Showing 249001 words to 252000 words out of 275313 words
Chapter 84 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
din, sai a debi cous cous kadan a plate a hada ko?" Heedayah tace "Toh" Nan Mom Islam ta fara hada abincin a tray, ta dauko ginger and zobo drink da tayi tare da snacks tace "Shi xa ki fara kai masa" Heedayah tace "Toh" kallon wayarta da ya fara ring tayi tace "Aunty kilan sun shigo" Mom islam na kallonta tace "Toh ki fita ki shigo da shi" Heedayah ta koma ta dauko mayafinta ta sa takalminta snn ta fita, har wani walwali take kamar amarya cikin kayan jikinta, a hankali take tafiya, ta gansa xaune inda suka ta6a xama tare da Shuraim, kallonsa take tun daga nisa don kaftan ne a jikinsa da hula, bata ta6a ganinsa da manyan kaya ba sai yau, sai yyi mata kama da balarabe da yyi dressing din hausawa, sosai kayan suka yi masa kyau, shi ma kallonta yake kamar yanda take kallonsa har ta isa inda yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Sannu da xuwa" Yace "Uhn baki gane ni bane?" Ta boye fuskarta tace "Ya hanya" yace "Alhmdllh" Tace "Toh ka shigo ciki" Yace "Bari in huta kadan" Ta kallesa tace "Toh a ciki ma ai xa ka huta" Mikewa yayi ta dinga kallonsa, a hankali tace "Kayi kyau" Yace "A'a ke dai kika yi kyau" Murmushi tayi ta fara tafiya ya bi bayanta, parlon baki ta kai sa tace "Bari in kawo maka ruwa" Daga haka ta wuce can kitchen din Mom Islam ta dauko tray din ginger drink da zobo sai bottle water da snacks ta fita ta koma parlon, xaune ta gansa ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, a hankali ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tana kallonsa ya bude idonsa yace "Thank you" ta xuba masa ruwa a glass cup ta mika masa ya amsa, Mikewa tayi tace "Ina xuwa" daga haka ta fita parlon, Bangaren step mum dinta ta tafi, tana kallonta tace "Aunty ya na parlor" Mom Islam tace "Ohk to bari in je mu gaisa, ki je ki sanar ma Ammin ki" Heedayah tace "Toh" fita tayi ta koma bangaren Amminta, cikin dakinta ta sameta, ta kasa kallonta gabanta na faduwa tace "Ammi ya iso yana parlor" Ammi tace "Wa ya iso?" Heedayah tace "Khaleel" Ammi tace "Ohk..." Bayan few seconds Heedayah ta juya ta fita dakin, a parlon da Khaleel yake ta tadda Mum Islam xaune suna gaisawa, Heedayah ta shigo ta xauna kasan carpet, Mum Islam na kallon Heedayah tace "Ki kai sa ya gaisa da su Yakumbo" Heedayah tace "Toh" Mikewa tayi tace masa sai anjima sannan ta fita daga parlon, Heedayah na kallonsa tace "Mu je yanxu?" Yace "Aa let me rest first" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Toh baxa ka ci snack din ba" Xaunawa yyi kan lallausan Carpet din parlon yace "Mun ci abinci a nan kano fa Heedayah, wllh I am not hungry" Lkci daya ta 6ata fuska, yyi murmushi ya dau samosa daya yace "Ke ma xo ki dauka idan kina son in ci" D'an murmushi tayi ta mike ta koma inda yake xaune leaving a little distance between them ta dau samosa daya, kallonta kawai yake har ta kai baki, sai a snn ya ci na hannunsa, kadan ya ci yace "Ban iya cin abin nan ba, yau na fara ci sbda ke" Heedayah ta xaro ido tana kallonsa, ya dau ruwa ya sha, yace "Ya isheni wllh" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Me kafi so cikin abinci?" Yace "fried rice, rice