Showing 258001 words to 261000 words out of 275313 words
Chapter 87 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
sallama, Jin tambayar da aka yi masa a wayar yace "Ehh, who is on the line" shiru Abba yyi as if trying to comprehend the message passed to him kafin ya ajiye wayar bayan an katse yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Shuraim dake ta kallonsa yace "Lafiya Abba?"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Washegari da sassafe Mami da su Heedayah suka gama shiryawa xuwa Nigerian Army Reference Hospital Kaduna, Mami na tsaye parking space da Heedayah Khaleel ya karaso tare da Farida, Mami tace "Ba lallai a barmu mu shiga gaba daya ba, ka dauko makullin motar Junaid kai da Heedayah ku tafi tare, ni kuma i will go with Farida" Yace "Alright" daga haka ya juya ya koma ciki, Mami ta jira har ya dawo da makullin motar snn ta bude tata mota da ke a kunne ta shiga Farida ta shiga front seat, suka bar compound din, Khaleel ya shiga motar Junaid ya kunna yana warming din motar, Heedayah dai na tsaye fuskarta bbu walwala, ko kadan bata ji dadin wucewar da Mami suka yi suka bar ta ba, ya d'an daga kai ya kalleta suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Are you waiting for me to help you in?" K'in cewa komai tayi ta dauke kanta ta turo baki, bata ankara ba sai ji tayi ya dauketa cak, ta xaro ido a tsorace ta rikesa tace "Noo, don Allah ka bari" Bai saurareta ba ya rungumeta jikinsa, ya xaga daya side din motar ya bude front seat ya ajiyeta a hankali yana kallonta, rufe fuskarta tayi da kafarta da sauri xuciyarta na bugawa, yyi murmushi ya rufe motar ya xaga driver seat ya shiga sannan ya ja motar suka bar gidan, har suka isa asibitin bata yrda sun hada ido da shi ba, shi ma bai ce mata komai ba, ya samu wajen parking yyi parking a babban asibitin, sai a snn ya kalleta yace "Uhn wai kunyata kike ji?" Ta saci kallonta suka hada ido, yyi murmushi yace "Ki dinga cin abinci ko xaki d'an kara weight, ur weight isn't encouraging" Hararansa tayi tace "Kai ma ka dinga cin abincin, ae naga baka ci da yawa" Ya wara ido yace "Ae idan na kara cin abinci a kan wanda nake ci ke ce xaki sha wahala" Tace "How?" Ya bude motar ya sauka yana murmushi yace "Xa ki san how" Bude motar tayi ita ma ta sauka, Khaleel ya fiddo wayarsa ya kira Mami, nan ta sanar masa suna Accident and emergency wards, Heedayah na biye da shi suka nufi wajen. Mami na xaune tare da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, ko wannensu yyi tagumi, sai su Rabi'ah da suka ci kuka suka gode Allah, Khaleel ya gaida su Hajiya Amina da ladabi, Heedayah ma ta gaishesu, duk suka amsa, Khaleel yace "Ya mai jiki?" Suka amsa masa da "Alhmdllh" Khaleel ya fita haraban asibitin ya xauna, Heedayah dai na ta tsaye gefen Farida, ko wa na wajen damuwa ne karara tare da shi, Bude kofar ward din aka yi likitoci biyu suka fito, ba a dau lkci ba Shuraim ma ya fito ward din, har xai wuce ganin Mami ya tsaya ya gaisheta, Mami ta amsa, a hankali tace "Ya Mai