Showing 114001 words to 117000 words out of 275313 words

Chapter 39 - Heedayah Book One Complete Hausa Novel

fita, bangaren Mami ya nufa ya bude parlon ya shiga, bbu kowa parlon amma yana jin muryarsu a daki, karasawa yyi bedroom din ya bude kofar, Xaune suke kan gado suna kallo a laptop din Farida, Heedayah na sanye da yar rigar bacci iya cinya haka ma Farida, Farida ta xaro ido, da sauri ta rufe jikinta da Pillow tana kallonsa, Heedayah ta sauka saman gadon da gudu ta shige bandaki ta rufe, yana kallon Farida yace "Bani wayar da kika shiga dakina kika dauka" Ta xaro ido tace "Ni?? I didn't take any phone wllh, tun daxu muna kallo a nan ban fita ba" ya fi minti daya yana kallonta sannan ya juya fice daga dakin, ya koma dakin kaka, kaka ta kallesa tace "Sojojin ne suka baka pareti da daddaren nan, naga ka shigo daxu baka ce min komai ba, gashi ka sake dawowa" Yace "Ina wayoyin da kika dauka a dakina?" Kaka ta mike tsaye ta wani xaro ido tace "Wayoyi kuma?" Yace "Ehh" Ta nemi waje ta xauna har ta fara salati sai kuma ta sakar masa kuka tace "Tunda uwata ta haifeni bbu wanda ya ta6a tsareni yana tuhumata a kan sata, satar ma ta waya, Shureen in rasa abinda xan sata a gidan nan sai waya? Ashe ma gantalalliyar barauniya ce ni, in saci motocin Amadu in gudu mana idan haka ne, Amma sai ka shigo min tsakar dare kace Ina wayar da na sata??" Shuraim ya gyada kai ya juya ya fita dakin. Bai sake maganar wayar ba har gari ya waye, Farida na share ma Kaka dakinta, Heedayah na kwance saman gado tana kallo a laptop, kaka tace "Shiru Shureen bai sake shigowa nemo waya ba gashi har karfe goma ko dai ya hakura ne, ni dubu biyar din ma kasuwa xaku je min ku siyo min kayan ciki in narka uban farfesuna mu yi sati muna ci, kayan cikin dubu biyar ai xai cika wancan kwallan ko?" Farida ta juya tana kallon katon abinda kaka ke nuna masu, kaka tace "Har yawuna ya tsinke maxa gama sharan ku tafi da wnn mara amfanin ku siyo min kayan cikin" Farida tayi kasa da murya tace "Ke dai kar kice masa komai a kan wayar ki ci gaba da boyewa" Kaka tace "Toh da fa, ai ni tasa wayar ma da kyar idan ba chechenia xa ku rakani ba in siyar da 'yar banxa in siyo kan saniya inyi farfesuna" Farida ta fashe da dariya har da kyakyatawa, murya can kasa tace "Xan raka ki wllh, gashi naga shi ma IPhone din ne har ya fi nawa" Kaka tace "Toh ko in shirya yanxu?" Farida tace "Shirya" mikewa kaka tayi xata fiddo da sabon kayanta, Ganin cup da Heedayah ta sha shayi ta kalli Heedayah dake kwance tace "Kai ni dai wnn yarinya ta isheni wllh, kwata kwata ba a morarta, son jikinta har tsoro yake bani ni dai, to Amadu kike jira ya dauke maki kopin nan ko Rakiya??" Heedayah ta sakko saman gadon ta dau cup din ta nufi kofa kaka ta bi ta da harara tace "Toh meye ma amfanin bude idon da Amadu ya kai ki aka yi idan ba asaran kudi ba" Heedayah na fita dakin ta wuce kitchen, Khadijah dake xaune dining ta bi ta da harara, ita dai ko kallonta bata yi ba, ta bude kofar kitchen din ta shiga, ta ajiye cup din a sink kenan ta ga Shuraim tsaye kitchen din yana hada shayi, sunkuyar da kanta tayi xata fita, yace "Zo nan" kin tsayawa tayi ta ruga da gudu ya