Showing 156001 words to 159000 words out of 275313 words
Chapter 53 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
Farida bata ce komai ba, Heedayah ta jingina da mota ta turo baki tace "I just feel like giving up, who brought this idea" Farida tace "Ni ki daina min tambayoyi kamar yar jarida, I don't know too" suna ta tsaye Farida ta jawo Heedayah tana perceiving jikinta tace "Ina kika samu turaren Yaya?" Heedayah ta xaro ido amma ta kasa cewa komai, Farida ta kara shinshina mayafinta tace "Wa ya baki turaren" Heedayah tace "Shine ya sa min wai ban sa turare ba" Farida tace "Lallai ko Mami baya ba turarensa, kinsan nawa ake sayar da turaren?" Fitowar Shuraim tare da Mami yasa duk suka yi shiru, Mami tace "Hope xaka kira Barrister ka sanar masa ko?" Shuraim yace "Xan kirasa" Mami tace "Ba don kar ku bata lkci ba kuma ai ya kamata su je can gidan suyi ma kaka sallama kasan halinta sai tace an walakanta ta ba a gaya mata ba" Shuraim yace "Aa ba sai an gaya mata ba, xan kira Abba in gaya masa" Mami tace "Toh shkkn, Allah ya kiyaye hanya, ya tsare ku da tsarewarsa, but plss drive carefully Shuraim" Yace "In sha Allah" Mami tace "toh jira ku ke a ce maku ku shiga motar ne" Farida ta bude back seat ta shiga, Heedayah ma ta shiga, Mami ta daga masu hannu tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya my daughters" Duk suma suka daga mata hannu, Shuraim yyi mata sallama tace "Don't forget to call barrister plss" yace "In sha Allah," tace "But wait kana da fuel ko kawai ka tafi da motar nan" ta fadi tana nuna masa spare motar dake gidan tace "Daxu aka tafi fueling station aka yi full tank" yace "No nima full tank ne" daga haka ya tada motar suka bar compound din, Mami ta bi sa da kallo har ta daina ganinsu sannan ta koma ciki. Kafin Shuraim ya karasa titi ya kira Abba, bayan Abba ya daga yace "Abba xan je Abuja, amma yau xan dawo" Daga daya bangaren Abba yace "Me xaka je yi a Abuja, Anyway Allah ya tsare ka, safe trip" yace "In sha Allah, nagode" daga haka ya katse wayar, Mumy ya kira, tana dagawa bayan ya gaisheta yace "Mumy I will be going to Abuja now but anjima da yamma xan dawo" Mumy ta mike xaune daga kwancen da take tace "Me kuma xaka je yi a Abuja Aliyu, hanyar nan da ya xama abinda ya xama yan kidnapping sun yi yawa" Yace "Allah xai tsare" Tace "Ni dai duk sai naji hankalina bai kwanta da tafiyar ba, dama nayi mugun mafarki da asuba, aiki ne xai kai ka Abujan ko me?" Yace "Ehh" Tayi shiru, sai kuma tace "Dole sai kai?" Yyi murmushi yace "Ehh, ai yau xan dawo" tace "Toh ni dai don girman Allah har ka isa addu'a ya makale a bakin ka, wllh hanyar bashi da kyau kwata kwata Aliyu dama jirgin kasa ne bbu abinda xai daga min hankali, amma yau kaji an dauke wannan gobe kaji an dauke wancan ai da tashin hankali" Yyi kasa da murya yace "Ina tunanin xuciyar ki a tsarkake yake, kuma baki nufin d'an kowa da sharri, don haka ki kwantar da hankalin ki, in dai haka ne bbu abinda xai samu xuri'ar ki" Mumy da ta wani xaro ido tace "Uban me ya shigo da wnn xancen kuma, shi dama tsarkakken xuciya a goshi ake rubutawa, Ina ruwana da d'an wani da xan nufesa da sharri ni kuwa...." Yace "Aa misali na maki kawai..." Ta ja tsaki tace "Ni dai Allah ubangiji ya tsare min kai, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya raba ka da sharrin mutum ko karfe, har ka karasa addu'a kada ya bace a bakinka" Yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, ya ajiye yana d'an murmushi. Tun da suka fara fita cikin gari, Heedayah ke jin vibration din wayarta a jaka, Farida dake kusa da ita ma tana ji, Heedayah ta kalli Farida, Farida ta kalli Shuraim ta madubi idonsa na kan titi, Heedayah ta kai bakinta kunnen Farida