and stew, meat ko wani iri na halal Ina ci, I love pizza, shawarma, sausage, burger, milk drink, tea.... I think that's all" Xaro ido Heedayah tayi tace "Tuwo, wake, taliya, macaroni, egg, fish, different soups...." Katse ta yyi yace "Hell No, abinda na lissafa maki kadai nake ci a duniya" da mamaki Heedayah ke kallonsa, Sallama aka yi a kofar parlon, Heedayah ta juya da sauri, Ammi ta shigo parlon, Khaleel ya sauke idonsa kasa, xaunawa Ammi tayi saman kujera tace "Sannu da xuwa" da ladabi yace "Ina yini" da murmushi fuskarta tace "Lafiya lau ka xo lafiya?" Yace "Alhmdllh, ya gida" Tace "Alhmdllh, daxu mun yi waya da Barrister tace min tana kano" Khaleel yace "Ehh tana nan" Ammi tace "Kun hadu da ita kenan?" Yace "Aa ba mu hadu ba" Ammi tace "Ohk anjima xa mu je da driver sai in daukota in sha Allah" Khaleel yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ameen, you are welcome" D'an murmushi yayi yace "Nagode" Mikewa tayi ta fita parlon, Heedayah ta wara ido tana kallonsa tace "Ashe Mami ma ta xo?" Yace "Ehh ta xo" Heedayah tayi murmushi tace "Xan bi ku mu koma" Ya wara ido bai dai ce mata komai ba, tagumi tayi tana kallon dogon hancinsa, ya shafa kansa ya bude goran ruwan ya diba a glass cup, a hankali tace "Zayyad fa?" Yace "Yana gombe mun hadu ma" tace "Wajen wa a Gombe?" Yace "Shi ma Yan uwansa na can gomben" Heedayah tace "Ohkkk" wayarta dake hannunta ne ya fara ring ta kalla ta ga Shuraim ke kiranta, a hankali tayi silencing wayar, Khaleel dake kallonta yace "Pick ur call" tace "Aa ban san waye ba" Wani samosan ta dauka ta fara ci tace "Me yasa baxa mu je mu gaida su kaka ba yanxu?" Yace "Xan je anjima kadan" Mai aiki ce ta shigo parlon ta gaida Khaleel da ladabi tana kallon Heedayah tace "Aunty tace ki je" Heedayah tace "Toh" mikewa tayi tana kallonsa tace "Bari in je in dawo" Ya gyada mata kai ta wuce, tana Isa bangaren Step mum dinta, tace "Abbanki ya kira yanxu yace yaje office ya samesa" Heedayah tace "A ina office din?" Aunty tace "Government house" Heedayah tace "Toh wa xai karasa da shi?" Aunty tace sojoji suna waje suna jiransa, Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita dakin, bayan ta sanar ma Khaleel abinda Aunty tace, ita ta rakasa har inda soldiers din suke snn ta koma ciki. Sai bayan la'asar Khaleel ya dawo, Heedayah har ta canxa kayan jikinta xuwa wani sabon atamfar me tsada, xaune ta samesa a parlor, ta xauna kasa tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" mikewa tayi tace "Bari in kawo maka abinci" yace "Na ci abinci" tace "A ina" murmushi yyi yana kallonta a hankali yace "Wllh na ci" Tayi shiru, shi kam kallonta kawai yake, murya can kasa tace "Mami ta xo tana sama wajen Ammina" Yace "Ohk..." Bude kofar parlon aka yi suka juya a tare, Shuraim ne ya shigo Heedayah ta dinga kallonsa, ya ja gefe ya tsaya, Sudais ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ta mike tana kallonsa tace "Ya Sudais" murmushi ya sakar mata yace "Cutie..." Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba, saura kiris ta rungumesa lkci daya ta ja baya, sai kuma ta fashe da dariya tana kallonsa, shi kam murmushi yake, Khaleel ya dauke kansa, Shuraim dama tuni yyi hakan....
