jin haushin kulawar da Yah Ahmad ya nuna a kaina cikin maganar maman Ama, sai kuma yanzune zuciyata ta sake gane yawan tsogumi da maman Ama keyi akan amaryar gidan, dan taga mijinta na bata kulawa, to ALLAH ya ƙyauta, ashe shiyyasa yaya Ahmad yaymin gargaɗi ɗazun.
A bayin ma nayo alwala ta dankar na tsaya wajen nazo na gittata tana ɗibar ruwa da yin wakar barmani choge.
Wuceta nai kamarma na manta da ita a wajen na koma ɗaki.
Koda na idar da salla duk yanda yace nayi haka nayi, bayan nasha maganin na gyara ɗakin sosai dan ɗazun bawani gyara mai kyau nai masaba saboda yah Ahmad, turaren wuta na tsinke na kunna a ɗakin, na ɗiba ruwa naje waje nai wanke-wanke.
Ina cikin yine Amaryarmu ta fito rakkiyar mijinta da alama fita zaiyi, sunyi gayunsu abin sha'awa, har soro ta rakashi sannan ta dawo.
Inda nake ta nufo, hakan yasa nai mata murmushi, ba wata babba bace itama, da alama dai irin sakin wawan nanne, baka daɗe da auren farkoba a sakeka.
Ta zauna saman rijiyar tana faɗin, “Kuyi haƙuri bamuyi gaisuwa da kowaba a gidannan irinta sanayya�?.
Cikin faɗaɗa murmushi nace, “Ayya ai babu komai, keda kikazo jiya da dare, ai ya kamata amiki uziri�?.
Sosai tai dariya, sannan muka gaisa, tace, “Ni sunana Kausar, kefa?�?.
Nace, “Kausar suna mai daɗi, ni kuma Umm-Rumana�?.
“Woow Nice name�? ta faɗa cike da iyayi.
Ni dariyama ta bani, dan haka na dara kaɗan, sai ga Maman Ama dake wanka ta fito tsilim tana cewa, “Mi ake tattaunawa haka amaren gidanmu?�?.
Mu duka kallonta mukayi muna cigaba da dariyarmu, ni dai bata samu amsa a wajena ba, sai Kausar ce ta bata amsar.
Yanda Maman Ama ta nuna son Kausar sai abin ya bani amamaki, wato dai matarnan kwararriyar ƴar barikice, koda ta shiga ɗaki kayan ƙwalliyar waje ta ɗebo ta dawo dasu, ta zauna a kujera ƴar tsugguno, a haka aka cigaba da hira, wadda su biyune keyi, iyakata dariya kawai, saboda firar ta koma akan abinda yafi ƙarfin girma na ne.
Har Kausar na fadin miyasa ni banson cewa komai?.
Nanma dariyar kawai nayi, sai maman Ama ke cewa “Ai indai amaryace haka take, inaga batason bamu nata sirrin�?.
Nace, “Maman Ama ni wane sirri gareni, ai sai dai ku manyan yayye�?.
Da haka na miƙe ina share ruwan wajen, kausar tai dariya tana bani amsa da cewar, “Kema kin shiga layin manyan ai tunda har aka kawoki ɗakin miji�?.
Maman Ama tai saurin cafe zancen “Kema dai ƙya faɗa Kausar, koda yake itafa ƴar gatace, angon nata rainonta yakeyi har yanzu, kusan sati uku kenan da aure kuma�?
Kausar tace, “Tab, dama har a wannan zamanin akwai waliyan maza irin waɗannan da suka rage? Ballema saurayi da kamar ji suke su ƙwata tun a waje?�?.
“Aiko dai gashi an samu a gidanmu kausar, nima dai ina jinjina ƙoƙarinsa, mu ƴan zamanin shekaru kusan takwas ma ba'a ɗaga mana ƙafaba balle na yanzun?, randa aka kawoni gidan da muka fara zama ALLAH tun farkon dare baban Ahmad yana gida, kamar jira yake ƴan kawoni su wuce ya hau sassafata�?.
Dariya suka kwashe da ita, ni dai na ɗauki ruwan wankana na nufi banɗaki ba tare dana ce dasu uffanba.
Ina jiyosu suna cigaba da hirarsu wadda ni kunyama take sani dukda bana a kusa dasu, dan Maman Ama tiryan-tiryan take zayyanoma Kausar daren farkonta, itama tana faɗa mata nata suna kwasar dariya.
A haka nazo na shige ɗakina ina ɗingisa kafata mai ciwo.
Ban sake fitaba duk da ina cigaba da jiyo hirar tasu kuwa, wadda naga tayi zurfi sosai dan har maman Ama tafara kiran ta shiga ɗari lokaci yaja bata dora abincin dare ba.
Kausar take cemata “Kai dama zakiyi abinci kika biyemin, tashi ki ɗora kam gaskiya dan mu saimun gama cin amarci, Amarya dai tunda ta shige tai bulum a ɗaki�?.
Dariyar maman Ama na jiyo tana bata amsa da “Ai ƙyaga da yawa indai amarya ce, sam bata gajiya da ƙumshe kanta a ɗaki kamar wata maijego�?.
“Zata barine, har yanzu da sauranta ne ai�? cewar Kausar.
Ni dai ko tari banyiba balle susan yaya nake.


______________________________



Ɓangaren Samina kuwa a hankali Ma'aruff ya fara cin galaba a kanta, yanzu kam babu fashi duk randa yazo hira wajenta saiya moreta da Romance, tun tanajin tsoro har itama idonta ya fara bushewa saboda jin daɗin hakan da takeyi, dan zuciyarta ta yarda da Ma'aruff ɗari bisa ɗari akan bazai cuta mata ba, a ganinta tunda aure zasuyi kuma ai babu wani abu, da yaje yayi da wata kamar yanda ya faɗa gara yayi da ita tunda kowa yasan akwai maganar aure a kansu.
Kuɗi kuwa da sayayya ya kara haukacewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login