murya can kasa tace "He has been calling tun daxu, I don't know why, how should I pick" Farida ta kara kallon Shuraim snn ta fiddo nata wayar a jaka ta mika ma Farida a hankali tace "Ki sa number a nan sai kiyi masa text message...." Da sauri Heedayah ta bude zip din purse din ta rufe da gyalenta snn ta haddace number don har snn wayar na vibrate ta mayar jakar ta kulle sannan ta sa number a wayar Farida ta tura masa message kamar haka "Muna hanya, I can't pick now" tana tura message din ta daga kai suka yi ido hudu da Shuraim da ya kallota, ya maida dubansa kan titi, a hankali cikin dubara ta koma gefe yanda ko ya kalli madubi baxai ganta ba sai dai Farida, ba a dau lkci ba Khaleel yyi mata reply yace "Kuna dai dai ina yanxu?" Heedayah ta kalli Farida, sai kuma ta jawota tana nuna mata text din, Farida ta bude hannu alamar bata sani ba, Shuraim yyi breaking silence din motar yace "Give me that phone u are holding" Heedayah ta xaro ido ta kalli Farida, Farida tace "Which phone, wayana ne fa" Yace "Ba da ke nake ba malama" Heedayah kamar xata yi kuka tace "Game fa nake yi" yace "Don't let me repeat my self" Farida ta saka wayar flight mode snn to koma can gefe, Heedayah ta turo baki ta mika masa wayar, fixgewa yyi daga hannunta ya ajiye kusa da nasa wayar. Bayan tafiyar kusan minti arba'in tun fitowarsu gida, Heedayah ta kalli Farida, rufe taga idonta har ta fara bacci, a hankali tace "Ya Shureen amai nake ji" ya wani hade rai yace "Amai??" Sai kiyi a nan ai, waye xai tsaya kiyi amai" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani minti sha biyar din ta marairaice da kyar tace "Wllh yana damuna sosai, ka tsaya plss xai taho" banxa yyi mata, ta rufe bakinta tana kakarin amai, a hankali ya fara slow down ya gangara gefen hanya yyi parking snn ya bude motar ya sakko ya bude side dinta, da sauri ta fito, ta xagayo ta duka gefen daji tayi ta kakalo aman amma ya ki xuwa, rungume hannu yyi yana kallonta, bayan few minutes ta dago da kyar tace "Kamar ya koma" ya wani hade rai yana kallonta, mikewa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Dama kika sake sa na tsayar da mota kika sauka sai dai ki samu wani da xai mayar da ke gida, that is idan har na tsaya ma kenan" ita dai bata ce masa komai ba, ya bude ta wajen da take xaune, ta shiga motar ya kulle sannan ya koma driver seat suka ci gaba da tafiya. Khaleel ne tsaye da 5 of colleagues dinsa, message ya shigo wayarsa, dubawa yyi ya ga daya daga excort din Mai neman takaran gwamna ne da suke targeting yau, ya bude text din mutumin ya ga kamar haka "Mun kamo hanya minti kusan hamsin kenan" Khaleel yyi masa reply "Ohk" sai kuma ya xauna ya xauna yana shafa kansa, Saif na kallonsa yace "Ya dai Brainiac??" Banxa Khaleel yyi masa. Heedayah dai sai mutsu mutsu take a mota, Shuraim kuma lkci lkci yake kallonta, daga karshe tace "Ya Shureen" banxa yyi mata, cikin rawar murya tace "Wllh amai xan yi yanxu, pls kayi hakuri ka tsaya" yace "Yi a wajen" ta fashe masa da kuka tace "Plss xai xubo" ya daka mata tsawa yace "Wai ance maki ana tsayawa a hanyar nan ne" cikin kuka tace "Toh Amai xan yi mana" yace "Kiyi a wajen" tace "Wayyo baxan iya ba" Farida dai sai baccinta take kamar warce ke saman gado, kuka Heedayah ta dinga yi a hankali, Shuraim sai duba inda xai iya tsayawa yake, cos he knows how risky the road can be, daga karshe dai ya gangara gefen titi ya tsaya, ya bude motar ya sakko snn ya xagayo ya bude mata tun kafin ta gama fitowa ta fara kwarara amai a wajen, ya ja baya yana yatsine fuska yana kallonta, ta duka wajen ta dinga kwarara amai, bude front seat yyi ya dau ragowar bottle water dake wajen, ya cire mata mayafin jikinta ya duka ya bata ruwan, ta