Showing 27001 words to 30000 words out of 275313 words
Chapter 10 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
sai xancen kotu da bail take, da takalmi ma ta shigo parlon don rainin wayo..." Hajiya Maryam da taji kamar xuciyarta xai fashe don kishi bata dai ce komai ba nan ko naxari iri iri take yi a xuciyarta tana tunanin ta ina kenan xata fara....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Abba ne xaune main parlor bayan isha, lkci lkci yake kallon agogon dake manne bangon parlon, Mami ta fito daga part dinta sanye da hijab har kasa ta karaso cikin parlon tace "Good evening Barrister" yana kallonta yace "Good evening Rahinah" xaunawa tayi one sitter dake parlon tace "Gani" Abba yace "Me ya sa kika dau lkci baki fito" tace "Putting things in other" Bai ce komai ba, ya kalli hanyar kitchen don Mumy na ciki, tun daxu take kai wa take komowa ko gaisuwa bai hadata da shi ba tun shigowarsa, shi kuma hakan bai hanasa ce mata yana da magana a parlor da ita da Mami ba, xata sake komawa kitchen daga bangarenta yace "Maryam" juyowa tayi fuska daure tana kallonsa bata ce komai ba, yace "Ke muke jira" Tana masa wani kallo ta karaso cikin parlon tace "Ni ku ke jira? in maku me? A kan me ma xa ku jira ni? Nace maku ina da wnn lokacin ne? Plss I have more important things to do then sitting and staring at you both, bani da wannan lokacin barrister...." Ta juya xata bar wajen, rai bace yace "Ina magana xa ki wuce?" Juyowa ta sake yi tace "Bbu tasirin da maganganun ka xa su min barrister, in xauna kace xaka mana nasiha ko me? Did I tell you I need that, ita dai xaka xaunar ka ja ma kunne ta tsaya iya matsayinta a gidan nan kar ta ce xata yi karambanin xuwa kusa da nawa matsayin, matsayina daban nata daban, ni uwar gidanka ce kuma uwar 'ya yanka, ita kuma uwar rainon yar tsintuwar ka ce, wa enda xaka dinga ciyarwa, kaga banbancin kuwa ba karami bane, idan tace xata yi gigin matsowa lane dina ita xata kwana a ciki, so bbu wani xaunawa da xan yi ka hada mu kayi magana, bata kai matsayin ba, ga most important maganganun nan duk nayi, sai dai kawai tayi taking caution, ka kara mata da wanda xaka kara mata" Tunda ta fara Abba ke kallonta, Mami tayi yar dariya tace "To ai da sauki tunda kamar yanda xa a kira ki matarsa haka nima xa a kirani ynxu, kuma tunda baki isa korar yar tsintuwa ba balle ni Alhmdllh, muna nan sai mun xame maki kadangaren bakin tulu, xa ki gane matsayina da naki bai kai banbancin da xa ki dinga bragging ba...." A fusace Mumy ta karaso kusa da ita tana huci tace "Karya kike wllh, nace karya kike..." Tsawa Abba yyi mata yace "Kina da hankali Maryam??" Mami ta mike tace "Ina fa, sai dai in koya mata cikin yan kwanakin nan...." Daga haka ta bar masu parlon ta wuce bangarenta, Mumy ta fashe da kuka tace "Ka cuceni barrister, ka ci amanata, ka rasa warce xaka auro ka kawo mana gida sai yar bariki...." Mikewa Abba yyi ya dakatar da ita in few seconds ta hanyar nuna ta da yatsa strictly yace "Don't you ever try that again Maryam...." Bai jira cewarta ba ya bar parlon. Mami ce xaune that same night tana kallon Heedayah tace "Ina jin ki..." Heedayah ta marairaice tace "Tea kawai...." Mami tace "Kece kike cewa kina son tea din kenan" Heedayah ta girgixa kai tace "Ammi na ce take bani in sha da daddare" Mami tace "To da safe fa?" Tace "Tea and bread and egg" Mami tace "Da rana?" Heedayah tace "Indomie" Mami tace "Sai kuma da daddare ki sha tea" Kai Heedayah ta gyada mata, Mami tace "Toh after this night baxa ki sake shan shayi ba duk abinda aka dafa aka baki shi xa ki ci is that clear?" A hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta mike ta dauke fried rice da chicken dake cikin plate da Heedayah ta ki ci wai sai tea ta nufi kofa ta fita, hanyar kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen din, tsaye ta ga Shuraim gaban kettle din ruwa alamar tea xai hada don ga kayan shayin a ajiye