jikin?" Yace "Alhmdllh" da damuwa tace "Baxa a bari a shiga ba ko?" Shuraim ya gyada mata kai ya bar wajen, Heedayah ta bi sa da kallo, slowly yake tafiyar, bata yi wani tunani ba ta bi sa da sauri, ta isa inda yake cikin sanyin murya tace "Yaya Shureen ya jikin Mumy?" Ya d'an kalleta yana tafiya still yace "Da sauki..." Bin sa tayi har suka fito ya xauna kan Concrete bench, ta xauna gefensa tana kallonsa, she could see how disturb he is, a hankali tace "Ya Shureen is it that serious?" Bai ce mata komai ba, ta dafasa tace "Talk to me" Sai a snn ya kalleta a hankali yace "You pray for her" Tayi shiru tana kallonsa, cikin sanyin murya tace "Will I be allowed to see her?" Ya girgixa mata kai, cikin kwantar da murya tace "Do not be press ya Shureen, this shouldn't oppress you, Allah xai bata lafiya in sha Allah ka ji?" Lkci daya Hawaye ya taru idonta jin ya ki cewa komai, tace "Ka ji ya Shureen" kallonta yyi amma ya kasa ce mata komai, kamo hannunta yyi a hankali yace "Ki taya ta da addu'a ke ma" Ta gyada masa kai, daga haka ya mike, pharmacy din asibitin ya nufa.... Heedayah ta bi sa da kallo, dai dai nan suka yi ido hudu da Khaleel dake xaune shi ma saman concrete bench ta side din da take, mikewa tayi a hankali ta nufesa, yana kallonta yace "Ya jikin mum din tasa?" Ta xauna tace "He said we should pray for her" Khaleel yace "Allah ya sauwake" A hankali tace "Ameen" Kamo hannunta Khaleel yyi, xata kwace ya ki saketa, ta shiga bin wajen da kallo kamar mara gaskiya, murya can kasa yace "What are your plans...." Tace "What plans?" Yace "For ur wedding" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, yana kallonta ta gefen ido yace "Kinyi shiru" A hankali tace "To ai ban sani ba, sai abinda Aunty ta ce" Yace "Ohk, jiya sai kika barni ni kadai a parlor ko...." Tace "Mami ce tace in je in kwanta" Murmushi yyi bai ce komai ba. Sai kusan sha daya suka bar asibitin har sannan kuma ba a bari sun shiga ward din da Mumy take ba, Abba kadai ne ya shiga sai shi Shuraim, duk iya dube duben Heedayah ko xata ga Shuraim bata gansa ba har suka bar asibitin, gaba daya hankalinta ya ki kwanciya, sai da suka kusa gida Khaleel ya kalleta ganin yanayinta yace "ko dai a maida ke asibitin ne?" Ta kallesa kamar xata yi kuka ta gyada masa kai, yace "Ohk" Wani layi ya shiga yyi reverse snn ya dau hanyar asibitin kuma, wajen da xai iya parking ya samu a nan bakin titin asibitin ba tare da ya kalleta ba, tana kallonsa tace "Toh xa ka dawo ka daukeni anjima?" Yace "Ehh" Tace "Toh nagode" Daga haka ta bude motar ta sauka ya dinga kallonta har ta rufe motar snn ya ja motarsa ya bar wajen, ta karasa karamin gate din shiga cikin asibitin ta shiga bayan ta gaida sojojin dake wajen, da kafa ta karasa har Accident and emergency. Shuraim ne kadai xaune saman kujeran dake gaban ward din, ya dinga kallonta har ta iso yace "What did you forget?" Ta xauna wani kujeran tace "Aa kawai ina son in tsaya nan ne" Ya girgixa kai yace "Aa da yamma ai xa ku dawo" Tace "Toh ai kowa ya tafi ya