Showing 162001 words to 165000 words out of 275313 words

Chapter 55 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

rasa" Fita tayi daga parlon Farida da duk jikinta yyi sanyi ta bi bayanta tana tunanin anya mutumin nan ba guduwa yyi da Heedayah ba kuwa, Banda haka ai duk abun Heedayah tasan baxata yarda ta bi sa da daddaren nan ba, tunanin hakan yasa xuciyarta ya tsinke taji tsoro ya kamata sosai, Maman Fadil ta tafi gun mai gadi tace "Mukhtar ka ga fitar bakuwata da daren nan kuwa?" Yace "Ehh nine ma na bude mata gate" a mugun fusace Maman Fadil tace "Don me xaka bude mata gate da daddaren nan ba tare da izini ba" Yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Hajiya naga ba yarinya bace shi yasa na bude wllh, na xata ko tadi xata fita" Maman Fadil ta bude baki with much surprise, can tace "Toh da ta fita ina kaga tayi?" Yace "Toh da ta fita naga dai kamar bata ji dadin kallon da nake mata ba, sai naga tayi can, nan kuma so nayi inga inda xata ne, Amma dai da wata mota da naga anyi parking a kofar gidan Honorable, ni dai sai na koma ciki na xauna sai da wnn bawan Allah ya xo na sake bude gate din to ko da na leka waje gaskiya ban ga motar ba kuma, ita ma ban ganta ba" Maman Fadil tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, haka dama Hadiyar take Farida, ki shiga motar saurayi a garin da ba naku ba ki bishi kuyi tafiyar ku?? Yanxu me xan ce ma Mami" Farida dai ta kasa cewa komai gaba ta tsorata ne sosai, Maman Fadil ta juya ta nufi hanyar shiga parlor tana cewa "Toh kuwa bari in kira Mami bbu wanda xai ja min matsala gaskiya" da sauri Farida ta bi bayanta tace "Noo plss don Allah aunty kar ki kirata, Mami won't take it likely with her, mu jira sanda xata dawo sai kiyi mata fada ke, don Allah Aunty kar ki kira Mami" Maman Fadil tace "Ya xa ki ce kar in kirata, wnn ai ba abinda ya kamata a boye bane, ya kamata a sanar ma Mami, gaba daya nawa take? Ta wuce 17 wnn da ganinta, amma ita har tayi wayon bin saurayi da daddare ba ma da rana ba, kai ko da rana ne hukunci me tsauri ya kamata ayi mata balle da daddare, samarin Abujan nan masu lalata yan mata, a gidan ubanwa ta san sa ma, snn kince Mami ma bata san da waya hannunta ba, ni bbu wanda xai xo ya ja min matsala daga ke har ita wllh" Farida dai ta ma rasa bakin magana, Maman Fadil ta xauna parlor sai dai bata kira Mamin ba, hankalin Farida ya d'an kwanta sai kallon agogo take tana addu'a, tana fatan Allah ya sa Heedayah ta dawo anytime from now, yanda duk ta tsorata sai kace ita tayi laifin ma. A wani tsadadden wajen shan ice cream Khaleel yyi parking yana kallon Heedayah da idonta ke saman titi ko kiftawa bata yi, yace "Kina shan ice cream?" sai a snn ta juya ta kallesa ta kalli gun siyar da ice cream din, tace masa "Uhn" yace "To mu je ki xabi flavor da kike so" a hankali tace "Aa ni baxan fita ba" yace "Me yasa?" Ta langwabar da kanta tace "Ba komai, kawai bana son in fita" yace "Ohk then, let me get you" bata ce komai ba ya dau face cap dinsa ya kafa a kansa, baka ganin komai sai dogon hancinsa da karamin bakinsa, ya bude motar ya sauka ya kulle, ta bi sa da kallo har ya shiga babban Ice cream parlor din, bayan wasu mintuna ya dawo rike da leda me dauke da packaged ice cream har uku ya bude motar ya shiga snn ya kulle ya mika mata ledan, amsa tayi ya tada motar suka bar wajen, ya kalleta ganin ta ajiye ledan a gefenta yace "Toh ki sha" tace "Ni kadai?" Yace "Yess" tace "Ai baxan iya shan duka ba" yace "Toh sha wanda xa ki sha" ba musu ta bude ledan ta dau vanilla flavor ta bude ta fara sha, a nutse yake driving din, just roaming round FCT, sai bin manyan wurare take da kallo, you can't say if she is happy or not, ita dai ga ta nan, suna isa wani joint na shawarma yace "Do you take shawarma?" Ta girgixa masa kai alamar Aa, yace "Why?" Tace "Na koshi" yace "Toh tsire fa?" Ta girgixa