kamata kafin ta isa kofa, kuka ta sakar masa a tsorace tace "Ni ban yi komai ba wlh, kaka ce tace in kawo cup din kitchen" leka parlor yyi ganin Khadijah ya rufe kofar kitchen din, har wani rawa jikinta yake yi sbda tsoro, ya jinginar da ita da kofa yace "Wa ya shiga dakina ya dau waya?" Ta bude hannu da sauri tace "Nima ban sani ba, bani bace wllh" kalle kallen kitchen din ya fara yi taga ya kallo inda muciya yake, xaro ido tayi ta rungumesa a rikice tace "Wllh Kaka ce ta dauka ta boye a dakinta, a cikin akwatinta ta boye" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yana kallonta duk da ta boye fuskarta jikinsa, a hankali cikin rawar murya tace "Yanxu xa su je su siyar da wayan da Farida"



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


Bude kofar Shuraim yyi bata jira yace ta fita ba ta sakesa ta fice da sauri... Dakin kaka ta koma, kaka tace "Me ya tsayar da ke kitchen din, ko wanke wanke kika yi?" Heedayah ta girgixa mata kai ta xauna gefen gado, gaba daya a tsorace take har lkcn, kaka ta gama saka sabon kayanta na xuwa chechenia tace "Nima dai da neman magana nake, wata Deedaya ce xata yi wanke wanke kamar an tsine mata Allah na tuba" Farida ta gama tattara dakin kaka tace "Ajiye masu tsintsiyar da makwashin sharan a nan bakin kofa mai aiki xa ta kwashe ki shirya mu wuce, daga checheniar dama sai mu biya bakin dogo bbu irin k'an san da basu siyarwa sae mu yi ciniki, ita wannan Deedayar dama ta xauna gida kar taje tana mana lagwai lagwai a kasuwa in shiga uku" Farida tayi yanda Kaka tace sannan ta dau mayafinta ta yafa, duk ta kagu su tafi siyar da wayar Shuraim, dama tuni ta amshi nata ta kai dakin Maminta ta boye, kaka na bude akwatinta ta ciro wayar kenan Shuraim ya bude kofar dakin ya shigo, da sauri ta boye wayar bayan jakan hannunta na rawa ta daga jakar ta mike tsaye, Kai kana ganinta kaga rashin gaskiya karara, cikin rawan baki tana kallonsa tace "Ha'an... yau ma baka tafi Zarian ba? Sannan yaushe xa a fara kwasan sojojin ne" Yace "Ban tafi ba, Ina kwana?" Tace "Lafiya lau, ynxu na shirya nace wannan yarinya Farida ta raka ni gidan Ta sallah kwana biyu ban je ba ita ma bata xo ba, gashi ka shigo ni kuma xan fita" Yace "Ohk, ko in ajiye ki?" Da sauri tace "Aa ba ruwana da ba mutane wahala ga dai adaidaita ta ko ina, kayi tafiyar ka kawai kar in wahal da kai" Farida dai ko kallon Inda yake bata yi ba ta bi gefensa ta fita dakin, Heedayah tuni ta kwanta kan gado ta rufe idonta, kaka tace "Toh mu je xan kulle dakina ne Shureen, kema Deedayah ki fita kije gun Rakiya ki kwanta baxan iya barin dakina a bude ba" Shuraim ya karasa Inda take tace "Ina kuma xaka kana jin ina ce maka xan fita??" Bai saurareta ba ya isa gun akwatin ya duka ya dau wayarsa da yake hangowa bayan akwatin ya fice daga dakin, kaka ta kasa kwakkwaran motsi inda take tsaye, can dai tace "Toh Allah ya isa" sai kuma ta xauna gefen gado ta goge xufan da ya karyo mata a goshi cikin rawar murya tace "Allah dai ya isa" A cikin satin nan Abba ya ba Mami kudi don yi ma Heedayah siyayyar da ya kamata na xuwa boarding, bbu abinda Mami bata siya mata ba har da nata karin, duk dakin kaka ake ajiye kayan