Showing 84001 words to 87000 words out of 165545 words
“K dan ubanki duniya kike faɗama yanda aikai ne?�?
Da sauri Adam ya janyesa yana masifa, “Wai kai MJ mike damun kankane? Yarinyar dama batasan ina a hankalinta yakeba kakema wannan Marin? Kaji tausayin halin da muka sakata mana, wlhy badan tanada sauran shan ruwaba a ɗazun zata iya rasa ranta, kai baka da wani abin birgewa sai dukan mace? Wannan fa matarkace ta sunna ba matan banza daka sabama wannan rayuwarba, Mtsoww, baka sha giyarba ma rasa hankalinka ake......�?
A fusace Ma'aruff ya dakatar da Dr Adam, “Malam karka faɗamin babu daɗi mana, bansan shishshigi kaima ka sani�?.
Banza Dr Adam yay masa, ya shiga ƙoƙarin ganin Samina da numfashinta ke fita da ƙyar bama taimakon gaggawa, dole dai allurar barcin ya sake mata saboda sam bata a cikin hayyacinta, a ƙasan ransa yana dana sanin biyema Ma'aruff akan wannan aikin.
Acan waje kuwa su mama gaje na iya jiyo hayaniyar su Ma'aruff, sai dai basajin mi suke faɗa, tuninsu ma duk ruɗewar halin da Saminar ke cikine ya jawo hakan, hakan yasa suma suka sake rikicewa ainun.
A fusace Ma'aruff ya fice daga ɗakin, ko kallon su Baba dake wajen dasu mama gaje baiyiba balle su sami mutuncin a gaishesu, su duk ganinsu halin da matarsa ke cikine ya sakashi a ruɗani🥺.
Basusan ma yana fita daga asibitin zuwa yay ya tanaji giyarsa ba tare da tsaleliyar budurwa suka nufi gida, tunda yau babu Samina a cikinsa anan zai warwasa abinsa😢.
★★★★★★★★★★�?
Ina bakin rijiya zaune ina wankin ƙarfin hali saboda kaina dake mani wani azabar ciwo, gaba ɗaya kwanakinnan haka nake fama da wannan ciwon kai, abinda kawai nasaka a raina basir ne yaymin mugun kamu da malleriya, sallamar yaran gidanmu ta sakani ɗago idanu na kallesu, ni kaɗaice dama a gidan, Kausar taje asibiti wai yaron cikinta na dawo mata a ƙirji, maman Amatullah kuwa tana gidansu sunan ƙanwarta data haihu, su Fa'iza kuwa tun da safema suka tafi gida yau.
Sallamarsu ta amsa fuskarta dai babu walwala.
“Ku kuma daga ina? Da wannan tsakar ranar khadija?�?.
“Yaya Rumana daga gida mukefa, Yaya Samina ce bata da lafiya tana asibiti�?.
Ajiye hijjab ɗin danake cuɗawa a cikin ruwan kumfar nai ina faɗin, “Ya salam, miya sameta haka?�?.
“Muma bamu saniba, amma dai su Ammi ma duk sunacan sunje dubata�?.
“Wayyo, to ALLAH ya bata lafiya, zan kira Yah Ahmad kuwa nasamu zuwa anjima naje na dubata�?.
Haka Rumana ta cigaba da wankinta su khadija na tayata da hira, duk da ma ita ba saka musu baki takeba dan kanta dake ciwo, da yake wankin baida yawa dan danan ta kammala, tana share ruwan wajen Kausar ta shigo tana ɗaga ƙafa da ƙyar saboda ciki, duk da yanzu bata min magana hakan bai hanani mata sannu ba.
“Uhumm�? kawai tace min ta buɗe ɗakinta ta shige.
Ban damuba, nima na haɗa robobin danai wankin na nufi nawa ɗakin, muna shiga na bama su Khadija kantu daya rage a kayan sana'ata nace suje gida kar'a nemesu, dan nagaji da surutunsu nikam.
Da murna suka amsa suka wuce, nikuma na shiga duba magani dan nasha sai dai ma ashe ya ƙare, ƙaramin tsaki naja na haye gado na kwanta kozan samu sassauci.
Ring ɗin wayartane ya tasheta daga nannauyan barcin datai nisa a ciki, ta kai dubanta ga agogon ɗakin tana ƙoƙarin lalubo wayar a ƙasan filo.