bar ni" Shiru yyi bai ce komai ba, Suna ta xaune a haka bayan wani lkci ta kallesa tace "Ya Shureen is she sleeping?" Ya girgixa kai yace "She is still unconscious" Da damuwa tace "Ta ji ciwo ne?" ya girgixa kai yace "Aa, may be internally" Lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi sosai, a hankali tace "Toh yanxu wani treatment ake yi?" Yace "Still on scanning, kafin a gano inda matsalar yake idan akwai sai a dau mataki, Ana jiran wasu results din" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Allah ya bata lafiya" Shuraim yace "Ameen" Suna ta xaune a haka har kusan sha biyu da wani abu, Heedayah ta kallesa ganin baya daukan phone calls dinsa yace "Why ain't you picking?" Girgixa mata kai kawai yyi ya mike yace "Lkcn sllh yyi, mu je in nuna maki inda xa kiyi sllh" Tashi tayi ta bi bayansa suka nufi kofar fita. Heedayah na idar da sllh ta xauna kan Concrete bench tana jiran fitowarsa daga masallaci, muryarsa taji ta bayanta ta juya da sauri, yana kallonta yace "Me xa ki ci?" Ta girgixa kai tace "Aa am not hungry" yace "Then you need to go back home now" Ta 6ata fuska ta mike tace "Anjima idan su Mami suka xo ba sai in bi su ba tohh" Bai ce mata komai ba ya fara tafiya ta bi sa, Xaune suka tadda Abba da Baffa a bakin ward din, Shuraim ya gaishesu, Heedayah ma ta gaishesu da ladabi, Abban Sudais na kallon Shuraim yace "Ya jikin nata, har yanxu dai shiru?" Shuraim yace "Ehh, duk scans din da suka fito bbu matsala saura uku yanxu ake jira" Baffa yace "Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta" Shuraim yace "Ameen" Shi dai Abba bai iya yace komai ba, Baffa yace "Sun dai ki barin a shiga a ganta" Shuraim yace "Ehh amma in sha Allah idan ta farfado shkkn" Baffa yace "Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta ya bata lafiya" Shuraim yace "Ameen" Sai karfe daya su Baffa suka bar wajen. Karfe biyu da 'yan mintuna Shuraim ya mike daga inda yake xaune ya kalli Heedayah yace "Nace ki tafi gida kin ki tafiya.... And you haven't eaten till now" Tace "Toh ai kai ma baka ci komai ba" Yace "Toh ki tafi gida idan kin ci sai ki kawo min" Kallonsa tayi tace "Da gaske?" Yace "Ehh" Tace "Toh xan iya ganinta kafin in wuce?" Ya d'an yi shiru, kafin ya bi corridor din da kallo, sai kuma yace "Toh taso" Mikewa tayi ta bi bayansa ya bude kofar ward din ya shiga ta bi bayansa, kallon Mumy dake kwance kamar me bacci Heedayah ta dinga yi, ta kasa karasawa gun gadon, Shuraim ya karasa ya duka yana kallonta, ya fi minti daya yana kallonta kafin ya kamo hannunta a hankali, lkci daya ya sake hannun ya kai finger dinsa gefen wuyarta, xame hannunsa yyi ya mike, Heedayah dai na tsaye sai kallonsa take, kofa ya nufa ya fita daga ward din ta bi bayansa, xaunawa ta ga yyi kan kujeran dake wajen ya rike kansa, sosai ta ji gabanta ya fadi ta karasa kusa da shi da sauri, ta xauna tace "What happened Ya Shureen" Jin bai ce komai ba da damuwa sosai tace "Talk to me plss, me ya faru?" A hankali ya dago kansa hawayen dake idonsa ya sauko....
