Showing 240001 words to 243000 words out of 275313 words

Chapter 81 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

Barrister, ko Hajiya Rahinah" Tace "Toh" Nan tayi masa sai da safe snn ta mike ta fita parlon, bangaren Ammi ta koma tana shiga parlonta taga wayarta kan kujera ta dauka ta wuce dakinta, sai bayan da ta kwanta tayi dialing number Farida da ta haddace, Farida na dagawa da taji muryarta tace "Why did you leave ur phone Heedayah?" Heedayah tace "Mancewa nayi, ya Mami fa" Farida tace "Alhmdllh, kun isa lafiya?" Heedayah tace "Lafiya lau" Farida tace "Kun hadu da Ya Shuraim?" Murmushi Heedayah tayi tace "Ehh, ya ma ce in gaishe ki idan muka yi waya" Farida tace "Ki gaisheni kuma??" Heedayah tace "Ehh mana, sai da ya tambayeni me yasa ba mu xo tare ba, Kinga dama kun kusa mid semester, kawai ki taho nan kiyi hutun" Farida tace "Toh ai Mami might not let me" Heedayah tace "Ba sai Ammi tayi mata magana ba" Farida tace "Uhm" shiru Heedayah tayi kafin tace "Ya Khaleel sun kai Lafiya?" Farida tace "Ehh daxu suka yi waya da Mami" Da sauri Heedayah tace "plss ki turo min number da ya kira da shi" Farida tace "Wani number Mami ne da ta bashi ya sa a karamin wayar Ya junaid" Heedayah tace "Send me the number plss" Farida tace "Ohk I will now, but tell me Ya Shuraim din kullum yake xuwa?" Dariya Heedayah tayi tace "Eh mana, kullum sai ya xo, ni dai ki turo min number yanxu" Daga haka ta katse wayar, cikin few minutes sai ga number Farida ta turo mata, bude kofar dakinta aka yi Ammi ta shigo tace "Ke kika dau wayata" Heedayah ta marairaice tace "Ehh Farida na kira" Ammi tace "Ina naki wayar?" Heedayah tace "Na mance a Kaduna" Fita Ammi tayi daga dakin, Heedayah tayi dialing number da Farida ta turo mata, yana fara ringing tayi murmushi, Daga kiran aka yi amma ba ace komai ba, a hankali Heedayah tayi sallama, Khaleel dake kwance har ya fara bacci ya bude idonsa dake a lumshe bayan ya daga kiran yace "Heedayah?" Tayi murmushi tace "Ka gane muryata ashe, good evening" Yace "Evening, Mami tace min kun tafi kano" tace "Ehh bayan kun tafi muka wuce" Yace "Yaushe xa ki dawo?" A hankali tace "Lkcn da xaka dawo" Shiru yyi kafin yace "Uncles dina sunce sai next week" Tace "Nima next week xan dawo" Yace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds a hankali yace "In tambayeki Heedayah" Tace "Ina jin ka" Jin bai ce komai ba tace "Hello?" Yyi kasa da murya yace "Xa ki iya aurena?" Sosai gabanta ya fadi, a hankali tace "Me yasa ka min wnn tambayar?" Yace "Ina ga kamar baxa ki yarda ki aureni ba" Tace "Toh ka daina wnn tunanin" Yace "Ban ta6a son 'ya mace ko kula 'ya mace duk tsawon rayuwata ba sai kanki Heedayah, ni kai na ban san irin son da nake maki ba, ko fado min kika yi sai naji xuciyata ya dameni, and I have to nurse it for sometimes kafin in dawo dai dai, kin san condition dina Heedayah kar ki gujeni plss" a sanyaye tace "I won't in sha Allah...." A hankali yace "But have you ever thought of living In same roof as husband and wife with someone that was once a Hoodlum??" Hawayen dake makale idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace "I am happy u said with someone that was once a Hoodlum, I love you not minding ur