Showing 162001 words to 165000 words out of 165545 words

Chapter 55 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

377

Sun sami tarba ta mutunci maiban mamaki ga ahalinsu Happy, kowa na mamakin canjawar ɗan uwansa, sai da suka sami nutsuwane da daddare Happy ke bama Rumana labarin yanda suka haɗu da Mudan.
Ashe Ahmad take so ita tun kan su wuce saudiyya, amma shi sam yaƙi nuna ya fahimceta, bayan tafiyarsa ta shiga tashin hankali, taita masa messeges da kalaman soyayya amma sai baitaɓa bata amsaba, hasalima idan ta kirashu koshi ya kirata bazai taɓa nuna mata ko messeges ɗin ya ganiba.
Ta shiga damuwa sosai harta samu Abubakar da zancen, Abu yay dariya a wancan lokacin tare da bata haƙuri akan abinda yayansu yay mata.
Itako tace babu damuwa, ita bai taɓa ɓata mata raiba dan ta fahimci yana son matarsane sosai, bayason haɗata da kowa a rauwarsa.
Abubakar ne ya bata shawara akan Mudanseer, yakuma nuna mata hotonsa da tabbatar mata cewa kamannin Mudanseer ɗaya da Ahmad, babu wani banbanci.
Koda taga Hoton yah Mudanseer ta aminta da zancen Abubakar, sai dai bataji son Mudanseer a rantaba, tadai cema Abubakar zatai tunani akai.
Koda suka rabu da Abubakar sai yakoma yayta cusama Mudanseer zancen Happy shima, tun Mudan na zagin Abubakar ɗin harya ɗan fara jin wani abu game da ita, saboda Ahmad ma dai ya shiga maganar, shi kuma Ahmad bason Happy ne bayayiba, har cikin ransa yanaji zai iya aurenta kodan ya tsamita daga duhun da take ciki, amma yana duba yanayin rayuwar da yake cikine, ƙarfinsa baikai ya riƙe mata biyuba a wancan lokacin, idan yace zai aje mace fiye da ɗaya rigima kawai zai haɗama kansa wajen ɗaukar nauyinsu na yau da kullum.
Hakan yasa yaso janta zuwa lokacin da zaiɗan sake ƙwari, to saikuma Abubakar yazo masa da batun Mudanseer, koda Ahmad ya tuntuɓi Mudan da batun yaga lallai ya karɓi zancen kuma yanason Happy ɗin saishi yaji zai iya haƙura ya barmass, dan da kai da kaya ai duk mallakar wuyane.
Da taimakon Ahmad Happy ta fara son Mudan, kafin wani lokaci soyayya tai ƙarfi a tsakaninsu, har Happy ɗin ta dawo karatu nan kano gidan wani uncle ɗinta.
Daga nanfa soyayya ta ƙara ƙarfi da shaƙuwa a tsakaninsu, da farko Gwaggo ta shiga damuwa da wannan soyaya tasu, dan ita a ganinta tayaya Mudan zai auri wadda bata salla?.
Amma sai baba ya zaunar da ita yay mata bayani yanda zata fahimta, yakumace suyi addu'a hankalin Happy ya dawo akan musulunci.
ALLAH mai komai da kowa kuwa da yake yaso Happy da rahama sai gashi ta musulunta a hannun Mudanseer ba tare da kowa nata yasaniba, ta zaɓi sunan Halimatussa'adiyya, Har zuwa yanzu kuma babu wanda yasan ta musulunta a cikin ahalinta, tayi alƙawarin sai tayi aure nauyinta ya koma kan mijinta sannan ta bayyanama iyayenta gaskiya, dan dama daƙyar suka yarda zata auri Mudan, saida aka kai ruwa rana sosai har abun ya sahafi Ahmad, daga baya kuma dai suka haƙura saboda tace zata kashe kanta kota gudu tabarsu har abada.
Rumana ta share hawaye tare da rungume Happy sunayi tare, ta tayata murna sosai da addu'ar fatan alkairi.
Samina ma da yake da ita sukaje har kuka tayi, da mamakin irin wannan ƙauna da Ahmad kema Umm-Ruman, saima ta fara tunanin kidai dama Ahmad yana son Rumana ne tuncan da?.
Bata da mai bata amsa, sai dai rayuwar Happy ta birgeta, ta kuma yarda Ruman ta mata nisa ita da Ahmad.

