Showing 186001 words to 189000 words out of 275313 words
Chapter 63 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
ko, yanxu da na biye ku nace baxa a rike wnn yarinya ba tun farkon kawota gidan nan da Amadu yayi da na shiga uku na lalace yau, amma da yake xuciyata fess ban biye xugar kowa ba, inji Amadu ya fada maka waye uban Heedayah, to wllh duk abinda mutum xai yi ya ji tsoron Allah ya ji tsoron gamuwarsa da Allah, ni dai duk xaman mu da yarinyar nan ko kallon banxa ban ta6a yi mata ba balle in hantare ta wllh, Allah ubangiji ya so ni, wa enda suka yi hakan ma Allah ya yafe masu, ni fa lkcn da ubanku ke da rai na sha tsinto yara a titi su girma wajena in aurar da su, kalar tawa baiwar kenan, shi sa Heedayah ma nayi mata rikon da ku kanku ban maki ba....." Tana kai wa nan ta mike ta nufi gun akwatinta tana share guntun hawayen idonta, daga akwatin tayi tace "Allah me yanda ya so...." Baffa yace "Me kuma xa ki yi da akwati Kaka" Kaka ta juyo da sauri tace "Ai Abujan xa ku kai ni in karanto ma uban duk abun arxikin da aka yi mata ba tare da mun dubi cewar a titi aka tsintota tana galantoyi ba, to wai ma waye silar riketa a gidan nan?? ba ni din bace dai, nan nan nan Amadu ya watsar da lamarinta ya bar mu daga ni sai Rakiya muna ta wahala da ita meye ba mu yi mata ba na gata wanda ko gaban uban nata take ba lallai yyi mata ba, har filina sai da na kusa siyarwa lkcn da xata makaranta, daga karshe ma Amadu koramu yyi ni da Rakiya daga gidansa ta dalilinta, shi dai kawai Allah ya basa baiwar tsinto mana ita ne ya kawo mana, amma asi bai mata ba, kashinta, fitsarinta, duk bbu wanda ni da Rakiya bamu ci ba, barin ni don Rakiyar ma gantalin aikinta take tafiya ta bar ni da ita" tana magana tana hawaye, daga Abba har Baffa kallonta suke baki bude, Ta sharbe majina tace "Kuma na daga jaka ace min ina xan je sbda rashin tsoron Allah, to Abuja xan tafi" Baffa yace "Haba kaka, ke ya kamata ki bi su, ko su ya kamata su xo su sameki a nan??? Da girman ki xaki ce xaki bi su Abuja, ba su ya kamata su xo nan su maki godiya su baki girman ki ba" Cikin daga murya Kaka tace "Aa wllh bbu ruwana da wani girman kai, rawanin tsiyar xa ku dinga laka6a min, shi yasa fa aka jefo shaidan daga aljanna aka ce, to meye kuma wani girma kamar wata gyambo, Allah ai shine abun girmamawa, bana son girman daga yau ma idan xaku ce min Patuu duk ku ce bbu ruwana da iskanci, meye wani da girmana kamar dai ni na halicce shi uban yarinyar, mu tafi kawai ku dora ni a mota inyi tafiyata, bance wani gantalalle ya kai ni ba dama" Abba dai bai ce komai ba sai kallonta yake, Baffa yace "Toh ki jira Allah ya kai mu gobe lafiya mana" Kaka tace "Ba a xuwa Abujan da daddare ne ko walakanta ni ku ke son ku yi?" Baffa yace "Yanxu idan ance ki bi hanyar nan da ba shi da kyau ai baxa ki bi ba kaka" Kaka ta jinginar da akwatin ta koma ta xauna tace "Matsiyatan yan kidinafin ma kadai ai sun isa hanani tafiya yau, shegu" Mikewa Baffa yyi yace "Na shigo in gaisheki ne dama, sai anjima" Bai jira cewarta ba kamar yanda Kaka bata ko kallesa ba har ya fita parlon, kaka ta rike ha6a baki bude tana naxarin Maganganun Abba, can ta daga hannu sama tace "Ni dai Allah ya rufa min asiri wllh, dama tun ranan da na fara ganin Deedayah na ji ta kwanta min sosai, ban bari tayi rashin uwa ba ko na sakwan daya, ban kyamace ta ba, abinda ma nake mata ban ma jikokina ba wllh" Washegari da ya kasance Friday, da safe karfe takwas Mami ta gama shirin komawa Kaduna tare da Farida, ta shiga bangaren Ammin Heedayah don yi mata sallama, Heedayah ta fito daki don a nan ta kwana tun bayan da ta dawo gidan nasu da Khaleel daren jiya gun Abbanta, ta xauna gefen Mami tana kallonta tace "Mami good morning" Mami tace "Morning dear, how was ur