Showing 273001 words to 275313 words out of 275313 words

Chapter 92 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

ci gaba da wanke wankenta, a tare suka gama aikin gidan gaba daya, wajen wanka sai da suka yi yar drama sannan aka yi wankan, tuni Khaleel ya shirya ya xauna dakin yana kallonta tana shafa lotion dinta kamar bata so, mikewa yyi ya amsa duk da tace bata so yace "I just have to help you" kallonsa take kamar xata yi kuka don ta san sauran, shiryawan da ba a gama ba kenan sai wajen sha daya na safe, shi ya fita ya shigo da bakuwar da baxata wuce ashirin da biyu ba, Heedayah ta sakko downstairs cikin atamfarta da ya mugun amsan jikinta, satin ta biyu gidan Khaleel tayi wani kyau ta murmure kamar ba ita ba, kallon kyakkyawan budurwar ta dinga yi har ta karaso cikin parlon ta xauna suka gaisa da murmushi fuskarta snn ta mike ta tafi dauko mata ruwa da lemo a Fridge, hira suke yi da Khaleel sama sama, ita dai Heedayah na xaune parlorn tana danna wayarta tana sauraron conversation din nasu, daga karshe ta mike ta wuce sama... Bayan few minutes Maryam na kallon Khaleel tace "Toh ni xan koma, na gaida amarya sai Allah ya sake hadamu" mikewa Khaleel yyi yace "Haba, so early Maryam?" Tace "Next time xan dawo in sha Allah" yace "Toh xaki kira driver din ne? naga ya wuce" Tace "Eh bari in kirasa" yace "Ohk I am coming" sama ya wuce ya tadda Heedayah kwance, hade rai tayi ganinsa ta juya masa baya, a hankali yace "Ki xo ku yi sallama" mikewa xaune tayi tace "Who is she?" Ya xauna gefen gadon yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Kamar yanda na ta6a kubutar dake shekaru masu yawa, ita ma haka nayi mata, yarinyar wani minister ne da baxan fada maki ba, bata tona mana asiri ba duk sbda ni, since then kuma mu ke xumunci sosai da ita a waya, always preaching and praying for me in dawo hanyar dai dai" Shiru Khaleel yyi yana kallon Heedayah dake kallonsa ko kiftawa bbu, ya sauke idonsa yace "Hijab din da na ta6a baki kika yi sallah wancan lkcn a gidana nata ne, I have many of her like that we are still frnds with till date, both male and females, Allah yayi sai mun sake haduwa dake rayuwata xai dawo sabo" Heedayah bata iya tace komai ba, ya dagota daga kan gadon yace mu je ku yi sallama, ba musu ta bi sa suka koma parlon, knocking kofa aka yi bayan sun shigo parlon a tare, Heedayah ta xauna tana murmushi tace "Na fa daura girki ki jira yyi sister don Allah" Maryam tace "Aa nagode sosai, sae kuma wani lkcn idan Allah ya yrda" Khaleel ya karasa ya bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim dake tsaye bakin kofar with his uniform, Khaleel ya mika masa hannu with surprise din ganinsa, nan suka gaisa sannan Shuraim ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ganinsa tace "Ya Shureen!!!" ya sakar mata murmushi ya karaso parlon yace "Deedayar kaka" dariya tayi ta rufe fuskarta, ya xauna saman kujera yana kallon Maryam da ta gaishesa ya amsa da murmushi, a hankali Heedayah tace "Ina yini ya Shureen" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, yaushe ka dawo?" Yace "Jiya da daddare" cike da jin dadi tace "Na ji dadi da ka xo ya Shureen, I'm so happy" Khaleel ne ya kawo masa ruwa da drink da kansa ya ajiye sannan ya xauna parlon, hira suka yi na few minutes, Maryam dake ta xaune ta kalli Khaleel tace "I will be on my way Khaleel" yace "Ohh wai da gaske baxa ki jira ki ci abincin ba?" Tayi murmushi tace "Nace next time in sha Allah" Khaleel yace "Toh ki kira driver din naki tukunna...." Shuraim dake kallonta yace "Where to?" Tace "Home" yana kallonta yace "Home din ba shi da location?" Murmushi tayi tace "GRA" yace "Ohk let me drop you" Maryam dai bata ce komai ba, ya mike yana kallon Khaleel yace "Xan koma sai wani lkcn idan Allah ya yrda, I just came to say hi" Khaleel ya mike shi ma yace "We really appreciate bro, Allah ya saka da alkhairi" Heedayah tace "Ya Shureen har yanxu su Rabi'ah basu xo ba" yace "Xa su xo" Rakasu Heedayah da Khaleel suka yi har bakin motar Shuraim dake waje, Khaleel na kallon Maryam yace "I really appreciate the vist Maryam, Allah ya bar xumunci" Shuraim ya kalleta da sauri jin sunan da Khaleel ya kirata, sae dai bai ce komai ba ya bude motarsa ya shiga, Maryam ta daga ma Heedayah hannu ta shiga front seat, sai da suka bar layin sannan Heedayah da Khaleel suka koma ciki, da yammacin ranan Sudais da Farida suka xo gidan, Heedayah tayi tagumi a bedroom dinta tana kallon Farida dake bata labari iri iri, a hankali Heedayah tace "Ni dai duk ba abinda ya dameni ba kenan Farida, all I want to know is... A ina kika samo ya Sudais har ku ka xo gidan nan tare" Xaro ido Farida tayi Heedayah ta kyalkyale da dariya sosai tace "Ke kika bi sa gidansu ko shi ya biyo ki kuka xo tare???" Farida ta jefa mata counter din hannunta tace "Ban sani ba...." Heedayah har da kwanciya sbda dariya. Sai kusan Magrib Sudais da Farida suka bar gidan, Da daddare Heedayah na kwance jikin Khaleel suna kallo a