Showing 81001 words to 84000 words out of 275313 words
Chapter 28 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel
don ba batun auren Shuraim ya fi damunta ba ita yanxu, suna nan xaune har minti ashirin din yyi sannan suka mike suka sake gurgurawa can sama, Hajiya Sadiya tayi kasa da murya tace "Toh ga mu mun dawo Malam, da fatan ka huce" Bai ce komai ba sai bayan kusan minti biyar yace "Tohh, yanxu me ku ke son ayi a kan lamarin, ita dai wnn makauniya naga xata warke nan ba da dadewa ba, sannan xata xame maki ciwon ido nan gaba ke Maryam...." Mumy ta marairaice tace "Toh Malam ya kaga ya kamata ayi, ni so nake gaba daya ta bace bat na har abada kuwa, in son samu ne ma ni kada idon ya bude malam ta dauwama a makance, Kai idan ma duniyar xata bari gaba daya ni dai oho in daina ganinta kawai, sannan shi kuma wnn yaro nawa ayi kokarin ganin an dakatar da batun auren nasa don ni ban shirya aurar da shi ba yanxu, ita kuma kishiyar ayi duk abinda xa ayi ta bar min gidana da mijina, in xama ni kadai ce a gidan, Kuma maigidana na da uwa fitinanniya, duk ta gallabe mu, so nake ita ma a rabata da d'an nata, ko biyayya ya daina yi mata, snn a rufe bakinta gumm ta xama kamar kurma ko bebiye, taji kuma bata son xaman gidan namu ta koma can gidan wansa har abada" Mutumin yace "Toh an gama...." Hajiya Sadiya ta gyara xama tace "Ni kuma Malam a kara rufe min bakin mijina a kan na da, duk da dai bbu wata matsala ynxu bai jin batun kowa sai nawa tun aikin da kayi min kwanaki, amma a kara min wani sabo ynxu dai" Mutumin yace "Toh a bani minti sha biyar a waje" Mikewa duk suka yi suka gungura kasa. Sai kusan magariba Mumy ta isa gida don ma ba ita bace da girki, a dar dar ta shiga parlon tana boye jakarta a Hijab, ganin bbu kowa kusan da gudu tayi bangarenta ta kulle kofar, ganin su Rabi'ah da Khadijah xaune suna kallo parlonta ta shige bedroom tana amsa sannu da xuwan da suke mata... Karfe goma saura na dare Mumy ta fito, Mami ce ta fito bangaren Abba, Mumy ta dauke kai kamar bata ganta ba ta shiga dakinsu Sajida, tana daga tsaye bakin kofa tace "Sajida me ya hanaki wanke min bandaki yau?" Sajida ta mike da sauri tace "Wllh Hajiya na wanke tun da safe" Mumy tace "Toh tafi ki ga bandakin da kika wanke ki dawo ki sameni yanxu" Sajida ta fita dakin xuwa bangaren Mumy, Mumy na kallon Karime tayi kasa da murya tace "Xuwa sha daya ko sha biyu ki taho bangarena ki sameni" Karime tace "Toh Hajiya" Daga haka Mumy ta juya ta wuce da sauri. Mumy na parlonta xaune tana ta jiran Karime sai ga ta kuwa karfe sha daya da rabi, Karime ta kulle kofar ta iso kusa da ita ta durkusa tace "Ga ni Hajiya" Mumy tace "Yanxu ita makauniyar gun Rahinar take ko gun Kaka?" Karime ta tabe baki ta gyara xama tace "Ehh toh, yau ta kwana dakin kaka, gobe ta kwana bangaren Rahinar, amma dai ta fi dai xama wajen kaka" Mumy tace "Ba naga tana yawan shan shayi da, ko ta daina?" Karime tace "Har yau tana sha, gwangwanin kayan shayin nata ma na dakin kaka, ta sha da safe wani lkcn har da rana sannan ta sha da daddare" Mumy tace "toh wani aiki xan baki Allah ya sa xa ki iya Karime" Karime tace "Haba me xai hana, ai bbu abinda baxan iya maki ba Hajiya, ke da kika rike ni tamkar 'yar ki, Ina xan samu haka banda wajen ki" Mumy tace "Toh, ba wani abu bane garin magani ne nake son ki juye a gwangwanin milon gaba daya sai ki gauraya, don idan an sa a madara xa a gane" Karime tace "Hajiya amma dakin kaka fa kayan shayin suke ba dakin uwa rikonta ba" Mumy tace "Toh sai me?? Ba tana sa ki share share ba?" Karime tace "Ta fi sa Sajida, komai Sajida take kira tayi mata" Mumy tayi shiru sai kuma tace "Wani aikin take sa Sajida?" Karime tace "Irin su Shara, goge gogen waje sai wankin bandaki" Mumy tace "Da yaushe take sa ta?" Karime tace "Da safe haka take kiranta ta saka ta" Mumy tace "Toh gobe kafin ma ta kirata xan aiki Sajidar, tana kiranta sai ki je kice bata nan, nan kuma xa ki tambayeta me xa ki yi mata" Karime tace "Toh shkkn, xan yi iya bakin kokari na Hajiya" Mumy ta mike ta tafi cikin dakinta sai ga ta ta fito da Kullin magani a kyallen atamfa tace "Gaba daya xaki juye kuma kiyi a hankali kar ki bari ya xuba" Karime ta amshe ta tura cikin rigan mamanta tace "Toh Hajiya in sha Allahu" daga haka ta fice daga parlon da sauri, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta kashe wutan parlon ta wuce cikin dakinta. Washegari da safe bayan Abba da Mami sun fita, kaka ta kwalo ma Sajida kira, Karime ta mike da sauri tana ta6a mamanta don ta tabbatar kullin na nan don Mumy tun safe ta sa Sajida ta bar gidan, Tana shiga dakin kaka da sallama tace "Gani kaka, Sajida an aiketa" Kaka ta dinga kallonta daga sama har kasa sannan tace "Ni dai na ga jaraba, wai ke baki wanka ne, kullum cikin naso kike kamar d'an wake, mata kazama kawai duk wari, me xa ki min to da kika taho toh?" Karime tayi kasa da kai tace "Na xata aiki Sajidar xata maki shine na xo in yi" Kaka tace "Ehh lallai, da kuwa lalacewa ta sameni, a hakan xaki kama min aiki inje wata cutar ta kama ni a banxa a hofi, wai ma daga wani kauyen kike??" Karime tayi kasa da kai tace "Doguwa" Kaka tace "Ko da na ji, to yi tafiyar ki, kar ki sake shigo min daki da sunan xa ki min aiki ni ba gantalalliya bace, bari Rakiyar ma ta dawo xan ji ko meye sauran amfanin ki a gidan nan tunda dai ga ni nan ina ma Deedayah komai, ke kuma ba sai a sallame ki ba" Karime ta juya da sauri ta fita tana waigo kaka a tsorace, Kaka tace "Ni naga jaraba, mata duk naso kullum fisabilillahi tayi ta shigo min daki" Heedayah dake kwance saman gado tace "Kaka to aiki fa xata taya ki..." Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "Ta je can ta taya uwarki Rakiya aiki, ni ba ruwana cewa ma xanyi a sallameta ko xan daina ganin fuskarta"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Mumy ta mike da sauri ganin Karime ta dawo tace "Ya, har kin xuba?" Karime tace "Korata tayi wllh, har cewa tayi xata sa a sallameni" Mumy ta xaro ido tace "Me kika mata????" Karime tace "Ban mata komai ba wllh, haka nn kinsan dama bata sona" Mumy tace "Toh baki bata hkuri ba kika fita ke kuma?" Karime tace "Cewa tayi bata son ganina" Mumy ta xauna tayi tagumi tana tunanin to ynxu ya xa ayi ta samu ta juye maganin nan cikin kayan shayin Heedayah, ta kalli Karime tace "Ba ni kayana ki fita" Karime ta fiddo kullin cikin rigarta, kin amsa Mumy tayi tace "Ajiye min kan kujera" ta ajiye, Mumy tace "Je ki sae na neme ki" fita tayi parlon Mumy ta bi ta da wani kallo, leda ta dauko ta rufe maganin da shi tana yatsina fuska sannan ta dauka ta wuce daki. A ranan Mumy ta shiga dakin kaka yyi sau biyar kafin yamma, fitarta na karshe kaka tayi mitsi mitsi da ido tace "Da kyar idan matan nan tana da gaskiya, na lura tun safe take min xarya kmr me nakuda.... Ni dai bari Amadu ya dawo in ji dalili gaskiya, Allah na tuba duniyar nan yanxu ko wanda ku ka fito ciki daya kaga yana maka xarya bbu dalili toh kayi ta kanka kawai" Heedayah dai na dakin tana jin abinda kaka ke cewa, Kaka ta mike ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri tace "Gani kaka" Kaka tace "Kasko xa ki dauka kije duk inda xaki samo gawayi ki hura min garwashi ki kawo min yanxun nan" Sajida tace "Toh sai dai inje kasuwa yanxu a siya gawayin" Kaka tace "Toh ni dai bani da ko sisi, tafi ki kira min Maryam" Sajida tace "Toh" sannan ta wuce, ba a dau lkci ba sai ga Mumy tana murmushi tace "Gani kaka, aiki xa a maki" Da sauri kaka tace "A'a, aikin me kuma kamar kuturwa, dari biyar xa ki ba Sajida xata je min kasuwa ynxu" Mumy ta d'an juya lkci daya ta daure fuska, sai kuma tace "Anya xa a samu kuwa, da yake jiya da naje can gida