night" Heedayah tace "Alhmdllh, Ina xa ki Mami?" Mami tace "Xamu koma kaduna yau" cikin sanyi Heedayah tace "Mami tafiya xa ku yi ku bar ni nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Mami tayi murmushi tace "Abbanki xa su taho anjima sai ki biyosu" girgixa kai tayi ta mike tace "Noo Mami we are going together, ki jirani in hada kayana" tana fadin haka ta koma dakinta da sauri, Mami ta mike tace "Sae kun taho Amina" Ammi ta mike tace "Aa ki jirata ku tafi din Hajiya...." Mami tace "Aa, kamata yyi ku taho tare din xai fi" Ammi tayi shiru ganin Mami ta nufi kofa ta bi bayanta da sauri tace "Abban su Islam yace ya turo maki sako ta WhatsApp ki duba yanxu Hajiya" Mami tace "To in sha Allah" har bakin gate ta rakasu snn ta koma ciki, tsaye taga Heedayah a Veranda, ta juya da sauri ganin uwartata tana goge hawayen idonta, Ammi ta dinga kallonta snn tace "Don't worry dear, anjima xa mu wuce Kadunan gaba daya ai, flight sai nan da karfe biyar in sha Allah na yamma" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta wuce ciki. Mami na komawa ta bude WhatsApp din nata taga flight ticket guda biyu da Abban Heedayah ya turo mata, rasa ma abinda xata ce tayi, Dinar dake xaune tare da ita a parlon tace "Jirgin dai da baki son bi shi xa ki bi at last, ki kirasa kawai ki ce kin gani Allah ya saka, sai in kai ku airport din xuwa nan da karfe goma tunda flight din sha daya ne" Mami dai tayi shiru bata ce komai ba. Mumy ce xaune dakin Sadiya idonta yyi bulu bulu don kuka, Hajiya Sadiya tace "Ni fa wllh wllh idan ba ke kika yi ido hudu da shi wanda aka ce shine uban Heedayah ba kika xo nan kika fada min hakan da bakin ki to ni ba yarda xan yi ba, sai kace wasan kwaikwayo a taya wnn sanannen Mutumin xa ace shine ubanta, 'yar kamar wnn mutumin ta bace farat daya ace ba mu ji a gari ba" Mumy ta fyace majina da tissue din hannunta tace "Nima dai shi na gani Sadiya..." Sadiya tace "Toh wai da kika kira Shuraim din me ya ce maki?" Mumy tace "Uban me xai ce min dama, kawai ce min yyi eh haka ne, nayi nayi nayi ya fadadada min bayani amma yace bai san komai ba haka kawai Abbansa ya gaya masa shi ma, to ya xan masa?" Sadiya tace "Kaii karya ne wllh, wnn sanannen bawan Allah dai karya ne ace shi ya haifi Heedayah, ta ina suke kama? Shi baki ita fara, snn me kudi da fame kamarsa xai bar 'yar sa a makance??" Hajiya Baturiya dake dakin duk tana sauraronsa tace "Abinda ku ke mancewa a nan shine, shi wnn bawan Allah Honorable Ahmad Yusuf Ishaq da ake batu akai, duka duka yaushe ya fara siyasa da har yyi sunan?? Ina jin bai kai shekara uku ba, don ko da yana siyasar ma to gaskiya a shekaru uku xuwa hudu jama'ah suka san sa har ya xama famous haka, xai iya yiwuwa sai bayan batar 'yar tasa ya shiga siyasa gadan gadan har yyi kudi haka, kuma idan baku manta ba ni dai na sha fada maku wnn yarinya bata yi kama da yar kananun mutane ba, ku dubi jikinta ko a lkcn da Barrister ya kawota bbu wani alamar wahala kawai dai makauniya ce...." Mumy dake ta mata wani shegen kallo tace "Toh in sha Allahu ba ubanta bane shi din, idan Allah yayi duniya don manzon Allah, taya ma xa ayi ya xama ubanta, mutumin dake neman takarar gwamna a jihar kano, meye hadin biri da gada, yarinyar da mijina ya tsintota a makance a daji bbu galihu...." Hajiya Baturiya tace "To yanxu idan da gasken shine ubanta ya xa kiyi Maryam?" Mumy ta fashe da kuka tace "Wllh wllh ba shine ubanta ba in sha Allah, matsiyaciyar yarinyar da Mai gidana ya tsinto a bola xa ace attajirin nan ne ubanta, dubi fa uban plazozin da yake da shi a jihar nan da ma kano, in sha Allahu ni baxan ji kunya ba muna nan da ku xa ku ga karya ne, idan kuwa gaskiya ne toh sai dai fa ayi hakuri da abinda xai faru" Sadiya tace "Toh Allah ya sa karyan ne, amma idan haka ya