Showing 117001 words to 120000 words out of 275313 words

Chapter 40 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

fita parlon, kaka tace "Kiji Ina batun ta maida kayanta ki wani tashi ki karbe Rakiya? Makira ce fa Maryam, to ni dai ba ruwana" Mami dai bata ce komai ba, Kaka tace "Haka kawai mata ta shigo mana tsakar dare tana tambayar yaushe ne tafiyar, nasan da bana parlon nan tonawa xaki yi ki gaya mata, ai mugu baka sa shi a harkan ka, muka san abinda ke xuciyarta" Mami still bata ce da kaka komai ba ta ci gaba da abinda take. Washegari da ya kasance lahadi, karfe goma na safe Mami ta shiga parlon Abba ta dalilin kiranta da yyi, as usual laptop dinsa na gabansa, ta xauna tace "I'm here barrister" Bayan kusan minti biyar ya dago yana kallonta yace "Dama nayi wata shawara ne daga jiya xuwa yau Rahinah" Mami na kallonsa ganin mood dinsa is awkward, a hankali tace "Shawarar me fa Barrister?" Abba yace "Ina ga xa a bar xancen tafiyar Heedayah boarding" da mamaki Mami ke kallonsa, da farko kasa cewa komai tayi, can dai cike da karfin hali tace "Ko saboda me Barrister" yace "That's my decision" ta girgixa kai tace "Noo ba a yanke irin decision din nan without reason, ka gaya min dalilin hakan Barrister" yace "You are not to question my order Rahinah" Da mamaki sosai take kallonsa, tace "I am not questioning you, I'm asking for ur reasons" Yace "Nace Heedayah baxa ta je boarding ba, I think I have done all what I am suppose to do for her, bbu wani da xai min tilas kuma, beside I have other commitments...." Mami tace "As in?" Yace "That is it" Ta girgixa kai tayi shiru, can ta kallesa tace "Are you talking of the expenses?" Yace "If you think so" Mami ta fi minti biyu ta rasa abun cewa, can ta girgixa kai tace "Ohk fine, the bills are on me you don't worry, in sha Allah" tana fadin haka ta mike xata fita, Abba yace "Bill or no bills banyi ra'ayin ta tafi boarding ba, xa ki iya biya mata kudin day amma ba boarding ba" juyowa tayi tace "Sorry... but are you sure you are okay Ahmad?" Yace "What are you insinuating?" Tace "Naga dai nace indai don kudi ne kada ka damu xan biya...." Abba yace "Toh makarantar ma gaba daya nayi canceling dinsa, she should stay at home, you have no issues with that" Mami ta kara kallonsa da kyau, bata kuma cewa komai ba ta fita, Dakin kaka ta wuce, Kaka da tayi wanka tun asuba xata yi rakiyar yan makaranta ganin Mami tace "Komai mutum xai yi ya dinga yi ido na ganin ido, yanxu fisabilillahi sai dare yyi muyi ta cin karo da juna xa mu kai yara makaranta?" Mami ta xauna saman kujera tace "Kaka ban gane abinda Barrister ke nufi ba fa...." kaka ta xauna da sauri tace "Lafiya?? Cewa yayi kar aje da ni ko?" Mami tace "Aa" nan ta koro ma Kaka duk yanda suka yi da Abba, kaka ta saki baki tana kallon Mami, can tace "To wiwi ya sha daren jiya kafin ya kwanta ne, ko lalacewa ce ta samesa, ko bala'i ne ya fada masa duk a daren jiyan?" Mami dai bata ce komai, kaka tayi wani dariyan boss tace "Ahaf, ba ina yawan ce maku bamu san xuciyar Amadun ba a kan Deedayah amma kun ki amincewa da ni, to yau dai anyi walkiya mun ganosa, yau mun ga irin xuciyarsa, kuma makarantar kwana kamar Deedayah ta tafi ta gama, ai ba shi kadai na haifa ba a duniya, iyaka in kira Umaru ya xo ya kai ta ya biya komai, ni ai ban gaji da amanar da Allah ya bani ba in shi ya gaji, Deedayah fa Amanar Allah ce a wajenmu wllh wllh, to duka duka nawa ya kashe mata da xai nuna gazawa banda lalacewa ta samesa, Allah ya sa ya kashe ya kai dubu dari a kanta, shi ma dubu darin sbda gyaran idon da ya kai ta aka mata, to wllh ki fita harkarsa ga wayata ki kira min Umaru, idan shi ma yace bashi da kudi ban ki in daga fili na in siyar in kai Deedayah makarantar kwana ba balle ma baxai ce min haka ba, d'an Albarka ne shi din" Tana fadin haka ta dau wayarta ta mika ma Mami tace "Xa ki ga an sa Dakta ki kira min shi" Mami ta sauke ajiyar xuciya don har lkcn mamakin Abba take tace "Aa ki d'an dakata kaka" A fusace kaka tace "Ki kira min shi nace Rakiya, in dakata a kan me, ki nemosa ki kira min shi dalla" Amsan wayar Mami tayi ta nemo lambar Baffa tayi dialing sannan ta mika ma kaka.



