Showing 150001 words to 153000 words out of 275313 words

Chapter 51 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

gulma idan xaki dauka ki dauka ki ci, idan kuma hanaku cin komai akayi sai na sani" Kaka tace "Ni dai ba ruwana sai ku ja ma Rakiya bakin jini nan kuma bata san hawa ba bata san sauka ba, idan xaku dau gasasshen naman ku dauka ku ci meye xaku dinga ma mutane kunbiya kunbiya gashi har na narka kwaina a ciki, nama ai abun marmari ne ba abinci ba" Farida dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce komai ba, Heedayah ta dau plate din naman ta dauki daya, wani ajiyar xuciyar da ya kusa fitowa fili Mumy ta sauke, Kaka ta kalleta tace "Lafiya?" Mumy ta d'an daburce tace "Wllh tun juya nake jin kamar ulcer na xai tashi" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya maki tsari da shi" ta gefen ido Mumy ta dinga kallon Heedayah da ta kai naman baki ta fara ci a hankali, wani ajiyar xuciyar ta kuma saukewa, Kaka tace "Toh Allah yayi maki tsari da shi dai, ulcer ai bala'i ne" Heedayah xata ajiye plate din Mumy tace "Har kin yi me? Me kika ci da xa ki ajiye" Kaka tace "Ni dai ba ruwana da wahalansu idan basa ci su kawo min in juye a jaka mu tafi kawai" Farida ta mike ta dau plate din nata ta tafi ta kai ma Kaka tace "Ni baxan ci ba" kaka ta kwace plate din, Heedayah dai ta ci gaba da cin naman, hira kawai Mumy ke ma kaka don Heedayah ta ci naman sosai, Heedayah dai cin naman kawai take ba wai don yyi mata dadi ba, daga karshe ta mike ta nufi kofa, Ta gefen ido Mumy ta bi ta da kallo don ta ci desired quantity din ba laifi, Heedayah na fita ta dau hanyar kitchen, xaune ta ga Shuraim a parlon this time around, ya mike ganinta, dauke kai tayi da sauri ta wuce kitchen din ta shiga, plate ta nema ta rufe sauran naman ya shigo kitchen din yana kallonta yace "What's that you are covering?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tsire ne" Yace "Waye ya ci?" Tace "Mumy ce ta bani" Shiru yyi yana kallonta, yace "Ke da wa?" Tace "Farida" yace "Ina na faridan?" Heedayah tace "ita bata ci ba" yace "Kece mayunwaciya kenan" Sai a snn ta kallesa, ya daure fuska yace "Baki ci abinci a gida ba kafin ku fito?" Kin cewa komai tayi ta dauke kai, yyi mata wani tsawa yace "Ba da ke nake ba" Ta ki juyo fuskarta ta d'an turo baki tace "Na ci" yace "Then meyasa kika ci naman?" Tace "Mumy ce tace I should eat it" karasawa yyi ya bude plate din sai ga Mumy ta shigo kitchen din, ganinsu a tsaye da mamaki tace "Me kuma kake yi a nan Aliyu?" Ba tare da ya dubeta ba yace "I came to make tea" Mumy tace "Wanda ka sha daxu fa" yace "Bai isheni ba" Ta kalli Heedayah da ta sunkuyar da kanta, Mumy tace "Ina naman da kika rage bani in tafi in ci ban karya ba dama" Heedayah ta karasa ta bude plate din ta dauko naman ta mika ma Mumy ta amsa, Heedayah ta bi gefenta ta fita kitchen din, Mumy tayi masa wani kallo tace "Da uban me ka shigo nan din kana gaya mata ko akwai hadin biri da gada ne?" Yace "Ni fa I just came in to make tea sai na ganta, and where is my meat?" Mumy tace "Gwara ya kasance haka don ma ka ji in gaya maka, ba hadin biri da gada, tsire kuma bbu sai ka dau na annabawa" yace "Toh bani wannan in ci" tace "Baxan bayar ba" daga haka ta fice daga kitchen din ya bi ta da ido. Mumy na fita kitchen dama Parlon Abba ta shiga ta kulle da mukulli, tana dube dube ta dau wani plane sheet paper ta juye tsiran a ciki sannan ta cukuikuye takardan ta tura can karkashin kujera yanda baxa a hango ba snn ta mike ta fito Main parlor, leka hanyar kitchen tayi ta ga alamar yana tsaye har sannan a kitchen din, ta mayar da plate din parlon Abba, sannan ta fito ta sa makulli ta tafi parlonta tana murmushi ta shiga tace "Sannun ku Kaka, Kwan ya ishe ki ko?" Kaka tace "Ya isheni sai na gobe kuma idan Allah ya kai mu, kin ji Farida wai mu wuce, bayan nace ma Amadu muna nan har dare" Mumy tace "Allah sarki, ta gaji da xama kenan, tunda kun