Showing 201001 words to 204000 words out of 275313 words
Chapter 68 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
dubi Hajiya Amina da ba son Heedayar take ba ita ma can cikinsu ke kuma kin kawo mu gefe don Allah" Mumy tace "Toh bari in je" sosai Mumy tayi gathering courage ta karasa gun da su Heedayah suke tana murmushin karfin hali tace "Ba mu yi hoto ba Heedayah...." da sauri kaka ta juya ta kalleta tace "Meye kuma hoto? Kawarta ta riga ki ma ai, ke Heedayah ki tafi can kawarki na jiran ki kuyi hoto, 'yar wajen Bulasawa ce fa kawar aka ce" Mami dai ta dauke kanta, Gaba daya sai Ammi bata ji dadi ba ta dinga kallon kaka, Yakumbo da ta hakikance kan kujera a wajen tace "To ma hoton me xa suyi ana xaune qlau idan ba gulma ba, mu ma kanmu da kika ganmu nan guda daddaya muka yi da ita, da mai girma Gwamna sai ubanta na kaduna ne kawai suka yi hotuna yayi biyar, ita kanta uwarta ta amana Rahinah sau uku suka yi..." Mumy ta juya sum sum ta bar wajen, Ammi ta hade rai tana kallon Heedayah tace "Follow her immediately and snap" Heedayah ta nufi Mumy me hoton ya bi bayanta, Kaka tayi ma Ammi wani shegen kallo tace "Dole ki xagemu da turanci ai tunda kin samu yar ki da rai, da a mace kika ganta ai baxa kice taje su yi hoto da Rakiya ba" Yakumbo tace "Dalla rabu da ita, makirarra ce ai da kike ganinta, banda makirci mu xata gwale" Ammi dai bata kallesu ba, Yakumbo tace "Toh wai ni banga sirkin nawa ba" Kaka tace "Toh shi Junaidu ai ba ya shiga mata, yana can yana neman na kansa...." Sai kusan Magrib Heedayah suka koma can gidan Mami gaba daya da su Ammi da kaka da Yakumbo, tunda suka dawo bata sakko parlor ba har bayan isha, Mami ta shigo dakin jin shirun yyi yawa ta sameta kwance, ta karasa gadon ta xauna kusa da ita tace "What's wrong Heedayah? You don't look happy today, upon it's a great day for you... ur parent, love ones and well wishers are all here today because of you" Heedayah ta mike xaune bata ce komai ba, Mami tace "Talk to me dear, meye ke damun ki?" Kuka ta fashe ma Mami, Mami ta dinga kallonta da mamaki tace "Meye haka?" Ta rungume Mami cikin rawar murya tace "Mami he told me xai dawo ranan graduation dina kuma ban gansa ba" Mami tayi shiru, bayan kusan second talatin ta dago ta a hankali tace "You mean Khaleel?" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tayi kasa da murya tace "But ae bai san yau graduation din naki ba ma...." Hawaye na sauka idon Heedayah tace "It's a year and 3 months now kuma bai dawo ba, his line isn't going through till today..." Mami ta share mata idonta tace "In sha Allah he is fine dear, kuma xai dawo da yardar Allah, kullum ina addu'an Allah ya karesa da kariyarsa ya dafa masa..." Heedayah ta gyada kai bata dai ce komai ba, Mami tace "Now kiyi sllh ki sakko downstairs, ur mum, step mum, relatives are all here for you, Ko kina son su gane wani abu ne?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mami tace "Good, do as I say now" Heedayah ta sauka gadon a hankali ta wuce bandaki Mami ta bi ta da ido, tun da Khaleel ya tafi yau shekara daya da watanni ita ma rana daddaya ne baya fado mata kuma kullum sai ta sa shi a addu'arta, kuma tana jin tana kewarsa sosai, sai da Heedayah ta fito bandaki Mami ta mike ta fita dakin. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh ta jinginar da kanta jikin gado tayi nisa tunanin da take aka bude kofar dakin, Farida ce ta shigo, ta karaso inda take xaune ta xauna gefen gado tana kallonta, Heedayah ta daga kai ita ma tana kallonta, Farida tayi kasa da murya tace "Congrats Heedayah, Allah ya sanya alkhairi" Heedayah ta sakar mata murmushi tace "Thank you Sis, ya lectures?" Farida tace "Alhmdllh" Shiru duk suka yi, Farida ta mike ta fita dakin Heedayah ta bi ta da ido, bayan fitar Farida Heedayah ta sake lulawa duniyar tunanin da take, hawaye ya sakko idonta ta sa hannu ta goge a hankali ta jawo wayarta ta sake dialing number Khaleel duk da ta san baxai shiga ba, hade kanta tayi da gwiwa bayan ta kira bai shiga ba hawaye na ci gaba da sakko