Ranar juma'a aka ɗaura auren Happy (Halimatu) da angonta Mudanseer, a ranar su Rumana suka taho da amarya nan kano, bisa rakkiyar tsurarun danginta, tanata kukan rabuwa da iyayenta suma sunayi.
An fara kawota nan gidan su Ahmad, mutane nata ƙananun magana akan Mudan ya auri ƙabila.
Washe gari kuma aka ɗaura auren Abubakar da ɗiyar ƙanwar Gwaggo mai suna Zubaidah, daga nan aka haɗe shagalin biki akasha aka more.
Samina nata ɓoye-ɓoye amma hakan bai hana mutane bincikota ba dansu gani, sukda ma taɗanyi fasali haka kaita zunɗenta.
Bayan anyi biki an shashshare aka miƙa amare gidajensu, su Umm-Ruman kuma suka shiga barcin gajiya.


★★★★★★

Bayan biki da sati ɗaya Ahmad suka nufi gidansu Inna mari bisa umarnin baba shi da Mudanseer.
Halin da suka iske mama gaje a ciki ya ɗaga musu hankali matuƙa, suka kwasheta zuwa asibitin dawanau.
Dukan wani taimako na musamman sun bada damar a batashi, cikin amincin ALLAH kuwa tafara samun sauƙi da yake abun baiyi nisaba, amma kuma likitocin sun tanbatar musu lokaci-lokaci ciwon zai ringa motsa mata, dan ɓacin raine ya taru mata a zuciya harya kai ga taɓa mata ƙwaƙwalwa.
An bata magunguna suka ɗakkota suka dawo da ita gida, a lokacinne Ahmad yay tunanin yakamata mama gaje ta koma gidansu kodan ta ringa samun kulawa, dan anan ƙarfin iya ya ƙare sosai, itama ƴarta sotake ta ɗauketa daga gidan, bai kamata kuma abar mama gaje ba kawai hakan zai sake girmama ciwonta.

Koda Ahmad yazoma da baba shawarar saiya aminta sosai, dan haka suka zaunar da baba Yusha'u sukai masa nasiha mai ratsa jiki akan yay haƙuri mama gaje ta dawo gidan da zama anan sashen iya ta ƙarasa rayuwarta, sai Samina ta cigaba da kula da ita har itama ALLAH ya bata miji tayi aure, dansu Ahmad watan gobe zasu koma saudiyya.
Yau ɗinma yaso turjewa, amma da sukaita lallashinsa sai ya yarda, dukda bada zaman aure zata dawo gidanba haka Ahmad yaɗan shirya masu ɗakin da zasu zauna ita da samina, katiface kawai sai kwabar kaya daɗan abin buƙata.
Haka aka dawo da mama gaje gidan abin tausayi, itama Samina akace ta dawo.
Jitai kamar ta fasa kuka, dan koda Ahmad baya kulata ganinsa da take yawanyi acan na saka zuciyarta yin sanyi, haka babu yanda zatayi ta dawo nan gifansu da zama.
Sai dai kuma sam babu jituwa tsakaninta da mama gaje, sai da su baba sukai mata faɗa akan hakan sannan ta nutsu ta fara bata kulawar da ake buƙata tana kaico da ALLAH wadai da rayuwar son zuciya da suka jefa kansu a ciki, da yanzu sune a daular dasu Ammi ke ciki, amma gasunan babu wan babu ƙanin, babu dukiya babu Ahmad, ita yanzu ko sunan ma'aruff ma batason tunawa a rayuwarta.
Tanaji tana gani fita ta gagari rayuwarta, saboda data fita yara zasu fara mata ihu, mazan dake majalissa na zunɗenta da dariya da kiranta *Matar manya*.
Wannan dalilan ya sakata haƙura da fita ko ina a rayuwarta, ga yaran Ahmad sam basa yarda da ita, Haysam ne kawai, shima zakiga yana ɗari-ɗari da ita, wanan abu har kuka yake sakata.
Dan akwai randa ta shigo sashen nasu Ahmad amsar ruwan zafi zata jiƙama mama gaje magani sai taci karo da Abu-Talib dake wasa a tsakar gidan ya faɗi, tai ƙoƙarin ɗagashi ya tashi yaronnan ya saka mata ihun kuka akan karta taɓashi.
Tana ƙoƙarin saukesane Ahmad ya shigo gidan, zuwansa kenan yazo gaushesu dan Abu-Talib ranar anan ya kwana shi da Haysam.
Jikinta har rawa yake wajen sauke Abu-Talib, a ranta tana tsoron kar Ahmad ɗin yay tunanin wani abu taima yaron ne.
Dan taga Ahmad ya tsatstsareta da idanu fuska a ɗaure, cikin rawar baki tace,
“Wlhy babu abinda nai masa, na iskesa ya faɗine shine nai ƙoƙarin tadashi amma yake kukan nan.......�?
Hannu Ahmad ya ɗaga mata batare da yace komaiba, ya kama hannun Abu-Talib dake ɓoye a bayansa suka bar wajen.
Hakan yasa Samina juyawa ta koma tana kuka batare da ta shiga amsar ruwan zafinba.
Wannan yasa duk son da take nason jan yaran a jikinta ta haƙura, sai dai ta kallesu daga nesa kawai.