*Ya dai fi babu, wai d'an agwai da bakin d'a, but you pple shud be pitying ur final year Khaleesat* 😩
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Komawa baya Heedayah tayi, lkci daya tsoro ya bayyana fuskarta, cikin tashin hankali tace "Yaya me ya faru tell me plss don Allah ka gaya min" Jin Shuraim ya ki bata amsa ta sakar masa kuka tace "Ka gaya min mana Yaya" Gathering courage yyi ba tare da ya kalleta ba trying to be very strong yace "We just pray for her" Mikewa Heedayah tayi tana dubansa gabanta na faduwa tace "Kamar ya?" Ya mike shi ma still ya ki kallonta ya kama hannunta suka bar wajen. Kaka ce ta bude kofar parlon da mutane ke cike a xaune, cikin mutanen parlon Yan uwan Abba ne na kusa da nesa, sai 'yan uwan Mumy, Mami ma na parlon tare da Hajiya Zuwaira da su Hajiya Amina, duk aka daga kai ana kallon kaka, kaka ta rushe da wani matsanancin kuka ta xauna nan bakin kofa tana nanata "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni Patuu, wai dama da gaske ake?? Da ma wnn mummunan labarin gaskiya ne?" Bbu wanda ya tanka mata a parlon, Kaka ta daura hannu a ka tace "La ila ha illallahu muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, yanxu da gaske Maryam ta rasu?" Ammi ta shigo parlon a sanyaye tare da Mum Islam dake biye da ita, Yakumbo dama a nan balcony ta xauna tana sharban kwalla, Heedayah dai da Farida na xaune kusa da Mami sun yi kukan har sun gaji, Hajiya Zuwaira ta mike ta nufi gun kaka ta dagota cikin sanyin murya tace "Addu'a xa ki yi mata kaka Allah ya gafarta mata" Kaka ta kara rushewa da matsanancin kuka ta rungumeta tace "Wllh matar kirki ce Maryam, duk abinda aka ga tayi bai kai xuciyarta ba xugar shegu ne, kaf shekarunmu da ita bata ta6a tanka ni ba, bata ta6a min rashin kunya ba, duk tsiyata da fitinata shiru take min, kuma anjima baxata fasa xuwa ta min magana ba, ita dai idan ka xauna wajenta cikinka ne xai gaya maka amma wllh ko kallon banxa baxata maka ba balle maganan banxa, kaf surkaina bbu me raga min sai ita, kuma ba dai kaga ta canxa fuska ba don Amadu xai yi maka abu ko xai baka abu, bbu ruwanta da wnn wllh wllh, ita dai kawai girki ne bata son yi balle ta baka ka ci ka koshi, yanxu Maryam ta rasu?? Jiya jiya fa ta sallame mu da yamma wai xata koma wai Amadu yace kar ta kwana, har Yakumbo ke ce mata ta bari gobe yamma yayi ashe ajali ke kiranta, yanxu ya isilin marayun nan da ta bari ni Patuu??" Kuka sosai Kaka ke yi Hajiya Zuwaira na lallashinta, Hajiya Amina hawaye ya kasa tsaya mata haka kishiyarta, ba karamin girgixa su mutuwar yyi ba, daga karshe Hajiya Zuwaira ta fitar da kaka daga parlon. Sosai aka ji rasuwan Mumy, ba 'yan uwa ba, ba makota ba, yawanci kuma duk kyawawan halinta ake fadi, kaka dai ta dage a kan bata ta6a mata rashin kunya ba, ko kallon banxa bata ta6a mata ba, yunwar da ta barta da shi ma ta yafe mata duniya da lahira, har kwana uku kaka bata daina kuka da jimami ba, ana xaxxaune parlor a kwana na ukun, Hajiya Sadiya ta shigo tare da Hajiya Balarabe, Sadiya ta rushe da kuka tana rufe fuskarta da Hijab din jikinta, kaka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonta, Sadiya ta karaso tana goge hawayen idonta ta xauna kasa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ya ji k'an Maryam, Allah ya gafarta mata, Allah ya yafe mata" Kaka na mata wani kallo daga sama har kasa tace "Sai yau kika ji rasuwan kenan?" Sadiya ta