masa kai nan ma, bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da driving slowly, kallon agogo dake nuna karfe tara saura minti sha biyar yyi yace "Are you sure baki son komai?" Ta gyada masa kai, tafiyar kusan minti sha biyar suka kara ganin inda suka nufa ta kallesa da sauri tace "Ina xaka kai ni?" Yace "Home, its late kar a neme ki, nasan yanxu ai so called yayan naku ya wuce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da driving, girgixa kai tayi a hankali tace "Ni baxan je gidan ba" Da mamaki ya juya ya kalleta, yace "Baxa ki je gidan ba kuma?" Ta gyada masa kai, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai kawai baxan je ba" Yace "Did you have any other guardians in Abuja" Ta kallesa tayi shiru, sai kuma tace "Ban san kowa ba" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tukin, Kuka sosai Heedayah ta fashe masa ganin sun kusa layin, hakan ya basa mamaki sosai ya samu gefe ya tsaya yace "Are you alright Heedayah?" Cikin kuka tace "Plss kar ka mayar da ni don Allah" kasa ce mata komai yyi yana kallonta, can yace "Me suka maki da baxa kije gidan ba" Tana share hawayen dake xuba idonta tace "Ni dai ban so, don Allah kar ka mayar da ni" He was lost of words don sai kallonta yake, ganin yanda take kuka yace "Talk to me Heedayah, sun maki wani abu a gidan ne?" Ta hade kanta da gwiwa tace "Ni basu min komai ba, bana son in je kawai" ya jingina da seat dinsa yace "To ina xan kai ki yanxu?" Cikin rawar murya tace "Ka tafi da ni kawai" yace "In tafi da ke ina?" A hankali tace "Inda xaka je" Jin shirun yyi yawa ya sa ta dago tana goge hawayen idonta, kallonta taga yake yi, ya kamo hannunta a hankali yace "Noo Heedayah, you need to go back home, xa su yi ta nemanki...." Ta fixge hannunta tana masa wani kallo tace "Ni baxan je ba nace maka, kuma ka ajiye ni a nan kawai inyi wucewa na" Da mamaki yace "Ki tafi ina?" Kokarin bude motar ta fara yi tace "Ni ka bude min" ya jawota yace "But Heedayah, what just came over you, Ina kike son in kai ki da daddaren nan, kince min baki san kowa ba a garin nan banda gidan warce ku ka xo, to ina kike son in kai ki kuma" Kuka kawai take masa xata kwace hannunta, ya jawota kusa da shi yace "Ki gaya min me aka maki a can gida" turasa tayi tace "Nothing I said, ni ka bude min in sauka" Khaleel couldn't stop looking at her, ganin ya ki bude mata motar ta hade kai da gwiwa. Har karfe goma saura Farida da Yayarta suna xaune parlor sun yi jigum, Farida ta san kiris ya rage yayarta ta kira Mami don ta cika daga xaunen da take, Farida ta dau wayarta duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, bude ido tayi tunawa da tayi ai ta ba Heedayah wayarta suna tahowa a mota daxu tayi ma Khaleel din message, shiga message tayi da sauri tana dubawa taga bbu message din sabon number, alamar Heedayah ta goge text din gaba daya, Number Shuraim ta duba duk da bata yi saving ba amma ita ma ta so haddacesa tunda bashi da wahala, tayi dialing number har ya katse bai dauka ba, ta sake kiransa, nan ma bai dauka ba, sai gashi ya kira, dagawa tayi ta kai kunne, da farko ta rasa abinda xata ce sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, shiru tayi, yace "Wacece?" Mikewa tayi ta mika ma Maman Fadil wayar tace "Don Allah aunty kiyi masa magana ni ban san me xan ce ba" Maman Fadil ta jefa mata wani kallo tace "Waye?" Farida tace "Ya Shuraim" amsar wayar tayi ta kai kunne hade da yi masa sallama, bbu bata lkci tayi masa bayanin komai cikin few minutes, shirun da taji yasa tace "Hello" Shuraim yace "Ina ji, and she is not yet back har yanxu?" Maman Fadil tace "Wllh kuwa, ni tunda nake ban ta6a ganin haka ba ma, har nawa take xata yi wannan aika aikan, Ina ta bi sa suka tafi, ni gashi ko abinci na kasa ci har yanxu, ta ina xan fara yi ma Mami bayani, me ma xan ce mata??" Shuraim gaba daya ya rasa abinda xai ce, don