gudun fitinarta, ranan Friday karfe uku saura Heedayah na xaune Main parlor tare da Farida dake karatun wani literature dinsu, Heedayah kuma tun safe take ta rubutu a exercise book kamar yanda Mami ta umarce don har sannan writing dinta isn't good duk da tana kokari, Salima da Rabi'ah kuma na can gun dinning, Rabi'ah na mata tsifan uban attachment din kanta, sbda lalacewa kuma a kan dinning, Bude kofar parlon aka yi Sudais ya shigo da sallama, daga Heedayah har Farida suka dinga kallonsa har ya karaso parlon, sanye yake da gezner fari kal, mikewa Heedayah tayi ta sakar masa cool smile tace "Ya Sudais" Ya buda mata manyan idanuwansa a hankali yace "Yes Cutie" karasawa tayi kusa da shi ta rungume sa tace "I missed you" Farida dai kallonsu kawai take, haka Salima da ta juya kanta tana kallon ikon Allah, Sudais ya maida Heedayah gefensa yana kallon Farida yace "Hi" ta d'an yi murmushi tace "Hello, ina yini" yace "Lafiya lau, Farida right" tace "Sure" yace "Ya hutu?" Tace "Alhmdllh" ta gefen ido Heedayah ta bi Shuraim da ya shigo da kallo, direct dakinsa xai wuce ganin Salima da Rabi'ah a dinning ya tsaya yace "Duk gidan nan ki rasa inda xa kiyi tsifa sae wajen cin abinci Salima" Ta kyabe baki sbda bata son fitina ta fara tattara gashin dokin nata, yau dai shima manyan kaya ne jikinsa, Sudais dama sau daya ya kalli direction din Salima shi ma sbda Rabi'ah da ta gaishe sa, ya amsa gaisuwarta, ya na kallon Heedayah yace "Kaka na dakinta?" Heedayah tace "Aa ta je anguwa" Ya d'an bude ido yace "Anguwa Kuma?" Tace "Ehh gidan frnd dinta tace xata tafi, Mami ce ta wuce da ita da safe" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya makaranta?" A hankali tace "I am scared ya sudais" yace "Noo don't be dear, you will like it in there, many of ur mates are there" Tace "Toh baxan kara ganin Mami da Abba ba?" Yace "No xaki dinga dawowa hutu ai, ba ga Farida tana dawowa hutu ba ita ma, tare xa ku je sannan ku dawo tare" a hankali Heedayah tace "Toh" Ya kalli Farida yace "Junaid na nan kuwa?" Farida tace "Yana Abuja, amma xai dawo Saturday" Sudais yace "Yes yace min xai je can, but two days ba mu yi waya ba" Shuraim na fitowa daki Sudais ya mike Heedayah ta xaro ido, murya can kasa tace "Ya Sudais wucewa xaka yi?" Ya mata murmushi yace "Yesss but xan dawo" tace "Me yasa ka daina xuwa?" Yace "Sbda bana nan Cutie" Tace "Toh har in tafi makaranta baxan ganka ba?" Yace "Aa ni xan kai ki makarantar ai" Ya ja dogon hancinta yace "Byee sai na dawo" Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo da sauri yace "Bye Farida" tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ya fita, Heedayah ta koma gun Farida ta xauna. Salima ce xaune dakin yayarta tana sauraron abinda take gaya mata, can dai ta tabe baki tace "Toh wai Yaya ke yanxu meye damuwarki, ita fa matar nan ba sanin kina yi take ba kullum ta fita da safe sai yamma take dawowa, ita kanta wnn makauniyar da ta ja maki komai yanxu makarantar kwana xa a kai ta aka ce to ba shkkn ba, a ina xaki dinga ganinta kina jin takaici kuma??" Mumy ta kunduma mata xagi tace "Dama ke kinsan ciwo na ne, ai damuwata ba taki bace, kin gwammace kiyi ta yawo