Showing 237001 words to 240000 words out of 275313 words
Chapter 80 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
lay ur sisters to bed nasan suna can suna wahalar da Nannynsu" shiru Heedayah tayi tana kallonta, Ammi ta mike tace "Sai ki ajiye masa drink da abinci" Daga haka ta fita parlon ta tafi bangaren da girls dinta suke, lkci daya hawaye ya kawo idon Heedayah, ta fi minti shidda a xaune kafin ta mike tsaye a hankali ta koma dakinta ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta dau hijab dinta har kasa ta saka tayi sllh, bayan ta idar ta fita xuwa can main parlor, bbu kowa parlon sai kamshi dake tashi ga sanyin Ac da ya cika parlon, tun kafin ta karaso cikin parlon take kallonsa, yana xaune saman kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran idonsa a rufe, har ta karaso cikin parlon bai sani ba, ta nemi kujera ta xauna fuskarta bbu walwala... Bayan kusan minti uku ta mike ta tafi xuwa kitchen, masu aiki uku ta samu a kitchen din ko wannensu da apron, da ladabi Amina tace "Kina da bukatan wani abun ne Hajiya?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa, Abinci xa a xuba ma bako in kai masa" Amina ta dau tray ta ajiye snn ta xuba shinkafa a plate, ta sa miya da enough cow meat a bowl, ta debi pepper chicken a wani bowl duk ta daura kan tray din, da Tamarind drink da bottle water sae lemon kwali, Amina tace "Ina xa a kai abincin?" Karban tray din Heedayah tayi ta fita, a hankali take tafiya har ta iso babban parlon, har sannan idonsa a rufe yake ta karasa kusa da shi ta durkusa ta ajiye tray din tana kallonsa, lkci daya ya bude ido, ta d'an koma baya ba tare da ta yarda sun hada ido ba, ya xauna da kyau yana kallonta, kallonsa tayi ita ma tace "Ina yini" yace "Lafiya" tace "Ammi tace a kawo maka abinci" ya kalli abincin yace "I'm full, thank you" Bata ce komai ba, yace "Yaushe kika xo?" Tace "Daxu" Yace "Tare da su Ammi?" Ta gyada masa kai, yace "Ya ku ka baro su Mami?" Tace "Lafiya lau" Komawa tayi kan kujera ta xauna, Yace "Can you help with a cup of tea" Tace "Ohk" daga haka ta mike ta yi hanyar kitchen ya bi ta da ido, bayan few minutes sai ga ta ta dawo da cup din tea, durkusawa tayi ta ajiye masa a kasa kusa da shi snn ta koma saman kujera ta xauna, Ammi ce ta shigo parlon da sallama, ta xauna tana kallonsa tace "Ya aikin Shuraim" Ya gaisheta da ladabi yace "Alhmdllh" tace "How are you feeling now?" Yace "Alhmdllh naji sauki" Ammi tace "Toh Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen" Tace "Ka shiga ka gaida su kaka kuwa?" Yace "Aa yanxu xan shiga" Ammi tace "To ka shiga ka gaishesu idan ka ci abincin, 3 days ago ma tace baka shiga ka gaishesu ba" Murmushi kawai yyi, Ammi ta mike tana kallon Heedayah da ta tsura ma TV ido tace "Tambayi Amina ko ta bada an kai masu Lipton Hajiyata" Daga haka Ammi ta bar parlon, Shuraim ya kalli Heedayah, tashi tayi xata wuce kitchen, yace "Did you rinse the cup before making the tea??" ta d'an kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "No I didn't" daga haka tayi wucewarta kitchen dawowa parlon Heedayah tayi bayan Amina ta sanar mata ta kai masu, tana tsaye tace "A ina su Kaka suke?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Xuwa xa ki yi?" Tace "Ehh" ya mike ya fara tafiya, bin bayansa tayi suka haura sama, wani kofa ya bude suka shiga wani parlor Kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya ta gama cin pepper chicken da aka kawo masu, Yakumbo kuma na kishingide gefe tana sakace hokara, Shuraim ya xauna yana kallonsu ya gaishesu, da damuwa Yakumbo tace "Ya ka kara ji da jikin?" Yace "Naji sauki" Kaka na kallonsa tace "Kaji wai Umaru bai san ka dawo kano da aiki ba, me yasa baka gaya masa ba muna xaman xamanmu ka janyo mana matsala a xumunci, wan ubanka ai ubanka ne" Shuraim dai bai ce mata komai ba, Heedayah ta xauna kasan lallausan carpet dake shimfide parlon