Ƙarfe biyar na yamma, agogon ya nuna, tashi nai zaune a rikice dai dai na gama ciro wayan, Yaya Ahmad ne, kafin na ɗagama ta tsinke.
Ina ƙoƙarin sakkowa ya sake kira, dakatawa nai na ɗaga ina kaiwa kunne.
“Kina lafiya kuwa? Tun ɗazun nake kira amma babu amsa�?.
Cikin yanayin wanda ya tashi a barci nace, “Kayi haƙuri Yaya, wlhy barci nake�?.
Daga can yace, “Barci kuma? Lafiya dai ko?�?.
“Lafiya ƙalau, kaina ne kawai kemin ciwo dan wankima na gama�?..
“Na rasa wannan ciwon kai na miye haka? Kusan kullum yanzunfa sai kinyi?�?.
“Wlhy kuwa Yaya, amma karka damu inaga basirne, zan aika iya ta bani magani�?.
“ALLAH ya ƙara sauƙi, yanzu kinsha magani ko?�?.
“A'a maganin ya ƙare, jira nake anjima idan Yah Mudan yazo sai ya sayo mani�?.
“Bara kawai na kirashi sai ya kawo miki yanzun, ina zama da ciwo yaga daɗi�?.
“To Yaya na gode, itama Yaya Samina ma bata da lafiya�?.
Shiru yay kamar bai jitaba, hakan yasa tai tunanin baijinba ta sake maimaita masa.
Cikin halin ko in kula yace, “ALLAH ya ƙarama kowa lafiya�?.
“Amin yaya, ammafa abin serious ne fa, dan tanama asibiti, na shirya naje na dubota dan ALLAH?�?.
A hasale yaja tsaki yana faɗin, “Malama kiji da naki ciwon kinji, inada abunyi sai anjima�? ƙit ya kashe wayarsa.
Shiru nayi a wajen tamkar ruwa ya cinyeni, na zame wayar a hankali ina kallonta kamar zan hangosa ta ciki, dama tun jiya nasan haushina yakeji saboda su Fa'iza sunce zasuje gidan Yaya Samina, nima saina tambayesa dan naje nagano ɗakin amarya daga nan mu wuce gidan sunan ƙanwar maman Ama da akeyi.
Aiko naci masifa, dan Yah Ahmad na asali dana sani ya komamin, tamkar zai jawoni daga wayar ya daka, daga ƙarshe ya kashe wayarsa ma baki ɗaya, na gwada kira yafi sau hamsin amma switch up, ni kuma yanzu sam banyi zaton abin zai ƙara ɓata masa raiba tunda dai ciwo akace.
Damuwa fal raina na tashi na fita, dan ko sallar la'asar banyiba, tsakar gidan shiru kamar babu mutum, dama dagani sai Kausar ne, mai raya gidan maman Ama ce kodan saboda ƙiriniyar yaranta.
Bayan na idar da salla na ɗauki waya na kirashi, amma harta yanke bai ɗagaminba, na kuma kira ban gajiba, sai da na jera masa kira goma sannan ya ɗaga.
A hasale yace, “Ke wai bakisan ina kasuwa bane? Idan kika takura min da maganar nan zan ɓata miki rai wlhy�?.
Bai jira ma mizan ceba yanzun ma ya sake yanke min wayar, hawaye masu ɗumi suka shiga rige-rigen fitowa a idanuna suna silalowa bisa kumatuna, ni bansan lokacin da ya farama Yaya Samina irin wannan baƙar tsanarba? nima dai na shagala wajen mantawa murɗaɗɗen halinsa ne, darajar aurenmu yasa na fara ganin haƙoransa a waje, suma ɗin a wannan zuwan.
Zamewa nai na kwanta ina cigaba da hawayena.
Sai bayan isha'i yau su Salima sukazo, dan sune ke a gidan saboda su Ammi sunje duba Yaya Samina a asibiti.
Yanda suke bani labarin halin da Yaya Saminar take ciki sai tausayinta ya kamani, na mata addu'a dan nasan tunda yace bazan jeba to bazanje ɗinba, dan sunan ƙanwar Maman Ama da yace bazanjeba jiya gashi banje ɗinba.
Sai da zan kwanta ne danaga har lokacin bai kiraniba nai masa text message na ban haƙuri da kalamai masu sanyi na tura masa.