past dear" Jin yyi shiru bai ce komai ba, a hankali tace "Are you there?" Yace "Sure, I love you with every breath of mine" Murmushi tayi tace "I love you same" Yace "Xan kwanta yanxu, coz I am very tired, how can I reach you always?" Heedayah tace "Ae wayar Ammi ne you can call me anytime" yace "Baxan dameta ba?" Tace "Aa" yace "Alright, thank you, sleep tight" Tace "But have u eaten?" Yace "Sure na ci abinci" Tace "Alright, Sweet dreams" Yace "Yes love" Daga haka ya katse wayar. Washegari da sassafe Heedayah ta tafi gaida Abbanta a bangarensa, Yakumbo ta samu a parlon, Ta duka ta gaida Yakumbo snn ta gaishesa, Yakumbo tace "Amadi in ji dai baxa a wani lafta uban lkci ba idan masu auren yarinyar nan suka xo, kaga gwara kasan ka sauke nauyinta a kanka, don kana gwamna bbu ruwanmu da lalacewar tura yarinya kasashen shegu karatu, gwara idan an mata auren mijin ya kai ta can ya jira har ta gama barin ma wayayye xata aura d'an boko" Shi dai Abba bai ce komai ba, Yakumbo tace "Kayi shiru" Yace "Aa su xa su yanke lkcn da yyi masu ai Yaya" Yakumbo tace "Aa ni fa babban damuwata Heedayah fa tana da budadden ido wllh, yanxu tana ganin fuska xata fara hotuna a babban gidan nan ta baxa shi a yanar gizo ayi ta yawo da shi ana cewa ai yar gwamna gari kaza ce, to kafin hakan ya faru gwara a mata aure don ni baxan ji dadi ba, ba naga yanda 'Yan yan manyan kasan suke ba, wani ma kusan a tsirara xai yi hoton" Abba dai bai ce komai ba, Yakumbo ta mike tace "Mu kam da mutunci da martabar mu, bamu yada al'adarmu da kunya ba don mun samu duniya" Abba na kallon Heedayah da hawaye ya kawo idonta yace "Ae kina son yaron ko?" Lkci daya ta fashe masa da kuka tace "Abba a matsayin Yaya na daukesa fa, ni bana sonsa" Da mamaki yake kallonta, can yace "Baki son sa?" Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace "Kina da wanda kike so ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "To waye shi?" A hankali tace "Khaleel" Abba yace "Waye kuma Khaleel?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dinga kallonta yace "Who is he?" Kasa basa amsa tayi, yace "Talk to me a ina yake?" Ta girgixa masa kai kawai, bayan wani lkci yace "To tashi ki tafi" Mikewa Heedayah tayi ta fita daga parlon, part din step mum dinta ta tafi, a parlonta ta sameta tana feeding din Islam, Ta xauna kusa da ita ta gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Har kin tashi Heedayah" Heedayah tace "Na tashi Aunty" Mum Islam tace "To ya gajiyan jiya" Heedayah tace "Alhmdllh" Mintin Heedayah kusan talatin a parlon kafin ta mike tace mata xata je ta gaida Kaka, tana fita parlon ta tafi wajensu kaka, Kaka na ganinta tace "Yauwa gantalallun masu aikin nan shiru shiru ban gansu ba, gashi ki kira min Shureen in ji ya jikinsa" Heedayah ta amshi wayar tace "Toh wai me ya samesa ba ya warke ba har ya xo jiya" Kaka tace "Atoh kuma baxan ji yanda ya kwana ba, bashi da kowa fa garin nan Allah ya rufa masa asiri na dawo garin" Heedayah ta tabe baki ta nemo numbersa tayi dialing ta mika mata, yana fara ring ya daga, kaka tayi sallama, ya gaisheta tace "Ya ka kara jin jikin Shureen?" Yace "Naji sauki" tace "Toh Allah ya kara lafiya, ka fita aikin ne?" Yace "Ehh" Heedayah ta amshi wayar