Showing 111001 words to 114000 words out of 165545 words
da gwaggo da Ammi dake nuna kawaici suma sukan kawo nasu taimakon.
Yayanta kuwa yana ƙoƙarin kiranta a duk sanda ya samu lokaci, musamman ma da daddare da sukam shafe dogon lokaci suna fira.
Mama gaje kuwa dawowar Rumana gidan ya sakasu farin ciki, koba komai zasu sami cikar burinsu a cewarta, dan haka ta shiga a jerin masu tattalin Rumana ko kunyar ALLAH bataji, kowa kuma a gidan kallonta kawai yake yi.
Samina kuwa bini-bini tazo gidan, taita kawoma Umm-Ruman abubuwa, duk abinda ta kawo amsa kawai Rumana take tana bama Ayyah na ajiyewa.
Wannan karon dai Ahmad yaja dogon zango bai zoba, dan wata harya mutu an shiga wani bai zoba, sai haƙuri ya abasu akan abubuwa sun masa yawa maybe zaiyi haƙuri sai Rumana ta haihu tunda ta shiga watanta.
Kowa ya amshi uzirinsa da masa fatan alkairi, garama Rumana taɗan masha shagwaɓa akan ita dai tana kewarsa gaskiya.
Dariya yayta mata yana lallaɓata har tace itama ta haƙuran.
_________________________________
Yau Umm-Ruman tana sati na uku a gidansu, har kuma ta shanye watan haihuwarta ta shiga wani, kowa dai fatan sauka lafiya yake mata a kullum, danma cikin ba wani irin girman nan yayiba can sosai.
Yau dai haka ta tashi ba wani walwala, da yake Ayyah tasan wannan yanayin mai tsohon ciki takan tsinci kanta sai takeya lallaɓata.
Tunda akai sallar la'asar takejin wani azababben zafi, Ayyah ta shinfiɗa mata tabarma a ƙofar ɗaki tace ta zauna tasha iska a wajen.
Gidan shiru saboda duk yaran sun tafi islamiyya.
Ayyah ta fito daga ɗakinta ɗauke da kwanika guda biyu, ɗaya ƙwaɗon zogale ne da yaji kayan su tumatur harda cucumber sai ƙamshi yake, ɗaya kwanon kam jiƙaƙƙen zoɓone, tunda Ayyah ta ajiye kwanikan Rumana ta canja fuska, Ayyah dai batace uffanba sai dariyarta data haɗiye.
Tunda Umm-Ruman tazo gidan babu abinda takeso irin kayan ƙwaɗayi, tace wannan, tace wancan, shiko Mudan da Abu da Baba basa gajiya da saya mata, Ayyah taga abin zai wuce gona da iri, dan randa taje asibiti na ƙarshe tare sukaje, Doctor yayma Rumana gargaɗin rage cin nama, harma da wasu abubuwan, ya basu shawaran taɗan ringa cin ganyayyaki haka zasu taimaka mata, wannan abu ya bama Rumana haushi, dan tunda suka dawo Ayyah ta ɗaura ɗammara, kullum da kalar da zata bata safe da rana, abinci ko shima bamai maiƙoba sosai.......
“Gashi nan maza a ci�? Ayyah ta faɗa tana katsema Rumana tunani.
Cikin kumbura fuska da tara ƙwalla a ido Rumana tace, “Ayyah banajin yunwa fa�?.
“Eh ai wannan basai anji yunwaba dama, zogale ai ba abinci bane maganine, ga jiƙon zoɓonan tun safe na yisa amma ko kurɓa guda baki masaba, kar na gama sharo ɗakin malam baki cinye zogalen nanba, inba hakaba ɗura zan miki yau a gidannan ehe�?.
Rumana da idonta ya cika da ƙwalla tace, “Kai Ayyah�?.
“Tom ki zauna harna fito ki gani�? Ayyah tai maganar tana shiga ɗan lungun Baba.
Gwaggo na daga ɗaki tana jiyosu, tai murmushi kawai abunta.
Kwanon Rumana taja ta ajiye gabanta, dan tana zaune ne ta miƙe ƙafafu, tagumi tayi ta zubama kwanikan idanu....
Dai-dai wannan lokaci Ahmad ya iso ƙofar gidansu, Mudan ne kawai a shago, anguwar babu yawan hayaniya saboda yara duk yawanci suna islamiyya, ko majalisar abokansa ma babu kowa sai Rabi'u kawai shi kuma yana daga cikin shagone baiga isowar Ahmad ba.
Mudan ya rungumesa yana mai nuna tsantsar murna da mamakin ganinsa.
Murmushi Ahmad yay yana faɗin, “Har yanzu dai ana nan da hali bai canjaba ɗan gidan Gwaggo�?.