gefe, ta kasan tiles yake kallon wanda xai shigo kitchen din, yana ganin wacece kuma ya kauda kai ya ci gaba da abinda yake, Mami ta ajiye abincin hannunta ta nufi inda cups suke ta dau daya da cokali, ko kafin ta juyo har ya fice daga kitchen din, karasawa tayi gun kettle din ta juye ruwan ciki a cup din ta bude kayan shayin ta hada tea sannan ta fita kitchen din, Khadijah ta gani parlor ta shigo daukan takardunta, tana ganin Mami ta kwashi takardun ta wuce bangarensu da sauri, Mami dama tun da ta kalleta sau daya bata sake kallonta ba har ta wuce nata bangaren, sai da shayin ya huce sannan Heedayah ta sha Mami ta sa ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta. Washegari Saturday tun kafin yan gidan su tashi bacci Mami ta hada ma ita da Heedayah breakfast, da yake abinda Heedayah take so ne tsaf ta cinye komai, Mami dai sai kallonta take, sannan tace "Kin koshi ae?" Heedayah ta gyada kai, Mami ta mike tace "To mu je ki gaida Abba" har parlon Abba Mami ta kai ta, Abba dake aiki system ya daga kai yana kallonsu, Mami tace "Weldone" yace "Har ina tunanin kawo maki ki karasa" tace "Noo nima ga nawa can" yyi murmushi yace "Akwai maganan da nake son xa mu yi Rahinah" tace "Alright, but before then nima ina da magana da kai" yace "Yanxu?" Tace "Later..." Abba ya xaunar da Heedayah gefensa yace "How are you my dear" tana washe hakora tace "I'm fine" Mami tace "Baki yi gaisuwa ba" tace "Abba ina kwana" yace "Lafiya lau daughter" Mami tace "Let me freshen up" daga haka ta fita parlon, yana kallon Heedayah yace "Wa ke koya maki English" tace "My teacher" ya d'an bude ido yace "Really?" Tace "Ehh" Abba yace "Me da me yake koya maki kuma a ina yake koya maki?" Heedayah tace "Ammi tace min she's a Female, tana koya min komai da komai a gidanmu" yace "Wani sura kike?" Da sauri tace "Jinnnn" Abba na gyada kai so impressed yace "Kullum take xuwa koya maki?" Heedayah ta gyada masa kai, Abba xai yi magana aka bude kofar, Shuraim ne ya shigo parlon da sallama yana sanye da jallabiya, Abba ya amsa, xaunawa yyi nan kasa gefen Abbansa yace "Ina kwana Abba" Abba yace "Lafiya lau" Heedayah tace "Abba har da boko take koya min ma...." Satan kallonta Shuraim yyi ya kara hade rai, Abba na kallonta yace "Toh xan kawo maki warce xata dinga koya maki a nan gida" Heedayah ta wara manyan idonta tace "Thank you Abba, but..." Yace "But what?" Tace "Yaushe xaka kai ni wajen Ammina? Kila tana ta nemana" a sanyaye tayi maganan, Abba ya shafa kanta yace "Ina sha Allah xan kai ki, har yanxu ana neman Ammin taki" Tace "Abba ai gidan Yakumbo take" Abba yace "Eh ban manta ba xa mu je can" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa yace "Sai anjima Abba" Abba yace "Da yaushe kake yi ma su Khadijah karatun qur'ani" Juyowa yyi yana kallon Abban nasa, ganin kallonsa Abban ma yake yace "Da asuba" Abba yace "Ohk, Heedayah will join also, sai ka dinga masu gaba daya" dawowa yyi ba tare da ya shirya ba ya durkusa inda ya tashi yace "Abba ai na kwana biyu ban koya masu ba" Abba yace "Eh to sai ka dinga yi mata ita kadai tunda ba Islamiyya xata je ba, su kuma dama suna xuwa islamiyya" Kasa cewa komai yyi yana kallon Abban nasa, Heedayah tace "Abba a suratul jinn nake" Abba yace "Eh daga nan xa ku ci gaba" Shuraim yyi karfin halin satan kallonta, Abba yace "That's all xaka iya tafiya, idan ya so sai in samar mata lesson teacher na boko kawai" Mikewa Shuraim yyi bai ce komai ba ya fice daga parlon ya kulle kofar, fuzar da iska yyi bayan ya fita ya juya yana kallon kofar da idanuwansa da suka sauya kala. Mumy ce xaune dakinta tayi tagumi, da ka ganta kasan tana cikin tashin hankali, kanwarta Salima ce xaune dakin, tace "Allah kuwa nake gaya maki Yaya, duk wannan tunane tunanen da saka kai a damuwa ba shi bane, just swing into action, dubi fa yanda take ta harkar gabanta a gidan kamar warce tayi wata da watanni ke kuma kina nan xaune kina ta wani