mata, gaba daya shekara dayan nan da watanni bata da wani sukuni bata ta6a tunanin xata yi kewar Khaleel har haka ba, she so misses him, to yaushe xai dawo?? Knocking kofar da aka yi yasa ta dago kai da sauri ta share hawayen idonta, jin an sake knocking ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Junaid ne tsaye, sosai gabanta yayi mugun faduwa don kawai a fixge sai ta gansa kamar Khaleel din a gabanta, lkci daya ta sunkuyar da kanta da sauri, Junaid yayi kasa da murya yace "Congratulations Heedayah, Allah ya sanya alkhairi" Ta dago kanta ta sakar masa da murmushin karfin hali tace "Thanks Yaya" yace "I'm sorry I couldn't make it to ur graduation" Tace "Ba komai, ya aiki?" Yace "Alhmdllh" murmushi ya sakar mata yace "Just to say congratulations" ta gyada masa kai a hankali tace "Nagode" Har ya juya sai kuma ya sake juyowa yana kallonta yace "Are you alright" Cikin sanyin murya tace "Sure...." Yace "Ohk then sai da safe" Daga haka ya juya ya bar wajen ta rufe kofar ta tafi ta kwanta saman gado tana jin wasu hawayen na taruwa idonta. Mumy ce ta bude kofar dakin Shuraim a hankali ganin tun da suka dawo bai fito ba gashi har karfe goma da rabi, xaune ta samesa gefen gado ya rike kansa, ta karasa tace "What's wrong Aliyu?" Bai dago ba kuma bai bata amsa ba, tace "Aliyu" nan ma yyi mata shiru, tace "Wai ba magana nake bane, meye haka Aliyu" Bai dago ba still yace "I am fine" tace "You are fine?" Ya gyada mata kai, tace "Toh me ya hanaka fitowa ka ci abinci?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu??" Still ya ki cewa komai, juyawa tayi ta fita daga dakin, ya dago kansa da idanuwansa da suka sauya kala ya hau saman gadon ya kwanta ya rufa da blanket, bayan fitarta da minti biyu sai ga Abba ya shigo dakin yace "Shuraim" Ya yaye duvet din jikinsa ya mike xaune yace "Na'am" Abba yace "Are you alright?" Yace "I am" Abba yace "Sure?" Kai ya gyada masa, Abba yace "To fito ka ci abinci" yace "I'm not hungry" shiru Abba yyi yana kallonsa, can yace "Meet me at my parlor" Shuraim bai ce komai ba, Abba ya fita dakin, bayan kusan minti biyar ya sauka saman gadon da kyar ya bi bayansa, Mumy na xaune main parlor ta kasa cin abinci gabanta, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai ya nufi parlon Abbansa ta bi sa da ido, Xaune ya tadda Abba a parlon, ya xauna nan kasa, ba tare da ya dago kansa ba cikin sanyi yace "Gani Abba" Abba na kallonsa yace "Tell me, meye damuwar ka?" Shiru yyi bai ce komai ba, Abba yace "Talk to me Shuraim" Lkci daya idonsa ya kada, da mamaki Abba ke kallonsa, can yace "Are you okay?" Shuraim ya kasa dago kansa, sai ga hawaye without him preparing for it, kasa ce masa komai Abba yyi yana kallonsa da mamaki, bayan few minutes Abba yyi karfin halin cewa "Talk to me son, what happened..." Girgixa masa kai kawai Shuraim yyi, sai kuma yace "Xan kwanta Abba, I will be fine" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo, bakin kofa ya tadda Mumy labe bai kalleta ba ya wuce dakinsa yana shiga ya sa makulli ya hau gado ya shige Duvet. Mumy ta shiga parlon Abba da har lkcn was surprise, da damuwa tace "Ya gaya maka Barrister?" Girgixa mata kai kawai Abba yayi, ta fashe da kuka tace "To kuma ka bar sa ya fita, ni ban ta6a ganin yayi haka ba, ko matsala ya samu gun aikin, dama ni tun da ya xo nagansa kamar yana tare da damuwa na dai yi shiru ne, plss Barrister ka koma dakin ka samesa ka lallabasa ya fadi me ke damunsa" Abba dai bai ce mata komai ba ya bude laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you.
Have u ever wondered how desserts are made?
Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from?
Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because
Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught:
*Profit analysis
*Ways to handle desserts
*Dessert marketing.
This class is all you need to start up a profitable side hustle.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos.
Registration is on and the fee is just N3000 Naira.
Class starts on 27th august,2021.