na kai Salima asibiti to bbu kudi wajena ynxu" Kaka tace "Toh kira min Amadu, shi baxai rasa yanda xai yi da ni ba ai" Mumy dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ki kira min shi da wayarsa" Barin dakin Mumy tayi murya can ciki tace "Toh" tana tsaye daga bakin kofarta ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri, Mumy ta jefa mata dari biyar din fuska a murtuke ta shige parlonta ta kulle kofa... Sajida na dawowa da gawayin ta rura ma kaka a Kasko, sannan ta kai mata dakinta, kaka na xaune tsakar dakin ta baje kayan wani tsohon jakarta, kullin magunguna ne iri iri kai kace boka ce, Sajida ta ajiye kaskon saman tiles tace "Gashi kaka" Kaka tace "Allah maki albarka...." Tace "Ameen" sannan ta fita, kaka ta xuba uban turaren icce a wutan, Tuni Heedayah ta mike ta fara tari tace "Kaka meye shi?" Kaka tace "Toh haka kawai aka ce maki xan xauna a kashe ni, jiya fa wani mummunan mafarki nayi..." Heedayah xata fita dakin kaka ta rufe kofar tace "Toh ko dai ke mayya ce ba mu da labari..." Heedayah ta fashe da kuka tace "Kaka yana shiga hancina" kaka tace "Ai dama ta nan din xai shiga, Ina xa mu tsaya a cuce mu, kowa fa ya lalace da mugun abu a xuciyarsa, tun ina gidan mijina nake tsare kai na, Rakiya ma idan ta dawo daga gantalin aikinta sai ta xo in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne fa..." Heedayah ta toshe hancinta, Kaka na ta surutunta tana kara cika iccen cikin wutan kaskon, sai da ta tabbatar ya ratsa ko ina na dakinta sannan ta fitar da shi parlor ta ajiye tace "Toh dama kada wanda ya dauke min kayana a nan" Mami ce ta bude kofar da sallama, tana shigowa ta fara yatsine fuska don hayaki ya cika ko ina, Ta karaso gun kaka tace "Meye wnn din kaka" Kaka tace "Ke ma idan xa ki samo leda in debar maki ki samo, duniyar ynxu ba gaskiya, Maryam ma idan ta ga tana so ta samo leda in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne" Mami ta gaida kaka xata wuce kaka tace "Yauwa Rakiya dama Ina jiran ki dawo ki gaya min me wnn me aikin taki take tsinana maki a gidan nan" Mami ta juyo tace "Aa ba komai kawai dai suna aikin gidan ne tare da dayar mai aikin" Kaka tace "Toh a gaskiya ki sallameta Sajida kawai ta ishe mu a gidan nan, baki ga ba kullum fa naso take, kazama ce fa da kyar idan ruwa na ta6a jikinta haka kawai wata cuta taje ta kama mu ta dalilinta bayan mu duk muna wanka muna tsafta" Mami tayi murmushi tace "Naga kamar aikin ya ma Sajidar yawa ne" Kaka tace "Sai a samo wata me tsaftar amma a gaskiya a sallami wnn, idan ko ba haka ni a sallameni" Mami na kallonta tace "Ta maki wani laifin ne kaka?" Kaka tace "Aa ko daya kawai na gaji da kazantar ta ne" Mami bata kuma cewa komai ba ta juya ta nufi bangarenta... Da daddare Abba na parlonsa sai ga kaka ta shigo da sallama, Mumy da ke yanka masa watermelon tace "Sannu kaka" Kaka ta xauna tace "Yauwa, Amadu ashe ka dawo" Yace "Ehh na dawo, Ina yini" tace "Dama xuwa nayi naji wa ke biyan kudin aikin matar da Rakiya ta dauka" Yace "Aa ita ke biya" Kaka tace "Au haba, to bari in bar mata mai aikinta kar ta kullaceni, wai da cewa xan yi a sallameta" Abba yace "Tayi wani abu ne?" Kaka tace "Oh oh kawai dai ni bata kwanta min bane ga kazanta malam, amma tunda ba kai ke biya ba ai shikenan, ae Rakiyar ma me kudin kanta ce, ba xaman banxa take ba kamar wasu, baka ga gidan wan tsohon mijinta ba da Junaidu ya kai ni shekaranjiya, Kai kace wani shugaban kasa ne" Mumy dai ko kallon kaka bata yi ba sai sauri take ta bar parlon, ko yankan kirki bata ma kankanan ba ta mike tace "Xan je in duba ruwan shayin da na sa a kitchen" daga haka ta fita, kaka ta kalli kankanan tace "Dubi wani yanka da tayi ma kankanan kamar bakatafiya..." Shi dai Abba bai ce komai ba, kaka tace "Toh ni dai na hada kayana tun ranan da ka min xancen tafiya gyaran idon Deedayah