gaisa da Barrister din ai xaku iya tafiya kaka" Kaka tace "Aa su dai su tafi, haka kawai bamu gama ganawa da d'a na ba kice in tafi" Mumy ta kauda kai bata ce komai ba, kaka tace "Sai dai ko kiyi ma Shureen magana ya ajiye su gida tunda ke baxai maki musu ba ni kuma sai ma ya iya xagina" Mumy ta d'an yi shiru, can ta saci kallon Heedayah, sai kuma tace "To dama dai driver na nan ne sai ya ajiye su, amma Shuraim kam nasan baxai je ba, ynxu ma na aikesa ya kai ma Sadiya sako yace baxai fita ba" Kaka ta rike ha6a tace "Wnn Sadiyar dai kinki rabuwa da ita har ynxu ko Maryam, bbu wanda fa bai san uwarta dillalliyar bokaye bace, kinsan uwarta kawar kishiya ta ce, to wllh bbu gidan bokan da basu xuwa lkcn Kaduna na daji, daga karshe ya kwabe masu shine kishiyar tawa uwarsu wnn yarinya da ta kusa sace min zinari jiya ta bani labarin komai, Kai har makabarta ta sha shiga ta binne laya a kabari, to in takaice maki a tsaye uwar Sadiya ta mutu kekam, ki gaya ma kowa wannan labarin kice in ji ni, a tsaye Talle ta mutu a bandakinta kamar tsohuwar soja, ta mutu da yan awanni kafin a ankara har ta kumbura suntum, toh ke dai kiyi hattara da kawance da Sadiya don barewa baxata yi gudu d'an ta yyi rarrafe ba, Kuma dai abokin barawo barawo ne, tale tale da nasan ki ke dai ko maganin tsari baki yrda da shi ba sai kice Allah ne me tsarewa, to yanxu dai ban san ya kike ciki ba gaskiya" Mumy dai sai danna wayarta take fuskarta bbu yabo bbu fallasa ta ki kallon kaka, Shuraim na tsaye bakin kofa tun fara labarin kaka hannunsa rike da makullin motarsa yana sauraronta, Mumy ta juya tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "Lafiya????" Yace "Xan je government house" Kaka tace "Atoh ka sauke min yaran nan a gida don girman Allah kar su fara min kuka, kuma me xaka je yi a gwamnet house?" Da sauri Mumy tace "Ae ba hanyarsa bace kaka" Kaka tace "Toh sai ya fara ajiyesu snn ya tafi gwamnet house din, Ina ruwana ni da xa ki ce min ba hanyarsa bane" Juyawa yyi yace "Su sameni a mota" daga haka ya fita parlon, Farida ta mike ta dau jakarta, kaka tace "Toh Allah ya kiyaye, kila anjiman ma Amadu ne xai ajiye ni gida" Farida tayi ma Mumy sallama tayi ma kaka sannan ta fita, Heedayah ta mike tsaye da kyar don tun fitowarta kitchen kanta ke juya mata, bata ce masu komai ba ta nufi kofa walking slowly, Mumy ta bi ta da kallon gefen ido har ta fita, kaka ta kyabe baki tace "Bana biye mata ba ta kai ni gaba gun Rakiya" Farida na tsaye bakin kofar fita main parlor tana jiran Heedayah, har ta iso kofar kallonta take, tace "What's wrong?" Heedayah ta dafe kanta da kyar tace "I'm not feeling okay" Farida ta kama hannunta tace "Ciwon kai??" Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Farida tace "Mu tafi gida sai ki kwanta, you will feel okay in sha Allah" tana rike da hannunta suka nufi motar Shuraim, har suka iso yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude back seat Heedayah ta shiga ta kulle sannan ta xaga ta bude daya side din ta shiga ita ma ta kulle tana kallon Heedayah da ta hade kai da gwiwa tace "Sannu" juyowa yyi yana kallonsu yace "What's wrong?" Farida tace "She said she is not feeling fine" Rufe motar yyi suka bar gidan, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikin motar, yyi parking kofar gidan yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude side dinta ta fita ta xaga ta bude bangaren Heedayah tace "We are home..." A hankali Heedayah ta dago kanta sannan ta sakko daga motar, Farida ta rufe tana kallon Shuraim tace "Thank you" Bai ce komai ba ta kama hannun Heedayah suka nufi gate, "Heedayah!!" a tare duk suka juya suna kallonsa, Farida ta sake hannunta, kamar me counting step dinta ta koma gun motar, yana kallon idanuwanta da suka kada yace "Me ya sameki?" Ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina jin jiri, kuma ina son in kwanta" yace "Why?" Ta buda hannunta a hankali tace "Nima ban sani ba" yace "Tun da kika tashi yau kike jin jirin?" Ta girgixa masa kai, Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Go...." juyawa tayi taga Farida ta riga ta wuce ciki, ta nufi gate din, dishi dishi ta fara gani kafin ta karasa gate din, lkci daya ta kwala wani kara ta sulale a wajen. Mami ce xaune gefenta a kan gadon dakin, Junaid na ta daya side din a tsaye pressing his phone, sai Shuraim dake tsaye kusa da window ya rungume hannunsa, Farida ta shigo dakin rike da bottle water da glass cup, ta duka gefen Heedayah ta bude ruwan ta xuba a cup, Mami ta dagota tace "Gashi ki sha" amsa Heedayah tayi ta sha kadan, Mami tace "Ya ciwon kan?" A hankali tace "Ya daina" Mami tace "Toh Allah ya sauwake daughter" Junaid ya kalleta yace "Jirin fa?" Tace "Ya daina" Kofa Shuraim ya nufa ya fita, Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami ina son inyi bacci ynxu" Mami ta kwantar da ita ta ja mata blanket tace "To yi baccin dear" Farida ta mike ta fita da ruwan, Junaid ya bi bayanta, sai da Mami ta ga ta fara baccin snn ta sauke curtain din dakin ita ma ta fita. Lkci lkci Farida ke shigowa dakin duba Heedayah dake ta bacci comfortable har kusan azahar, Farida tayi alwala ta fito bandaki ta tafi gaban mirror ta dau darduma dake kan kujeran mirror din taji vibration din waya, bude inda taji vibration din tayi ta daga dictionary ta dau karamin wayar tana kallo, bude ido Heedayah tayi ta mike xaune da sauri tace "Is it ringing??" Farida ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar sannan ta juya ta fita.


*Let it not be as if I didn't update today, yanda kowa ma ya tafi gidan lalle haka nima na tafi can don ni ba gantalalliya bace, ehe* 🌚




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Heedayah ta daga kiran ta kai kunne amma bata ce komai ba, sallama yyi mata ta amsa sannan tace "Ina yini" yace "Lfya lau, how are you?" Tace "I'm fine" yace "Always not picking calls, why?" tace "Mun fita ne" yace "Xuwa ina?" Tace "Gidan Abbanmu" yace "Ohk" shiru tayi, shima yyi shiru, can yace "So you ain't coming out anytime soon" ta jingina da pillow tace "Nima ban sani ba" yace "Yaushe xa ku koma schl?" Tace "In a week time" yace "Ina son mu hadu" bata ce komai ba, yace "Kin ji?" Tace "A ina?" Yace "Idan ma kince gidanku ae sae in xo" tace "Don a min duka?" Murmushi yyi yace "Aa ba wanda xai maki duka, now tell me a ina xan gan ki?" Shiru tayi, yace "Think about it, then u call me, wayar a bude take and akwai airtime a ciki, I will be expecting ur call" daga haka ya katse wayar, ta cire a kunnenta a hankali, bayan kusan minti biyar da gama wayar aka bude dakin junaid ya shigo, karasowa yyi gefenta yace "How are u feeling Heedayah" tace "Alhmdllh" yace "Bbu inda ke maki ciwo ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Look at me Heedayah" juyowa tayi ta kallesa suka hada ido, yace "Me xa ki ci?" A hankali tace "Shayi kawai xan sha" yace "Ohk, no bread?" Ta girgixa masa kai tace "Aa bana so" juyawa yyi ya fita dakin, ta boye wayar da ta rufe da palm dinta karkashin pillow da sauri. Heedayah na gama shan shayin da Junaid ya kawo mata ta mike ta tafi yin alwala, bayan ta idar da sllh ta daga karkashin pillow ta dau wayar da ta boye ta mayar inda yake sannan ta dawo ta kwanta, nan da nan wani baccin ya kuma dauketa. sai after la'asar Heedayah ta fita dakin bayan tayi sllh, Mami na xaune parlor da wata colleague dinta suna hira, Heedayah ta gaishesu Mami tace "How are you feeling now" Heedayah tace "Da sauki" Barrister Khadijah tayi mata Allah ya sauwake ita ma sannan Heedayah ta wuce kitchen da cup din hannunta, Farida ce kitchen din tare da Zainab suna girka dinner, Farida ta juya tana kallonta tace "Ya jiki?" Heedayah tace "Na ji sauki, tuwo xa ku yi?" Farida tace "Shi Mami tace mu yi" Heedayah ta marairaice fuska tace "To ni me xan ci da daddare?" Dariya Farida tayi tace "Ba ga Indomie ba sai ki dafa" a hankali Heedayah