kishi da damuwa, wllh tuwo da lafiyayyen miyan agushi tayi ynxu a kitchen, makauniyar kuwa na can ta kafa mata kujera a kitchen din tana xaune...." Mumy ta fashe da kukan takaici tace "Wllh Salima har ynxu na kasa yrda cewar kishiya barrister yyi min, gani nake kamar bakuwa nayi xata wuce, baki ji ynda xuciya ta ke min xafi ba, Kuma fa tun jiyan ko lekowa dakin nan bai yi ba, ita kuwa ta shiga bangarensa ina lura yau yafi a kirga, wllh ji nake kamar in banka ma gidan nan wuta kowa ya huta" Salima tace "Ba wani banka wuta Yaya, gashi kin fara bata chance ta kwace maki miji ta xama ita ce kan komai a gidan...." Mumy tace "Duk ba wannan ba nata bai tsaya min kamar yanda na makauniyar ya tsaya min a rai ba, ki bani shawara ta ina xan fara, me kike ga xan ma wnn yarinyar in huce takaici, ni dai baxan kasheta ba amma ina son abinda xan mata kissa ya fi mata alkhairi da shi, wllh na tsaneta, na tsani duk wani me son ya ganta kusa da shi ma, wllh sai na tarwatsa rayuwarta" Salima tayi dariya tace "Ni fa ban wani jin yarinyar nan Yaya, minti nawa ne xa a kada ta ta bar gidan ma gaba daya, ita dai wnn yar bokon ya kamata ki fara tunanin ynda xa ayi da ita ba yar yarinya ba" Mumy tace "To ni ta yarinyar nake tukun" Salima ta mike tace "Toh ki kwantar da hankalin ki Yaya, wnn me sauki ne, mu da muka san kan komai, yanxu dai ana jirana tun daxu a waje, xan dawo ko xuwa jibi" Mumy tace "Ba wani nan, ke din ce xan gani kwana kusa, idan kika tafi gantalin ki ba sai an gan ki ba" Salima tayi dariya tace "Ai ynxu na daina kwana a waje...." Mumy tace "Toh ni dai gobe xan taho gida kar ki fita don Allah" Salima tace "In sha Allah yaya, sai mun hadu goben" Daga haka ta fice daga dakin..... Bakin gate Salima ta kusa cin karo da Junaid xai shiga cikin compound din, ja baya tayi tana kallonsa, yace "Sorry" bata iya ta amsa ba har dai ya wuce ta, ta juya ta bi shi da kallo ko kiftawa babu, underneath her breath tace "Waow...." Tana tsaye tana kallonsa har ya isa entrance din shiga main parlor, ya kwankwasa kofar, Mami da ta san yana hanya ta fito daga kitchen ta bude kofar tana kallonsa tace "Har ka iso?" Yace "Ehh ina yini Mami" ta basa hanya tace "Lafiya lau" daga haka ta koma cikin parlon ya bi bayanta, saman kujera ya xauna tace "Ya su Uncle din naka" yace "Alhmdllh..." Kitchen ta nufa tace "I have been waiting for you since xaka dauko min sako a gida" Kafin ta shiga kitchen yace "Mami ina..." Mami ta juyo jin yyi shiru, tace "Wa?" Yace "Wannan babyn" dariya tayi tace "Sunanta Heedayah" yace "Oh ohk, Heedayah" Mami tace "Tana can tana bacci, let me get you water" Drink ta kawo masa parlon, duk suka kalli direction din da suka ji footstep, Mumy ce ta fito rike da makullin motarta fuskarta a murtuke, Mami ta nufi bangarenta don tado Heedayah, Junaid yyi kasa da kai cike da ladabi ya gaida Mumy, kallonsa ta kara yi snn ta amsa a dakile tayi ficewarta xuwa gidan Hajiya Sadiya ta ji ita kuma nata shawaran. Ba a dau lkci ba Mami ta fito rike da Heedayah dake sanye da doguwar riga iya gwiwa, duk gashin kanta a bude, kana ganinta kasan daga bacci ta tashi, Mami ta xaunar da ita nan kusa da shi tace "Ga Yaya ki gaishesa" daga haka ta koma kitchen don karasa abinda take, hannu Heedayah ta kai a hankali tana ta6a sa, har ta kai hannunta fuskarsa, ya kama hannun yana kallonta yace "Ina maki wasa ne?" Turo baki tayi tace "Nasan kai ne ai" hancinta ya ja yace "Sai na....." Ganin ynda ta 6ata fuska xata yi kuka ya jawota kusa da shi yace "Ohk sorry, let me pour you juice, xa ki sha?" Ta turo baki sai kuma ta gyada masa kai, ya bude drink din da Mami ta kawo masa ya diba, tace "Baka kawo Farida ba?" Bai ce komai ba ya kai glass din bakinta yace "Bude bakin" bude bakin tayi ya fara bata juice din a hankali, Mami ta fito kitchen din tana kallonsu tace "Da baka bata ba, bbu wani abincin da take ci sai kayan xaki" Heedayah na jin haka ta karasa shanye lemon da saurinta, murmushi yyi ya ajiye cup din, Mami tace "System dina xaka dauko min a gida yanxu" Junaid yace "Ohk..." Heedayah tana ta6a sa tace "Xaka je da ni??"