Dariya Mudan Yayi, yace, “Ina da kai Yah Ahmad ai ni kullum shagwaɓaɓɓe ne�?.
Murmushi kawai Ahmad yayi, shigewarsa yay yabar Mudan da mai Napep ɗin suna sauke kayan da yazo dashi.
Bai gamu da kowaba a soron harya ƙarasa sashensu, da Umm-Ruman ya fara tozali, ya ɗan wawwaiga ko ina baiji mitsin kowaba, sai ita kaɗai tayi tagumi tare da ƙurama kwanikan gabanta idanu.
Wani tausayinta ne ya sake kamashi, ya tura hannayensa duka cikin aljihun wandon shaddarsa kalar ruwan ƙasa yana murmushi, a hankali ya buɗesu ya sauke akan cikinta daya fito sosai, sai dai kuma bai wani irin girman nan na tsiyaba kasancewarsa cikin fari, gashi ita kuma doguwa ba laifi.
Takawa ya farayi a hankali zuwa gareta, amma sam bataji koda motsinsaba, saboda tayi zurfi a tunani.
Harya iso ya zauna a hankali kusa da ita gab, ƙafarsa ɗaya a ajiye ya ɗora hannunsa, ɗayar kuma ya tanƙwasheta yayi dafe da hannunsa a ƙasa, yanayin zaman sai ya basu kusanci sosai.
Gashi dai ƙamshin rurarensa ya cika tsakar gidan har hancin Rumana, sai dai hankalinta sam baya tare da duniyar mutane.
Sassanyar murmushi Ahmad ya sakeyi tare da matsar da kansa dab da kunnenta, cikin magana raɗa-raɗa yace, “Gwal ai ga abinda kike tunanin kusa da ke�?.
Firgigit Rumana ta dawo hankalinta, ta zaro ido waje babu shiri dan ita tsoratama tayi, catake ko aljanine yazo mata a suffarsa...
Da sauri yace, “Surprise�?.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Rumana ta sauke tana kumbura masa fuska, harda kai masa ɗan ƙaramin naushi kamar gaske, shiko yay saurin matsawa baya da riƙe hannun nata yana ƙaramar dariya.
“Yi haƙuri manyan mata�? yay maganar yana sumbatar hannun nata daya riƙe, tare da sakata jikinsa ya rungume.
Sam ta manta a inda suke, dan haka tai luf tana sauke ajiyar zuya.
Ahmad yay murmushi sosai yana ɗagota daga jikinsa, ya zuba idanunsa cikin nata, bata janyeba, dan wani irin mugun kewarsa takeyi, sai cika sukai da ƙwallan da ita kanta batasan dalilinsu ba, hakan sai ya ƙarama idanun ƙyau, fuskarsa ya matsar dab da tata tamkar zai haɗe, hakan ya saka Rumana lumshe idanunta ƙwallan da suka taru a ciki suka gangaro bisa kumatunta.
Bakinta da ta tsuke ya sumbata shima yana lumshe ido, yaɗan janye kaɗan yana ɗora hannunsa saman cikinta, “ALLAH yay miki albarka Babie R�?.
Bata iya cewa dashi komaiba sai goshinta data jingina da nashi tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, itama ta ɗaura hannunta saman nashi dake kan cikinta, tace, “Yayana nayi kewarka, musamman yau da son ganinka na tashi sosai, ban saniba ko bazan tsallakeba mutuwa zany....�?
Gwaggo da taji motsi ta ɗaga labule zatonta ko dabbobine, da sauri ta saki labulen saboda ganin Ahmad da Ruman, ita dai bataji motsin shigowarsa gidanba sam.
Su Ahmad da basusan anaiba Saurin buɗe ido yay yana janye kansa daga jikin goshinta, ƙirjinsa sai wani fat-fat yake alamar tsoro, sam baiyi zaton wannan furucin daga bakinta ba,
Yace, “Gwal karna sake jin haka daga bakinki kinji ko�?.
Kallonsa tai, yanda fuskarsa ta nuna alamun ruɗani sai ya bata tausayi, murmushi tai masa, cikin son kauda masa tsoron data hango cikin idanunsa tace, “Wasa nake fa, mutuwa ai tana wuyan kowa, kuma kowa zai iya tafiya a kowane lokaci�?.
Duk da maganarta bata kore masa abinda yakejiba hakan bai hanashi mata murmushi ba, ya riƙe hannunta da take shafa masa fuska, shima cikin ƙoƙarin son kauda zancen ya shiga buɗe kwanikan gaban nata.
“Ƴar gata minene aka jera miki anan?�?.
Baki ta cona gaba dan ya tuna mata aikin dake gabanta, ga gargaɗin Ayyah.
“Woow Gwal duk ke kaɗai?�?.