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


Abba na parlonsa tare da Baffa wanda shigowarsa parlon kenan, bayan sun gaisa Baffa yace "Mun yi waya da kaka kuma ban fahimce bayanin da take min ba daxu" Abba yace "Bayanin me kenan?" Baffa yace "Na tafiyar Heedayah makaranta, what's going on?" Abba yace "Eh I just decided tayi day, baxata je boarding din ba kuma" Baffa yace "Ko saboda me?" Abba yace "Kawai ina ga hakan xai fi, she is going no where" Baffa yace "But kana tunanin xa a iya convincing dinta da haka, Ina nufin ita kaka" Abba yace "Toh xancen gaskiya shine I can't sponsor her to Nigerian Turkish boarding, day din ma ba yanxu xata fara ba" kallonsa kawai Baffa ke yi bai ce komai ba, Shuraim na shirin wucewa zaria da safen kaka ta shigo dakinsa ko sallama babu, Ta madubi yake kallonta yana jiran jin da me ta shigo, tace "Shureen ka ga dai anyi walkiya mun gano Mahaifin ka ko?? To ga dai irin xuciyarsa yau Allah ya bayyana mana, Ashe dama ba son Allah da annabi yake ma yarinyar nan Deedaya ba, kaji wai ba shi da kudin kai ta makarantar kwana duk uban arxikin da Allah ya hore masa, a takaice dai yace bbu makarantar da xata je" Shuraim ya juyo yana kallonta da mamaki, tace "Wllh kuwa, Ina jin fada suka yi kaca kaca da Rakiya a kan haka don naga ranta a bace, ni dai na kira Umaru ya taho, nasan kuma yana hanya ynxu, bbu ruwana da biye Amadu mu yi tashin hankali makota na jin mu" Shuraim yace "Yaushe Abban ya fada haka?" Kaka tace "Yau din nan wllh, bala'in da ya tashi da shi kenan, ni ko nace anya lafiya kuwa, don naga shi ya bada kudi aka yi ta siyayyar xuwa makarantar, ni ban masa baki ba balle ace da bakina ya tashi yau, to me ke faruwa? Ko da yake dama ai yana da bakin hali" tana fadin haka ta fita dakin, Shuraim ya bi ta da ido, Kaka na fitowa ta hadu da Baffa a main parlor ya fito parlon Abba, kaka tace "Kaji tsiyar ku ai, Amadu ya kiraka ko ni? Shiga kayi ya giggilla maka karya ko kuwa neman fitinata kake?" Baffa yace "Shigowata kenan fa Baaba" kujera ya xauna ya gaisheta ta amsa tana daga tsaye tace "Toh bamu san me Amadu ke ciki ba yau dai" Baffa yace "Aa ba fa wani abu bane kaka, kawai makarantar jeka ka dawo xa a sa ta in sha Allah, bbu xancen makarantar kwana" da karfi Kaka tace "Bamu yarda baaaa, tunda har bbu wanda ya matsi bakinsa da farko yace xai kai ta bording to bai isa ya juya mu kamar waina ba ynxu, ko don yaga bata da kowa sai Allah sai shi sai ni??" sai kuma ta fashe da kuka sosai ta xauna tana kunce ha6ar xaninta, Baffa yace "Haba Baaba, yanxu meye abun kuka a nan kuma? Dama ba abinda mutum xai iya xai daukar ma kansa ba? Yanxu wnn Makarantar kika san nawa ne? Ya kai miliyan daya fa" Kaka tace "Bbu ruwana da wnn, meye kuma miliyan daya da yanxu ina ihu xan gansa gabana, da can bai san ko nawa bane ya furta a kai ta? To wllh sai dai kai ka biya idan ba haka ba in tattara yanawa yanawa inje duk inda Allah ya nufa, don ni ba karamar mutum bace baxa a kunyata ni a gaban yar yarinya ba ance mata makarantar kwana xa a kai ta" Baffa yyi shiru yana kallonta ya ma kasa cewa komai, mikewa tayi tana matsar kwalla ta wuce dakinta tana cewa "Ba da ni ba wllh" Shuraim ne ya shigo parlon bayan tafiyar kaka, ya gaida Baffan nasa, Baffa yace "Je ka ka kira min Barrister Rahinah" Ya amsa masa sannan ya nufi bangaren Mami, Da sallama ya shiga parlon, ganin tana waya ya jira har ta gama sannan yace "Ina kwana" Tace "Lafiya lau" yace "Baffa yana magana a parlor" Mami tace "Okay, but do you have any idea on why Barrister changed his mind toward sending Heedayah to boarding schl?" Ya girgixa kai yace "Ban sani ba gaskiya, but I will try talk to him now" Mami ta mike ta dau Hijab dinta, sai da ta fita ya bi bayanta, xaunawa tayi parlon suka gaisa da Baffa, Baffa yace "Ke kika sanar ma Kaka yanda ku ka yi da