ki dago kanta tana matsar kwalla tace "Eh wllh, na yi tafiya naje Sokoto, garin da naje bbu network sai yau na dawo kaduna, ina dawowa aka sanar min wai Allah yyi ma Maryam rasuwa" Tana kai wa nan ta saki kuka da karfi, Kaka ta mike tana rike da carbinta tace "To tashi ki fita, algunguma mayya yar jaraba, Allah ya isa tsakaninmu da ke...." Da sauri Sadiya ta mike har tana neman faduwa ta nufi kofa Balaraba ma ta mike ta bi bayanta da sauri, kaka ta fashe da kuka tace "In sha Allahu karshen ku baxai yi kyau ba, duk ku kuka gurbata tunanin Maryam, mata me kirki bbu ruwanta da mugun abu kai dai idan xaka xo gidanta to ka xo da shirin dinga shiga kitchen ka nema ma kanka abinda xaka ci, amma tsinannun mutane kawai kun nemi hallakata ku ka fara sa ta yawon banxa, to in sha Allahu muna nan muna mata addu'ar Allah ya gafarta mata, ya yafe mata kurakuranta, ku kuma Allah kadai yasan yanda xai yi da ku, duk ku ne sanadin canxa halin Maryam" tuni Hajiya Sadiya da Balaraba suka fita daga parlon, kaka ta koma ta xauna tana matsar kwalla. Da yammacin ranan Khaleel ya xo gidan tare da Junaid, Kaka na parlor da Yakumbo sai Ta rasulu da wasu step sisters din Abba, Kaka ta amsa gaisuwarsu cikin sanyin murya tace "Tun da aka yi rasuwan sai yau ku ka xo min gaisuwa Junaidu?" Shi dai Khaleel bai ce komai ba, Junaid yace "A'a jiya mun maki gaisuwa kaka, kuma ko da safe ma mun xo har mun gaisa ma...." Kaka tace "Toh duk na rude, ai mutuwar maryam ya girgixa ni d'an nan, ga mutane kamar kiyashi, duk ana ta xuwa min gaisuwa gidan nan ba masaka tsinke, har daga Nijar, maiduguri da Taraba an xo min gaisuwa, kaga ai baxan lura da ku ba, to kun ma Amadun gaisuwa kuwa? Shi ma dai duk karfin hali yake, mutuwar mata ai babban tashin hankali ne, shekaransu talatin da tara tare, sai da suka yi aure da shekara shidda marigayiya ta haifi Shuraim d'an ta na fari" Junaid yyi kasa da kansa yace "Allah ya gafarta mata" Kaka ta goge kwallar idonta tace "Ameen dai, Allah ya yafe mata kurakuranta, mu ma kuma Allah ya kyautata namu karshen" Junaid yace "Ameen" Yakumbo dai sai satan kallon Khaleel take tana wuri wuri da 'yan idanuwanta, Junaid yace "Shuraim fa?" Da damuwa Kaka tace "Wa ma ya sani, ni dai nace da ma kukan yyi yanda duk muke yi ko xai ji dadi ya samu salama, rashin kukan ya fi cutarwa, daxu dai ya shigo da d'an uwan, ban san ko ya fita ba" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Allah ya kara hakuri da dangana" Kaka tace "Ameen, Rakiya na can parlon ku shiga ita ma ku kara mata gaisuwa, yau kwananta uku a nan gidan ita ma" Mikewa Junaid yyi ya nufi parlon da Kaka ta nuna masa Khaleel ya mike shi ma ya bi bayansa, Kaka ta bi sa da kallo kasa kasa tace "Yo ba sai ya sa6a xama cikin jama'ah xai sake ba, mutum dai kamar bass din shirin Indiya, ko murmushi bai yi, naga yanda Deedayah xata xauna da shi tunda tace ta ji ta gani, ba ruwanmu" Yakumbo tace "To ba dai ita da uban sun ji sun gani ba, har ynxu fa a dari dari yake da mutane, abin ka da wanda ya saba xaman daji" Mami na xaune parlon tare da su Hajiya Amina da Zuwaira, Heedayah ma na parlon da Farida da su Rabi'ah da su Zainab, Junaid ya xauna nan kasan carpet din parlon ya gaida su Mami, Khaleel ma ya xauna ya gaishesu kansa a kasa, Gaba daya 'yan matan parlon suka gaida su Junaid, Heedayah dai na kwance idonta rufe ta juya ba, Junaid na kallonta yace "Bacci Heedayah take" Mami ta