parlor ya kamo hannunta yace "Ranan lahadi xa a kawo gaisuwan Farida idan Allah ya kai mu" Heedayah ta mike xaune da sauri tace "Really?? But she didn't tell me" Ya d'an yi murmushi bai dai ce komai ba, tace "Who is she getting married to??" Ya buda ido yace "Wanda suka xo tare daxu" Heedayah ta wara ido tace "Waow ya Sudais.. I'm very happy wllh" Khaleel ya ja hancinta yace "Da gaske" tace "Ehh mana" mikewa yyi ya dauketa ya kashe TV da switches din parlon suka wuce sama tana masa kukan shagwaba wai bata so. 2 years later.... Kaka ce xaune main parlor din gidan Shuraim tayi kane kane tana bayani ga plate din farfesun da ta gama sha a gefenta, yau watan ta uku kenan a gidan taki tafiya, Maryam ce xaune gefenta tana ta sauraron jawabinta, Kaka tace "Ynda kika xauna haka kusa da ni wllh haka marigayiyar ke yi farkon da aka aurota kafin shaidan ya shiga tsakaninmu, sai dai ita bata samu ciki da wuri ba gaskiya, ke kuma gashi har kin tsufa haihuwa ko yau ko gobe, snn ynda naga kike da yawan ibada haka take ita ma da farko" Maryam dai murmushi kawai take kanta a kasa, kaka tace "Aa gaskiya mun yi rashi mu kam, Allah ma ya sani, shi sa da Allah ya ba Shureen ke, ga ki da sunan mahaifiyarsa gaki da hankali naji dadi sosai, wllh na fi kowa murna, ba gashi yanxu kamar ba shi ba tunda yana ganinki, ynxu fa idan Allah yyi mace xaki haifa ae sai dai a kirata da Maryam" Ita dai Maryam bata ce komai ba, Ganin xancen kaka ba me karewa bane nan kusa tace "Kaka bari in karasa abinda nake kada bakin su karaso sunce suna hanya" Kaka tayi tagumi tace "Ae ni ba xuwan Deedayah gidan nan ba, wnn Mayyar 'yar tata me sunan Rakiya kukan banxan ta tsaya min yake a rai, ke yarinya gaki kamar aljana amma sai fitina, Kaiii ai yarinyar nan fitinanniya ce" Dariya Maryam tayi tace "Kaka tsoronki fa take amma bata da kuka ai, ba suna xuwa ba" Kaka ta hade rai tace "Tsorona a kan me? Me nayi mata? To taje ita da Allah, gashi babu abinda ta bari na basamuden ubanta, sae dai wllh ba dai hankali ba Khaleel har ya fi min gantalallen Sudais din nan dake makale da matarsa, daga shi har matar tasa Farida basa gaida kowa a duniya, su kadae ke rayuwarsu irin na turawa, ki ji fa tunda suka xo min gaisuwar Salima da ta mutu a kasar waje duk da ban hada komai da ita ba ban sake ganin keyarsu ba, d'an nasu ma me sunan Umaru basa kawo shi gun kakanninsa balle ni karan kada miya, shi Junaid dama duk sati xaki gansa da salahar matarsa, har miya take min me kyau wani lkcn wllh, amma tunda na dawo nan shi ma sai ya ga dama, wnn d'an albarkan Khaleel kadai nake gani jifa jifa" Mikewa Maryam tayi da kyar ganin kaka ba gama xancenta xata yi ba tace "Bari in je kitchen kaka" kaka tace "Toh gwara ai kina yi kina motsa jikin, Allah dai ya raba lafiya" Maryam bata kai kofar kitchen din ba, Heedayah ta shigo parlon tare da cute Rahinarta da suke kira da Noor a hannunta, Kaka ta washe baki tace "Kabo kabo, ynxun nan na gama cewa shiru shiru baku karaso ba ko lfya ashe kuna kusa" Maryam dai sai murmushi take tana kallon Heedayah tace "Har na fara cire rai" Dariya Heedayah tayi tace "Wllh mun fara biyawa gida gun Mami ne" Kaka ta kya6e baki tace "Amadun na nan ko ya fita shi kuma daya?" Heedayah tace "Aa Abba ya fita aiki, Mami ce kadai a gida" Kaka tace "Toh ina d'an albarkan mijin naki" Heedayah tace "Yana waje" Kaka tace "Toh ya shigo mana sai kace wani bako, ni bai fiye min Sudais da Junaid ba ma, shi dama Shureen kwanan nan kora da hali yake min ba don matar na masa jan ido ba wllh" Dariya kawai Heedayah ke yi Maryam na tayata, Noor dai ta kankame uwarta sai kallon kaka take da manyan idanuwanta kamar taga dodo, Maryam ta karaso ta amsheta tace "Little Mami taho mu gaisa..." Kaka tace "Kya haifi irinta kuwa, ke baki ganta kamar xabiya ba sai tsayin gashi kamar aljana, ae kyan na uban ne, don uwarta haske ne kawai ya ceceta, daga hanci sai idanuwa" Heedayah dai bata tanka kaka ba tayi murmushi kawai, Kaka tace "Naji kun je kano, me yasa baki bar ma uwarki ta yaye maki ita ba, ga dai shi nan karamin ciki ne a jikin ki wllh" Dariya kawai Maryam ke yi tana kallon Heedayah da ta ki tanka kaka ta fita don ce ma Khaleel ya shigo, shigowar Khaleel parlon yasa Shuraim ya fito, kaka na kallon Khaleel dake xaune gabanta ya tankwashe kafa bayan sun gaisa da Shuraim tace "Tun safe wllh Shureen bai fito gaisheni ba, kilan daga nan ma ni gidanka xan koma naga kafi sanin mutuncin babba" murmushi kawai Khaleel ke yi yace "Ki hada kayan naki mu tafi" mikewa kaka tayi ta wuce dakinta ta fara hada kayanta kamar jira take, Shuraim ya kalli Heedayah yace "Toh mu mun huta yanxu kuma, sai ke da mijin ki ku shirya" Turo baki Heedayah tayi tana kallon Khaleel tace "Allah bar maku gidan xan yi kai da ita ni dai...." Maryam ta xauna ta dinga dariya, shi dai Khaleel banda murmushi bbu abinda yake yana shafa kansa, sai ga kaka ta fito da katon jakarta da handbag tace "Ku mu tafi, gidan Amadun ma ba dadin Rahinah nake ji ba"