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Barin su Shuraim yyi a wajen ya karasa cikin parlon ya mika ma Khaleel hannu suka gaisa, Heedayah suka karaso parlon tare da Sudais, Sudais na murmushi ya mika ma Khaleel hannu shi ma, Khaleel ya mika masa nasa suka gaisa, Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo tace "Ya Shureen are you going??" Ba tare da ya juyo ba yace "Yea" daga haka ya fita, Heedayah ta mike ta tafi ta kawo ma Sudais ruwa yana kallonta yace "Cutie shine kike gudo kika bar mu a kaduna?" Murmushi tayi tace "Aa ya Sudais na xo hutu ne xan koma soon" yace "Toh ya su mama?" Heedayah tace "Bari in kirata ku gaisa" Yace "Noo ba kina da bako ba kar ki damu anjima xan dawo, yanxu sauri mu ke kawai nace bari in xo mu gaisa, xan wuce jigawa ne immediately" a hankali tace "Toh yaushe xaka dawo?" Yace "Before Magrib idan Allah ya yrda" Daukan ruwan yyi ya sha yace "Let me get going don in dawo da wuri" tace "Kai da ya Shureen xa ku je?" Yace "Aa nan kawai nace ya rakoni" mikewa yyi ya karasa gun Khaleel ya sake basa hannu still smiling yace "Xan koma" Khaleel yace "Allah ya tsare hanya" Heedayah ta bi sa da kallo tace "Allah ya dawo da kai lafiya ya Sudais" Yace "In sha Allah cutie" daga haka ya nufi kofa, Khaleel yace "Ki rakasa mana" ta kallesa tace "In rakasa?" yace "Ehh" mikewa tayi ta nufi kofa da sauri ta fita, tsaye ta gansa inda Shuraim ke xaune a karkashin thatched roofing, ta karasa inda suka Sudais na kallonta yace "Why did you leave him?" Murmushi Heedayah tayi tace "Raka ka xan yi" yace "Noo, Kar ki damu ki koma kawai, amma fa kar ki ce da kaka na xo" tayi murmushi tace "Baxan gaya mata ba" Ta kalli Shuraim dake danna wayarsa tace "Ina yini ya Shureen" without looking at her a takaice yace "Lafiya" Mikewa yyi yana kallon Sudais yace "Toh mu je" Daga haka ya fara tafiya, Sudais yace "Sai na dawo Heedayah" daga masa hannu tayi ya bi bayan d'an uwan nasa, sai kuma ya juyo yana mata murmushi yace "Saurayin naki so handsome.... Kamar balarabe" Da sauri Heedayah ta juya ta koma ciki tana murmushi, bayan ta shiga parlon ta xauna kasa kusa da Khaleel tana kallonsa da murmushi fuskarta tace "Ya Khaleel kasan waye ne shi" Yace "I think xan xo in wuce yanxu, so that I can reach Kaduna early" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike yace "Erm kice da su Ummi na wuce, bana son night journey" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta sauke idonta kasa, ya dau wayarsa yace "I bought you perfumes, suna mota, but bari in wuce da su kaduna anytime kika dawo ki karba" Jin bata ce komai ba still yace "Ain't you talking?" Hawayen dake makale idonta ya sakko, shiru yyi yana kallonta, can ya koma ya xauna yace "To me na maki kuma kike kuka?" Ta rufe fuskarta da kujera hawaye na sauka idonta, kallonta kawai yake, can yace "Hasbunallah, yanxu kukan me kike Heedayah?" Ta share idonta ta mike tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka ta juya xata bar wajen ya fixgota, fadowa tayi gefensa kan kujeran, ta fashe da kuka a hankali.... Ya kwantar da ita shoulder dinsa a hankali yace "Tell me plss me yasa kike kuka" taki cewa komai yana jin hawayenta na sauka jikinsa, sosai jikinsa yyi sanyi, ya sa daya hannunsa yyi wrapping dinta much closer to him, sai ta