Haka na kwanta cikin damuwa, da ƙyar barci ya ɗaukeni kuwa, dan ya sabamin duk dare ko bazamuyi hira mai tsaho ba dai zamu gaisa yaji lafiyata naji tashi kafin na kwanta.
Da safe ko da su Fa'iza sukace na shirya muje dubota, canai musu suje kawai banajin daɗi, danma karsu zargi wani abu sai nace jiri nake gani.
Sannu sukaita jeramin kafin su wuce, nace suce ina gaisheta dan ALLAH.
Bayan wucewarsu na ɗauki wayata na sake dubawa, a zatona ko zanga reply ɗin Yah Ahmad, amma sai naga wayam, tagumi nayi na zubama wayar ido kawai.
Duk da motsin Kausar da nake jiyowa a tsakar gida ban fitaba sai da zanyi sallar zuhur, dan kafin su Salima su wuce komai sunmin har ɗibar ruwa.
Banga Kausar a wajeba yanzun, ta shige tuni, na laru dai batajin daɗi kwana biyunnan, ɗakinta na nufa nai sallama, sai da nayi kusan uku sannan ta amsa min, ban damuba na shiga ciki, kwance take a ƙofar ɗaki, ɗakin kaca-kaca babu gyara, na zauna a kujera ina mata sannu da tambayarta yaya jikin?.
Nanma da ƙyar ta amsamin cewar da sauƙi.
Duk da nima ba ƙarfin nakeji ba haka na tashi na fara kimtsa mata ɗakin, dan yayi datti da yawa, da alama dai tama daɗe batai gyaransa ba, wanke-wanke kansu cike da babbar robarta ta tara, bayan na gyara gadon nace ko zata koma can.
Bata musaba ta yunƙura zata tashi amma ta kasa, taimaka mata nai ta miƙe ta koma saman gadon, nikuma na ƙarasa kimtsa ɗakin harda morping duk nai mata, na kwashi wanke-wanken na fita dasu.
Har la'asar ina ma Kausar hidima, sai da naga komai yayi fes sannan nace mata ta daure tayi wanka zataji ƙarfin jikinta, kanta ta ɗagamin kafin ta fara jeramin godiya.
Nai murmushi da faɗin babu komai karta damu, koda na fito nai alwalar la'asar ɗaki na koma, ban sake fitowa ba sai da Maman Ama ta dawo gab da magriba.
Sannu da zuwa nai mata tare da ALLAH ya raya, na kuma bata haƙuri akan rashin ganina da bataiba.
Ta ɗanyi dariya tana bina da kallon ƙurulla, “Babu komai Amarya, ai dole nai miki uziri tunda ban saniba ko ogane ya murɗa kambunsa, dan ba kasafai suke son yawan fitarba�?.
Murmushi nai nace, “A'a bama shi bane, kawai dai jiya na yini ne da ciwon kai wlhy�?.
“Ayyah, to UBANGIJI ya ƙara lafiya�?.
Da Amin na amsa ina tsokanar Amatullah dake cin biscuit.
________________________________
Ɓangaren Samina kam sai washe gari ta farfaɗo cikin hankalinta, taƙi magana wa kowa sai hawaye, hakan ya saka Inna mari fara mata masifa akan ai ba kanta aka fara ɓarin ciki ba, idan tayi haƙuri ALLAH ne zai bata wani.
Ita dai batace uffan ba, sai da taga ƴan dubiya nata zuwane sannan ta daurema ranta ta daina kukan, sai tsoro ya kamata sosai da lamarin mutane, dan wasu idan akace ɓari tai sukan jinjina maganar, harda masu cewa ikon ALLAH, yanzu cikin sati uku har yakai ai ɓarinsa?.
Wannan furuci da mutane ke yawan yi sai ya fara ɗarsama mama gaje da inna mari shakku suma a ransu, ga mamakin rashin dawowar Ma'aruff asibitin, tun daren jiya daya fita cikin fushin abinda Aliyu yay masa su kuma suka ɗauka damuwar halin da matarsa ke a cikine, sai kuma rashin ganin danginsa da basu zo duba Samina ba.
Koda mutane suka tsagaita zuwa yamma inna mari kasa haƙuri tai sai da tai maganar rashin dawowar Ma'aruff ɗin da rashin zuwan danginsa.
Uffan Sanina dake kwance bata ce ba, duk da kuwa taji mi Inna Mari ɗin ta faɗa sarai.
“Wai Samina bakiji mina faɗa bane halan?�?.