And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕
Contact 08135358038 for ur *dessert* class
follow us on Instagram via *najaatu Yakudima*
Washegari karfe takwas da wani abu Mumy ta isa gidan Baffa, Bangaren Hajiya Amina ta nufa ta sameta tare da Sudais, bayan sun gaisa da Hajiya Amina, Sudais ya gaisheta da ladabi sannan ya mike ya fita parlon, Hajiya Amina ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?" Mumy tayi kasa da murya tace "Wajen Dr na xo, to ban ga motarsa a parking space ba, shine na fara shigowa nan" Hajiya Amina tace "Yana can asibiti bai dawo ba" Mumy tayi tagumi bata ce komai ba, Hajiya Amina ta kara sauke ajiyar xuciya tace "To mu dai sae dai mu ce Allah ya kyauta da yanda abubuwa suka xo kamar wasan kwaikwayo, amma fa ni wlh ba wai kin jinin yarinyar nan Heedayah nayi ba har ga Allah, kawai naga ba a kyauta maki bane, ni kuma baxan iya juya maki baya ba shi sa nima nace baxan riketa ba, banda haka ai yaro na kowa ne wllh" Mumy dai ta ki cewa komai amma ji take kamar ta fashe da kuka a lkcn, Hajiya Amina tace "Kinsan dama Sudais tun tana makauniyar ta ya nuna damuwarsa sosai a kanta, to shine fa yanxu na aika aka kira min shi nake tambayarsa ko yana da interest ne a kanta kada in tauyesa...." Mumy da ta shiga yi mata wani irin kallo da sauri tace "Sai yace maki me?" Hajiya Amina tace "Rabu da shi ni xai raina ma hankali kamar shi ya haifeni, wllh kinji har na rantse yana son yarinyar nan, Wai ni xai kawo ma iskanci... dama can ai ba wai gaba daya na raba sa da ita ba sbda ke ce nace ya daina xuwa gidan wajenta kada xumunci a ya samu matsala tunda baki so" Mumy da duk ba wnn take son ji ba tace "Sai yace maki me ni dai??" Hajiya Amina ta tabe baki tana gyara xama tace "Ai karya yake bai fada min gaskiya ba, wai cewa yyi shi ba son aurenta yake ba, kawai dai ya dauketa tamkar kanwarsa ce sbda maraicinta a lkcn, amma bbu wani soyayya na aure da yake mata, wai fa ni xai raina ma hankali, to baya sonta xai dinga kashe mata uban kudade yanda ya dinga yi a lkcn, ni dai nace masa kar fa ya ji komai tuni na janye bakin da nayi a kan taraiyarsa da ita, idan ma aurenta xai yi ni baxan hanasa ba sai in fada ma Barrister a san abun yi, amma yaron nan ya dage shi ba sonta yake da aure ba yana da warce xai aura...." Mumy dake ta yi mata wani kallo ta katse ta tace "Amma Wlh Amina baki da kunya, ynxu don kin ga ubanta Gwamna ne shine kike nema d'an ki ya aureta?? Kike makala masa ta karfi da yaji? Wnn kwadayi har ina Amina" Hajiya Amina ta mike tace "Ehh na nema din, kuma kwadayi ai a gun danginki nayi gado, duk ba ke kika ja mana ba da muguwar xuciyarki da bakin halin ki, gwara ni nawa bai wani fito sarari ba, ai yau ga irinta nan kashi ma ya fi ki daraja a gun iyayen yarinyar, dubi yanda aka walakanta ki jiya gaban jama'ah kika yi tsamo tsamo da ke ba kyan gani, muna nan da ke in sha Allah sai na lallaba Sudais ya nemi auren nata tunda dama sonta yake nice na rabasa da ita ta karfi da yaji sbda sharrin shaidan, kuma naga yarinya ma a lkcn ai tana son sa...." Mumy tayi wani dariya ta mike tana mata wani irin kallo tace "Sai dai ki mutu ki ru6e amma wllh wllh Sudais baxai auri Heedayah ba, me kika ta6a tsinana mata daga ke har Dakta din? Gwara ni mijina shi yyi mata komai na rayuwa, Allah ne gatanta shine gatanta, shine tsaye kan komai nata, idan ma yau d'an Barrister yace xai auri Heedayah ya cancanci a bashi, to shi kuma Sudais a wa?? Idan ma auren ne Shuraim ya dace ta aura" Mumy bata jira cewarta ba ta nufi kofa da sauri tana cewa "Ni