xama yar karama kusa da shi, lkci daya ta tsayar da kukan da take, ya daura goshinsa saman kanta cikin sanyin murya yace "I am sorry Heedayah...." ita dai ta kasa ce masa komai, ta ji gabanta ya hau faduwa, xame jikinta ta fara yi amma ta kasa kwace kanta sbda irin rikon da yyi mata, kamar xata yi kuka tace "Ka sakeni" ya ki saketa, a hankali yace "Tell me kukan me kike?" Tace "Plss ka sakeni ya Khaleel" ya dago kanta yana kallon kwayar idonta da idanuwansa da suka sauya launi lkci daya, ta ki yrda su hada ido gabanta sai faduwa yake, a hankali yace "Me yasa kike son kula wasu mazan??" Xaro ido tayi ta kallesa, yace "Me yasa kullum sai Shuraim ya xo wajen ki? And what stopped you from hugging the other guy??" Kamar xata yi kuka tace "They are all my brothers fahhh...." Kauda kanta tayi ganin kallon da yake mata, bata ta6a jin xuciyarta na bugawa irin haka ba, gaba daya jikinta yyi sanyi, xata kwace kanta still ya ki saketa, ta juyo ta kallesa kamar xata fashe masa da kuka tace "Yaya plss ka sakeni, kar wani ya shigo" sosai canjawar da idanuwansa suka yi ke bata tsoro, ya kamo hannunta cikin taushin murya yace "Heedayah" bata yrda ta kallesa ba, ya juyo da kanta da damuwa yace "Don't break my heart Heedayah, Ina maki son da nima ban san irinsa ba, Ina maki son da bbu macen da na ta6a yi ma..." Sauke idonta tayi kasa jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ya daura forehead dinsa saman nata yace "Kin ji?" Muryarta na rawa tace "I won't...." Ya daura lips dinsa saman dogon hancinta ya lumshe idonsa, ta kwace kanta da karfi gabanta na faduwa ganin abinda yake son yi, xamowa kasa tayi ta xauna, ya biyota kasan a hankali yace "I am... Am sorry" kasa kallonsa tayi, shiru duk suka yi na kusan minti biyar, can yace "Xan shigo da daddare in sha Allah" Daga haka ya mike tsaye da kyar ta saci kallonsa ta sunkuyar da kanta, ganin ya fara tafiya, a hankali tace "Don Allah da gaske xaka dawo?" Ya juyo yace "In sha Allah, Mami tace in bari mu tafi gobe" Ta sunkuyar da kanta ya nufi kofa, a hankali ta dago ta bi sa da kallo gabanta na faduwa har ya fita. Har Magrib Mami na can bangarensu Kaka, tun da Heedayah ta je ta gaisheta bayan tafiyar Khaleel bata sake xuwa ba tana bangaren Step mum dinta, sai bayan da tayi Magrib ta fita xuwa gun Amminta, Ammi na bedroom dinta tare da su Ashnaah, Xaunawa tayi ta gaida Ammi, Ashnaah ta nufeta tana nuna mata takardan hannunta tace "Aunty Abba ne ya siya min da Ashfah" Heedayah ta amshi takardan tana dubawa, Ammi tace "Bakon naki ya tafi?" Heedayah tace "Ehh tun da yamma" Ammi tace "Kadunan ya wuce?" Ta girgixa kai tace"Yace min da Mami xa su koma gobe" Ammi bata kuma ce mata komai ba, bayan wani lkci Heedayah ta mike ta fita tunawa da tayi Khaleel yace xae xo da daddare, dakinta ta tafi ta dau wayarta ta xauna gefen gado tayi dialing number din Shuraim, har ya gama ring bai daga ba, ajiye wayar tayi tana ta xaune gefen gado sai ga kiran Khaleel, Dauka tayi a hankali tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Come out now..." Tace "Ohk baxa ka shigo ku gaisa da Mami ba?" Yace "Mun yi magana ta waya da ita" Heedayah ta 6ata fuska tace "Aa ka dai shigo plss" ya d'an yi shiru snn yace "Ohk" katse wayar tayi ta mike