tace "Mami baxa ta bari ba ai cewa xata yi sai na ci" Farida tace "Vegetable soup ne fa" Heedayah ta girgixa kai tace "Bana ci" Farida tace "Guess what Heedayah" Heedayah ta d'an bude ido tace "No plss tell me, kinsan I am not a good guesser" Farida ta wara ido tace "At last Mami tace I can go to Abuja tomorrow" Heedayah tace "Only you?" Farida tayi dariya tace "Kin ma san da ya ta bar ni, nace ke fa tace baki da lafiya baxa ki je ko ina ba" a hankali Heedayah tace "Ni ai naji sauki, don Allah Mami ta bar ni" Farida tace "Ki bari anjima sai kiyi mata magana" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, can ta juya ta fita kitchen din, Mami ta dawo daga rakiyar Barrister Khadijah ta xauna nan parlor tana kallon Heedayah da ta xauna kasa kan carpet tace "Are you sure bbu inda ke maki ciwo Heedayah?" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba ko ina Mami" Mami tace "Toh Allah ya sauwake" Heedayah tace "Mami ai tare xa mu tafi Abuja da Farida" Mami tace "Noo you are going no where, tashi ki kai min system dina daki" Mikewa Heedayah tayi ta dau system din ta wuce sama, nan kuwa ji take kamar ta rushe da kuka. Bayan Magrib duk suna xaune parlor suna cin abinci banda Heedayah dake xaune tana kallo, Junaid ne ya shigo parlon bayan ya gaida Mami ya amsa gaisuwar da Farida ke masa, yana kallon Heedayah da ta gaishesa ita ma yace "Why are you not eating?" Shiru tayi bata ce komai ba, Farida tace "Ae bata cin tuwo" ya kalli Mami, sannan ya kalli Heedayah yace "Me xa ki ci?" Mami tace "Bbu wani abinda xata ci, idan baxa ta ci tuwon ba ta bar shi, meye da tuwon da xata ce bata iya ci?" Junaid dai bai ce komai ba, can dai ya wuce sama, ba a dau lkci ba ya sakko sanye da jallabiya, yana shafa kansa yace "Mami frnd dina na jirana waje xan basa sako cikin mota" Mami tace "Idan ma gidanku ne ke jiranka a waje that's not my concern, my only concern is that kar ka kuskura ka shigo min gidan nan da wani abinci" ya xaro ido yace "Abinci kuma? Abincin me Mami" Mami tace "I've told you my own" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya fita gidan, Heedayah dai na xaune sai wasa da fingers dinta take, Farida sai murmushi take, Mami ta kara gyara xama parlon tana jiran shigowar Junaid daga wajen frnd din nasa, yana fita ko minti goma ba ayi ba aka bude kofar parlon, Shuraim ne ya shigo da sallama, ya karaso cikin parlon, Mami na kallonsa tace "Welcome" ya xauna sannan ya gaisheta, ta amsa tace "Ya aikin?" Yace "Yanxu xan wuce" tace "Night Duty kawai kake yi ne ynxu?" Yace "Aa amma na fi yin night din ne" Farida ta gaishesa ya amsa, Heedayah ta dauke kai murya can ciki tace "Ina yini" Bai ce komai ba, Mami tace "Ya mutanen gida?" Yace "Lafiya lau" Tace "Kaka ta koma can gidan Baffa ne?" Yace "Aa tana nan gida" Mami tace "Ohk" yace "Ya mai jiki" Mami tace "Aa ta ji sauki sosai" Yace "Allah ya kara sauki" Mami tace "Ameen, Farida ki kawo masa abinci duk da nasan he is full always" Shuraim yyi murmushi amma bai ce komai ba, Mikewa Farida tayi ta tafi kitchen, bayan wani lkci ta fito ta ajiye masa tray din abincin a gabansa, ya d'an bude warmer din, lkci daya ya rufe yace "Ai bana cin tuwo" Kallonsa Mami ta tsaya yi, can tace "Baka cin tuwo??" Yace "Bana ci" Heedayah ta gyara xama tace "Mami to ai kinga yanxu dai ba ni kadai ce bana cin tuwo ba, kince baki taba jin wanda baya cin tuwo ba, shi ma ba gashi baya ci ba, sai in je in dafa masa Indomie" sau daya Shuraim ya kalleta ya dauke ido, Mami tace "Kar Allah ya sa ya ci tuwon, Farida dauke min abincina ki mayar kitchen yunwa bai ishesu bane" Murmushi kawai Shuraim yyi, Mami tace "Tuwo ba dai da miyar kuka ba ko kubewa ace baxa a ci ba" Ya girgixa kai yace "Aa ni fa ina ci, don na koshi ne yasa nace bana ci" daga haka ya mike yace "Xan wuce" Mami tace "Allah ya tsare" ya nufi kofa ya fita, Heedayah ta bi sa da harara, can ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login