dama ba wajen ki na xo ba, ganin motar Dakta baya gidan ya sa na shigo wajen ki ashe da rabon inji kayan takaici, kwadayayyiya kawai" Bangaren Kaka ta shiga, ta sameta xaune da Hajiya Hauwa dake gyara mata kayanta a akwati, kallo daya kaka tayi ma Mumy ta ci gaba da bada labarin da take, Mumy ta xauna cike da ladabi tace "Ina kwana kaka?" Ba tare da kaka ta kalleta ba tace "Lafiya lau" Mumy ta gaisa da Hajiya Hauwa, Hajiya Hauwa ta tambayeta ya yaran, tace "Alhmdllh" Mumy na kallon kayan da ake xuba ma kaka a akwati tace "Tafiya xa kiyi kaka?" Kaka tace "Ehh Gwamnet house xa ni a kano, yanxu ai mune gwamnati tunda xuciyar mu da kyau bama nufin d'an kowa da sharri" Mumy dai bata ce komai ba ta hadiye wani abu da kyar, Hajiya Hauwa ta mike tace "Toh bari in dauko maki turaren kaka" Kaka tace "Yi maxa, duk da idan naje can baxan rasa ba amma kar inje masu tsiya tsiya ko?" Murmushi kawai Hajiya Hauwa tayi ta fita, Kaka ta kalli Mumy tace "Ai Aminar na can bangarenta baki duba bane...." A hankali Mumy tace "Aa wajen ki na xo" Kaka tace "Wajena kuma?? Ikon Allah, to ina jin ki, kinga shirye shirye nake kar lkci ya baci a banxa a hofi, a jirgin Uban Deedayah xa a tafi da mu wai jirgin baya jira inji Kumbo" Mumy tace "Allah sarki, to Allah ya kai ku lafiya Kaka" Kaka tace "Ameen, Ina sauraron ki" Mumy ta d'an yi shiru, kaka ta mike tace "Ni dai fa wanka xan shiga Maryam, baxan 6ata ma manyan mutane lkci ba" Mumy tace "Dama kaka a kan Shuraim ne" Kaka ta koma ta xauna tace "Waye kuma Shureen?" Mumy tayi shiru, kaka tace "Nace waye Shureen" Mumy tace "Shuraim dai daya, jiya ya dawo mun rasa gane kansa wllh, nayi nayi ya ki gaya min meye damuwar ya ki, shi ma Barrister ya samesa har daki ya ki gaya masa, yau ina ta xuba ido ko sallan Asuba bai fito ba, kuma kofar tasa a rufe yake yaki budewa" Kaka da ta saki baki tana kallon Mumy tace "Toh ko yayi masu bakin halin ne suka koresa gun aikin" Mumy dai bata ce komai ba, kaka tayi kasa da murya tace "Allah kuwa xai iya yiwuwa haka ne, me hali ai baya fasa halinsa, to amma ko koransa suka yi ga dai Uban Deedayah yana sa baki xa a mayar da shi, ai gwamna ne shi" Mumy dai tayi shiru, kaka ta rike kanta a hankali tace "Oh oh Allah, Ni wllh lamarin Shureen na damuna sosai... mutum magidanci gandarere haka amma har yanxu daga ke har Amadu kun xuba masa ido bbu me ce masa Ina matar aurensa, bbu me ce masa komai fa, to ko dai miskilancin nasa xai aura ne bani da labari? ga dai Sudais wllh jiya ya kawo min yarinyar da xai aura xankaleliya da ita, ga ta dai ba yar kowa ba yar talakawa ina jin a tudun wada ma take da iyayenta, to ai da kyau ya fi babu, yarinyar sai kyau da hankali da nutsuwa ga kunya to ai hakan da kyau, bai ma yarda ya kai ta gun kwadayayyiyar uwarsa ba, shi kuma Junaidu Uban Deedayah yace ya basa Deedayah duniya da lahira daga ni sai shi sai uwar Deedayah muka san wnn xancen, sirri ne bbu wanda ya sani, ko Rakiya bata sani ba wllh, nan Junaidu ya xo ya fada min damuwarsa na son Deedayah ni ko na ja sa har gidan uban Deedayah a Abuja, ashe wata fitinanniyar tsohuwa da na ta6a haduwa da a kasuwa da dadewa tana bala'i da jama'a kamar karya yayar uban Deedayar ce, gaskiya na girgixa ainun har buhun tafarnuwar na mata alkawari a lkcn Allah bai yi xan bata ba, to in gaya maki har ita tayi Na'am da Junaidu tunda uwarsa ce ta rike Deedayah da amana bbu ha'inci, kuma tace Deedayah na gama sakandari bbu ruwanta da wani Jami'a xa ayi aurenta da Junaidu, to yanxu sai naje xa mu fara shirin bikin ma, daga nan kuma sai a kira kowa a