ta kai kunne tace "Ya Shureen you didn't go with the laptop Charger, kuma charging bashi da yawa kamar" yace "Ohk baki bani ba" tace "Are you coming to collect it?" Yace "Ohk I will" Tace "Tohm sai anjima" Daga haka ta katse wayar, Kaka ta rike ha6a tace "Yaushe kuma ku ka fara shiri da Shureen har kuna juya yare??" Dariya Heedayah tayi tace "Aa ba shiri muke yi ba, kawai abu na ya ara" Kaka tace "Meye ya ara?" Heedayah ta ajiye mata wayarta tace "Idanuwan kaka" Daga haka ta fice da sauri daga parlon tana dariya. Bayan Magrib Heedayah na xaune kan darduma ta idar da sllh daya daga house maid dinsu ta kwankwasa kofar dakinta, mikewa tayi ta isa gun kofar ta bude, Maid din ta gaisheta da ladabi snn tace "Hajiya tace ki je" Heedayah tace "Ohk" juyawa Mai aikin tayi ta wuce, Heedayah ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye snn ta fita xuwa bangaren Amminta, Ammi na kallonta bayan ta shigo parlonta tace "Waye kika kira da wayata?" A hankali Heedayah tace "Khaleel ne" Ammi tace "Waye Khaleel?" Heedayah ta sauke kanta tace "Yayan Junaid"




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Shiru Ammi tayi tana kallonta, Heedayah ta kasa kallon Mahaifiyartata sai fidgeting din yatsunta take, mika mata wayar Ammi tayi, ta karasa ta amsa ta juya ta bar parlon ta kulle mata kofa ta koma dakinta, gefen gado ta xauna tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Ina yini?" Cikin Husky voice dinsa yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ya kowa da kowa" Yace "Fine....." D'an murmushi tayi tace "Do you like it in there?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Nop, not when u are not here Heedayah" Tace "Uhn you need to get use to ur relatives, and nasan Sumayya xata dinga keeping dinka company ai" Yace "Wace haka?" Tace "Cousin dinka mana" yyi shiru, tace "Ko ba haka ba?" Yace "Haka ne" turo baki tayi kamar xata yi kuka tace "Haka xaka ce min?" Yace "Toh yi hakuri, ba haka bane..." Knocking kofarta aka yi, tayi kasa da murya tace "Hold on pls xan bude kofa ana knocking" a hankali yace "Ohk dear" ta mike ta bude kofar taga Maid dinsu ce Amina, gaisheta Amina tayi tace "Hajiya kin yi bako a parlor yana jiran ki" Da mamaki Heedayah tace "Bako?" Amina ta gyada mata kai tace "Ehh" Juyawa tayi ta koma dakin, Amina ta bar bakin kofar, Khaleel yace "Wani bakon kika yi?" Heedayah tace "Nima ban sani ba wllh, let me go and check idan na dawo daki xan kiraka" A hankali yace "Alright..." Tace "Bye..." Daga haka ta katse wayar, ta dau mayafinta ta yafa snn ta fita, parlon baki ta nufa ta bude a hankali ta shiga da sallama tana leka ciki, Shuraim ta gani xaune idonsa a kan screen din wayarsa, ya dago kai suka hada ido, ta turo baki tace "Toh kai ne bako?" Bai ce komai ba har ta karaso cikin parlon ta xauna kujeran dake kusa da nasa tace "She told me nayi bako" Shuraim yace "Ohk to kilan bakon ki ka yi a waje, ki je ki samesa" Ta buda ido tace "I tot kai take ce ma bako?" Yace "Nima ban sani ba, na dai san nace ta kira ki ki amshi laptop dinki" Heedayah ta langwabar da kai tace "Ohk... A xubo maka abinci?" Yace "I'm not hungry" Tace "Good evening" Yace "How are you" tace "I am fine" ta wara ido tace "Two minutes