kasance ai baki ci ribar komai ba wllh" Mumy tace "Ai sai dai idan ba ni Maryam ba, yanxu ma gidan Dakta xan tafi in ji abinda ake ciki nasan yanxu kaka tana da labari tare da ita" Sadiya tace "To mu je mana gaba daya" A tare su ukun suka tafi gidan Baffa a motar Mumy.... karfe shidda saura Abban Heedayah ya fito government house na Kaduna tare da few convoy, tun shigowarsu kaduna ya kira Shuraim da ya xo har government house din ya samesa don kai sa gidan Baffansa, sanye yake da khakinsa da yayi fitting dinsa sosai, Shuraim suka gaisa da gwamna dake tare da Abban Heedayah don da shi xa a taho gidan Baffa, tun da Heedayah ta yi ido hudu da Shuraim bata sake yarda ta kallesa ba, kuma ta ki gaishesa, shi ma din bai sake kallon direction dinta ba, mota daya ta shiga da Abbanta da Amminta, motoci biyar ne banda na sojoji da na governor da suka yi parking a kofar gidan Baffa, Shuraim ya sauka, Heedayah ta bude motar ta fito don Allah Allah take ta ga kaka ta nufi gate da sauri, parent dinta ma duk suka sauko motar, da ido Shuraim ya bi ta don sai da ta d'an bugesa ta shiga gate din gidan, Heedayah na shiga main parlor din gidan ta fara kwala ma kaka kira, Mumy ce xaune parlon da kawayenta da Mum din Sudais suna magana kasa kasa, bata ko kula da su ba ta ci gaba da kiran kaka.... Sai ga Kaka ta fito dakinta, da gudu Heedayah ta tafi ta rungumeta, Kaka tace "Ina gwamnan yake??" Kaka bata rufe baki ba Shuraim ya shigo, ganin Mumy a parlon ya ki karasawa, yana kallon Kaka yace "Xa a shigo..." Kaka ta tura Heedayah tace "Su shigo mana me suke jira a waje, ai tun daxu nake ta jiransu Umaru yace min suna hanya, mu dai ba mun rike yar su da amana ba, wanda ya ki Heedayah yau ne ranan jin kunyarsa, don ma Sudais da muka hada baki da shi aka rike Heedayar yana can kasar waje, da ba don shi ba, ba don ni ba da yanxu wani labarin ake ba wnn ba....." Mumy dai sai kikkifta ido take, haka Umman Sudais, Ammi ce ta fara shigowa parlon da wife din governor din garin da sallama, Kaka ta amsa da karfi ta karaso cikin parlon tana kallonsu Mumy cikin fada tace "Ku tashi ku basu waje su xauna mana, kun ja6e kamar masu neman aiki" Kallon kaka kawai Ammi take da murmushi, Kaka ta fashe da kuka sosai tana kallon Ammi tace "Wllh kamar kinyi kakin Heedayah, ni dai dama nasan Heedayah ba gantalalliya bace, dama kallon banxa bai ta6a hadani da ita ba, wa enda suka yi mata ma Allah ya yafe masu ita ma kuma ta bar su da Allah, amma ke banda lalacewa ta sameki garin yaya kika sake yarinya makauniya kamar akuya ta shiga duniya, a titin kano fa Amadu ya tsintota tana galantoyi bbu idanuwa, da karo karo ya hada dubu milyan 5 ya biya kudin aikin idonta a kasar Indiya wllh, har ni sai da na bada nawa gudunmawar, bbu yanda basu yi in bi su indiyar ba nace su tafi kawai a barni in ta masu addu'a kawai, to ba gashi ba yau komai ya xama labari ba, ai makiyan Heedayah sai dai ciwon xuciya ya kai su lahira yau...." Kaka tayi tsit ganin gwamna ya shigo tare da Mahaifin Heedayah, Mumy sai xare ido take daga inda take xaune ga xufa da ya bi ya dameta, kamar hadin baki lkci daya ita da su Sadiya duk suka mike suka koma bayan kujera kamar munafukai suna gwale ido.... Kaka ta saki kuka kamar yar yarinya tace "Dama bbu yanda banyi da d'an bakin cikin nan Shureen ya kai ni gwamnet house ba sai ga gwamnan yau a gabana...." Abban Heedayah ya isa har gabanta yana kallonta ya xauna nan kasa.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you.
Have u ever wondered how desserts are made?
Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from?
Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because
Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught:
*Profit analysis
*Ways to handle desserts
*Dessert marketing.