★★★★★★

A wannan tsakanin Sadiya ta haihu ƴan biyu duk mata, su Rumana suka shiga jerangiyar zuwa gidan har akai suna, kwanaki hudu da sunan ƴaƴan sadiya Fa'iza ma ta haihu na uku, suka sake rankayawa katsina, Samina bataso zuwaba amma ƴan uwan sukace ta cire komai a ranta ta ringa shiga cikinsu, haka suka sakata dole taje, cikin ƴan shema ma ta kasa sakewa tanata laɓe-laɓe.
Bayan dawowarsu daga sunan Fa'iza Umm-Ruman ta roƙa Ahmad ya barta suje gidansu da suka zauna ta gaishe da su maman Ama idan suna nan.
Bai musaba ya barta, shima da kansa ya kwashesu amota dukansu ya kaisu.

Tun sallamar da Rumana tai a cikin gidan jikinta yay sanyi, gidan dukya canja kamanni tamkar ba shiba, ga kaya kaca-kaca, wanke-wanke a bakin rijiya ƙuda natabinsu.
Yara sai hayaniya suke suma kaca-kaca dasu babu mai shigar arziƙi.
Sai dai ganin ƴan gayu sun shigo gidansu yasa yaran yin tsit suka zuba musu idanu, Rumana ta sauke idonta akan Ahmad din maman Ama daya zama ɗan saurayi yana wanki a bakin rijiyar, yaron kamanninsa na nan basu canjaba, murmushi tayi na ƙarfin hali tana faɗin, “Ahmad ne wannan halan?�?.
Ahmad ya ajiye kayan hannunsa yana mutsika kumfar dake jikin hannun idonsa a kansu cikin ɗari-ɗari ya amsa da “Eh nine�?.
Murmushi ya ta sakeyi tace, “mamanka fa?�?.
Shiru yaron yayi cikin ƴar damuwa, kafin ya nuna mata ɗakin da Rumanan ta zauna.
“Tana nan ciki�?.
Rumana tace, “To ko barci take?, yimata magana kace ga baƙi�?.
Ɗauraye hannu yaron yayi yanufi ɗakin, babu jimawa ya fito yace, “Tace ku shigo�?.
Zuciyar Umm-Ruman cike da ɗunbin mamaki tabi Ahmad hannunta riƙe da Abu-Turab, su Haysam na biye da ita shi da Abu-Talib, sai kallon gidan suke cike da tsantsami.
Maman Ama dake kwance bisa wata yololuwar katifa ta tashi da ƙyar, gabanta da tsohon ciki, dukta lalace tayi baƙi tamkar mai ciwon yunwa.
Sam bata gane Umm-Ruman ba, amma ganin baƙuwar ƴar gayuce duk sai ta rikice, tai yunƙurin tashi danta nemo aron tabarma wajen kishiyarta amaryar dan sunfi shiri akan ta tsakkiyar amma sai Rumana ta dakatar da ita saboda tausayi.
Taja kujera ƴar tsugunno dake gefe ta zauna tana fadin, “Yi zamanki maman Ama, wlhy nanma ya isa�?.
Karon farko da gaban maman Ama ya faɗi. dan kuwa tasan Amarya ce kawai ke kiranta da wannan sunan.
Rumana ma data fahimci bata ganetaba, sai tace, “Niko maman Ama sai naga kamar baki ganeniba, Rumana ce fa�?.
Har taune harshe maman Ama keyi wajen faɗin, “Wai kina nufin Amarya matar Ahmad da suka zauna anan ɗakin?�?.
Rumana tai murmushi da cewa, “Lallai kam baki mantaniba, itace kuwa�?.