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Mikewa Junaid yyi ya da makullin sa yace "Sai na dawo Mami" Mami tace "Alright" a hankali Heedayah tace "Mami ki ce in rakasa plss" Mami ta kalleta sannan tace "Ki rakasa ina?" Tace "Inda xai tafi" Shi dai Junaid bai ce komai ba ya nufi kofa har xai fita sai kuma ya juyo yace "Mu je da ita Mami?" Mami ta hade rai tace "Ku je da ita ina" Yace "A'a na ji tace xata je ne" Mami tace "To baxa ta je ba, kayi wucewar ka malam" Heedayah ta tashi tsaye kamar xata yi kuka tace "Mami nooo, pls ina son in je, I want to meet with farida, ki ce in bi sa" Mami ta kamo hannunta tace "Farida na Abuja Heedayah, she is not back yet, idan ta dawo you will see her" Shiru Heedayah tayi kamar xata yi kuka, Mami ta kalli kofa ta ga har Junaid ya fita, bangarenta ta tafi ta dauko ma Heedayah hularta da takalmi sannan ta dawo ta sa mata, ta kama hannunta suka nufi kofa, Mami na kallon Mai gadi tace ya leka yace ma wanda ya fita yanxu ya tsaya, hakan Mai gadin yyi, Heedayah ta ji dadi jin fresh air ta gane sun fito waje, sai da suka kusa gate Heedayah tace "Mami kin san me?" Mami ta kalleta tace "Aa my dear, what?" tace "Ina jin kamshin ruwa...." Da mamaki Mami tace "Kamshin ruwa ku ma daughter?" Heedayah tace "Ehh" Mami tayi yar dariya ta leka gate, ganin Junaid tsaye jikin motarsa tace "To ga ta ku tafi amma kar ku dade plss ka ga yamma yyi" ya karaso ya kama hannunta yace "Toh Mami" daga haka ya wuce mota da ita, Mami na tsaye har taga ya nufi mota da ita sannan ta koma ciki, front seat junaid ya bude, kawai ya ga ta fara kokarin shiga, ya dagata ya sa ta cikin motar ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar layin. Heedayah ta juya Inda take tunanin yake tace "Ya sunan ka? Sai in dinga kiran ka" Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace "Ke ya sunan ki" Tace "Sunana Heedayah Ahmad...." Yace "Heedayah is not a real name" Ta wara ido tace "Ohk, Ammina tace min sunana Fatima" Sai a sannan ya kalleta, ya dai ci gaba da tukin da yake, tace "To ka gaya min naka sunan" Yace "Sunana Fatima nima" ta xaro ido kamar tana ganinsa tace "To ai kai ba na mace bane" yace "To ni na menene?" Tace "Kai namiji ne mana" Ya d'an yi murmushi yace "Ya aka yi kika sa ni namiji ne? ni ma mace ne kamar ki" Ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa, juyawa yyi da sauri yana kallonta, murmushi kawai yake ya ci gaba da tukinsa, tayi dariyarta mai isarta sannan tace "Toh ai naji muryarka kato ne, ba irin na mata ba, kuma....." Matsawa tayi kusa da shi ta fara tattaba sa tun daga saman kansa, Bai san sanda ya samu waje yyi parking ba da sauri yana kallonta, ta sakko da hannunta har fuskarsa ta fara jan dogon hancinsa sannan ta shafa beard dinsa ta sakko da hannunta har chest dinsa, dariya ta kyalkyale da tace "Namiji ne wllh" kasa daina kallonta yyi, can yayi murmushinsa me kyau yace "How did you know?" Tace "Gashi naji gashin kan ka d'an kadan ne ba irin nawa ba, kuma kana da beard a fuskar ka, kuma you don't have breast" He couldn't help it but laugh out loud jin maganar ta na karshe, ita ma ta fashe da dariya tana taya sa, sosai Heedayah ta basa dariya, lkci daya ya daina dariyan yana kallonta yace "To ai ke ma baki da shi balle ni" ta tsuke fuska tace "Teacher na tace grown up people ne kawai suke da breast ni yar yarinya ce ai" Murmushi yyi yace "Ashe kema namiji ne kamar ni" Lkci daya ta 6ata fuska tace "Ni ba namiji bane, ni na mace ne..." tana fadin haka ta cire hularta dogon gashinta ya xubo kasa tace "Ka kalla ka ga" Ya fi second ashirin yana kallon gashin nata sannan ya motarsa after watching and making sure there is no car coming, sai da ya d'an yi nisa yace "Ke ma dai namiji ne bbu ruwana da gashin