barrister daxu?" Mami tace "Ehh ni na sanar mata" Baffa yace "But you shouldn't have Rahinah, kinsan yanda take abubuwanta, sannan don barrister yace wnn yarinya baxata makarantar kwana ba I see no cause for alarm, ga makarantu dai iri iri na day, tunda kika ga yace baxa ta je ba kinsan baxai iya bane commitments sun masa yawa, meyasa baki yi consider din haka ba" Mami ta girgixa kai tace "Amma ya san da commitments din ya bada kudi me yawan gaske aka yi mata siyayya sannan tun last week yayi niyyar tura min kudin schl fees din nata na dakatar da shi nace ya bari sai wnn satin, why the change of mind all of a sudden, and abinda ya fi ban mamaki na nuna masa idan expenses din ne damuwan na bar komai a wuyana kar ya wani damu, Amma barrister ya bude baki yace min makarantar ma baxata je ba kwata kwata har day din ma" Baffa yace "Yanxu dai ni duk ba wnn ba, ku bar maganan boarding a tafi gobe Monday ayi mata registration ko a makarantar su Khadijah ne, ki bar batun kaka kawai...." Muryar kaka suka ji tace "Algungumi, to daga kai har Amadun idan ban kora ku kun bar mana gidan ba ku ce ba ni ba, tun kuna yara dama ku ka iya munafurci da tsegumi, Banda rashin tsoron Allah don me xaka ce a fita batun uwarka, wato ga ni gantalalliya ko, kawai don Mahaifin ku ya mutu ya bar ni cikin ku sai in xama bola ku yi ta cin dunduniyata kuna munafuratata kuna walakanta ni" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka sosai ta xauna ta rike kai, Baffa yace "Subhanallahi, meye haka kaka, to shikenan in dai boarding ne xa a biya mata idan Allah ya yarda yau xata tafi" Kaka ta mike tana share guntun kwallarta tace "Da dai ya fi, don ni ban gaji abun kunya ba, da wani idon xan kalli Deedayah ince an fasa kai ta bording" Daga haka ta wuce dakinta, Mami tace "Ni matsalata yanxu shine kawai barrister ya amince ta tafi makarantar ko ni xan dau responsibility din komai wllh, Allah xai hore in sha Allah" Baffa dai bai ce mata komai ba... Da farko kasa cewa komai Shuraim yyi ganin kallon da Abbansa ke masa kamar ya san abinda ya kawosa parlon nasa, Abba yace "Nace ina jin ka kayi shiru, I'm doing something important now" Yyi kasa da murya yace "Abba me yasa kace Heedayah baxata je boarding din ba kuma, I thought...." Abba ya mike ya dakatar da shi strictly yace "Haka nayi ra'ayi, and who are you to question my order??" Shuraim ya girgixa kai yace "Kayi hakuri" Abba yace "Leave now" mikewa yyi ya fita parlon. Bbu kowa main parlor din, Baffa ya shiga dakin kaka ya kara bata hakuri ya tabbatar ta hakura, Mami kuma ta koma bangarenta, part din Mami Shuraim ya tafi ya bude kofar parlon ya shiga, xaune ya sameta a parlon, she looks so tensed, Shuraim ya xauna bayan few seconds yace "He don't seems to want to listen...." Mami tace "You don't worry Shuraim, nace Baffa yyi masa magana ya bada permission din tafiyar nata, just permission... Ni xan bada kudin makarantar" Shuraim yace "Toh shikenan, Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi" Mami tace "Ameen" Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da sallama, sau biyu yana kallon Shuraim dake xaune, ya gaida Maminsa, ya dai dake suka gaisa da Shuraim din, Junaid ya xauna yace "Ya ake ciki yanxu Mami?" Mami tace "I don't know, Doctor nake jira in ji ya ake ciki" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Ido hudu suka yi da Mumy da ta fito daga kitchen, da mamaki take kallonsa, ya karasa inda take walking slowly, Mumy na kikkifta ido tace "Daga ina naga ka fito Shuraim?" Yace "Kaka ce ta aikeni..." Ta wani daure fuska xata yi magana sai ga Baffa ya fito, murmushi tayi tace "Aa ashe Dr na gidan nan, sannu da xuwa" Baffa yace "Yauwa sannu, Shuraim yi min kiran Rahinah" Shuraim ya d'an kalli Mumy dake ta murmushi, Ya juya xuwa bangaren Mami, ba a dau lkci ba suka fito tare, Baffa na