gari gari..." Mikewa Salima tayi tace "Aa kar ki bata min rai Yaya, taya kike son in tafi in ajiye maki laya a dakinta bayan ba shiga dakin nata na saba yi ba, ba gwara ki ba wa ennan fitsararrun yaran naki ba da basa girmama mutane" Mumy tace "Shkkn ni kuma bani da sirri sai in bari yarana su ji wnn magana, ke ma don kina 'yar uwata ne shi yasa nake neman taimakon ki" Salima tace "Kai gaskiya Yaya Ina ga da kamar wuya..." Mumy tace "Haka xa kiyi min Salima?" Salima ta wani murguda baki ta dauke kai, Mumy tace "Toh shkkn, tashi ki wuce, amma ai kina ma Salaha wanda ya fi haka" Salima tace "To Salaha ai biyana take yi ita" Mumy tace "Toh ni nawa xan baki?" Tana taunar cingam din bakinta tace "Dubu hamsin" Mumy ta mata wani shegen kallo tace "Toh bani da shi, idan xaki amshi dubu ashirin gashi nan yanxu" Salima tace "Toh kawo" tashi Mumy tayi ta dauko mata dubu ashirin din ta bata, sannan Salima ta amshi katon layan ta saka a karamar jakarta ta sa cikin handbag ta mike ta fita, Mumy ta sauke wani ajiya xuciya tace "In sha Allahu komai ya xo karshe sai dai idan ba uban kudina na kashe ba" Da daddare Salima ta fito da uban kayanta da aka wanke ta ba talatu Mai aiki tayi mata guga aka bude kofar parlon, Abba ne ya shigo tare da Junaid, Sosai gabanta ya fadi ganin Junaid, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsarsa, bbu wanda xai kalli junaid sau daya ya kauda kai, he is just too handsome, komai nasa is almost perfect, tayi kasa da kai ta gaida Abba, ya amsa yayi wucewarsa Parlonsa, Bangaren Kaka Junaid ya nufa, Salima ta bi sa da kallo a hankali cikin sanyin murya tace "Welcome Jayy" Banxa yayi mata har ya shiga dakin, Salima ta wuce bangaren Mami ta bude kofar ta shiga da sallama, Mami na xaune parlon tana hada ma Farida da Heedayah kayansu don gobe ne tafiya makarantar, Mami ta daga kai tana kallonta, Salima na murmushi ta gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa tace "Ya kike" Tace "Lafiya lau wllh ya aiki" Mami tace "Alhmdllh" Farida ta gaida Salima, ganin haka Heedayah ma ta gaisheta, Salima ta amsa da fara'a sannan tace "Dama wllh dutsen guga na xo amsa Aunty, na Mamansu Khadijah ya lalace, Shuraim kuma kamar bai nan" Mami tace "Ohk yana can daki dauko mata Farida" Xaunawa Salima tayi saman kujera tana ta kallon Heedayah ganin wani kyau take karawa kamar wata baindiya, ga gashinta da yyi tsayi sosai, Cikin dubara ta dinga saka hannu cikin rigan mamanta da yake hijab ne har kasa jikinta kuma layan na cikin rigan maman, Har ta fiddo idonta na kan TV kamar me kallo, a hankali ta ciro hannunta ta cikin hijab din tana kokarin tura layan cikin kujera aka bude kofa, juyawa tayi da sauri, Junaid ya shigo da sallama, da sauri Heedayah ta mike xaune sai dai bata yi gigin xuwa kusa da shi ba sbda warning din da Mami tayi mata daxu don ta rungume Sudais da ya shigo, Junaid da idonsa ke kanta shi ma ya xauna kujeran dake facing Salima, Mami na lura da kallon da yake ma Heedayah ta dai ci gaba da hada kayan da take yi cikin jaka, Heedayah ta sakar masa murmushi tace "Good evening Yaya" yace "Evening how are you?" Tace "I'm fine" Kallon Mami yyi yace "Mami ina yini" Mami tace "Lafiya lau ya hanya?" yace "Alhmdllh" Salima da ta gama narkewa Inda take xaune tana kallon Junaid cikin tattausan murya tace "Ina yini?