Da sauri tace, “Dan ALLAH tayani ci yaya kafin Ayyah ta fito�?.
Yaɗan zaro idanu yana magana ƙasa-ƙasa sai kace mai gulmar wani kuma baiso a jisa, “Kina nufin ke nan baƙya son ci?�?.
“Eh mana�? tai maganar tana kuma tura baki.
Yace, “K baƙauyace dama ai�? yay maganar yana ƙoƙarin ɗauraye hannunsa da butar kusa da ita.
Ita duk zatonta shine zai taimaketa ya ci, sai taga koda ya ɗebo zogalan da hannunsa ya nufo bakinta. Ta kallesa ido cike da ƙwalla tana narke masa fuska dan yaji tausayinta.
Kansa ya girgiza mata alamar kar tayi kuka, tare da lumshe ido da buɗewa alamar ta daure.
Bakin ta buɗe masa ya zuba mata, ta shiga taunawa a yamutse, shi dai kallonta kawai yakeyi a ransa tana bashi tausayi da dariya.
Kuma ɗebowa yayi ya kuma kaiwa bakin nata, nanma sai da ya marairaice fuska alamun lallashi sannan ta amsa.
Mudan dake laɓe shi da Ayyah suna kallonsu kowa ya saka hannu ya toshe baki yana ƙoƙarin danne dariyarsa.
“Ayyah kinga ɗanki fa, shiru-shiru dashi amma hummm...�?
Ranƙwashi Ayyah taima Mudan, har zaiyi ƙara sai kuma yay sauri toshe baki yana shafa inda ta rankwasheshin kawai.
Ayyah dai murmushi take tayi, dan taji daɗin yanda Ahmad ke bama Rumana kulawa.
Gwaggo kam bata sake yinƙurin ko ɗaga labulenba, saima ƙarar redion ta data ƙaro daga cikin ɗaki.
Daga Ahmad har Umm-Ruman shauƙin juna yama mantar dasu wani zai iya shigowa, musamman ma Mudan daya baro da kaya a waje, yana ƙoƙarin sakama Rumana laumar zogalen kusan ta baƙwai su Zainab sukai sallama, wani ihun murna ta saki na ganin yayan nasu.
Hakanne ya maido su Ahmad hankalinsu suka tuna a inama suke, amma duk da haka bai daina bata zogalen ba.
Ayyah da Mudan ma suka fito daga maɓoyarsu ta lungun Baba suna dariya.
Anan ne kunya ta kama Ahmad, yaɗan matsa baya kaɗan daga nanuƙe Rumana da yayi, yay mata nuni da idanu wai ta cigaba daci.
Ita kanta taji kunya, hakan ya sakata duƙar da kai ƙasa.
Ita dai Ayyah sai ta hau masa lale da wannan zuwan bazata danta kauda kunyar dataga ta lulluɓesa............✍�?
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_36_*
*_Mai gadon kara🥳😲_*
..............Koda Ahmad ya gama gaisawa da mutan gida da ƙannensa harma da iyayensa, yaci ya ƙoshi Ayyah tai masa maganar tafiya can gidan sai ya ɓata fuska.
Tace, “Tofa ɗan albarka yaya dai?�?.
“Nifa Ayyah ni kaɗai zan koma can yanzu? Duk kowa yana nan ni sai a wareni?�?.
Kasa daurewa Ayyah tayi ta kwashe da dariya, Rumana ma ƙasa tai da kanta tanayin tata, hakama Zainab da suka faɗa cikin ɗaki, dan bazasuyi a gaban saba tunda sunsan sauran.
Harara yaketa zubama Umm-Ruman yana sake kumbura fuska.
Ayyah tace, “To yanzu ya kakeso ayi kenan?�?.
“Nima Ayyah ban saniba dai, ki kawo shawara�?.
Ayyah tace, “Ga shawarar na kawo nace katafi gida ka huta ka kamamin shagwaɓa�?.
Yace, “Toni Ayyah tsorofa nakeji, ni kaɗai a ɗakin ai sai wani abu ya cinyeni kafin safiya�?.
Ba Ayyah ba hatta Gwaggo dake ta ayyukanta bata saka musu baki sai da tai murmushi tana girgiza kai, yayta mazurai wa yaran gidan da shan toka, amma idan yana gaban Ayyah jinsa yake tamkar wani ƙaramin yaro.
Zama Ayyah tai tana lallaɓa Ahmad, dan tuni su Fa'iza suka tafi kimtsa masa ɗakin, aiko da ƙyar ya yarda ya tafi.
Rumana ta sauke ajiyar zuciya tana maijin ƙaunarsa har can ƙasan ranta.