ta d'an gyara fuskarta ta feshe sabon hijab dinta da turare sannan ta fita dakin tana rike da wayar, parlon baki ta samesa, ta nufesa tana murmushi ta durkusa gefensa tace "Ina yini?" Ya shafa kansa yace "Lafiya lau" ta mike tace "Mu je ku gaisa" yace "Where?" Tace "Sama" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta, tafiya sosai suka yi har suka iso bangaren da su kaka suke, ta bude kofar a hankali tare da sallama, Kaka na xaune parlon da Yakumbo, Mami ma na parlon tare da Shuraim, kaka na ta kallon Heedayah tace "Rakiya ba don iyayen Heedayah 'yan halaq bane da shkkn mun taimaketa a banxa ko bi ta kanmu baxa ta sake yi ba a rayuwa, Ina lura da ita bata wani farin ciki da xaman gidan nan da nake yi, toh bata farin ciki mana tunda ba gaisheni take ba kwata kwata yanxu" Heedayah ta hade rai ta ba Khaleel hanya ya shigo parlon da sallama cikin cool voice dinsa, Tsit kaka tayi, Yakumbo ta sunkuyar da kanta, Heedayah na kallon Shuraim ta nufi Mami ta durkusa kusa da ita da murmushi tace "Mami good evening" Mami tace "How are you dear" Xaunawa Khaleel yyi daga inda Shuraim yake, Shuraim ya basa hannu suka gaisa, Khaleel na kallonsu kaka yace "Ina yinin ku?" A tare kamar hadin baki suka ce "Lafiya lau" ko wacce na kirkiran murmushi, ya kalli Mami yace "Ina yini Ummi" Mami tace "Lafiya lau, how was the journey?" Yace "Alhmdllh" tace "Ka baro su lfya?" Yace "Suna gaishe ku" Mami tace "Maa sha Allah" Kaka da Yakumbo dai kallo kawai suke a TV, Khaleel ya mike yace "Xan koma" Kaka tace "Toh madallah, Allah yyi maka albarka, ina Junaidu?" Mami tace "Yana Kaduna" Kaka tace "Atohh, shi dama ba mai son yawace yawace bane" Mami dai bata ce komai ba, Khaleel yyi ma Mami da Shuraim sallama snn ya nufi kofa, Heedayah ta mike sai da ta ga ya fita parlon ta kalli Shuraim ta hade rai kamar xata yi magana sai kuma ta fasa ta bi bayan Khaleel da sauri, Yakumbo ta bi ta da kallon damuwa. Khaleel bai yarda ya xauna parlon baki ba wai ya fi son waje, bbu ynda ta iya masa kawai suka fita, tana kallonsa a inda suka xauna tace "Toh abinci fa?" Yace "Naga alama kina da son abinci sosai, ke dai kawai aci abinci?" Dariya tayi ta rufe fuskarta tace "Toh laifi ne don an ci abinci" Murmushi yyi bai ce komai ba, tace "Kayi shiru?" Yace "Na sha fruit before coming" Tace "Just fruit?" Yace "Yea and am okay" Sun fi minti arba'in xaune wajen daga karshe ganin yanda yake lullumshe ido tana basa labari, ta bata fuska tace "Wai bacci kake ji?" A hankali ya bude idonsa yace "Yes dear, na gaji da yawa" Shiru tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa, Can tace "Toh ai Abbanmu yace ka kwana nan" da sauri yace "Noo, I've already lodged a hotel" tace "Toh me yasa baxa ka kwana nan din ba" Yace "Nothing" Tace "Toh shkkn, gobe ai xaka xo kafin ku tafi" Yace "Uhn xan xo" Ta rungume hannu ta hade rai tace "Ban yarda ba" Yyi murmushinsa me kyau ya kai hannunsa a hankali kan hancinta yace "Ko mun yi auren wnn wahala kawai xaki dinga bani, kin fiye rigima" Ta rufe fuskarta da hannunta, ya mike yace "Ai ni nace maki xan shigo idan Allah ya yrda" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" tashi tayi tace "Bari in raka ka first gate din can" Yana kallonta yace "Okay dear" a tare suke