basu kai sa mamaki ba ma, can yace "Ba wa Farida wayar" Mika ma Farida wayar tayi, Farida ta amsa ta kai kunne, Yace "All this while dama akwai waya a hannunta" Farida ta koma ta xauna ta rasa abun cewa, yace "Baki ji na ne?" Tace "Nima ban sani ba...." a fusace Maman Fadil tace "Munafuka kika ce baki sani b, wllh tana sane ita ma munafukar ce ai, kuma kema ta ja maki matsala tunda kike boye abinda take yi" Shuraim yace "Waye shi Mutumin??" Farida tace "Ni fa ba gaya min komai take ba" Katse wayar Shuraim yyi ya mike daga kwancen da yake, ya dau makullin motarsa ya fita. Khaleel bbu irin lallaba Heedayah da bai yi ba ya mayar da ita gida amma kememe ta ki, har sannan suna tsaye gefen hanya a motarsa sai kallonta kawai yake, ji yyi tace "To naji xan tafi gida, amma ka sauke ni in karasa da kafa kar ka kai ni street din" Yace "But it's late and they are dogs everywhere...." tace "Ni kuma a nan xaka ajiyeni nace" yace "In ajiyeki ki tafi wani waje kenan?" Ta kallesa tace "Ehh, don baxan koma gidan ba" ya fi minti uku yana kallonta kafin ya tada motar ya fara tafiya, har ya dau hanyar gidansa sae ya tuna abinda Zayyad yace masa daxu, can kuma kawai ya nufi gidan nasa. A cikin motarsa ya ciro makullin gate din gidan, ya sauka ya bude gate din, Heedayah sai bin anguwar that is so quiet ta ke da kallo har ya dawo cikin motar ya shiga, a parking lot ya tsayar da motar ya kashe ya sauka ya koma gate din ya kulle da makulli snn ya koma gun motar yana kallonta yace "Are you satisfied now?" Ta gyada masa kai yace "To sauko" bude motar tayi ta fito tana bin gidan da kallo tace "Gidansu waye?" Yyi shiru yana kallonta, ganin ynda take kallonsa a hankali yace "Gidanmu ne" tace "Mum dinka da Dad and siblings suna ciki" Yace "No" tace "Why? Where are they?" Kulle motar yyi bai ce mata komai ba, ya nufi entrance din katon gidan, ta bi bayansa tace "You are not saying anything?" Yace "Duk basa nan" tace "To ina suka je" Yace "Gobe xa su dawo, they travelled" tace "To ni da kai kawai xa mu kwana gidan?" Bai ce mata komai ba ya sa makulli yana bude kofar parlon, tace "Ehh??" Sai da ya bude kofar snn ya juyo yana kallonta yace "Aa da mutane" daga haka ya shiga parlon yana haska fitila da wayarsa ta bi bayansa, a hankali tace "Ni tsoro nake ji, babu wuta?" Yace "xan kunna yanxu" Ajiye wayarsa yyi da ya haska some areas of the parlor snn ya fita ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba haske ya gauraye ko ina na katon parlon, ta dinga bin parlon da kallo don yyi mata kyau sosai kamar ba a Nigeria ba, parlon is so neat don bai yi kama da wanda ba a amfani da ba, Khaleel ya shigo parlon ya kulle kofa snn ya dawo ya xauna yana kallonta yace "Now tell me Heedayah, me aka maki a can gidan?" Ta girgixa kai tace "Aa ni ba a min komai ba, kawai bana son komawa ne" yace "Noo, there must be reason for that, haka kawai baxa kice baxa ki koma ba" Tayi shiru tana kallonsa, mikewa yyi ya nufi fridge dake dinning area ya bude ya dau drink din gwangwani me sanyi snn ya dawo yace "I am tired, and sleepy... Mu je in nuna maki inda xa ki kwanta" Shiru tayi tana kallonsa, stairs ya nufa, ta mike ta bi bayansa, ya bude mata wani daki yana kallonta yace "Here...." Bata ce komai ba ta shiga dakin ya kulle kofar snn ya koma downstairs. Rai bace Maman Fadil tace "Baxa ki bude baki ba ana maki magana munafuka kawai, Banda kukan munafurci meye wnn kike yi, baxa ki basa amsan tambayar da yake maki ba" Farida ta ki cewa komai ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, Maman Fadil ta kalli Shuraim tace "Don Allah da ta ganta da waya who is first person da ya kamata ta fara sanar ma wa, idan ma baxata iya fada ma Mami ba tana ganin Mami won't take it likely ba sai ta gaya ma Yaya Junaid ba? To wllh bbu ruwana dubi karfe har sha daya saura bbu yarinya bbu labarinta, me xan ce ma Mami daga