Babu shiri maman Ama ta miƙe zumbur jikinta na rawa, tama manta da nauyin cikin jikinta, sai tafa hannaye take jikinta na rawa tana sallalami.
Rumana dai nata dariya, cikin sassarfa Maman Ama ta fice tana ƙwalama kishiyoyinta kira, takuma aika yara su kira mata su maman Aysha duk da yanzu ba shiri sukeba, dan tuni anyi uwar watsi saboda maman Ayshan yanzu ta haɗe kai da kishiyar Maman Ama ta biyun.
Tuni gidan ya kacame, maƙwafta nata shigowa, wasuma dai ƙin yarda sukai Rumanan ce, saida ta rantse musu.
Rumana ta tambayi ina Kausar, anan suke sanar mata ai ALLAH yayma Kausar rasuwa wajen haihuwar ɗanta na huɗu, dama tuni sun tashi daga nan gidan an haɗa da kishiyarta, haihuwarta ɗaya acan ana biyun ta rasu bama ta haifesaba.
Hankalin Rumana ya tashi harda kuka, sai rayuwar ta kuma bata tsoro sosai, da haka da hakafa kowa zai kama gabansa.
Sai da gidan ya natsa aka barta daga ita sai Maman Ama a ɗakin take bata labarin halin rayuwar data shiga itama, yanzu su ukune a wajen mijinsu, kowa haihuwa take kamarmi saboda gasa, yanzu haka yaranta bakwai ga cikin na takwasa, taga wulaƙanci kala-kala wajen mijinsu bayan aurensa na biyu, dan shiya sakata ta dawo nan ɗakin aka saka shikiyarta a nata ɗakin, lokacin Kausar na nan bata koma gidan kishiyartaba, zaman dai babu daɗi damuwar yau daban ta gobe daban, kishiya ta sakata gaba wajen miji, yazo ya saketa taje gida tai zama kusan shekara ɗaya, harma ta kwashe kayanta ta saida, sai kuma ya dawo da ita, kasancewar ta saida kayan ɗakin daga ita sai katifa da ƴan kwanika ta dawo, ta dawo babu jimawa su Kausar suka tashi, tana ɗoki zata koma ɗakin da kausar din ta tashi tunda shima ciki da falone sai kawai mijinsu yazo da zancen zai ƙara wani auren na uku.
Kishiyarta tata tsiya, babu dai yanda zatai ya auro suka zama su uku, da farko sun haɗe mata kai kamar yanda Kausar suka haɗe mata kai itada kishiyarta ta farko, to da zama yay zama kuma sai amaryar ta dawo wajen maman Ama din suke mutunci, yanzu haka ƴaƴan gidan kusan goma sha tara, dan kishiyarsu ta tsakkiya sau biyu tana haihuwar ƴan biyu.
Tace yanzu haka dai gasunan zaman babu daɗi, miji nauyi ya masa yawa yama barmusu nauyin kansu kowa itake cida kanta da ƴaƴanta a gidan, inya samo ya miƙama kowa abinda ya samu, idan bai samoba bamaya zuwa gidan sai sulusin dare, daga sallar asuba kuwa bazai dawoba, dukda wannan halin da suke ciki yanzu haka sunji labarin aure kuma yake nema na wata bazawara.