tace "Sannun ku" Yakumbo tace "Kun gaisa da baban naki ko bai shigo ba" Heedayah tace "Bai shigo ba" Tana fadin haka ta mike tace "Dama na xo ne in gaisheku" daga haka ta nufi kofa, Kaka ta bi ta da kallo tace "Naga ikon Allah ni Patuu, kamar dai warce Rakiya tayi ma wani mugun abu, ba fa ta son xaman gidan uban nata kwata kwata" Yakumbo tace "Ashe dai kin gano, tun barowar mu Kaduna take cika take batsewa, ai na fi ta iskanci ita da komawa Kadunan nan wllh sai dai idan sallaman ubanta na can taje yi da uwar rikon nata" Kaka tace "Sallaman aure?" Yakumbo tace "Da fa? Ai wnn yarinyar naga kamar idonta a bude yake, ko shekaranjiya sai da nayi ma uban magana a aurar da ita kawai babu ruwana, kuma kinsan komai na fada ya xauna" Kaka tace "Toh ke kenan da ba haifansa ma kika yi ba, ni kuwa wnda na haifan ma nayi nayi da shi yyi ma d'ansa magana ya fiddo mata ayi masa aure yaki, gwara Sudais har an kai gaisuwa" Yakumbo tace "Atoh sai ki bar su kawai ai kin fita hakkinsu" Kaka tace "Toh Alhmdllh sai dai na tuna na ta6a nema masa aure da dadewa, can xan lallaba kawai in koma, amma ita Deedayar ina mijin da kike cewa xa ayi mata aure??" Sake baki Yakumbo tayi tana kallonta tace "Atoh lalacewa ta sameki kuma, ba ke kika kawo mana Junaidu d'an gidan Rahinah ba dama?" Kaka tace "Auhoo, ca nake watsa mun kasa xa kuyi a ido ku kunyata ni a idon yaron" Yakumbo tace "Aa ni ai na ya6a da halin Junaidu yaro me nutsuwa da hankali ga ladabi wllh, amma tsorona kawai yayan nan nasa da ya bayyana kwanan nan, banda haka ai xuri'ar nan tasu tayi wllh, barin uwar nan tasa" Shuraim dai kallonsu kawai yake, Kaka tace "Aa ba ruwanmu da wani yayansa har yanxu ni ban gama yrda d'an Rakiya bane wllh, kila dai wata dubara da hikima ce yin hakan sbda wani aiki da take, kilan akwai wani kess da take kai kuma dole sai ta billo ta haka" Yakumbo tace "Atohh, Allah dai ya sa haka, amma ai ba lafiya in dai gaskiya ne, shi ma Junaidun ai da shekaranjiya xa su kawo gaisuwar to wan ubansa ya kira wai a d'an basu kankanin lkci ko xuwa nan da sati biyu ne" Kaka tace "Toh Allah ya kai mu" mikewa Shuraim yyi yace "Sai da safen ku" Kaka tace "Toh Allah ya kai mu" Kofa ya nufa ya bude, da sauri Heedayah dake makale jikin kofar ta bar wajen ya bi ta da kallo yace "Wait" dai dai stairs ta tsaya ta ki yrda su hada ido tana turo baki ya nufeta, Kaka na kallon Yakumbo murya can kasa tace "Dama na ta6a nema masa auren Farida, yanxu gobe xan sa a kira min kawun faridan kawai inji inda aka kwana" Yakumbo tace "Toh ko dai da warce yake so ne, naga ransa bai masa dadi ba maganganun nan da kike yi" Kaka tace "Toh ba shi ya jiyo ba ni ina ruwana" Yakumbo tace "Aa yaron na da hankali ga rashin son magana balle hayaniya, gobe idan Allah ya kawosa xan ja sa parlona in tambayesa ko yana da warce yake so ne ya sanar min" Kaka tace "Tab 6ata lkci kawai, ba sai idan yana kula yan matan ba xai samu warce yake so" Yakumbo tace "Wllh yana tare da damuwa ni dai na lura" Kaka tace "Shi dai Amadu kullum tausayin irin d'an da Allah ya basa nake yi masa wlh, muna nan dake xaki ga wataran jikana Sudess xai xo, yaro wayayye d'an boko me faram faram da jama'a ba dunkum ba" Yakumbo tace "Toh ai halitta ce Patuu, wani haka Allah ya haliccesa wllh, baki ga irin dagewar da Amadi yyi da shi ba kafin ya dinga xuwa mana nan tun ma bai dawo kanon gaba daya ba, yanxu haka har kwana Amadi yace ya dinga yi a nan amma baya yrda ya kwana yana xuwa xai yi wucewarsa, wllh da ina da 'ya mace da na basa aurenta ni dai" Kaka tace "Ki raba kanki bakin hali ke garesa wllh, Shureen abun tsoro ne bar ganin kamar mutum" Yakumbo ta tabe baki tace "Ke kika ga haka ni ban gani ba" tana fadin haka ta mike ta shige daki, Heedayah na tsaye har Shuraim ya isa inda take ya tsaya yana kallonta.