xuwa gidana yarinya ta bi saurayi da daddare" sai ita ma ta fara kuka, Shuraim dai na tsaye parlon just as the soldier he is, Farida ta saci kallonsa don tunda take bata ta6a ganin anger dinsa irin na wnn lkcn ba, gaba daya idanuwansa sun sauya daga yanda ta san su, Maman Fadil na share hawayen dake kwarara idonta tace "Ni kawai don kace kada a tada ma Mami hankali daren nan ne wllh da na kira na sanar mata Yaya Shuraim, amma duk da haka bari in kira Yaya yanxu ya san abinda ke faruwa this is almost after eleven" tana barin parlon shuraim ya juya yana kallon Farida fiercely yace "For how long wayar ke hannunta" Tayi shiru bata ce komai ba, tsawar da yyi mata ya sa ta mike a hankali tace "Ni bata ce min ya bata waya ba, kawai boyewa take ta yi har na gani" xaunawa yyi saman kujera ya sauke boyayyen ajiyar xuciya ya dafe forehead dinsa da ya ji yyi masa nauyi, sake mikewa yyi yana kallon agogo dake manne parlon.... Khaleel ya gama duk abinda xai yi ya kashe wutan parlon ya kwanta saman 3 seater wajejen karfe sha biyu da rabi, sai a sannan ya cire wayarsa a flight mode, bayan few minutes sai ga text din Zayyad ya shigo masa har uku, ya bude ya mike xaune yana duba messages din.... Lkci daya ya mike ya nufi kofar parlon ya bude ya fita da sauri.



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Kashe wutan gidan yyi gaba daya snn ya dawo parlon ya dau wayarsa ya kunna fitila ya wuce sama, a hankali ya bude dakin dake kallon wanda Heedayah ke ciki, ya shiga ya rufe, kusa da kofar bathroom ya isa ya duka ya daga foot mat dake kasa ya daga tiles din da aka daura kawai a wajen, sai dai idan mutum bai lura ba baxai gane daura tiles din kawai aka yi ba xa a iya dagawa, wani karamin under ground ya haska a wajen bayan ya bude wani box, ya ciro bindiga guda daya cikin bindigogi biyar dake nan snn ya dura bullet dinsu dake wajen su ma, ya mayar da tiles din ynda yake ya daura foot mat din ya mike ya saka bindigan a aljihunsa, ya fita dakin ya kulle kofar gently, har xai sauka sai kuma ya kalli kofar dakin da Heedayah ke ciki ya dawo ya bude kofar shi ma gently yana kallon cikin dakin, all with the aid of his phone flash, kwance ya ganta ta dukunkune waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya bude press dake ciki ya fiddo babban blanket me laushi ya lulluba mata, still yyi sai kuma ya kashe flash din da wuri ganin ta gyara kwanciyarta, sai da ya tabbatar ta ci gaba da baccin snn ya tafi gun curtains xai gyara ya hango mota biyu sun tsaya dai dai gate din gidan don ta window din ana yi ganin wasu bangare daga surrounding din street din, kallon motar yake har bayan kusan minti goma shi dai bai ga alamar an sakko daga ciki ba, wanda idan ma an sakko din ma ba sani xai yi ba sbda jikin wall din gidan motar ya tsaya, nan kuwa mutane biyar har sun sauka daga motar xuwa bakin gate din nasa, daya daga mutane biyar din da suka diro daga motar ya tafi ya durkusa bakin gate din gidan yana haska fitilar wayarsa ko xai ga tambarin tayar mota da xai yi nuni da mota ta shiga gidan, mikewa yyi yana kallon sauran yace "Yes yana ciki" dayan cikinsu yace "Cikin darkness?? da yana ciki ai xa a ga wuta a cikin gidan, but no light and akwai wuta a anguwar ai" Bindiga wanda ke kallonsa ya daura masa a fuskarsa strictly yace "Ka raina kitabar Brainiac kenan? Tunda har baya gidansa na asokoro, baya can gida, to yana gidan nan, coz he have no business with the other gender ballantana ace yana hotel, baya ma kwanan hotel, so now you guys should just find a way da xa mu shiga gidan nan in hukuntasa" Mutumin yace "Talent dinsa na yanda yake shiga gidan mutane in every operation xa mu yi amfani da yanxu" Tuni Khaleel ya fita dakin da Heedayah take ya sakko downstairs ya fito compound, ta jikin bango ya dinga bi har ya iso gate

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login