plss" Daga haka ta mike da sauri tanufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, can dakinta ta koma ta dauko wayar Ammi ta fito, tana kusa parlon da Shuraim yake ta tsaya tayi dialing Number Farida, yana fara ring Farida ta daga, Heedayah tace "You know what sweetheart?" Farida tace "No, what?" Heedayah tace "Ya Shuraim ya xo ya tambayeki bari in kai masa wayar ku gaisa ynxu" bata saurari Farida ba ta shige parlon da sauri ta isa kusa da Shuraim dake kallonta, ta mika masa wayar hannunta murya can kasa tace "Xa a gaisa da kai" Bata jira yace komai ba ta kai masa wayar kunne ganin sai kallon wayar yake, ya kama wayar da mamaki, ta xauna arm din kujeran murya can kasa tace masa "Toh kayi magana mana" A hankali yace "Assalamu Alaikum" Murmushi kawai Heedayah ke yi tana kallonsa, Farida da taji gabanta ya fadi daga daya bangaren ta amsa a hankali ita ma tace "Ina yini Ya Shuraim" Shuraim ya kalli Heedayah da mamaki, ta wara masa ido, dauke idonsa yyi yace "Lafiya lau ya kike?" Farida tace "Alhmdllh, ya kano? Ya aiki?" Yace "Fine, ya su Mami?" Tace "They are all fine" Yace "Maa sha Allah, ana ta lectures?" Tace "Aa exams xa mu fara next week" Yace "Toh Allah ya bada sa'a, ayi karatu sosai" Murmushi Farida tayi tace "In sha Allah...." Xai cire wayar a kunnensa Heedayah ta mayar da sauri ta wani tsuke fuska murya can kasa tace "Kace yaushe xata xo kano joor" Kallonta kawai Shuraim ke yi, can dai yace "Yaushe xa ki xo Kano?" Farida tace "After my exams In sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu muna jiran ki" Farida na murmushi tace "In sha Allah, ya kano weather?" Shuraim ya wani hade rai ya sake kallon Heedayah, wara masa ido tayi tana washe masa hakora, can dai yace "Alhmdllh" Farida tace "You like it there?" Yace "Sure it's cool, ki gaida su Mami" Heedayah ta turo baki ta matsa kusa da kunnensa kuma, murya can kasa tace "Kace kana son ta fito da first class" Hannu yasa ya ja bakin nata, tayi wani kara ta rufe bakin da hannunta da sauri, Shuraim dake sauraron Farida dake masa sai da safe yace "In sha Allah, thank you" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta bar wajen da sauri ganin Fixgota yake son yi, ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kallonta kawai yake, tayi me isarta ta koma kujeran da take xaune ta xauna tana wani murmushi tace "Kasan me ya Shureen?" Ya hade rai yace "What's the meaning of what u just did?" Turo baki tayi taki cewa komai, ganin kallon da yake mata tace "Toh muna magana da ita ne shine take tambayata Ina ya Shureen shine na baku ku gaisa, is there anything wrong with that?" jingina yyi da kujera bai ce mata komai ba, ta ta6e baki tayi shiru, bayan few minutes yace "Abba yace xa a siya maki waya, wani iri kike so" Kallon wayarsa dake ajiye tayi ta mike ta karasa ta dauka tana duba wayar sannan tace "Irin wannan" Kallonta kawai yake, can yace "Toh sai ki rike wnn din kawai" Ta xaro ido tace "Ba sabo Abba yace a siya min ba" Yace "Wnn ma sabo ne ai" Ajiye masa tayi ta koma inda take tace "Bana son irinsa kuma" Murmushi kawai yyi bai ce komai ba, can ya kalleta yace "Ban taho maki da laptop din ba sai gobe" tace "Ohk, in kawo maka chargern?" Yace "Ehh" Mikewa