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Heedayah ta ki yarda su hada ido, yana kallonta yace "Why were you eavesdropping?" Kin cewa komai tayi, bayan few seconds ta d'an daga kai suka hada ido da shi, ji tayi gabanta ya fadi ta fara kame kame, da sauri ta juya xata bar wajen taji ya riko wrist dinta, ta kalli hannunsa, 6ata fuska tayi taki bari su kara hada ido tace "Ni bana so ya Shureen, I wasn't eavesdropping, zobe na ne ya fadi nake dubawa kuma ban gani ba a wajen" Lkci daya tayi shiru, can tace "Toh ka sake ni" Yace "In contrast to that?" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai ka sake ni" Dago kanta yyi yana kallon tun daga lips dinta har xuwa eye balls dinta, suna hada ido, ta rufe bakinta da hijab dinta da sauri tuna wani abun da tayi, gabanta ya shiga faduwa, saketa yyi a hankali yace "Kin dai makale kina sauraron ranan da xa a kawo gaisuwar ki ko?" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "To nan da sati biyu ne" Turo baki tayi tace "Gaisuwana da wa?" Yace "Ahmad Junaid" Ta 6ata fuska tace "To ni nace ina son sa da aure ne, bayan shi yayana ne, ta ya xa ace xa mu yi aure???" Yace "Ta yanda ake yi" hawaye ya kawo idonta tace "Ni dai baxan iya ba, ta ya xa ace haka" Yace "Toh kina da wanda kike so ne?" Tace "Ehh" Yace "Waye shi?" A takaice tace "Khaleel..." murmushi yyi yana kallonta yace "Sai ki gaya masu" Ta share idonta a hankali tace "Ni baxan iya ba" Yace "Why?" Tayi shiru, yace "Idan ma kin iya fada masu Allah ya sa su bar ki da shi" Tana kallonsa da sauri tace "Me yasa baxa su bar ni da shi ba??" Yace "Aa ban sani ba, ae xa ma su bar ku" Shiru tayi bata ce komai ba, ya fara tafiya ta bi bayansa har suka dawo parlor, juyawa yyi yana kallonta yace "You rinse another cup and make me a cup of tea" Ta kalli shayin da suka bari a parlon tace "How will I use a cup without rinsing it at first?" Ya xauna yana kara kallon shayin yace "Rinsed or not.... We left it open" Ta hade girar sama da ta kasa, shi dai idonsa na kan tv dake aiki a parlon, ta karaso ta durkusa ta dau shayin ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye masa wani shayin, dauka yyi yace "Did you come over to kano with ur laptop?" Tace "Eh" yace "Let me see" shiru tayi tana kallonsa, can tace "Ina son tambayar ka ya Shureen" Ya daga kai ya kalleta yace "Ok... but before then, what's Shureen?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Don't call me that again" Ta d'an ta6e baki don ba kallonta yake ba, can tace "Me yasa lkcn da nake gidanku baka min magana, baka kulani sai yanxu? This is really weird" Yyi shiru yana kallonta directly in the eyes, can ya d'an yi murmushi yace "Apart from you... kin ga ina kula kannina ko wani a gidan? And if I am not mistaken kin ta6a min wnn tambayar kwanaki ae" Ta buda masa hannu alamar bata san ko yana kula kannin nasa ba snn tace "I am asking you again because ina mamaki ne har ynxu, I never knew u can talk for 3 mins without stopping, why ur sudden change toward me??" Kallon cup din hannunsa ya dinga yi kafin yace "Baki ta6a xuwa kin tareni ko kin xo inda nake kin min magana naki kulaki ba, ko an ta6a haka duk period din da kika yi gidanmu?" K'in cewa komai tayi, ya ajiye cup din hannunsa yace "Look Heedayah, babu abinda xaman ki a gidanmu ya rageni da for good 5 years da kika yi tare da mu, tun kafin Abba ya kawo ki responsibilities dina ya fita kansa I was independent then, rayuwa kawai nake yi a gidan, balle ace ko haushin wani abinda xa ayi maki nake, kinga ynda nake da kannina har yanxu, Even my Grandmum I don't spend much time with her, So why didn't u complain about them too..." Heedayah ta girgixa kai kawai, yace "Ohk let me let you know this, At first I was confused xuwan ki gidanmu, coz then my family was a happy one, all of a sudden xuwan ki abubuwa suka fara faruwa marasa dadi, and I can't just disappoint my Mum a lkcn, I don't want to double her disappoinment, nasan kina bukatan taimako sosai at then I even