fashe da kuka tace "Yaya har yanxu bamu kai ba, ni baxan iya tafiyan ba kuma gwara in koma gida na gaji" ya daure fuska yace "C'mon amsa ki wanke fuskar ki" kin amsan ruwan tayi, ya xuba ruwan a hannunsa ya dago kanta ya wanke mata fuskar, bayan ya gama ya dagata suka mike ya bude motar yace "Shiga" ta shiga motar ya mika mata mayafinta snn ya kulle ya koma driver seat, ta jingina da kujeran motar tana sauke numfashi. Khaleel yace "Oga na san abinda nake cewa, na kuma san abinda na gani, beside dole in a week time Mutumin nan xai koma Kano, we should let it till then" Oga Manga yace "Wani maganan bnxa kake haka Khaleel, bbu fa wasu excort din kirki tare da shi, daga motarsa sai na bayansa, shkkn... Komai ya xo cikin sauki knn, this is just the right time da ya kamata ayi duk abinda xa ayi, snn mun samu labarin babu wasu jami'an tsoro a hanya, Khaleel I am saying ku san duk ynda xa ku yi mutumin nn ya shigo hannun mu yau yau din nan, bbu wani excuse dinka da xai shige ni wllh, nan da wani lkci xa su isa kauyen nan da muka shirya, kuyi maxa ku fito kawai, you guys just have to hurry up...." Khaleel dake ta sauraronsa yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Zayyad yace "Wai yane Kayy, kwanan nn fa you are not just active, anya mace bata shigo rayuwar ka ba?? Kar fa irin abinda ya faru da Ishaq ya faru da kai, kana dai nan kuma duk muna kallo Arne ya harbesa...." Khaleel ya wani tabe baki yace "Ni ayi gunduwa gunduwa da ni" Da mamaki Zayyad yace "Kana nufin tambayar da nayi maka da gaske ne?" Khaleel yace "Wnn ba matsalar ka bace, all I want u all to understand here is that in dai har kuka fita yau din nan.... don ni dama bbu inda xanje and nobody can force me out, to ina me tabbatar maku da kyar xa ku sha, kuma sai an kama wasun ku, mu hadu a garin Abuja" daga haka ya fice duk aka bi sa da kallon mamaki suna ji ya fita da motarsa... Shuraim ya hade rai yana kallonta ta mirror yace "Meye hakan??" Da kyar tace "My head is turning me" yace "Turn it back" bata ce masa komai ba ta goge hawayen da ya makale mata ta jingina da motar, suna isa wani junction, yana kallonta ta madubi yace "Xa ki ci Ayaba" ta bi wajen da kallo taga masu ayaba, ta girgixa masa kai tace "Amai xan yi idan na ci" yayi parking ya sauka, ya siyo mata apples, Farida sai lkcn ta farka tace "Why are we not moving?" Heedayah ta langwabar da kai tace "Xai siya min wani abu" Farida tace "Daxu ba naga kina amai ba" Heedayah tace "Amma baki ce komai ba ko" Farida tace "Toh ba gashi har fuska ya wanke maki ba, ni kawai sae na ci gaba da bacci na" Tana fadin haka ta kara gyara Kwanciyarta, Shuraim ya dawo motar rike da ledan apples, with bottle water guda biyu, back seat ya bude ya ajiye xae rufe tace "Ya Shureen xan koma gaba" Bai ce mata komai ba ta sauko rike da abinda ya siya mata, ya rufe motar ya mika mata ledan ta amsa ta koma front seat, shi kuma ya shiga driver seat suka ci gaba da tafiya.... Sai karfe daya suka shigo garin Abuja bbu wani tashin hankali, Heedayah ta juya ta tada Farida, Shuraim ya hade rai yana kallonta yace "Ance maki dakin ki ne nan" Farida bata ko kallesa ba ta gyara mayafinta, yace "Wani anguwar xa mu" Farida ta fada masa, har suka iso gidan yayarta kuma bata sake bacci ba, da ganin anguwar dai kasan na manya ne sosai, driver ya bude masa gate ya shiga yyi parking, farida ta bude motar ta sauka, Heedayah ma ta sauka, Maman Fadil ta fito da mai aikinta da murna tana welcoming dinsu, gaisawa suka yi da Shuraim tace "Bismillah, ka shigo ciki" yace "Aa xan juya ne" tace "Haba don Allah" yace "In sha Allah" Heedayah tayi wucewarta ciki tare da Farida ya bi ta da kallo, can yyi ma Maman Fadil sallama yyi reverse.