Maman Ama ta share hawaye da cigaba da faɗin, “Amarya wlhy yanzu haka yaran gidannan babu mai zuwa koda islamiyya, haka suke tantal baɗeɗe cikin anguwa kamar ƴaƴan akuyiyi, Wlhy ki godema ALLAH amarya, ƙyaƙyƙyawar zuciyarku ke da mijinki itace taimuku jagoran zama masu nasara a rayuwa, baku ɗauki duniyar da zafiba, kunyi haƙuri da kaɗan da ALLAH ya baku gashi yau kune ke riƙe da mai yawan, Amarya dan ALLAH ki yafemin abinda nai miki a zamanmu, wlhy nayi nadama, na gane manufar rayuwa a yanzu, dan dukkan abinda mukai miki nida marigayiya Kausar nima saida sukaimin ita da kishiyata, bayan barin kausar gidan kuma kishiyiyi suka kuma min, tun anan na gane mun cutar dake matuƙa, zafin da naji yasa har yanzu na gaza yafema Kausar abinda sukaimin ita da kishiyata a gidan nan.........�?
Cikin hanzari Umm-Ruman tace, “A haba maman Ama, dan ALLAH karkice haka, ki yafema Kausar dan ita tata tarugada ta ƙare kuma, wlhy ni dama ban taɓa riƙeku a rainaba, nakuma yafe muku. ALLAH ya gafarma Kausar ya raya abinda ta bari�?.
“Hakane Amarya, amin ya rabbi, shikenan na yafe mata, ngd nima da kika yafemin, dan ƙila da wuya nima na tsallake din a wannan haihuwar, ban taɓa ɗaukar cikin dake bani wahalaba kamar wannan cikin�?.
“Insha ALLAHU lafiya lau zaki haihu Maman Ama, raiyuwa da mutuwa duk a hannun UBANGIJI suke ai�?.
“Hakane amarya, ALLAH ya tabbatar, dan nima ba mutuwar nake soba kodan gudun halin da nake hangoma ƴaƴana zasu shiga�?.
Rumana ta tausaya mata sosai, ta saka aka kira mata ƴaƴan maman Ama duka ta gansu, ta saka musu albarka.
Su Abu-Talib kam ai Haysam ne kawai ya yarda maman Ama ta taɓashi da maƙwafta da suka shigo, Abu-Turab kam dama shi babu yarda, hakama Abu-Talib ƙin yarda yayi dukda hararar da Rumana taita antaya masa.
A gidan Rumana ta yini, da rana Maman Ama taciyo bashin gurasa ta kawo mata, Rumana bataƙiciba, su Haysam ne dai saida taimu jan ido sannan sukaci, bayan sallar la'asar ta kira Ahmad akan zataje tai gaisuwa gidansu Kausar.
Ya tambayeta wanene ya rasu?.
Anan take faɗa masa ai Kausar ɗince ta rasu, sosai shima maganar ta daki zuciyarsa, yayta jinjina abin a ransa, yace ta jira yazo sai ya kaisu dan yana ta wajen anguwarma.
Shine yazo ya ɗaukesu harda maman Ama da ganin Ahmad ya sake rikitata, wlhy idan a hanya ta gamu da Ahmad da Rumana sam bazata taɓa ganesuba.
Sunje har gidan su Kausar sukaima mamanta gaisuwa, Ahmad yay musu alkairi tare da alƙawarin aiko da taimakonsa wa ƴaƴan da Kausar ɗin ta bari, suka kuma biya ta gidan auren Kausar din sukaima mijinta gaisuwa.
Daga nan suka maido maman Ama gida Rumana tai mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login