tayi ta wuce dakinta ta dauko masa chargern ta dawo ta basa ya amsa yace "Thanks" Mikewa yyi yace "Sai da safe, kar ki ce ma kaka na xo" Tace "Baxa ka sha shayi ba?" Yace "Na koshi" Tace "Ohk, ina son xan maka magana, can I escort you say in gaya maka a waje" Ya kalleta yace "As u wish" bin bayansa tayi suka fita parlon.... Tafiya suke a tare tana gefensa, baka ta6a cewa dare ne don ko ina tarr da hasken fararen fitilu ga shukokin dake kewaye na ta bada Iska me dadi, bayan wani lkcn Shuraim ya kalleta yace "Har gida xa ki rakani kenan?" 'yar dariya tayi tace "Aa, ai parking space din da nisa, but idan na rakaka sai ka sake rakoni rabin hanya sannan ka koma" Bai ce komai ba, jin taki magana ya kalleta suka hada ido, tace "Ya Shuraim ka gaya min irin qualities din da kake so a wajen mace?" Tsayawa Shuraim yyi yana kallonta yace "Why did you ask that?" Tace "No just tell me" Dauke idonsa yyi daga kallonta, ta kalli wani thatch me kyau dake dauke da kujeru tace "Mu je can mu xauna sai ka gaya min" Bata jira cewarsa ba ta nufi Thatch roofing din ta hau stairs dake wajen snn ta xauna kan daya daga kujerun, bin bayanta yyi xuwa wajen, ya xauna saman kujera, ta tallabi chin dinta tana kallonsa tace "Ina jin ka?" Ya shafa beard dinsa bayan few second yace "Ohkk... ina son mace me tsafta, me kuma rikon addini" Jin yyi shiru ta xaro ido tace "Shi kenan?" Yyi murmushi yace "Aa Ina son 'yar doguwa fara, me manyan idanuwa da dogon hanci with cute lips" Heedayah ta wara ido tace "Dimples fa?" Yyi shiru yana kallonta, can yace "Yi dariya mu ga" Bata san lkcn da ta kwashe da dariya ba, yyi murmushi yana kallonta, ta gaji don kanta tayi shiru, bayan few seconds yace "Bana son dimples" Ta marairaice tace "Why" yace "Kawai haka nan" Tace "Toh baka son me gashi har gadon baya?" Ya d'an yi shiru, can yace "Toh ai ban san ya gashi yake har gadon baya ba, do you mind showing me?" ta d'an yi shiru kafin tace "Toh ai ni nawa bai kai gadon baya ba" Yace "Ehh xan iya measuring with my eyes ai" ta fara bin inda suke da kallo ganin sojoji ne can nesa da su bakin daya daga many gates din building din ta sauke mayafin kanta snn ta cire hulan gashinta ta cire ribon din da ta daure dogon gashinta da shi, tuni kamshin gashin nata ya cika wajen, kallonta kawai Shuraim yake, ta juyo tana nuna masa bak'in gashinta da ya sauko kasan shoulders dinta bai karasa gadon bayanta ba, jin bai ce komai ba ta juyo, sauke idonsa yyi tace "Have u finish measuring?" Yace "Yeah" ta daure gashinta ta mayarda hulan snn ta daura mayafinta a kai tana kallonsa, flowers ya tsura ma ido, tace "So?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban son gashin da ya kai gadon baya" Da mamaki tace "Me yasa?" Ya juyo yana kallonta a takaice yace "Haka nan" Ta langwabar da kai tace "Toh kana son me wushirya?" Yace "Meye hakan?" Tace "Gapped teeth" Yace "How? In ga naki wushiryan?" Tace "Aa bani da shi ni" Daga haka ta bude masa fine set of teeth dinta, Kallonsu ya dinga yi tace "Uhm??" Ya girgixa kai yace "No, bana son wushirya" Tace "Ohk hips fa?" Yace "Meye shi?" Tayi dariya tace "Hips ne baka sani ba?" Yace "Ehh" Tace "Ohk forget that" yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login