*Gwara ku yi ta cancanasa, let me not hear pim from now till next tomorrow ehe*
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
House maid din Maman Fadil suka bari da shigo masu da kaya, Heedayah ta xauna babban parlon da ya kayatu da kayan alatu, Farida tace "Ta so mu wuce ciki" Heedayah tace "Ae ba mu gaisheta ba" Farida tace "Wlh I am so tired xata biyo mu daki" Ita dai Heedayah bata tashi ba, Farida tace "To sae ki sameni daki ni dai" daga haka ta wuce, lkci daya ta juyo tace "Innalillahi, baki amsar min wayata gun Shuraim ba" Heedayah ta bude ido tace "Lah, kuma gashi ya wuce" Farida ta hade rai tace "Why are you talking as if it's normal, wayana ne fa da nake amfani da shi, kuma duk xaman da kika yi gaban motar xa ki ce baki kallon wayar??" Heedayah bata ce mata komai ba sae tabe baki da tayi, Farida ta ja tsaki ta dawo cikin parlon ta dau wayar yayarta ta nufi kofar fita, a bakin kofa suka hadu, Farida tace "Aunty don Allah ki bude min, I want to make phone call, Shuraim ya tafi da wayata" Maman Fadil tace "Ohh shi ne Shuraim din dama?" K'in cewa komai Farida ta yi, yayar ta amshi wayar ta bude mata lock, Farida ta karba ta juya ta koma gun Heedayah tace "Tunda har kin haddace number sa sae ki sa min ni dai" Heedayah tace "Toh da na haddace number akwai abinda nace xanyi da shi ne, ko amfanin me xai min" Farida tace "Oho" Heedayah ta tabe baki ta amshi wayar ta saka number Shuraim ta mayar mata, Farida tayi dialing, sae da ya kusa katsewa ya daga, tace "Ni fa amfani nake yi da wayata kuma ka tafi da shi" yace "So??" Tace "Ka dawo in amshi wayata kawai" Yace "I see, idan na baki wayar a kaduna kar ki amsa" daga haka ya katse wayarsa, Farida ta kalli screen din da sauri, Maman Fadil tace "Me yace maki" Kamar xata yi kuka tace "Maganan banxa fa yyi min" Da mamaki Maman Fadil tace "Maganan banxa kuma" Farida tace "Ehh mana ai haka yake, ni dai Aunty ki yi masa magana don Allah ya maido min da wayata tun bai yi nisa ba, ni wllh baxan iya xama gidan nan bbu wayata ba" Maman Fadil tace "To ke garin yaya wayar ki ya je hannunsa" Farida tace "Ba ga warce ke amfani da shi ba ya amshe" Maman Fadil tace "Toh don tana amfani da waya sai ya karba, an hanata rike waya ne?" Farida tace "Ina fa, shi dai ne ya hanata rikewa" Maman Fadil ta amshi wayar ta sake dialing numbersa ta kai kunne, yana dagawa tace "Haba Yaya Shuraim ayi hakuri da su pls, ynxu dai kana ina sai in tura driver ku hadu ya amso wayar kawai" shiru tayi tana sauraronsa sannan tace "Toh shkkn, ba damuwa, nagode" Daga haka ta katse wayar, Farida ta wani xumburo baki tace "Me ya ce" Maman Fadil tace "Yace bai ma tafi ba tukun, idan bai dawo ba xai kirani in turo driver din ya amsa wayar" Farida ta wani tabe baki tayi wucewarta daki, Maman Fadil na kallon Heedayah tace "Deedayar kaka an xama 'yan mata, ya gajiyan hanya?" Heedayah tayi murmushi tace "Alhmdllh" sannan ta gaisheta, Maman Fadil ta amsa tace "Ya su Mami da Yaya" Heedayah tace "Duk suna gaisheku" Maman Fadil tace "Toh muna amsawa, ki shiga ciki kiyi wanka kiyi sllh, sai ku sakko ku ci abinci" Heedayah ta mike tace "To, ina Fadil?" Maman Fadil tace "Yana can neighbors dinmu" Heedayah tace "Ohk" snn ta wuce ciki ita ma. Heedayah na kwance dakin Farida ta fito daga wanka ta shirya ta dau darduma xata yi sllh, Heedayah ta mike xaune tace "You are taking it personal as if ni nace Ya Shureen ya amshi wayar ki" Farida bata tanka ta ba ta fara sallarta, Heedayah ta tabe baki ta mike tsaye ta cire kayanta snn ta wuce bandaki, tana fitowa wanka taga Farida ta fita dakin, ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi snn ta saka hijab dinta ta shimfida darduma ta fara sllh. Bayan ta idar ta mike ta dau purse dinta ta bude ta ciro waya, miss calls din Khaleel ta gani da yawa, tayi dialing number, yana fara ring ya daga, tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, kun isa Abujan ko?" Tace "Ehh mun kai" yace "Ya hanya" tace "Lafiya lau kuma bbu abinda muka gani a hanyar, ba wasu kidnappers din da kace" D'an murmushi yyi yace "Da gaske?" Tace "To kai so kayi ayi kidnapping din mu dama?" Ya girgixa mata kai yace "Idan aka yi kidnapping din ki ai ni aka yi kidnapping" Tace "Ban gane ba" Yace "Tun da dai you arrived safely shkkn" Ta tabe baki bata ce komai ba, yace "Ke da wa ma ku ka tafi Abujan??" Tace "Ni da Farida, da Ya Shureen, shi ya kawo mu" yace "Waye shi?" Tace "Ba na ta6a gaya maka ba, yaron Abbana ne, yayanmu ne" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ohk soldier din nan?" Tace "Ehh" yana gyada kai a hankali yace "I