★★★★★★
Koda Ahmad ya isa gida ya iske su Salima sun gama komai suna wanke masa bayi ne da duk ya ƙazance, saboda su Maman Ama sai sun gadama suke wankewa, amma fa ba kullum bama saboda kowa na ganin ƙyashin ya gyara wani ya amfana, dai dai da tsakar gidan yasan Rumana bata gidan, dan duk ya fitta hayyacinsa, wani lokacinma Ahmad suke sakawa sharar ɗan ƙarami dashi.
Su Kausar dai mamakin yanda Ahmad kullum ya dawo sai kaga sabon canji tattare dashi sukeyi, harsu fa'iza suka wuce ya shiga wanka basu bar satar kallonsa ba.
Shi baima san sunaiba, saurin kimtsawa yay dan gidan duk babu daɗi yakejinsa, jinsa yake kamar wani maraya da baida kowa, gidan ya masa girma saboda rashin Gwal ɗinsa a ciki.
Sauri-sauri ya gama shiryawa ya sake fitowa, lokacin anata kiran sallar magriba.
Bayan anyi sallar isha'i Rumana na kwance tana kallo a waya bisa gadon Ayyah ƙarami na ƙarfe kawai sai ganinsa tai ya shigo ɗakin da sallama.
Da mamaki ta ajiye wayar ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonsa, Yaya dama baka tafiba?.
Zama yay a bakin gadon yana harararta, “Oh baƙyason ganina ne?�?.
“Taɓ ni na isa�?.
Yace, “Ina su Ayyah?�?.
“Su Ayyah sunje gidan Inna mariya wai bata da lafiya, dama da yamma sukaso zuwa dubata sai kuma ka dawo, shine sukace tunda sunyi niyya gwara suje dubata a darennan dan Sadiqu na nan gidan malam ne ya tafi kaisu�?.
Gaba ɗayansa ya juyo yana kallonta, yace, “Tun yaushe suka wuce?�?.
Rumana bata fahimci bin ƙwanƙwanton maganarba tace, “Yaya yanzun nanfa, dan namayi mamaki da baku haɗu dasu a ƙofar gida ba�?.
Wani nannauyan numfashi taji ya sauke, yace, “Su fa'iza fa?�?.
“Suma yanzu suka wuce makarantar dare, kusan tarema suka fita dasu Gwaggon�?.
Shiru yay yana ƙiyasta nisan inda su Gwaggo suka tafi da lokacin da zasu iya ɗauke. Ita dai Umm-Ruman kallon mamaki taketa masa, gani tai kawai ya miƙe ya kama hannunta yana fadin,
“Kinga sakko muje kiga wani abu Gwal ɗina�?.
“Wani abu kuma Yaya a ina?�?.
Bai bata amsaba ya taimaka mata ta sakko, haka ya jawo hannunta suka shige ɗakinsu Fa'iza, sam bata kawo komai a rantaba, ta daiga ya sakama ɗaki sakata, dama ɗakin babu fitila da wayarsa ya haska.
Yaja hannunta suka hau saman katifar, danma karta kawo masa togaciya yasha toka.
Tunda ya kashe fitilar wayar tasa kuma sai tsoro ya kamata, tace,
“Yaya wai lafiya?�?.
“Shiiii!�? ya faɗa yana kwantota jikinsa, da ɗora fuskarsa akan dokin wuyanta.
Duk yanda taso hanashi ta kasa, bawai itama bata buƙatar inda taga ya dosa bane, a'a kunya takeji da tsoron kar wani ya shigo gidan, tunda Abu da Mudan da Baba duk suna a anguwar, sannan su Ayyah ma ai zasu iya dawowa, kokuma wani a cikin gidan, musamman ma Iya da bata gajiya da leƙowa dubata, garama su Fa'iza da sauran lokaci.
Duk salon da yasan zai mata jikinta yay laushi shi yayta bi, sai da yaga tayi tuɓus ta miƙa wuya sannan.
Bakinta na rawa tace, “Yah Ahmad ba gidanmu bane fa nan, dan ALLAH kayi haƙuri....�?
Muryarsa a sheƙe yace, “Idan nayi haƙurin kina da maganin bani ne na samu nutsuwa?�?.
Kanta ta girgiza masa, ta sake buɗe baki zata masa bayanin da zai fahimta, ya rufe bakin gaba ɗaya ma........
__________________________________
Tamkar jira, Ahmad na samun nutsuwa ciwo ya tashi daga Umm-Ruman, ta fara da kukan bayanta, mararta.
Saurin saka kayansa yayi itama ya maida mata nata duk ya rikice saboda kukan da takeyi.
Da ƙyar ya samu suka fito daga ɗakin tanata yarfa hannu da ƙara ƙarfin kukanta, dole dai ɗakin Ayyah ya maidata yay saurin nufar sashen Ayyah ya