Kallo ɗaya Samina tai mata ta janye idanunta gefe, “To idan najiki mizance Inna mari? Naga dai kwance nake anan ta yaya zansan lafiya ko saɓanin hakan�?.
“Kefa dama baki da kunya Samina, daga tambaya minene namin baƙar magana dan rashin arziƙi�?.
Shareta nanma Saminar tayi, saima ta rufe ido kamar mai shirin barci.
Har suka kwanta babu Ma'aruff babu dalilinsa..........✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(28)*
.............Yau ɗinma har na kwanta banga kiran Yah Ahmad ba, duk da abin nacin raina haka na danne nima na sharesa kawai.
Washe gari da safe na fito zanyi wanke-wanke sai naji Maman Ama da Kausar na gulmata wai bilicin nake, saboda nayi wani mugun haske fatata har ƙyalli take.
Ni dariyama suka ban, toni tunma ina budurwa bayan basilin zanma iya rantsewa ban taɓa siyan wani mai dan na sama jikina ba, ina naga kuɗin sayen to, sai dai idan munje kamar gidan yayunmu mun ganine mukan shafa wani lokacin......
Maganar Kausar dake cewa, wai jiya da nake mata aiki itafa kasa ɗauke kanta tai daga kallona, saboda nayi ƙiba ga fari, anyama mai nake shafawa kuwa ba allura naje akaiminba na kumasha maganin ƙiba dan ace inajin daɗi wajen miki? Dan inda maine da ƙafata saita nuna, amma dukfa jikinane yay hasken.
Kaina na girgiza kawai ina murmushi, fitarma da zanyi saina fasa na koma ɗaki na kwanta, dama ruwa zan ɗiba.
Bansan lokacin da suka tashi a wannan gulma tasu ba, lokacin dana fito alwala kuwa idanunsu tamkar zasu faɗo saboda kallona.
Ni wlhy zuwa yanzunma rayuwar waɗannan matan tausayi take bani, to ace kai baka kula da matsalolinka ba saina wani, ga nauyin cin naman ɗan uwanka da kullum kake azama kanka?, ALLAH shi kyauta to.
Koda na idar da salla tsakar gidan na dawo nima na fara ƴan ayyukana, kallo kam sukeda lokacin yinsa, nakan ɗan jefa musu baki a hirarsu idan sun sakkoni, amma fa ban saki baki ba kamar wadda bata da aikinyi.
_______________________________
Ɓan garen Samina kuwa dai har yammar ranar basuga ƙeyar Ma'aruff ba, sunma Samina tambayar duniya a kansa taƙi kulasu.
Sai bayan magriba suna shirin kayansu kamar yanda Doctor yace suyi dan zai basu sallama sai ga Ma'aruff yazo, abin mamaki babu wanda ya gasar tsakanin Inna Mari da Mama gaje, sai ma faman hura hanci yake yana wani ɗaɗɗaure fuska.
Mama gaje ko jiki na ɓari take gaidashi, ya amsa a cinkushe babu wani alamun girmamawa agareta.
Wannan abu ya saka Samina tsantsar takaici, shiyyasa da aka sallamesu zasu wuce tace ita gidan Inna Mari take so ta wuce, sai taji ƙarfin jikinta zata koma.
Da farko Ma'aruff yaso yin gardama, mikuma ya tuna oho masa yace taje amma sati ɗaya kacal.
Ta yarda da hakan, maimakon ya ɗibesu ya kaisu gidan a motarsa sai kuɗin napep ya danƙa musu wai shi akwai inda zaije ana jiransa.
Baƙin ciki tamkar Samina ta haɗiyi zuciya ta mutu, amma dai sai batace dashi uffanba.
Tunda suka shigo gida iya keta haba-haba dasu, ita ta dafama Samina ruwan zafi tai wanka dan taji daɗin jikinta, tare da nuna mata dabarun da zata gyara jikinta duk da kuwa ɓari tayi.
Uffan inna mari bata ce dasuba, dan ita abinda Ma'aruff yay musu ne kecin ranta, so take ta gano ina malar take suyi ƙoƙarin gyarawa kafin Saminar ta koma, dan sosai ta fahimci akwai matsala, to kafin mutane su farga gara suyma tufƙar hanci.
Aiko da dare Samina na kwance bisa gadonta, itako tana ƙasa zaune mama gaje ma haka dan bata wuce gidaba wai sai da