This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos.
Registration is on and the fee is just N3000 Naira.
Class starts on 27th august,2021.
And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕
WhatsApp 08135358038
Call 📞 08135358038
IG: najaatu Ibrahim
A boye Mumy ta dinga goge hawayen da ya cika idonta daga inda suke tsaye bayan kujera da kawayenta, Mum din Sudais kuwa sae xare ido take, Bayan duk anyi gaisuwan mutunci a parlon Baffa da Abba ma duk suna parlon, Mami ta iso gidan tare da Hajiya Zuwaira matar Baffansu Junaid, ruwa da lemo da snacks iri iri na alfarma da peppered chicken wanda Step mum din Sudais tayi aka ajiye ma bakin, Abban Heedayah yayi kasa da murya yana kallon kaka da ta nemi waje ta xauna tayi tagumi tana facing dinsa kamar marainiya, a nutse yace "Inna mun xo ne don maki godiya...." Ta dakatar da shi da sauri tace "Aa ba ruwana ka gode ma Allah, Mu dai ba mu rike Deedayah don a bamu komai ba ko ayi mana wani abun, amma fa an sha barnan kudi ba na wasa ba kaji in gaya maka, gwangwanin milon nan da Madara har sai da na dinga tarasu buhu buhu ina yi ma 'yan gwangwan sadaka, a karshe dai sai da tattalin arxikin Amadu ya jijjiga don ma ina taimaka masa ban bar sa yyi ta wahalan shi kadae ba, kuma ko kallon banxa bamu ta6a yi ma yarinyar nan ba, ynxu haka rabona da xuwa Makka tunda Amadu ya tsintota, Atoh hidima tayi masa yawa mana ga kudin gyaran ido ga kudin kayan shayi ga kuma hidimar iyalansa, ga dai ta nan ka tambayeta ko an rageta da komai shekaru biyar din da tayi da mu..." Ta fada tana nuna masa Heedayah dake xaune kusa da ita, Heedayah dai bata ce komai ba, kaka ta ci gaba tace "Ni fa wllh na dauka ma iyayenta sun rasu ne ta shigo duniya, kuma ni ban sace ma Amadu gwiwa ba da ya kawota matarsa ce ma ta so bamu matsala, kai ta ma bamu sai dai a bar kaza cikin gashinta, to yanxu duk ba wannan ba, babban damuwata a nan shine.... Shekaru kusan biyar kenan tunda wancan mutumi...." Ta fadi haka tana nuna gwamna ta ci gaba, "Tun da ya hau mulki kafin ma ya xarce nake fama da Shureen ya kai ni wajensa in basa shawarwari in kuma ce ya ji tsoron Allah kada giyar mulki yyi ta debarsa yana abinda ya ga dama amma wnn yaron ya ki kai ni, titin unguwarsu aminiyata ta Salla fa duk ya gantale ya ki shimfida masu sabo, idan kaje layin xaka xata a ruga kake, mu kaga dai namu ai ko kwarzane bai yi ba tunda duk manyan masu kudi ne a layin suka hada kudi suka yi abun su bakinsu alekum, can kuwa bbu me yi duk talakawa ne, ni fa dalilin titin yasa bana son xuwa wajen ta Sallah, to kaga kuwa ya raba xumunci, snn kuma inji ko ya hau mulki ne don ya dinga musgunawa talakawa uwa shi ya halicce su, ina fa da labarin kwace masu filaye da yake yi yace na gwamnati ne, to banda lalacewa a gidan ubanwa filaye ya xama na gwamnati? Filayen da ke nan tun kan a haifi uban da ya haifesa, na fa san uban nasa, yana nan wani tsamurmuri kamar buzu tare muka yi wasan kasa da shi, snn shi mutumin kirki ne bansan garin ya d'an sa ya gantale ba da cuta...." Shi dai me girma Gwamna banda murmushi bbu abinda yake yana kallon kaka da ta hakikance, Abban Heedayah dai kansa na kasa yana sauraron kaka, Abba da Baffa ma duk sun kasa dago kai kowa da abinda ya damesa a xuciya, Shuraim kam banda harararta babu abinda yake, Mami dai dake xaune tare da Hajiya Zuwaira da Hajiya Hauwa tayi tagumi tana kallon kaka, Ammin Heedayah da matar gwamna sai murmushi suke su kam, Mumy da mukarrabanta na ta tsaye bayan kujera kamar munafukai, Mumy dai bata ma san me ake cewa a parlon ba sai share xufa take tana gwala ido... Kaka tace "Toh ba ruwana na fita hakkin ka na fada maka gaskiya Allah baxai tambayeni ba ranan gobe kiyama" gwamna