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya lau" Farida ta mika mata iron din hannunta tace "Ga shi" amsa tayi tace "Nagode" Kasa tura layan tayi cikin kujeran sai kallon Junaid kuma take, can ta mike hannunta na rike da layan a cikin hijab tace "Toh nagode" Mami tace "No thanks" daga haka ta nufi kofa, Junaid ya bi ta da kallon gefen ido. Salima na shiga dakin Mumy, Mumy ta mike da sauri tana murmushi tace "Kaddai har kin sa" Salima ta wani turo baki tace "Gaskiya baxan iya ba Yaya" Still Mumy tayi tana kallonta tace "Baxa ki iya me ba?" A takaice Salima tace "Yin abinda kika ce in yi mana" Mumy ta dake tace "Saboda me?" tace "Ni fa wllh yaya son Junaid nake, so ba na wasa ba kuma, ni ban jin ma xan iya rayuwa babu shi, ganinsa fa ya sa na kasa saka layan a kujera wllh" Bude baki Mumy tayi tana kallonta can ta mika mata hannu tace "Toh bani" Salima ta fiddo layan ta mika mata, Mumy ta kwace a mugun fusace ta kunduma mata xagi tace "Amma ke dai Allah ya wadaran ki wllh, Junaid din banxa, meye hadin ki da wani shegen junaid da xaki bakanta min sbda shi, toh bani kudi na tun wuri kada in fasa maki kai yanxun nan a dakin nan" Mikewa Salima tayi ta nufi kofa da gudu tace "Har na bada deposit din Human hair weave-on da kudin, bani da shi bani da dalilinsa" daga haka ta fice daga dakin. Kuka ne kawai Mumy bata yi ba ta rasa yanda xata yi kuma ranan aka sa ta saka layan a bangaren Mami, ance mata duk runtsi kada ya wuce yau ganin lkci na wucewa ta mike tana kallon agogo dake nuna karfe goma da wani abu, a jikinta ta saka layan sannan ta dau hijab dinta ta sa, ta bude gun kayanta daga kasa ta dau sinkin sabulu biyu da omo manya biyu ta nemi yar leda me kyau ta xuba su a ciki sannan ta fita xuwa main parlor, cike da karfin hali ta nufi bangaren Mami, ta bude kofar da sallama, Kaka ta tarar a parlon tsaye Mami na kara fiddo mata sauran siyayyan da tayi daxu tana nuna mata, kaka ta juya tana kallon Mumy tace "Waye wnn?" Mumy na murmushin karfin hali tace "Ni ce kaka, Ashe baki yi bacci ba" kaka tace "Inyi baccin lafiya gobe yara xa su wuce makarantar kwana" Mumy tace "Allah sarki..." Xaunawa tayi saman kujera tana kallon Mami tace "Mun yini lafiya?" Mami tace "Alhmdllh, ya aiki" Mumy tace "Mun gode Allah, da safe yara xa su wuce koh?" Kaka tayi saurin cewa "Aa, mu ma dai bamu sani ba bamu da tabbas, kila a daga tafiyar tasu ma" Mumy tace "Allah sarki, toh Allah ya kai mu lafiya, ga wannan dai babu yawa" Kaka tana kallon ledan da take mikowa tace "Meye wnn din" Mumy tace "Aa d'an sabulu ne da omo" kaka tace "Toh ai gashi nan har ya masu yawa naji Rakiya na cewa ma ba duka xa su kai makarantar ba" Mami na kallon Mumy ta mike ta amsa tace "Allah ya amfana Hajiya, an gode" daga haka ta ajiye ledan gefen kayansu Farida, Mumy da har ta cusa layan hannun cikin kujeran taji ya shige can kasa ta mike tana murmushi tace "Aa bbu komai wllh, sai da safe" Mami tace "Allah ya tashe mu lafiya" Mumy ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login