Heedayah isn't free, you read for free ๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


_Ina bukatar addu'ar lovely fans a kan Allah ya ba ni, da duk wani me karatu sa'a, ya sa mu gama lafiya, and reap the fruit of our labor in sha Allah, special greetings to all fudite (Fed uni dutse), Khaleesat Haiydar ta gaishe ku kyauta๐Ÿ˜_



*To those that i disappointed after I made mention of no disappoinment from the beginning of the book su gafarceni domin girman Allah ba don ni ba, I just found out that everyone is entitled to his or her point of view, snn wasu opinion dinsu kadae suka sani be it on the right track or not, duk yanda nayi I can't please everyone, it's just not possible, kuyi min adalci don ku ma kunsan haka, but ni a tunanina yanda nayi din shine dai dai don ba komai mutum ke nema ya samu ba a rayuwa, and masu tunanin xurfin ciki da miskilanci nature ne su yi eradicating wnn tunanin*



_Alhamdulillah a nan na sauke littafina me taken *Heedayah* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min, darussukan ciki kuma Allah ya sa mu amfana da su, ya sa mu cika da imani, a shekaranjiya na fito da main lessons din littafin Allah kuma yasa ya xama ishara garemu baki daya_ *Na Saudakar da littafin nan xuwa ga lovely sister na Fatima M Bello, Allah ya albarkaci rayuwar ki Lil sis* _My special greetings goes to my lovely Mum Hajiya Hajarah, Allah ya bar mana ke ya daukaka ki ya kare ki Hajiya Yaya, my small momies... I greet you all with respect, and I appreciate ur encouragements from the beginning of *Heedayah* till the very end Jiddoh na godiya, my lovely siblings Ahmad, Maryam, Yahya, fatima, Baby, Haiydar, Ilham, Sudais, Fadil, papi Allah yayi maku albarka baki daya, Lovely cousins, Jamila, Ilham, Mujaheed, Khaleesat, Baby, Haneef... Allah ya raya min ku gaba daya ina sonku sosai sosai_ And My fans๐Ÿ˜ku ne farko ku ne karshe, without you... They won't be Khaleesat Haiydar, I appreciate every atom of ur support toward me, Allah ubangiji ya cika maku burikanku na alkhairi ya raba ku da iyayenku lafiya, ya kara maku budi da daukaka, I really appreciate ur patronage and patient. Duk wanda na 6ata ma daga farkon littafin nan xuwa karshe ko na fada ma maganan dai bai ji dadi ba ya gafarceni, nima na yafe. *And those that read Heedayah for free should keep it in mind that I owe them just 300 naira* ๐Ÿ‘๐Ÿป

Thank you thank you thank you ๐Ÿ’–.... Taku har ko da yaushe Hauwa Bello Jiddah (Kha,leesat Haiydar)


*You can kindly exit the groups if you wish*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login