a india" Abba yace "Mutane biyu kacal xa su je tare da ita fa Baaba" Kaka tana kallonsa da kyau ta gyara xama tace "Ban gane mutane biyu ba, su wa da su wa kenan mutane biyun?" Yace "Aa ba ni nace ba, ka'idar wajen ne haka, Doctor ne ma ke gaya min" Kaka tace "Toh ba sai ni da kai mu kai ta din ba, ko akwai wani wanda ta hada wani abu da shi banda ni da kai din" Abba yyi shiru yana kallonta, kaka tace "Toh dama ai ni da kai ne dolenta, ita Rakiya yaushe ta xo gidan ko yaushe ta san Deedayar da xa ayi marmarin tafiya da ita?" Shi dai Abba bai ce komai ba.... Mumy na fita sai da ta fara wucewa bangarenta snn ta fito da sauri, ta dinga bin main parlon da kallo kamar munafuka sannan ta shige dakin kaka ta kulle, hannunta na rawa ta isa gun kayan shayin ta sauke gwangwanin madaran amma ta rasa da me xata bude na milon, kan Fridge ta hango cokali cikin cup, ta tashi da sauri ta dauko ta bude gwangwanin ta ciro ledan dake rigarta, hannunta na rawa ta bude kyallen ta juye bakin content din cikin gwangwanin ta gauraya da cokalin snn ta rufe gwangwanin ta mayar Inda yake ta tashi, ta goge cokalin da xaninta shi ma ta mayar cikin cup din, gaba daya a rikice take, ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, sai da ta shiga parlonta ta sauke wani ajiyar xuciya ta juyo tana kallon yaranta tace "Uban me ku ke jira ba ku tafi kun kwanta ba? Maxa a kashe min tv tunda bance ku lalata na dakinku ba" Sai da suka fita parlon snn ta wuce cikin dakinta tana wani murmushi.... Washegari da sassafe kaka na share sharen lungu da sako na dakinta ta dauke gwangwanin madara da Milo ta tabe baki tace "Mayyar ma bata sha shayin jiya da daddare ba, dama fa gulma ce, a gidan uwarta da ubanta ina xata samu haka, ita dai kawai ta samu d'ana sai kashe mata kudi yake a banxa a hofi, sbda ita abubuwa da yawa an daina min, tasa sai maneji muke yi, ga uban kudi xa aje a gyara kaddararrun idonta nan da kwanaki kadan, mu dai kawai Allah ya bamu lada, bafa dangin iya balle na baba" Tana ajiye gwangwanin milon taga murfin ya fadi, ta dau murfin tana kallo da mamaki, can ta ajiye tace "Ikon Allah, ni fa na hada mata shayin jiya da yamma, to wani barawo ne ya xo ya bude ya sata ya manta bai rufe ba, gashi har Milon yyi kasa, ni dai ba haka na bar sa ba wllh, sata aka fara yi gidan amadun bani da labari??" Ajiye tsintsiyar tayi ta fice daga dakin, direct parlon Abba ta nufa ta kwankwasa kofa, Mumy ce ta fito, kaka tace "Amadun fa?" Mumy tace "Yana ciki" Kaka tace "Ce masa gani a tsaye" Abba na fitowa kaka tace "Amadu wllh shigar min daki aka yi aka yashe milon Deedayah tass, ynxu ba sai ace ni ke shanyewa ba ko da ba a fito fili an gaya min ba ayi ta xagina a xuciya, toh gaskiya ni dai a san matakin da xa a dauka ynxun nan" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Ikon Allah, toh bari in debo na wajena sai a kara mata a kai tunda yyi kasa, ba abun tada hankali bane kaka" Kaka tace "Oh oh ba wani debo naki da xa kiyi, ko ma waye ya diba sai ya maido wllh, xan fara ta kan masu aikin nan tass sai na bincike kayansu don nasan ba shan lkci daya xa ayi ma milon ba deba xa ayi a leda a boye, Kai har kayan Deedayar ma sai an bincika da nasu Rabi'ah" tana fadin haka ta nufi dakin masu aiki tana kwala ma Mami kira ita ma ta fito, kayan Sajida ta fara dubawa ta xaxxage gaba daya Ghana must go din bata ga komai ba, Kaka ta kalli Karime dake ta xufa tace "Ke ina jakarki" Karime ta nuna mata ghana must go din, ba komai ya sa hankalinta ya tashi ba sai kullin Madara da millo na Mumy da take diba a leda idan Mumy tace taje ta hada shayi, har na Mami ma tana diba, snn ga kullin soyayyen nama na jiya da ta boye a kayan, ga kuma Cornflakes a leda shima duk ta boye, kaka ta yatsina fuska tana xaro kayan kamar Kashi tana ajiyewa kasa, da ledan naman ta fara cin karo, ta