advice Abba ya bar ki gidan Marayu and I will take every responsibility naki a can, snn I promise duk weekend xan dinga xuwa duba ki, shi ma idan yana da lkci sai ya je, but he was reluctant, ni kuma na kawo idea din ne ganin Mumy baxata ta6a rike ki ba no matter, a ranan da kika dawo gidanmu da Mami da daddare mum dita ta kirani daki..." Shiru yyi, Heedayah dai sai kallonsa take, can ya girgixa kai yace "I don't want to say anything about that, you can't make me say anything about that, but just know that there is no one to console her, and I have no choice then to follow her instructions ko xata samu sauki ta wani bangaren, because of you or Mami baxan iya bata ma mahaifiyata ba tunda dai abinda tace inyi ba abinda xai cuceni ko ya cuce wanin ku bane, shi yasa ko karatu naki koya maki idan kin tuna...." Heedayah dai kawai murmushi tayi, Yace "Get this, I am not telling you all this for you to change ur silly thinking toward me, stick to ur thinking" Heedayah tace "Toh ka ci gaba ina ji" yace "Ohk... Duk da bana maki magana bana shiga harkan ki a gidan mu, ni nasan irin taimakon da na maki wanda ke baki sani ba kuma baxa ki ta6a sani ba, just know that i kept an eye keenly on you, ban bada room for anyone to get you harmed ba duk da ko kowa yasan bna sake maki a gidan, kuma sake maki da bana yi yasa bbu wanda xai kawo xanyi abubuwan da na dinga maki most especially my mum, I missed a lot of opportunities don kada inyi nisa da ke ki cutu, har kika bar gidanmu you weren't safe, barin ki gidanmu ya bani courage din tafiya soldier da ban tafi ba bayan na sake samu for the 3rd time, ko da ace ni din me magana ne rashin maki magana a lkcn shine mafi alkhairi Heedayah, balle ma ni bani da lkcn magana, a ta dalilinki Mahaifiyata ta jefa kanta ga halaka wanda har gobe nake fatan Allah ya ganar da ita, but ban ji haushin ki ba duk da ta dalilin ki hakan ya faru, ni dai kawai I made sure I protect you by all means" Heedayah tace "Wai Protect me from what?" Yace "Bana tunanin gaya maki xai maki wani amfani, Back to what I was saying.... Duk da biyayyar da nake ma mahaifiyata sai da na tsallake umarninta na bi ku har New Delhi na duba lafiyar ki, kuma da kike cewa ashe ina maganar minti uku without stopping, go ask Zainab, I talk when I am comfortable doing so, kuma da ita kadai nake magana haka sae ko colleagues dina, ko kannina baki ga ina masu haka ba, it's a
nature I know I can't eradicate, coz I've tried my best doing so but no result, Kar fa kiyi tunanin don ki canxa ra'ayinki a kaina nake gaya maki abubuwan nan..." Yana fadin haka ya mike ya dau laptop din yace "Idan na shigo gobe, will bring u back ur laptop, idan kuma ban xo ba sai Thursday, good night" Bin sa da kallo tayi ganin ya nufi kofa tace "Toh shayin fa?" Juyowa yyi ya kalli shayin yace "Oh, thank you" daga haka ya fice ya kulle kofar, tafi minti biyar xaune tana naxari kafin ta mike ta karasa kujeran da ya tashi ta dau shayin ta xauna ta fara sha. Heedayah na gama shirin kwanciya Ammi ta shigo dakinta tana kallonta tace "Ki xo ku gaisa da Abbanki" Daga haka Ammi ta juya ta fita, Heedayah ta dau hijab dinta har kasa ta saka snn ta bi bayanta har xuwa babban parlon Abbanta, Yana xaune ta shigo parlon ta durkusa kasa gefensa ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "Kun xo lafiya Heedayah?" Tace "Alhmdllh, Ya aiki Abba" Yace "Mun gode Allah, ya kika baro iyayenki na can" Tace "Duk suna lafiya, suna gaisheku" Yace "Toh maa sha Allah, hope babu wani matsala baki bukatar komai" Tace "Abba ina son in canja waya, ban xo da nawa ba" Yace "Toh xa a kawo maki gobe idan Allah ya kai mu" Tace "Toh nagode Abba" Yace "Allah yayi maki albarka" Tana murmushi tace "Ameen, kuma Abba wani makarantar xan yi ynxu?" Yace "Aa wnn we are not to decide, iyayenki na can xa su yi deciding ko?" Ta gyada masa kai tace "Toh Abba" Yace "Sai ki tambayi