tsaye yace "Ki turo min account details din ki, xuwa anjima sai ku kai ta makarantar" Mami tace "Noo it's not ur responsibility Dr, you don't have to, in sha Allah baxai gagara ba I will pay everything" Baffa yace "I said you should forward to me ur details" Bai jira cewarta ba ya wuce parlon D'an uwansa, Mumy na kallon Mami tace "Mun tashi lfya Hajiya" Mami tace "Lafiya, ya yara" bata jira cewar Mumy ba tayi wucewarta, Mumy ta bi ta da wani kallo tana wani murmushi, Shuraim na kula da kallon da Mahaifiyar tasa ke yi ma Mami, tana juyowa kansa ya juya da sauri ya nufi kofar fita parlon. Ko da Baffa ya shiga gun Abba domin sanar masa shi xai biya kudin makarantar Heedayah kamar yanda Kaka ta umarce sa, Abba yace "Toh bbu ruwana a kan lamarin yarinyar daga yanxu, and I have taken my hands off her...." Baffa ya mike yace "What nonsense? dama wani ne ya kawo maka ita da xaka ce ka cire hannunka a lamarinta, or is something wrong with you Ahmad?" Abba bai ce masa komai ba hakan yasa ya juya ya fita daga parlon. Karfe biyu na rana Mami ta sa Mai gadi ya gama shirya kayan Heedayah da Farida a bayan motarta, duk kaka na tsaye bayan booth din yafe da katon gyalenta wai bata yarda da Mai gadin ba kar ya rarumi wani abun ya boye, Mami ta fito cikin gidan tana isowa gun motar kaka tace "Kinga Rakiya ki saki ran ki, naga kamar kin sa ma kanki damuwa, kada ki wani cuci xuciyar ki a banxa sbda Amadu, ya je mun bar sa da halinsa, ni dai tunda ba shi kadai na haifa ba ai da sauki" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Toh xa mu je da Heedayah tayi masa sallama yanxu" Kaka tace "A kan me? Shi ya biya mata kudin makarantar kwanan ko ko akwai abinda ta hada da shi banda tsintota da yyi, ai kinga yasan fushi nake da shi amma har ynxu bai shigo ya ce min ci kanki ba, to don me xa ki kai masa yarinya ga xuciyarsa mun fara sani, ya je ya cuceta a banxa" Mami tace "Aa kaka gwara dai ta sallamesa" Kaka ta rungume hannunta tace "Toh ni dai ba ruwana" Mami bata ce komai ba ta sa Heedayah ta sakko daga cikin motar don har sun shiga da Farida tana rike da hannunta suka koma cikin gidan, da sallama ta shiga parlon Abba, bata samesa parlon ba yana can cikin daki, Mumy ce ta fara fitowa rike da hularsa alamar dai xabar masa hulan da xai sa take, tana kallonsu daga sama har kasa tace "Ya aka yi" Mami bata tanka ta ba ta nemi gu ta xauna, Heedayah ta tsaya kusa da ita, Mumy ta wani tabe baki ta juya ta koma dakin, ba a wani dau lkci ba Abba ya fito, Mami ta mike ganinsa tace "Sallama Heedayah ta xo yi maka, xa mu wuce yanxu" yana gyara karin hularsa a takaice yace "Ohk, that's good... Very good" Mami bata kuma ce masa komai ba, Heedayah na kallonsa tace "Abba me yasa baxa ka bi mu ba?" Mami ta kama hannunta suka nufi kofa, Mumy dake tsaye bakin kofar dakin tace "Toh Allah ya kiyaye ya tsare Heedayah, ya bada abinda aka je nema..." Mami tayi ficewarta ta rufe kofar, bayan mota Heedayah ta shiga tana kallon kaka dake xaune Farida kuma na gaba, Mami ta shiga driver seat ta tada motar suka bar gidan ta kama hanya xuwa Rigachikum. Suna hawa babban titi kaka tace "Toh ke Rakiya kin ga ya dace wnn yarinya ta tafi bata je ta sallami kawunta ba?" Mami tace "Wai Farida?" Kaka tace "Eh mana" Mami tace "Aa sun yi waya kaka, yace ta wuce kawai" Kaka tace "Toh kinga da kyau haka ai, shi kuma Amadu Allah ya shiryesa, dama ni don kar xuciya ta debeni in je in yi mugun alkaba'i a kansa kawai ki saukeni gidan Umaru idan muna dawowa" Mami tace "Aa ba xa ayi haka ba kaka, kiyi hakuri" Kaka tace "Wllh baxan koma gidan ba, ce maki nayi gidan ubana ne? dama ba sbda Deedayar nake xaune ba aka ce maku, iyaka duk ranan da xa ki je dubata a makaranta ki taho mu tafi tare, ko kuma idan na ga hanya ni kadai ma xan dinga xuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login